Showing 6001 words to 9000 words out of 30186 words
Chapter 3 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]
ba lalle hankalinmu yakai kaiba"
Kallonsu tayi taci gaba da cewa "yanzun dai abinda zamuyi mu nemi hanyan fita daga nan nasan hankalin sauran students zai tashi idan basu ganmu ba gobe"
Wayanta taciro saidai emergency yasa mata kwata kwata babu network gaba daya ya dauke tsaki tayi ta maida wayan.
Basma tace "amma Hassy kizauna saboda ciwon hannun ki"
Kanta kawai ta gyada saboda tanaji a jikinta tabbas wani abu yafaru dasu amma batasan mene ba.
Nan fa suka fara bin katangar suna haskawa da torch saidai basuga alamun akwai kofa ba a bala'in gajiye suka dawo inda Hassy take a zaune kallonsu tayi tace "kun samu hanyan fita daga nan ne? "
Atare suka girgiza kai.
Tace "ina ganin kawai mu kwanta idan yaso gobe da safe saimu duba da kyau nasan bazamu rasa hanyan fita daga nan din ba"
Blanket suka shimfida basuyi cikakken 2mns da kwanciya ba bacci yadaukesu, saboda ba karamin gajiya sukayi ba.
Washe gari bayan sun yi sallah zama sukayi kowacce akwai abinda take tunani kallon su Hassy tayi tace "zaman nan fa bazai yimana ba gara mutashi mu nemi hanyar fita daga nan wajen"
Mikewa sukayi suna duba ko ina. Tsayawa Merapati tayi ta zubawa rubutun jikin wani dutse ido, kwala musu kira tayi tace su zo sugani.
Hassy ce takaraso wajen saboda ita Basma tana can daya bangaren bata karaso ba.
Zubama rubutun ido sukayi amma sam basu gane komai ba saboda wasu irin kalmomine sam mutum bazai iya sanin me aka rubuta ba, daidai lokacin Basma ta karaso wajen bin rubutun tayi da kallo a fili tafara karantawa kamar haka:
_Βόρειος_
_Νότος_
_Ανατολή_
_δυτικά_
Saikuma daga can kasa akwai wani rubutun kamar haka "_Αυτή είναι η διέξοδος"_
kallonta suke saboda ko kalma daya basu gane ba a cikin abinda data fada ba.
Merapati tace "mene ma'anar wannan rubutun? Kuma kina ganin zai taimake mu mufita daga nan"
Basma tace "wannan rubutun da greek akayi shi bari dai nayi muku bayanin rubutun"
_Βόρειος(Voreios) Means North_
_Νότος(Notos) Means South_
_Ανατολή(Anatoli) Means East_
_δυτικά(Dytikq) Means West_
Saikuma rubutun karshe
"_Αυτή είναι η διέξοδος (Afti einai I diexodos) Means This is the way out._"
Cigaba tayi da cewa"anawa ganin wannan rubutun yana nufin tsakanin Gabas,yamma kudu,arewa tabbas akwai hanyar dazamubi domin fita daga nan wajen,saidai takamaimai bamusan wace hanya bace ba Yanzun dai mene shawaran ku? Wace kofa kuke ganin zamu bi?"
Hassy tace "mubi yamma"
Merapati tace "aa ina ganin mubi arewa"
Basma tace "nikuma anawa ganin kofan gabas yakamata mubi,
Amma fa sai mun duba inda key din yake wanda zamu bude kofan dashi."
Kallonta sukayi suka ce "wani irin key kuma?" Smile tayi tace "bawai normal key dakuka sani ba ne ba zakuga wani rami a jikin kowace kofa to idan muka danna shi kofan zata bude"
Merapati tace "tayaya akayi duk kika san wannan?"
Basma tace "saboda ina karanta littafan tarihi so I know lots of things....let’s go girls bamuda lokaci."
Nan dai suka tattara kayansu sannan suka duba daidai inda gabas take bin jikin katangar suke suna taba ko ina ajikin katangar harsun cire rai da samun kofar nan hannun Basma ya taba wani karamin rami cikin farin ciki tace "ina tunanin mun samu mabudin" dannawa tayi nan da nan wajen yafara girgiza kamar za a yi girgizan kasa.
A hankali bangon yake budewa harya bude gaba daya take wata karamar kofa ta bayyana acikinta akwai wata matattakala mai tsayin gaske wanda mutum duk iya hangensa bazai iya ganin karshen stairs din ba.
Cikin rashin tsoro suka shiga cikin kofar suna gama shiga kofar takoma ta kulle kanta. torch suka kunna saboda duhun wajen.. babu komi a ciki sai wasu irin zane kala kala kwata kwata na mutane da gidaje da kuma flowers kala kala.
Merapati ce ta taka wani abu tsayawa tayi tace "Hassy Basma ku tsay..." kafin takarasa gaba daya wajen ya rufta fadawa sukayi dukansu banda ihu babu abinda sukeyi..wajen yanada balain zurfi gakuma wata irin iska mai karfi tana yawo dasu dalilin hakan yasa dukansu sumewa...
Lokacin dasuka bude idon su a cikin dajin dasuka sauka suka gansu sosai suke farin ciki ganin sun dawo ainahin inda suke..Hassy ta dauko wayanta ta duba saidai itama babu network haka ya nuna mata kallon Merapati tayi tace "dan dubamin wayanki da network kuwa inason nakira Ruky naji ya ake ciki"
Dubawa tayi tace "wallahi kinga tundazun ya dauke kuma har yanzun baidawo ba"
Cigaba sukayi da tafiya har suka isa inda tents dinsu yake, gani sukayi sauran students din sunayi musu wani kallo kamar yau suka fara ganin su gashi kuma duk sun hada kayansu zasu tafi,driver din ne ya kallesu yace "Idan tafiya zakuyi ku shigo mutafi daku,"
Basma ce ta matsa kusa dashi tace "amma naga kwana biyar zamuyi meyasa za'a tafi yau?"
kallon marar hankali yayi mata saboda tsabar takaici baice mata komai ba aranshi kuwa cewa yake "lalle yarinyar nan tacika yar rainin wayau wato duk kwanakin dasukayi bata gani ba shine yanzun zatazo dawani salon rainin hankali"
Ganin yaki kulata yasata komawa kusa dasu Hassy ta tsaya.
Nan fa duk suka cire tents din dasuka kafa sannan suka shiga mota..
Su dai su Merapati mamaki sukeyi ganin duk student's basa kulasu hatta Ruky ma nunawa tayi bata san suba sudai abin ya daure musu kai amma sunbar abin a zuciyansu idan sunkoma zasu tambaye su kowani abu sukayi wanda basa son kulasu?
Daidai lokacin Idanun Hassy yasauka akan sunan school din
*YAMAN SCIENCE ACADEMY*
Tabo su Merapati tayi tace "Ikon Allah daga tafiyan mu har an sanja sunan school? wannan abu da mamaki yake gaskiya." Dukansu kowa mamaki takeyi..Bayan kowa yasauka suka nufi hostel saidai gaba daya sun tsargu saboda irin kallon da students ke musu wasu ma har nuna su sukeyi ganin hakan yasa jikinsu yin kara sanyi.
Kebewa sukayi Basma tace "nifa nagama tsarguwa kodai munyi laifine?"
Hassy tace "wallahi nima abinda nike tunani kenan meyasa suke kallon mu kamar wasu baki?"
Merapati tace "Hmm kubari kawai nikuma abinda yafi bani mamaki meyasa basa kulamu meyasa suke mana kallon tuhuma?"
Manage it please,been busy!!
Thanks For Reading My Story!!!
Mwah mwa sending warm hugs and kisses❤️
@NM__🦋♥️
[14/01, 1:57 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #bff#dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 6: Something Happened 2.
Gabadaya mutane kallon baki sukeyi musu, tun bayan da suka koma school. Hassy ce ta je kwana din su Zaynab waje ta nema ta zauna a kusa da gadon.
Kura mata ido Zaynab tayi tana mata kallon sabon halitta tamkar wacce bata taba ganinta ba, with full of surprise Hassy starts talking to her, Amma me shiru tayi mata bata ce da ita komai ba.
Kallonta sosai ta yi tana ganin yanda mood dinta ya sanja tace "What's wrong with you? What did I do to you? Why are you treating me like a stranger now? If I wrong you unknowingly just tell me so that I will apologize to you.."
"Nop ban sanki ba ta yaya za a yi kuma ki mun laifi? All I know shine bana kula wanda ban sani ba that's all"
Ba karamin mamaki Hassy tayi ba da kyar ta iya budan bakinta tace "kaman yaya baki sanni ba after long that we are together?".
"Excuse me young lady I swear I don’t know you..." Zaynab ta fada bayan ta tashi daga wajen, mamaki ne yakara kama Hassy, nan ta shiga tambayar kanta "me yasa tun lokacin da muka dawo daga excursion kowa yake mana kallon strangers? Ko dai wani abu ya same mu a can ne?."
Tsayawa tayi takara kallon kanta ajikin mirror saidai sam bataga wata alama ba yanda take haka dai take haryanzun. Da sauri tabi bayan Zaynab don ita duk a tunaninta wasa takeyi mata.
Jiki a sanyaye ta dafa kafadarta tace "Don Allah ki daina idan ma wasa kike yi zaki sani a rudani, kinsan dai banason irin wannan wasan"
Hummmm ajiyar zuciya ta sauke tace "seriously ni ban san ki ba i swear tun da nake ban taba ganinki ba ma,kinga kuwa babu ta yanda za a yi ka san wanda baka taba gani ba after that kowa ya sani duniya ta baci ba ta yadda za a yi kizo kina mun magana haka kawai daga mun taimaka muku bayan mun ganku a cikin daji sai ace kin biyo ni kina cewa kin sanni Please! Leave me alone I don’t want any trouble” hannunta ta cire daga kafadarta ta bar wajen.
Mutuwar tsaye Hassy tayi baki bude take binta da kallo gaba daya maganganun Zaynab sune ke mata yawo a kunne, babu abun da ya yi mata ciwo kaman cewa da tayi bata santa ba, wai yau har ita ce Zaynab zata ce bata sani ba? Rayuwa kenan! Jiki a sanyaye takoma dakin.
Washegari ta kama Monday, da wuri suka shirya zuwa class, abun dayake kara basu mamaki shine yanda kowa yake kallonsu, sai kace an ga sabbin halitta, gaba dayansu tsarguwa sukayi,nan fa suka fara bin jikinsu da kallo ko akwai wani abun da ya sa ake kallonsu, amma basu ga komai ba.
A haka suka shiga class desk din da suke zama suka zauna, shiru class din ya yi, mutane na ta binsu da kallo, su dai shiru suka yi ba su ce komai ba.
Hassy gefenta ta kalla saidai bataga Ruky ba, bin yan class din take kallo amma babu ko daya daga cikin gang's din su Ruky aranta tace "to ina sukaje?"
Bangaren Merapati kuma ganin su Ruky tayi a class din su wanda hakan ba karamin mamaki yabata ba tunda tasan cewa ba class din su daya ba...
Monitorn class din ce ta tashi ta tafi office din principal ta sanar da ita ga sabbin fuska sun shigo class dinsu ba tare da sun san ko su waye ba, anan ta tarar da headgirl din itama tana shigar da report akan bakin fuska din dasuka shigo school din nasu, aikawa ta yi a kira su, jiki a sanyaye suka taho office dinta.
Hassy ce a gaba sai Merapati a tsakiya sai Basma a baya. A can gefe suka takure a waje daya.
Tambayarsu ta shiga yi "ku su waye? Daga ina kuke? Ya za a yi ku shigo mun makaranta ba tare da permission ba?".
Hassy ta kalli Basma, Basma ta kalli Merapati, ba karamin mamaki maganar pc ta basu ba, Bama wannna ba gaba-daya principal din da suka sani ba ita bace wannan.
"Mummy ta yaya za a yi kice mu ba daliban ki ba ne? Ki duba cikin list dinkin zaki ga sunanmu, har da mu aka je excursion din nan kuma tun da muka dawo sai mukaga ana mana kallon baki gaba daya abun ya daure mana kai". Merapati ta fada tana mai goge fuskarta da tissue.
List students din aka dauko aka fara dubawa amma kuma abun mamaki babu sunansu gaba daya a ciki, ajiye wa tayi ta dauko na class dinsu nan ma babu sunan su a ciki, sawa tayi aka kira wasu daga cikin teacher's din nan fah suka shige bincike a system tun farkon fara bude school din nan ma abun mamaki babu ko alamun sunansu....
Tashi Principal din tayi cikin bacin rai tace "ku tashi ku fita mun a makaranta, babu ta yanda za a yi ku shigo mun makaranta har ku zauna ba tare da an dauke ku ba, kunbatamin lokaci a banza" security takira taci gaba da cewa "a tabbata sun kwashe duka kayan dasuka shigo dasu cikin school din sannan a fitar dasu daga school din cikin gaggawa saboda ba asan wani irin mutane bane ba su."
Tana cikin surfa masifa taji an yi knocking din kofar office din, umarni ta bayar a shiga, kawarta ce wacce take Principal a wani private day school, tana shigowa idanuwanta suka sauka akan na Merapati, gabanta ne ya buga, mamaki ya kamata a take fuskar ya dawo mata tabbas ta san wannan yarinyar amma kuma ta manta a inda tasanta sosai take mata kallon sanni wanda Basma ta lura da hakan.
"Ku fice mun daga office" jiki a sanyaye suka fita, bayan fitarsu ne kawar Principal din tace "nasan wannan yarinyar ta baya fa, amma kuma na manta a inda nasanta kawai abu daya nasani nasanta..."
Shiru kawai tayi mata suka shiga hiran abun da ya kawo ta.
Gaba daya rasa abun yi suka yi bayan sun fito, ga shi yamma tayi ga yunwa ta addabesu ko breakfast basu yi ba, gabadayansu babu yar gari, kowacce daga wani state aka kawo ta ba su san kowa ba,tunda basu taba fitowa cikin gari ba.
Merapati taciro wayanta da niyan kira amma haryanzun no connection yake samata.gaba daya ma network din ya dauke...
Tafiya suka shiga yi har suka ga wani restaurant, Basma ce tace su shiga su samu wani abu su ci, shiga su kayi, har bakin wajen, aka'idan restaurant din ba a cin abinci har sai an biya.
Bayan waiter ya kawo musu order list sun yi ordern abun da suke so, kudi Hassy ta ciro tunda dama student ba a rabasu da pocket money daga bag dinta ta bashi.
Karba ya yi yana kallon kudin da mamaki dauke a fuskarsa, kallonsu ya yi yace "wannan wani irin kudi ne? ai bama amfani da irin wannan kudin".
Zuwa yanzu mamaki yagama kashe su,Hassy tayi karfin halin cewa "yaushe aka sanja kudin? bamu sani ba? yaushe aka daina amfani da wannan din?.
Shima da mamaki yace "Kai! Aa gaskiya mu bamu taba amfani da irinsa ba a wannan kasar tun asali, dan zance miki tun da aka haife ni ma ban taba ganin irin wannan kudin ba kwata-kwata sai yanzu kuma a kalla shekaruna yakai 27"
Dafe kai kawai suka yi, saboda basu san me za su ce ba,wani dake zaune a gefensu ne yace a basu abincin zai biya musu, kawo musu abincin aka yi suka ci, suka fita.
A waje suka hadu da mutumin sosai suka masa godiya yace musu ba komai, kallon sani ya shiga bin Merapati dashi. Ita kuma ko kusa ma bata san shi ba duk da ta tsargu da kallon da yake mata.
Wucewa sukayi suka bar wajen, tafiya kawai suke batareda da sun san inda zasuje ba, bakin magana ma basu da shi kowa da tunanin datakeyi aranta tabbas suna zargin akwai abinda yake faruwa dasu...basu dade suna tafiya ba sukaga wani katafaren hotel babban building ne dauke da more than 1000rooms reception sukaje nan ma still, kin karban kudin suka yi, saboda basa amfani dashi sosai hankalin su yatashi nan fa suka shiga rokonsu akan su taimaka musu basuda wajen kwana, baice komai ba yadauka telephone security yakira yace azo a fitar dasu..kin fita sukayi sosai suke rokonsu daidai lokacin manager din ya shigo cikin hotel din kallonsu yayi yace "release them" daya daga cikin guards din ne yace "but sir" hannu yadaga mishi yace "I dont wanna hear anything!" kallonsu Merapati yayi yace mata "Madam we are very sorry duka ma’aikatan sabbin zubi ne kiyi hakuri key ya mika mata yace VIP section room 102."
Baki bude Merapati take kallonsa aranta tana maimata kalmar Madam? share zancen tayi tace may be haka suke treating din bakinsu.
Hassy,Basma gaba daya mamaki ya ishesu, ko da suka shiga dakin tunani suke me yasa abubuwa suka sanja gaba-daya a cikin garin gashi mutane duk sun sanja, wanda suka sansu sun nuna basu sansu ba.
Gashi kudi ma ance ba a sani ba kuma ba wai sanjawa aka yi ba to mene ya faru a kwanaki biyar din da sukayi basa nan bayan sunje excursion?
Me yasa a kwana biyar kacal komai ya canza?
Wani irin rayuwa kenan suke shirin fuskanta a yanzu?
An ya babu wani babban kalubale a gaban su kuwa? .
"You guys menene abun yi? Wani irin rayuwa muke shirin fuskanta?" Hassy ta fada.
Ido suka zuba mata gaba daya sun yi tagumi.
"We dont even know".
"Ni kaina ya kulle" Basma ta fada.
Merapati tace "tabbas akwai wani abu wanda bamu san shi ba da akwai wani abu daya faru damu ya zama dole mu san koma menene, tun kafin mutane su fara gudun mu".
Ido kawai suka zuba mata kowa da abun da yake sakawa a ransa.
Shiru sukayi sai can
Basma ta kalleta "Merapati zaki tuno wadda muka gani a principal office?" Kanta ta gyada alamun eh cigaba tayi dacewa "the way she's looking at you kamar tasanki hakama wanda yabiya mana kudi a wancan restaurant din shima yana yi miki kallon sani and the Manager lokacin dayake miki magana muryansa cike takeda girmamawa shin duk cikin su babu wanda kika gane a ciki?"
Kanta ta gyada "gaskiya bansan suba kuma bantaba ganin suba nikaina nayi mamaki danaji yakirani Madam! Koma dai menene yake faruwa zamu gano idan ma pretending sukeyi duk zamu gano..."
Hassy ta kalle su "ni yanzun tunani na idan masu hotel din nan suka gaji damu fah?"
Gaba daya shiru sukayi saboda basu da answer.
*~
Washe gari dukansu suna zaune akan bed din kowa da abinda yake ranta Merapati ta mike wajen telephone din dake bed side drawer taje number din Dad dinta tayi dialing saidai ga mamakinta sam kiran yaki shiga daga karshe ma cemata akayi "Dear customer the number you are trying to reach doesn't exist... Please check the number and try again.." Tsaki tayi ta ajiye wayan.
Kallonsu tayi tace "yanzun mene abin yi?"
Basma tace "nidai yanzun yunwa nikeji"
Hassy ta dafe cikin ta "wallahi nima haka gashi bamuda kudi yaya zamuyi?" kallon Merapati sukayi atare sukace "kimana order please tunda munga kamar sun sanki"
Binsu take da kallo harsun cire ran zatayi magana saikuma ta mike takira tafadi duk abinda sukeso for breakfast...
Ba a dauki lokaci ba aka kawo musu duk wani abin da sukeda bukata.
*~
"Yanzun kuna ganin mene abinyi? ni abinda yafi damu na yanda duk numbers din da muka kira basa zuwa kuma network din mu duk ya dauke!" Kallonsu tayi ganin kawai abinci suke ci "Hassy,Basma I'm talking to you" tana nunasu da hannu amma kin bata amsa sukayi saima kara maida hankalinsu kan food din dake