Showing 18001 words to 21000 words out of 30186 words

Chapter 7 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]

cikin tashin hankali, damuwa da fargaba.

Matsowa Catrina tayi cikin sanyi murya tace "My queen karki damu tunda har abin bauta ya tabbatar mana zasu taimake mu to kibar damuwa kuma zanje nakawo miki su har cikin masarautar nan nayi bincike a madubin tsafina nagano suna tareda Princess Mithian" dagowa tayi da sauri "poiá eínai aftí?,(Who is she)?"

"Princess Mithian The Wolf Queen
Tana can cikin kogon ta wanda babu wanda zai iya shiga harsai idan itane taso hakan," cikin girmama wa taci gaba da cewa "kuma dalilin daya sa ban kawo miki su ba saboda lokacin da suka shigo wannan duniyar tamu da ita suka fara haduwa kuma itama akwai wani burinta datakeson cikawa kuma ta hanyar wadannan bakin fuska din ne kadai zata iya cikashi! Ki gafarceni yake gimbiyatah naso ace kece kika fara haduwa dasu ba Princess Mithian ba!" Lady Catrina takarasa maganan tana durkuwa sa akan gwiwoyinta.
Dagowa tayi ta zuba mata ido wanda harsun fara sanja color saboda tsananin damuwan data ke ciki...A hankali tafara magana "inason ahadamin keken doki yanzun amma banson kowa yasan zan fita daga ni saike kawai, as páme sto spílaio tóra, let's go to the cave now"
"your wish is my command" tana gama fadar hakan ta fice daga cikin fadar...

~*

Merapati Hassy Basma suna zaune a makeken bed din dake dakin shikan shi bed din ba kamar irin wanda kuka sani bane ba, Gado ne wanda akayi shi da fatar dabbobi sannan jikinsa anyi masa ado da gashin dawisu wanda hakan yakara masa kyau da tsaruwa sannan idan mutum yahau saboda tsananin laushin gadon mutum ji zaiyi tamkar zai lume a cikin sannan ga wasu irin kwari masu haske wanda sune a matsayin fitila din dakin kuma suna sanja color duk bayan minutes.
Basma tace "nifa ji nike tamkar mafarki nikeyi" Merapati ma murmirshi tayi tace "nima haka, bantaba tunanin zan tsinci kaina a irin wannan wajen ba!thank you" ta karasa maganar idon ta kan Hassy, Da ido tayi mata alamun "for what.?" Kafadarta ta gyada alamun Bansaniba gaba daya dariya suka saka....Hassy tace "amma nifa da akwai abinda ke bani mamaki. Kun lura da cewa tunda mukazo gidan nan bamuga sunyi sallah ba,gashi kuma kamar wani Gunkin mace suke bautawa nikam abin yana damuna!" Suna shirin bata amsa aka bude dakin wannan yarinyar ce wadda har yau basu san sunan taba Zama tayi a kusa dasu tace "hiran me kukeyi ne?"
Basma ta kalleta "kawai muna mamakin yadda komi yake faruwa tamkar a mafarki muke ganin hakan." Smile kawai tayi Hassy "gashi kuma haryanzun bamu san sunanki ba? Bamusan komi akanki ba"
"Princess Mithian haka shine sunana sannan maganar baku san komai akaina ba lokaci nike jira a wannan lokacin zan fada muku ainahin ni wace dakuma taimakon da nikeso a wajenku.." Kallon kallo aka shiga Merapati tace "taimako kuma? wani irin taimakon kike bukata daga garemu? Kalleki fa sam bakiyi kama da mai neman taimako ba you have everything.." Kanta kawai ta gyada saidai kafin tayi magana sukaji wajen yafara motsawa kasar wajen ma tafara girgiza da sauri ta fito daga dakin suma haka.
Wata budurwa ce sanye da kayan sarauta saikuma wata budurwan daban sanye da kayan fata amma sunyi bala'in yi mata kyau...Da Mamaki Mithian take kallon su saboda wannan shine karon farko da wata ta shigo har cikin gidanta batareda izinin taba hakan ya fusata ta take tafara karanta wasu magic words saidai kafin tagama taga wannan budurwan ta nuna su da hannu gaba daya sama sukayi kuma atake komai ya tsaya cak hatta ruwan dake zuba daga wani kogi suma tsayawa sukayi saidai kadan kadan dasukeyin circle nan suka fara zagayesu saikuma duk wani abu mai motsi shima saida yayi sama gashi sun kasa koda motsa hannun su...Kallonta tayi tace "Princess Mithian banzo nan da niyan fada dake ba na zo nan ne saboda mu hada karfi da karfi domin magance damuwar mu...." Su Hassy ta nuna taci gaba da cewa "Kinsani nasani wadannan bakin sukadai ne zasu iya taimakamana duk da cewa munada karfin sihirin da duk fadin nahiyar nan babu koda wanda yakama kafarmu a harkan tsafi dakuma iko saidai kash duk ya tashi a banza tunda bazamu iya magance matsalan muba....Ina rokon Alfarma kiyadda dani mu hada hannu da hannu nikuma nayi rantsuwa da darajar abin bautana bazan ci amananki ba....daga karshe sunana Queen Nimueh...Amma anfi sanina da Drakaina."

Kara nuna su tayi da hannun gaba daya suka zubo a kasan wajen..

Dukan su zama sukayi saidai an rasa mai mgana can Hassy tace "shikenan zamu taimaka muku amma saimunji ainahin abinda ke damunku kafin nan muma akwai sharadin da mukeson kuyi mana kafin mu yadda da bukatun ku."

Drakaina tadago ta kalli Mithian "yanzun ke mene zabin ki? Ina ganin yakamata kubiyoni zuwa masarauta ta domin muyi magana sosai...nasan kinada bukata amma kuma bansan wace iri bace ba kamar yadda kema bakisan tawa ba shi yasa nikeson mu zauna waje daya domin kowa taji bukatar kowa dakuma matsalan da muke ciki" shiru tayi harsun cire rai akan zatayi magana...Mikewa kawai tayi ta dauki wata jakar fata tacema su Merapati suma su dauka bag dinsu.
Hakan yana nufin cewa ta yadda zata bisu kenan.

Bayan sun fito a sannan suka lura cewa keken dokin yayi musu kadan, Princess Mithian batace komai ba, wata karamar tsuntsuwa ta fito da ita daga cikin bag dinta wasu magic words take fada saikuma ta jefa tsuntsuwan sama take ta bace cikin gajimarai ba ayi cikakken minti daya ba su Hassy sukaga sama tafara hada hadari gakuma tsawa ta cika dajin wata katuwar eagle ce ta bayyana, A gaban Princess Mithian...Baki bude suke kallon girman eagle din take mamaki ya gama cika su...Kan ta suka hau ta lula dasu can cikin sararin samaniya ganin hakan yasa itama Drakaina kallon Keken dokin ta nunashi da hannu shima yadawo wata katuwar dragon hawa sukayi suma suka shige cikin gajimaren....

@Drakaina Kingdom


Dukan su suna zaune a babban parlourn bakin....Kowacce da abinda ke ranta....Gyaran murya tayi ta fara cewa "Mithian,Merapati,Hassy,Basma inason kubani hankalinku nan inason ku nutsu kuji labarin dazan baku saboda a cikin sane zaku gane irin matsalan da muke ciki dakuma irin taimakon dazakuyi mana kafin nan da cikar kwana goma." Mikewa tayi wani babban littafi ta dauko wanda saboda ajiya duk yayi kura da yana...Sukam su Merapati basu taba ganin littafi mai girman wannan ba tsab karamin yaro zai iya bacci akai saboda girman littafin.

Anyi Rubuta da manyan harufa

THE CHRONICLES OF NAINAH.

"As I told you before dama wannan novel din zai tabo bangare biyu a ciki zakuji asalin labarin Nainah (Macijiya My first novel) wanda bansamu na karasaba Ma Shaa Allah the time has come let's go to another world...🤣 I hope you will enjoy this story Of *Nainah The Mysterious Girl*"

Shafin farko ta bude zanen wata Kyakykyawar budurwa ce saidai rabinta mutum rabinta kuma maciji, cikeda al'ajabi suke kallon hoton Basma tace "who is she...??"

"Her name was Nainah the most beautiful princess in the world she's a serpent...." Next page ta bude saidai babu komi sai wani rubutu baifi layi uku ba "Some time ago, over a thousand years ago, a baby girl was born the mysterious girl.....Let me tell you the complete story"

~*

Mallam Habu Shine Asalin Sunanshi yana zaune a wani kauye duk karkashin Drakaina suke Talakane Futuk Domin Sana'ar gyaran takalmi yake bashida kowa a garin kuma babu wanda yasan daga ina yazo acikin haka yahadu da suwaiba yarinyar wani babban malami ne a wancan karnin...shine ya nemi aurenta suwaiba macece mai biyayya,kawaici,dakuma hakuri Sundauki tsawon lokaci basu haihuba saida suka kusan shekara goma sha biyu sannan tasamu ciki murna wajen Mal Habu ba a magana yakanyi kokarin ganin yafaranta mata duk da shi din talakane amma yanada zuciyan nema duk wani abu datake bukata yana siyo mata idan yashiga kasuwar Drakaina a wancan lokacin babu kasuwar data kai ta Drakaina saboda garin yanada ni’ima sosai...Saidai wani abu dake bama Suwaiba mamaki tun lokacin data samu ciki take mafarkin macizai amma abinda yafi daure mata Kai acikin macizan akwai wani fari ne tass wanda take gani yana wani irin kuka wani lokacin har magana yake mata amma da zarar safiya tayi saita manta abinda yake cemata Kwanci tashi asarar mai rai yau cikin suwaiba ya isa haihuwa wata ranan asabar cikin dare nakuda takama suwaiba nan MAL Habu ya fito domin kiran ungozoma yana fitowa yaganta a kofar gidansa batareda tunanin komiba yace ta shigo dama kiranta zaije itadai batace komai ba tabishi zuwa cikin gidan da taimakon wannan tsohuwar suwaiba ta haifo santaleliyar yarta nanda nan wannan tsohuwar ta gyara maijego da jaririyarta sannan tagyara wajen tas kamar ba ayi haihuwaba kunna turaren wuta tayi sannan tafice daga gidan batareda sanin kowaba washegari anata zuwa barka har ranan suna ta zagayo akasama yarinya suna NI'IMATULLAH suna cemata NAINAH Mal Habu Yayi komi daidai karfinshi.....




Manage it please!


Thank You For Reading My Story!!

@NM__🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)

Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?

Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger

~*
Episode 12: NAINAH.

Washe garin suna suwaiba tana bawa Nainah Tsotso saitaji kamar wani Abu Ya cije ta a Mamanta sosawa ta farayi sai kuma tafara wani irin amai yin aman take kamar ta amayar da kayan cikinta dasauri mallam yafito yana tambayanta "lafiya menene sameta?" kafin wani lokaci tuni ta fita hayyacinta Mal Habu ne yaruga aguje yakira wani Malamin gargajiya lokacin dasuka iso harta suma awajen da taimakon Mal suka kaita inuwa bayan wasu yan gwaje gwaje Malamin ya tabbatar masa dafin macijine ajikinta kuma irin macijin yanada babban hadari bare kuma ace ya zuba ma mutum dafin sa wata irin faduwar gaba Mal yaji "dafin maciji kuma tayaya dafi ya shiga jikinta alhalin Nainah Take bama nono?" Malamin yace yakawo yarinyan yagani Mallam Habu yaje ya daukotah tana kwance luf da ita tasa hannu a bakinta suna fitowa Malamin yatashi a firgice yana kallonta saikuma ya aro jarumta ya makalawa zuciyanshi mallam Habu ya zauna rike d Nainah sabanin malamin dayake mata kallon MACIJIYA Malamin ya fiddo wani magani daga jakansa yasa a garwashi take wannan macijiyan tafara mutsu~mutsu shi kam Mal Habu gani yayi Nainah tafashe da kuka saiyafara rarrashinta nantake tausayin Malam Habu yakama wannan malamin gargajiya din domin su suna mata kallon mutum shikuma yana mata kallon MACIJIYA Bayan wasu yan mintina yacema Mal Habu "wannan yarinyar ba mutum bace MACIJIYA Ce.!" Wani Kallon Bakada Hankali Malam Habu yayi masa sannan yace "kamar ya banganeba? yarinyantawa zakace MACIJIYA ce akan wani dalili zakacema ya'ta Macijiyace?" yana maganane cikin bacin rai danuna tsantsar damuwa ganin yanayinsa yasa malamin dafa kafadarsa sannan "kayi hakuri Mal Habu Iyakan gaskiyata nake fada maka yarinyan nan MACIJIYA Ce" ran Mal Habu ne yakara baci yace "fitarmin a gida bana son ganinka" fiewa Malamin yayi ransa yana masa kuna saboda yasan wannan macijiyar muguwace kuma saita sasu zubda hawaye..

Jikin Suwaiba yayi sauki wata ranan alhamis suna zaune Mal Habu yake cemata "wannan malamin dayayi miki magani haka yace Nainah macijiya ce bakiga rashin mutumcin danayi masaba dama nasan a garin nan kowa haushina yakeji akan Nainah saboda sunga yarinya kamar balarabiya duk fadin garin babu mai kyau dinta" Suwaiba dan jim tayi sannan tace "Mal yakamata aduba maganan nan domin tun lokacin dana samu cikin yarinyan nan nake mafarkin..." "keeeeee!!!" yadaka mata tsawa.."bantaba sanin bakya sonaba sai yau kema maganar makiyana zaki dauka ko? to bari kiji nafada maki Wallahi duk ranan dakika kwatanta irin wannan maganar to abakin aurenki!" ya fice fuuuu yanata masifa ...wata faduwar gabace ta ziyarci Suwaiba "meyasa Mal yakasa fahimtar ta tabbas akwai kamshin gaskiya a maganan wancan malamin ko itama shaidace yau kwanan Nainah ashirin cif a duniya amma duk dare idan ta farka bata ganinta.."

Al'amarin wannan malamin kuwa bayan yakoma gida yana shiga daki yaga wannan macijiyar ko dar baijiba cikin bacin rai yace "meya kawoki gidana meyasa kika zabi cutar da bayin Allah nan alhalin su da zuciya daya suke zaune dake?Duk abinda sukayi miki basu cancanci haka daga garekiba" wata irin dariya ta kece da ita shi kanshi malamin saida ya firgita..

Saida tayi dariyan mai isarta sannan tayi shiru cikin wata irin murya mai ban tsoro take magana "shin wani tsautsayine yake rinjayar ka meyasa kakeson shiga hurumin daba nakaba? to kasani kasai ajalinka da kudinka" kafin yace wani abu tuni idanunta sun sanja color zuwa bakin kirin babu alamar digon fari a ciki, matsawa tayi kusa dashi hannun ta tasa duka ta kama wuyansa ta dagashi sama wani irin koren hayaki yafara fitowa daga idanunta yana shiga jikin malamin nan take jinin jikinsa yafara komawa jikinta....shure shure yafara anan rai yayi halinsa Batt tabace daga cikin gidan Mal Habu ne zaune yana rike da Nainah suwaiba kuma na cikin kitchen (waje ne aka zagaye kawai) tana dafamusu abincin rana dakyar take aikin saboda Kwana biyun nan duk batajin dadin jikinta haka take fama kamar ance ta kalli can gefenta na hagu saitaga wani irin koren maciji abun mamaki dariya yake mata irinta ta mutane gani tayi yayo kanta aituni tayi waya irin zarananniyar kara tafadi sumammiya Mal...ne yajiyo karar faduwarta cikin sauri yakaraso kitchen din yana maimaita "innalillahi wa inna ilaihir raji'un Suwaiba meyasa meki" ruwa ya debo ya zuba mata firgit ta tashi Sannu yafara mata yana tambayanta meke damunta?Amma sam takasa bude baki tayi magana sai nuna wajen take inda har yanzun macijin yana nan yanayi mata dariya....shikuma Mal yana cemata baiga komiba wasa wasa saida tayi sati daya ba magana kullum cikin firgita da ihu take ankira masu magani dayawa daga sauran kauyukan dake gefen Drakaina amma maganan dayace macijiyace take bibiyarta shikam Mal baya yadda saidai yace so suke suci kudinshi a banza....abu kamar wasa suwaiba takoma abin tausayi saidai a kwantar a tayar ciwo yagama cinye jikinta domin wasu irin kuraje ne suka firfito mata itakam Nainah Babu abinda yadameta sai kara qiba take kuma bata kukan yunwa don tuni an cireta daga tsotso saboda bata iya sha duk kuraje sun fito har akan nonon suwaiba din....

Wata ranan litinin cikin dare jikin suwaiba yayi tsanani domin wani irin yellow amai takeyi kafin cikar sa 'a daya tace ga garinku nan Tabbas mutuwar suwaiba ta tsara duk yan kauyen haka nan Mal Habu Yaji mutuwarta domin suwaiba macece mai tsananin hakuri da biyayya shiyasa Mal Habu yake ganin ba lallai yasamu kamar taba , mutane anata zuwa yimasu gaisuwa kowa da tausayin Nainah yake komawa gida ahaka har akayi sadakan bakwai baban suwaiba yace abashi Nainah tunda acan zatafi samun kulawa amma sam Mal yaki yarda yace abar masa diyarsa zai iya kula da ita dakyar aka lallabashi yabasu ita...Rayuwa kenan yau an wayi gari babu suwaiba kullum Mal yana dakinta yana fadar alherinta wani lokacin kuma yayitah kuka ahaka har akayi arba'in.

Kwanaki suntafi lokaci yaja Al'amura da dama sun faru ciki harda girman Nainah yanzun haka shekaranta bakwai amma har yau Mal bai kara aureba suwaiba tana makale a ranshi yana ganin bazai samu kamarya itaba...

Yau ranace mai cike da al'ajabi a gidan Baban suwaiba...yarane wanda duk sa'annin Nainah ne suna wasan kasa saiga maciji yafito daga rami yaran ne suka fara ihu suna cewa "maciji,maciji" baban suwaiba yafito dauke da katuwar sandarshi yana shirin buga masa yaji muryan Nainah tana cewa "Baffa karka kasheshi gurina yazo aboki nane." cak yatsaya yana mamakin jin kalamnta kafin yayi wani yunkuri tuni taje gaban macijin ta daukeshi ta dorashi kan cinyanta tana yi masa wasa cikin tsananin tashin hankali Baffa ya nufeta amma me dagowata tayi ta zuba mishi ido tanayi masa wani kallo idonta ya sauya color zuwa fari hakan yasashi jan burkin dabai shiryaba cikin wata irin murya mai ban tsoro take cewa "idan har wannan zancen yafita to kamar ka sanar d jana'izar kane" tuni yafara fitsari a wando....Ba shiri yaruga daki a guje ganin yafita a guje yasa yara da manya suka hau gudu suna fadawa dakinsu....nima tuni nafece daga gidan saboda naga tana hararatah Badamar dauko maku rahoto.....

Short Chapter I Know..!!!:)

@NM__🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)

Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?

Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger

Dedicated to Merapati♡❥
~*
Episode 13: The Dream.

Bayan kamar minti ashirin wannan macijin, ya sauka daga jikin Nainah yakoma ramin daya fito. Baban suwaiba kam yana shiga daki yafara goge zufan data ketomasa, can yaji ana kwankwasa kofan fadawa yayi kan gadon shi yana ihu yana cewa "Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan fadaba,bazan fadama kowa ba natuba" muryan matarshi Tani yaji tana cewa "nice fa kabudeman" kara rudewa yayi saboda muryan Nainah yaji tana masa amo a dakin tana kara shaidamasa idan harya sake wani yaji wannan labarin to kamar ya yafad'a ma jama'ar gari mutuwarsa ne. Tani kam takara tsorota saboda ihun da Kaka yake yaki tsayawa can tayi dabaran kiran karamin danshi yashiga ta window yabud'e mata kofan, ganin Kaka tayi cikin bargo sai danna ihu yake yana cewa "ya tuba" itakam abin dariya ma yabata jin dariyanta yashashi bude bargon. Ganin Tani na dariya yasa Kaka mikewa cike da kunya borin kunya yafara Tani dariya taji ta ce "yaje yayi wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login