Showing 3001 words to 6000 words out of 30186 words

Chapter 2 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]

kus kus ganinsu tare saboda kowa yasani kullum ita kadai take rayuwanta.

"Oh my goshhhh I forgottt
What's your name?"

"Hassana M Muhd" tace a takaice, murmishi tayi tace "nice name nikuma sunana Fatima Salis Muhammad...you can call me Basma,,,"

Saurin kallonta Hassy tayi aranta tace ya akayi nakasa ganeta tun farko?

Bayan sun shiga class gani tayi ta tafi can baya ta zauna hakan yasa Hassy cewa tadawo sit din gaba badan taso ba tadawo,saidai kafin ta zauna taji an fisge ta ta baya nan fa class suka hau dariya da shewa juyowa Hassy tayi ganin wata student daban kallo daya zakayi mata kagane cewa batajin magana wani banzan kallo tayi mata tace "who the hell are you? meyasa zakisa tadawo gaban sit? Kaf class din nan kowa yasani karshen bench nan ne wajen zamanta, saboda da can wajen ta dace" takarasa maganar cikeda da izza.

Hassy kam da mamaki take kallonta wannan wace irin school ce?
Hannu tasa da niyan jan Basma saidai kafin takarasa taji an rike hannun... Juyowa tayi taga Hassy ce ta rike mata hannun tace "karki kuskura ki tabata kuma tanada yancin zama a duk inda taso,, don haka baki isa kibata umarni ba." Janye hannunta tayi tafara clapping hands dinta tana cewa "wow..wow ina kuke yan group?
Kuzo kuga abin mamaki yau acikin class din nan ansamu mai tankawa Ruky."
nan fa gang dinta suka matso ciki harda maza kallonsu tayi "naga alamun tanason shiga abinda babu ruwanta don haka kuyi mata service" tana gama fadar hakan tasamu desk ta zauna.

ganin hakan yasa Basma mikewa tashiga gabansu tace "please don’t touch her, saboda batasan komai ba rigimata iyaka..." kafin ta karasa akayi wurgi da ita gefe guda dasauri Hassy taje ta dagota tace "are you hurt?" Kanta kawai ta girgiza
Hannu taji a kafadarta cikin bacin rai ta mike tana juyowa ta zabga masa mari sannan tasa kafanta tayi masa wani irin bugu a ciki nan ya baje a kasa..
Ganin hakan ya fusata sauran gangs din sukayi kanta saidai kowa naushi daya take masa saidai kaga sun zube a kasa.
Nan fa class din suka hau ihu da tafi suna jinjina mata ko babu komai yau ansamu mai tankawa gang's dinsu Ruky saboda sam basajin magana ga shegen tsokana saboda suna ganin sunada karfi kuma they are popular and rich.
Bayan antashi daga class suna tafiya Basma takalli Hassy tace "thank you,thanks for everything you..." saurin dakatar da ita tayi tace "kibar godemin since we are friends we have to help each other,And i just did that." murmishi tayi tace "yes you’re right duk da haka nagode."

Tundaga ranan suka zama best friends,duk inda kaga daya to zakaga daya yanzun Basma ta sake babu mai takura mata kuma suma sun zama popular a school din.

Bangaren su Ruky kuwa yanzun andaina tsoronsu suma duk jikinsu yayi sanyi so suke su kulla kawance dasu Hassy amma basuga fuskaba.

Sosai suke shige musu yanzun ma indai sunje Hall saidai kaga su Ruky sundawo table dinsu duk dan su samu shiga.

Gaba daya student's sun shiga busy saboda akwai wani shiri dasuke son gabatarwa a karshen term din kuma suna son abasu izinin zuwa wajen school saboda duk cikin school din babu inda yadace ayi shirin... Su Ruky ne kan gaba wajen zaben yan wasa mutane 50 sukesu amma sai Ruky tace abawa Hassy ta zaba itakuma tace batasan suwaye suka dace suyi participating ba kawai su zaba da kansu list din Ruky tabata tace "Dan Allah ko mutum daya ne tazaba" karba tayi tafara bin list din da kallo Idanunta ne yatsaya akan sunan Mega Aura Pangesti aranta tace Mss Arrogant kasa taci gaba dayi saikuma tadawo kan sunan Mega tayi tick mika mata tayi ganin sunan datayi ticking Ruky tace "Kai Merapati kika zaba? To Allah yasa taje don batason zuwa kowani excursion."

Tabe baki Hassy tayi aranta tace "dama ta ina zataje tana fama da girman kai?"

Bayan antashi daga evening prep a hanyarsu takoma hostel Hassy,Basma,Zaynab,Ruky tafiya suke suna labarin malamin maths dinsu dakuma yanda suke mamakin basa ganewa sam jisukayi ance "Ruky!" tsayawa sukayi dukansu suka waiwaya Merapati ce.

Cikin nutsuwa take takowa harta iso kusa dasu daya bayan daya take kallonsu sannan ta tsaida idonta akan Ruky tace "meyasa kika sa sunana a yan zuwa excursion?kin manta cewa babu abinda na tsana kamar zuwa excursion how dare you put my name on the list?" Ruky kallon kinma rainawa kanki wayau tayi mata sannan tace "oops sorry mss bani nasa ba Hassy ce tasaka" kara kallonsu tayi tace "a cikin ku wacece Hassy?"

kut jimin mata saikace wata boss Hassy tace aranta.

"erm nice amma tunda bakiso za a cireki tunda babu lalle babu dole..."

Shiru tayi tana kallonsu saikuma tace "kawai kubarshi tunda kunsa amma a kiyaye gaba, bakowani abu ne nike shiga harkansa ba."
Tana gama fadar hakan ta juya tabarsu baki bude tsaki Basma tayi tace "bantaba ganin yar rainin hankali kamar wannan yarinyar ba, wasu ma nema suke asa sunan su amma basu samu ba sai ita dontaga ansa nata" mtsw takara jan tsaki. Hostel suka tafi zuciyoyin su cikeda mamakin Merapati

Kamar yadda suka tsara hakan ne yakasance domin kuwa duk wasu shirye shirye sungama kuma kwana biyar zasuyi a inda zasuje din duk wanda za ayi tafiyan dasu kowa ta hada kayanta a suitcase saikuma school bag inda suka zuba su toothpaste and toothbrush,perfume,lotion,torchlight,dadai sauran abubuwan bukata.

Principal Office sukaje anan takara ja musu kunne akan su kula saboda inda zasuje wajen babu mutane cikin daji ne sosai tsawon shekaru babu wanda ya zauna a wajen.

Mota suka shiga sauran students sukayi musu fatan nasara....Daga nan driver yaja suka tafi..


Now The Story Begins.


@NM__🦋♥️
[14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)

Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?

Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger

~*
Episode 4: Excursion.

A kalla sunyi tafiyan 8hrs sannan suka isa ainahin inda za suje din, kowa a gajiye yake sallah ce kadai take tsaida su.

Bayan kowa ya sauka da kayan sa nan fa mazan suka fara hada musu tent su kuma matan su ka fara yi musu girki kafin magrib sun gama komai kuma ko wani tent daya mutum uku ne nan fa akabawa Hassy Merapati da Basma tent daya, suitcases dinsu suka shigar ciki, masu wanka sukayi sannan sukayi sallah a jam'i.

Nan fa suka fito wajen tent din gaba dayansu, dama tundazun mazan sun samo ice, decorating din wajen sukayi da wasu bulb sannan suka kunna icen a tsakiya bayan sun zagaye icen da kananun kujeru sosai wajen zai birge mutum, gaba dayansu kowanne ya samu waje yazauna.

Kallon Hassy Ruky tayi tace "yakamata afara bawa kowa abinci tunda yanzun dare yayi babu abinda zamuyi gashi wajen bamu san yanayin saba gara kowa yaci abinci yaje ya kwanta." mikewa sukayi suna zuba abincin a plate wasu kuma suna mikawa na zaune tareda soft drinks.
Harsaida kowa yasamu sannan suma suka zuba nasu.

Bayan angama cin abincin Ruky ta kallesu taje "kowa yaje ya kwanta."
Daya daga cikin students din mai suna Kabir yace "gaskiya bamajin bacci kuma a ganina bai kamata mu kwanta yanzun ba Let's make a lot of unforgettable memories,let's have fun guy's....."
shewa suka fara suna cewa mun yadda da hakan,
Kallonsu Kabir yayi yace a "cikinku wane kokuma wace ta iya waka?"
Gaba daya kallon Basma sukeyi dagawo tayi a hankali tace "What?!" kamar hadin baki dukansu suka fara cewa "Basma!Basma!”
Kallon Hassy tayi ita kuma tayi mata alama akan tayi wakan.
Mikewa tayi tace shikenan zanyi muku...cikin melodious voice din ta tafara...

_Someday this could be,this could be ordinary._
_Someday could we be something extraordinary?_
_You and me side by side yeah yeah out in the broad daylight if they laugh we'll say we're gonna be someday someday someday._

_So let them talk if they wanna, let them talk if they're gonna,we're gonna do what we wanna let them talk let them talk if they wanna they wanna._

_Someday this could be this could be ordinary, Someday could we be something extraordinary?_

_You and me side by side yeah yeah out in the broad daylight if they laugh we'll say we're gonna be someday we're gonna be._

_Someday someday someday we're gonna be someday we're gonna be someday.._

mikewa sukayi suna yimata tafi da karfi nan fa duka suka shiga filin kowa yana wakar datazo bakinsa kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin tsantsar farin ciki.
basu kwanta ba sai wajen 12:30am.


Bayan sun shiga tent dinsu Hassy tace "Gaskiya Basma kin iya waka sosai itakuma wannan wakar awani cartoon akayi ta?"

murmishi tayi tace "no ba a a cartoon akayi ba sunan film din Zombies"

Smile itama tayi tace "amma wakan tayi dadi sosai" kallonta tayi tace "ahaka ma ba duka nayi ba..its one of my favorite songs"

Daidai lokacin Merapati ta shigo kallo daya tayi musu ta dauke kanta "anata ganin girman kai ne dasu"

*LMAO 1-1 kenan.*

Washe gari bayan sun kamalla abinda zasuyi nan suka shirya domin zuwa cikin dajin su duba inda yafi dacewa suyi shirin.

Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka ga wani tsohon gida kallo daya zakayi masa kagane cewa andade ba a shiga ba, nan wasu sukace a shiga a duba wasu kuma sukace aa kar a shiga saboda Principal tace su kula sosai ganin hakan yasa Merapati cewa "duk wanda yakeson shiga ya daga hannunsa " Hassy ce first aganinta wannan itane damarta taganin abun Al'ajabi. Mutum 25 ne suka daga hannu. Saikuma wanda basu so mutum 24 kallon Merapati Hassy tayi tace "saura ke wanne kika zaba?"

Kamar bazatayi magana ba saikuma tace "nima na zabi kar... Saikuma tace Nazabi a shiga din, amma da zarar munga wani abu wanda baidace ba zamu fito sannan kuma gaba dayan mu awaje daya zamu tsaya ma'ana babu wanda zai shiga wani waje batareda damu ba idan kunyadda da wannan to idan kuma baku yadda ba bazamu shiga ba and that’s final" nan dukansu sukace sunyadda.

Nan fa suka nufi cikin gidan bayan Merapati ta ciro camera dinta nan tafara daukan pics.

Cikin gidan yanada duhu sosai ga yana duk ta rufe ko ina hakan yasa suka fito da torch suna haskawa, bayan kamar minti 5 basuga komai ba daidai lokacin Basma ta kwalla kara ganin skull💀 (kwarangal😂), Ruky tace "menene mekikagani" ajiyan zuciya tayi tace "wallahi na tsorata ashe skull ne."

Bangaren Hassy kuwa zamewa tayi tabi wata hanya daban nan taci gaba da daukan pictures motsi taji a bangarenta cikin dakewa takarasa wajen haskawa tayi da torch nan taga wani abu bakin kirin,hannunta takai ta yaye yanar data rufe abin cikin mamaki tace "laptop bag??"
cikin sauri ta dauka bayanta goge sannan ta rataya a hannunta,Sannan takama hanyar fitowa.

Bayan sun fito daga gidan nan fa Basma ta lura Hassy bata taredasu cewa tayi "wait guys banga Hassy ba?"

Merapati tace I don’t get it kamar ya baki gantaba?" Dafe kai tayi taci gaba da cewa "Aishh this girl bataji wato duk irin warning din danayi saida ta karya doka,"
Kafin Basma tabata answer gani sukayi Hassy ta fito daga gidan cikeda tuhuma duk suke kallonta...
Smile tayi tace "why are you all looking at me like that...?"
basu ce komai ba hannun Basma takama suka ci gaba da tafiya.

Bayan sun isa inda suka kafa tents kowa ya shige saboda tsakar rana ce kowa ya debo gajiya...Kallon Basma tayi tace "zokiga abinda nasamo acan" sannan ta bude system din,

Basma tace "amma kina ganin tanayi kuwa? Saboda wajen fa kamar anfi 30yrs babu wanda ya zauna gashi duk yayi yana.." Smile tayi tace "bari dai mugani Allah yasa takawo."
Kunnawa tayi amma sam taki kawo wa cigaba tayi da danna switch din amma yaki kawowa tuni Basma tafara mata dariya tana cewa "aidama nina sani bazata kawo..." Saidai kafin takarasa gani tayi laptop din takawo..amma babu chargy sosai
nan tafara bincike idanunta ne yasauka akan wata folder shiga tayi short note tagani cikin nutsuwa tafara karantawa a fili
"Sunana Doctor Jalal Mahmud Muhammad inason duk wanda yaga wannan sakon nawa yayi gaggawar barin wajen saboda wajene mai cikeda hadari."

Dariya Basma tayi tace "kujimin mutum kawai yanason bama mutane tsoro shiyasa zaice hakan,"

Hassy tace nikuma a ganina dagaske yake saboda a inda nasamu wannan system din wajen baki gani ba abin tsoro sannan gawasu irin bakaken abubuwa kamar mutane amma kuma sun kone da wuta...Dole nakoma wajen nan saina gano ainahin abinda yafaru.."

Merapati ta kalleta tace "nima zan iya yadda da abinda yace saboda kalli nan kigani mika mata camera din tayi nan suka fara kallon pictures din data dauka indai mutum ya nutsu zaigane cewa tabbas mutane ne amma kuma sun sanja halitta, wani picture ta nuna musu tace kunga wannan shine gidan da mukaje amma kalli da kyau zakiga wata mata sanye da fararen kaya daga tsakiya gefenta kuma zakuga wani abu shi ba bat ba kuma shiba tsuntsu ba, duk yanda akayi akwai wasu halittun anan wataqilan ajlanu wata qilan kuma vampire's.."
Hassy tace "bana tunanin vampires ne saidai aljanu din amma koma menene anjima zan koma saina gano mene acikin gidan can."

kallonsu Merapati tayi tace "amma karku fadama kowa bnson nasa kowa a matsala,domin ni kadai zanje" Basma tace "kinsan kuwa hakan bazai yiwu ba bazan taba bari kije ke kadai ba komine saidai ya same mu atare."

Nan fa suka fara sa'insa Hassy tana cewa bazata bita ba ita kuma tana cewa saita bita.

"Both of you shut up!" Merapati tace da karfi da mamaki suke kallonta taci gaba da cewa "nima kuma bazan taba barinku kuje ku kadai ba" Basma tace "kekuma a mtsayinki nawa?"

Wani banzan kallo tayi mata tace "A matsayina na wadda kuke sharing tent tare.."


_1:00am_

Bakajin motsin komai sai kukan tsuntsaye dama already sungama hada kayansu cikin sanda suke tafiya harsuka fice daga ainahin inda suke.
Direct gidan suka nufa saidai ga mamakinsu yanzun basuga gidan ba duk iyakan kokarin su nagano gidan amma sama ko kasa basu gani ba.harsun juya sun fara tafiya Merapati tace "ku tsaya,ku tsaya bakuji motsi ba?"
Hassy tace "motsi kuma a ina?"
"Shhh" tace sannan taci gaba da tafiya wasu flowers tagani kuma ta tabbatar daga nan motsin yake fitowa cikin karfin hali ta bude flowers din ajiyan zuciya tayi ganin cewa water fall ne, daidai lokacin su Basma suka karaso wajen, tunda suke basu taba ganin water fall mai kyau din wannan ba, ruwane mai balain hasken blue sannan a samanshi ga fure nan kala kala,ga wani kamshi na musamman yana fitowa daga cikin ruwan.
Basma tace "kai gaskiya ruwan nan ya birgeni kujirani nayi wanka" tana gama fadar hakan ta cire kayanta underwear kadai tabari ta shiga cikin ruwan. Ganin haka yasa itama Merapati shiga cikin ruwan...dariya sukeyi dukansu,suna watsawa jikinsu ruwan.
Hassy ma ruwan ne yabata sha'awa itama shiga tayi saidai ita can gefe daban taje...Bayan 5mns Hassy tafara ganin wani haske acan gabanta hasken yanata circling shi kadai juyowa tayi tace "Basma Merapati zoku gani," matsawa sukayi suna kallon wajen, nan take gaba daya ruwan yafara motsawa da karfi ganin hakan yasa su kokarin fita amma sam sun kasa nan take wani irin hadari ya hado gawata irin tsawa da walkiya da akeyi gaba daya ruwan ne yahau girgiza manya manyan igiyar ruwa suka fara fitowa...
Wata irin tsawa akayi cikin seconds komi yakoma daidai tamkar babu abinda yafaru...

I Hope You Guys Enjoyed This Story!!!


@NM__🦋♥️
[14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)

Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?

Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger

~*
Episode 5: Something Happened.

Free Page

~*

Merapati ce tafara bude idonta a hankali harta bude shi gaba daya, da sauri ta mike daidai lokacin Basma ma ta bude nata idon nan suka hau dube duben Hassy can gefe suka hangota da sauri suka ka rasa wajenta Basma ce tafara girgizata bude idonta ta yi saidai dishi dishi take gani hakan ya sa takara rufe idon, girgiza ta takeyi tana cewa "please wake up! kitashi Don Allah..." Sai a lokacin Merapati ta lura da ciwon dake hannun Hassy kallon Basma tayi tace "Oh my God she's bleeding" mikewa tayi tafara duba bags dinsu can gefe ta hango su da sauri takarasa ta dauko karamar first aid kit.

_It's important to have a well-stocked first aid kit a duk lokacin daza kuyi tafiya mai nisa kokuma a gida ma so you can deal with minor accidents and injuries._

Cikin karamin lokaci ta gama treating din hannun Hassy.

_After 1hrs_
Dukansu suna zaune kowa da abinda ke ranta Basma tace "Merapati kina ganin zata tashi kuwa?"
Merapati tace "Basma karki damu zata tashi saboda ciwon dataji bashida yawa kawai ta zubar da jini ne sosai shiyasa"
Bude idon ta tafarayi fes ta sauke su akan su Basma da Merapati matsowa suka farayi suna yimata sannu dukansu tambayanta sukeyi yaya jikin nata yakuma takeji ajikinta?
murmishi tayi tace "nagode sosai da kulawanku a gareni kuma yanzun banjin komai"
Hamdala sukayi atare.
Kallon wajen tafara cikin tsantsar mamaki tace "a ina muke? menene kuma yafaru damu?"
Sai a lokacin suma suka lura da wajen da inda suke sam hankalinsu baikai kai ba saboda duk suna cikin damuwa ganin Hassy taji ciwo...Zagayayyen gini ne wanda saboda tsananin tsawon katangar mutum baya iya ganin karshenta sannan ga wasu irin manyan duwatsu a jiki....Basma tace "Ikon Allah nidai nasan lokacin da muke zagaya dajin nan babu wannan katangar kuma ni abinda yafi bani mamaki nakasa tuna abinda yafaru"
Merapati tace "bana tunanin hakan saboda kinsan dajin yanada girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login