Showing 93001 words to 96000 words out of 114909 words

Chapter 32 - Babban Goro By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

6104

ɗinta ta ɗauko lil minal tana bata nono kwalo ido matar tayi

“Aiki idan zaki bata nono rufewa kike?”

“Eh bana son ana gani”

“Toh miye abun ɓoyo naga dai ni yar uwarki ce mace shi kuma mijin ki ne”

“Shima ai ina rufewa idan ma yana gida Hijab naƙe sawa”

“Akan me a a gaskiya ki daina wannan ai shi kike cutarwa”

“Haƙa ɗazu yake ce min wai na dai na saka masa hijab cikin gida”

“Aiko ke ko dai ba ki kyauta ba baki san wasu mazan basa son haka ba? karki saba ma mijinki da abunda bai saba ba ki daina nisantar mijinki kinga body contact yana matukar muhimmaci, da kuma saka tufafin da zai kama jikin ki ka fitar da halintar da Allah yayi miki ga mijin ki ki daina ɓoye masa jikin ki
  sannan bari na baki wani sirrin idan zaki ba mijin ki abu ki rika basa a baki ko kuma kiyi masa da hannu sannan ki karanta masa bismillah kafa tara ki tofa ga abunda zaki bashi ko da ruwa ne hakan ma wata mallaka ce ta sosai duk abunda kika san mijin ki na so kiyi kokarin ganin kin aikata masa shi idan kika san lokacin da mijin ki zai dawo toh kiyi saurin yin wanka ki shirya ko da zaizo ya tararda ke kamar amarya abincin da kika san mijin ki naso kuma kiyi kokarin ganin kin tanadar masa shi shi koda yaushe kinga wannan nono da kike ba yarsa wallahi na tabbata ba karamin daɗi yake ji ba, shima kuma kansa yana bukatar kulawa ki rika kula dashi tun da naga kina da mai kula miki da Minal ɗin, ki rike yan'uwansa kamar naki ki rike mahaifiyarsa kamar taki ko ko abu yayi miki kar kiyi saurin nuna masa fushin ki kar ki zamo mace da ko yaushe zata ta kai karar mijinta gida kar kuma ki zamo cikin matan dake faɗar sirrin mijinsu. kinga shagwaɓa tana sa namiji ya so ki fiye da tunanin ki idan zaki masa magana ki rika masa cikin lafazi mai daɗi kuma mai kamar shagwaɓa ki rika shige masa a jiki idan har yana gida karki yarda ki zauna ba a kusa dashi ba ko kuma saman jikinsa idan kuma dare ne ki kwanta a kusa dashi sosai ta yadda idan ya kwana shi kaɗai ko kuma da wata zai rika tunawa dake, ki koya ma kanki cin fruit da madara suna da muhimmaci sosai a jiki mace ki kuma kasance cikin kanshi koda yaushe, ki rika masa kunya hakan nada kyau ko da kin shekara ɗari da mijinki hakan nasa kauna kuma mijinki zai miki kallon cikakkiyar mace sai dai kuma ba irin wannan kunyar take mai cutarwa ba sannan idan yana miki faɗa karki tamka sa har sai ya sauka sai ki zauna ki fahimtar dashi idan kuma a waje ne aka ɓata masa rai sai ki kwantar masa da hankali kuma ki zama mai yawan kyauta ga kowa hakan zaisa ki zamo tauraru ga yan uwan mijinki da kuma makota kuma ki zama mai yawan fari da ido a gaban mijinki”

Zugum Kairat tayi tana kallonta har ta kai aya sannan ta ja numfashi

“Ki ce littafi zan ɗauko kina faɗa min ina rubutawa”

Dariya tayi tace

“Zaki iya haddace wa ai, amman dai kinga wannan sirrin idan kika rika shi zaki mallaki mijin ki babu boka babu malam idan ma gaba ya karo miki kishiya ita bata saba da wannan ba sai yaga dabam sai ki ga kullum dai kece dai wannan abun ne yasa matan waje ki karɓe masa mazaje ko kuma idan aka miki kishiya sai ace ta kwace miji wata kuma ba magani wallahi wannan abun kawai ya ishe ta”

Dariya Kairat tayi

“Lallai Ummu Namra kice da wannan kika mallake mana Abban Namra”

“Sarai baki ba baya son nayi nisa dashi ba? gobe gobe fa zan koma bai yarda na kara ko kwana ɗaya ba”

Ta faɗa tana wara ido. Sun ɗan daɗe suna fira sannan ta tashi tayi shirin tafiyaƙalheri Sosai Kairat ta haɗa mata ta kuma rakanta har gurin mota.

    

    DARE.........

Tana zaune ɗakinta tana ba Lil Minal Nono Saif ya shigo, rasa tayi inda zata saka kanta kamar ta tashi ta ɗauko mayafi ta rufe jikinta sai dai kuma ba dama tun da har ya zauna kusa da ita yana kallon Lil Minal. Ita kuma duk ta tsargu gani take ita yake kallo aiko nan da nan tayi saurin rufe rigarta daman lil minal ɗin tayi bachi.

“Idan an gama da ita ayi dani Please”

Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, Kallonsa tayi kaɗan

“Tea”

Yana faɗa ya tashi ta nufi kofar fita. Kwantar da lil minal tayi sannan ta tashi ta nufi kicin. Cikin kankanen lokaci ta haɗa masa ta nufi ɗakin nasa ba karamin jihadi tayi ba na shiga ba tare da lullube a jikinta ba. Cikin ciki tayi sallama ya amsa mata tana kallon laptop ɗin gabansa. Tana kokarin aje kofin ya mika mata hannu alamar ta bashi ba muau ta mika masa sai ya haɗa da hannun nata ya karɓa ita kuma ya zaunar da ita saman gadon kusa dashi ya sauko da kafafunsa yana sauke ajiyar zuciya.
    Kaɗan ya kurɓa tea ya aje ya kalleta

“Thank you”

“Always”

Ta faɗa tana unkurin tashi. Tashi shima yayi yana murmushi,

    “Bari naje gida na dawo Momy tana son gani na Safiyyah ce ba lafiya me kike so na kawo miki”

“Ba komai”

Ta faɗa kamar bata son magana, shi dai da kallon ya bita har ta fice sam baya jindaɗin yadda take kin sakewa dashi bai san abunda yasa ba sai yaga kamar zaman gidan baya mata daɗi.

                          ***         ***         ***
     A palo ya tararda Momy kamar yadda ta saba sai dai wannan karon har da Gwgaggo da Shafa da kuma wata yarinya da bata wuce sa'ar Shafar ba, Nasir na gefe yayi zugun yana kallon yarinyar.
    Saif sai da ya gama kallon takardun hannunsa sannan ya kalli Momy yace

“Toh Momy ko mu fitar da ita waje? tunda su nan sunce babu abunda yake damunta”

“Wannan lamarin bana asibiti bane Saif al amarun jinnu ne”

Gwaggo ta faɗa

“Kamar ya?”

Nasir ya taɓe baki Ya nuna yarinyar dake.zaune gurin yace

“Wai wannan yarinyar ko aljanunta suka ce wai aljanu ne.daga gidan ka suka fito shine suka yo nan sai suka tarar ita ce kawai ba tayi addu'ah ba shine suka shige mata”

Wani kallo Saif yayi ma yarinyar. sai kuma ya kalli Momy ya kalli Nasir.

“Ni fa ban gane kan wannan maganar ba”

Momy tace

“Wai ajiyar su ce a gidan mafita shine akwai a barsu su ɗauki ajiyar tasu sai su kyale Safiyyah, idan kuma ba haka ba wai har Matar ka sai sun taɓa kuma sunce kar a kuskur a banye ajiyar su zasu ɗauki abun su da kansu”

“Rubbish”

Saif ya faɗa yana murmushin gefen fuska dan shi bai yarda da wannan labari ba. tashi yayi

“Momy bari naje da safe zamuyi magana yanzu kan kaina yana ɗan ciwo”

“Wannan fa ba maganar wasa bace Saifullahi”

Nasir dai in banda taɓe baki babu abunda yayi, Saif bai saurare su yasa kai ya fice. Momy kuma ba tayi unkurin hana shi ba dan ita kanta bata yarda da wannan lamarin ba.


     Yayi kaɗan ko? Don't mind na muku alkawarin wani tomorrow morning just keep voting and commenting



52


Ko da shigo Kairat har tayi shirin bachin ta tana kwance saman gadonsa Iil Minal na gefenta, a zatonsa tayi bachin da gaske sai ya kai hannu ya shafa fuskarta yayi mata kiss yayi ma lil minal.

“I love you all”

Ya faɗa sannan ya xaga ɗayan side ɗin ya hau saman gadon yana picking call ɗin da alayi masa. Sai da Nasir ya kai Aya sannan yayi dariya yace

“Ni ma ai nasan kuɗin su kawai take son taci yaushe rashin lafiyar ta kamata a barmu mu gama na asibitin mana idan ba mu dace da tukuna a kawa mana wata maganar aljannu,
   Amman wannan ni sam ban yarda da ita ba kuma kaji wani iskanci a rasa inda za a ce sai gida na”

Sun ɗan daɗe suna wayar sannan ya kashe ya rage wutar ɗakin ya kwanta. washe gari suna cikin breakfast ɗaya daga cikin yaran gidan suka ya shigo bayan ya gaida su ya kalli Saif yace

“Wai wani ne a waje yana son ganin Madam ni kuma ban yarda dashi ba shiyasa ban barshi ya shigo ba”

“Wanene?”

Kairat ta tambaya,

“Wai ko shine Abokin Minal”

“Jeka ce ya shigo”

Da sauri Kairat ta faɗa Saif ya girgiza masa kai

“Karka barshi ya shigo”

Sai bayan ya fita ta kalli Saif kamar zatayi kuka

“Miyasa ka hana shi ya shigo dan Allah ka barsa wata kila yana da abun cewa”

Baice mata komai ba ya tashi ya nufi hanyar Stairs, da sauri ta sha gabansa

“Dan Allah Saif ka barsa ya shigo ina son nayi masa wasu tambayoyi”

Kafaɗunta ya dafa

“Me zaki ce masa me zai zo nema gare ki? gurin Mummy ya kamata yaje”

“Please idan baka son ya shigo maka gida ka barni naje na gansa”

“Fine”

Ya faɗa ba dan yaso ba ita kanta tasan ba da son ransa ya amsa mata ba. har ta juya sai kuma ya riko ta ya rungumeta a kirjinsa

“I can't I'm sorry”

Lumshe ido tayi, sam bata ji daɗin hakan ba sai dai kuma babu yadda zatayi tunda wanda yake da iko da ita ya hana ta.

    MUMMMY..........
A gajiye ta dawo daga aiki, wanka ne kawai ya zame mata dole daman hakan take duk ta dawo aiki ruwa kawai take kurɓawa ta wanka sannan ta ci abinci. bayan ta gama cin abincin ta buɗe laptop ɗinta tana nazarin wasu abubuwan. Sallamar Tsohuwa ce ta sata ta ɗago kai

“Wa'alaikissalam”

“Hajiya sannu da hutawa kin yi baki a parlour”

“Baki?”

“Eh Hajiya Suwaiba ce da wasu mutane”

Aje Aikin Mummy tayi ta cire gilas ɗin idonta ta tashi ta nufi parlour.
      Tsayawa tayi tsakiyar parlour ta kasa rasawa kisa dasu ta kuma kasa komawa, Dukansu kuka suke ban da Mummy da idonta take a kafe yake.

“Na daɗe da manta ina da ku a duniya bana tunanin kuna da bukata ta kamar yadda nima bana bukatar ku miya kawo ku nan ?”

Tashi hajiya suwaiba tayi ta karasa kusa da ita ta dafa ta,

“Kiyi hakuri ki zauna Salamatu za kuyi magana a natse”

“Bana bukatar magana da kowa miye haɗin ki dasu?”

“Sune suka bukaci ganin ki”

Juyawa Mummy tayi da nufin barin palo sai kuma ta samu kanta da kasawa hawaye suka cika idonta.
  
“Salama tu”

Wata tsohuwa ce ta kira sunan nata idonta na zub da hawaye, juyowa Mummy tayi itama tana hawaye ta kalleta rabon da taji muryarta a kunnen har ta manta wasu hawayen ne suka kara kawo mata ziyara, sai kuma ta fashe da kuka da bata san dalilin yinsa ba.

   “Ki saurari iyayenki ki kuma yi musu uzuri sai yanzu suka fahimci baki da laifi ta dalilin Alhasan”

Wani tsoho mai tsaga a fuska ya faɗa yana hawaye,

“Ko da ina da laifi Baba abunda kuka yi min bai dace kuyi min ba, ko da da gaske na aikata kamata yayi ku rumgume ku yarda da kaddara ku tausaya min amman sai kace baka san haka ba. Ka raba ni da mamana tun ban kai lokacin rabuwa da ita ba, kace ka bar maka gidan ka na manta ka kar na sake waiwayar ka akan abunda ba zai taɓa tabbatuwa ba baka damu da duk halin da zan shiga ba. shim haka ya dace iyaye su yima yayan su idan kaddara ta faɗa musu?”

Kuka take sosai tana faɗin maganar. shima kukan yake abun tausayi

“Nayi hakan ne dan gujema zagi da ɓatancin suna a idon duniya sai gashi kuma ban tsira ba, tun lokacin da na kore ki ban sake dogon farinciki ba sai Allah ya ɗora min sonki yasa min tunanin ki da kuma tunanin irin rayuwar da zakiyi. duk kuma lokacin da naso neman ki sai abunda kika aikata ya tsaya min a rai shi ya hana ni ganin farin ki ya hana ni na neme ki saboda a tunani na da gangan kika aikata sai a sanda Alhasan yazo neman ki mu ka tabbatar da gaskiya”

Gurfawa yayi kasa yana kuka kuka wanda yake na gaske ya haɗe hannayensa

“Salamatu ki gafarta min”

Da sauri itama da duka sai kuma ta tashi ta rumgume Mamanta itama kukan take sosai kaminnta ɗago kai ta kalleta tace

“Ki yafe mana Salamatu”

“Na yafe muku Mama mai rai ajizine kuma kowa baya wuce kaddarar sa har gobe ku iyaye na ne no matter what happen”

Sun daɗe suna kukan har hajiya suwaiba babuɓmai iya ba wani hakuri, har sai da sukayi kukan suka gaji sannan Mummy ta koma kukan farinciki, sai dare Hajiya Suwaiba ta bar gidan.
  Washe gari Mummy da kanta ta haɗa musu abun kari cikin zumuɗi da jindaɗi. sai dai ku ɗin sun kasa sake jikin da ita kunyarta suke ji musamman Baba sun kan su sunsan abunda sukayi mata basu kyauta ba. itakan sai ta nuna musu kamar komai bai faru ba cikin jindaɗi ta kawo musu breakfast ta bisu da kallo zuciyarya cike da farinciki.

Allah mai Hikima lokacin da ya karɓe min ku sai ya bani Minal yanzu kuma ya karɓe abunsa sai ya dawo min da ku

A ranta take wannan maganar tana kallon yadda suke cin abinci. ba karamin daɗi mummy taji ba ganin Mahaifanta kusa da ita.

                       ****       *****       *****

A hankali Kairat ta kai hannu ta buɗe kofar ɗakin


lil Minal sai a lokacin ta samu damar tsayawa tana kare masa kallo. ɗakine da aka kawata shi da kayan masu kyau ɓangaren tufafinta daban ɓangaren da gadonta yake dabam abun gwanin sha'awa.



Murmushi tayi ta karasa kusa da kayan nata ta buɗe ta ɗauko wata riga mai kamada ta sanyi da hula da talkami ta fito, a palo ta tsaya tana nuna ma Talatu kayan da za a saka mata, karɓa tayi ta tashi tare da Ita ta nufin ɗakinta dan Saif ya hana ayi mata wanka ko ina sai ɗakinta. itama ɗakinta ta nufa taje tayi wanka ta shirya cikin jar a tamfa mai ratsin baki. tana fitowa ta nufi kicin girki tayi na musamman dan Mummy ta faɗa mata tana nan zuwa kuma zata zo mata da wani abun mamaki.
    Bayan ta kare ta dawo parlour ta zauna akai akai ta kalli kofa duk ta kosa Mummy tazo sai da ɗauki wayarta kamar ta kira sai kuma ta fasa tana haka har lil Minal ta tashi daga bachi aka kawo mata ita karɓa tayi tana shirin bata nono, taji an taɓa kofa,

“Oh my god”

Da sauri ta tashi tare da ita ta nufi kofar da zumuɗi ta buɗe, da mamakinta sai taga ba Mummy ba,

“Wanene ka.....”

Kasa karasa tayi lokacin da ya ɗago kai ya kalleta, kamannin Minal ta gani shimfiɗe a fuskarsa.

“Shigo”

Ta ce dashi cike da ladabi, ba musu ya shigo cikon palo ya xauna a gurin da ta nuna masa, sannan ya soma magana kamar zaiyi kuka

“Wata alfarma nake nema a gare ki”

“Faɗi ko ta micece zanyi maka matukar bata fi karfi na ba amman ka fara faɗa min wanene kai?”

“Zaki san wanene ni a cikin alfarmar da zakiyi min”

“Wace alfarma ce wannan”

“Na bi duk hanyar da zan bi wajen ganin Salamatu ta saurare amman taki a yanzu ma bana da hurumin bi koda kofar gidan ta ne an faɗa min ta hanyar ki ne kawai zata iya saurare har kuma ta yafe min, so nake ki shiga dani gurin da take ki kuma roke ta data saurare ni ko da ba zata yafe min ba”

Shiru tayi tana kallon yadda yake hawaye jikinta duk yayi sanyi, suna haka wayarta tayi kara alamar kira a sanyaye ta ɗauki kiran

“Hello Mummy”

“Na'am Dear ba zan samu damar zuwa ba amman na kira Saif zak kawo ki yanzu a nan zaku ci abincin rana har Abbahn ki yana nan tare da Suwaiba”

“Okey Mummy”

Ta amsa kamar ba taji daɗi ba, ta kashe wayar. tashi tayi ta nufi ɗakinta, bata fito ba sai da taji shigowar Saif sannan ta aje Lil Minal ta, taso ta nufo downstairs,

“Wow Beauty na”

Ya faɗa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi,

“Sannu da zuwa”

Sai da ya aika mata kiss sannan ya rumgume ta yana faɗin

“Yauwa Wannan kwaliyar fa?”

Gurin wuyanta ya ɗora kansa yana goga mata dogon hancinsa, ita kuma sai kokarin zame jikinta take

“Akwai mutane a falon fa”

Bai kula ta ba sai da ya gama abunda yake son mata wannan ya juyo yana kare ma falon kallo, sai a lokacin ya lura da abunda take magana a kai, juyowa yayi ya kalleta da ɗan ɓacin rai

“Amman kuma shine baki saka hijab ba?”

“Kai kace min na daina sawa a gida”

“A ina nufin idan mi kaɗai ne a gidan ba jeki ki saka hijab ɗin ki”

Murmushi tayi mai sauti har da fitar da halshe tana masa kallon zolaya, ta juya ta nufi upstairs, shima da kallon ya bita dan bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba tun da tazo gidan.
     Tana shiga ɗakin ya shigo juyowa tayi ta kalleshi

“Mummy tace ka kai mu gida a can zamu ci abincin rana shine tace mu wuce da wannan mutunen”

Ta faɗa dan tasan sai ya tambaye da wanene kuma bata san karyar da zata nasa ya yarda suje dashi ba,

“Really?”

Ya tambaya kamar bai yarda ba, taɓe baki ta ɗanyi

“Na taɓa maka karya ne?”

“Na sani ko yanzu zaki fara”

Yaja hancinsa juyawa tayi.sanin nufinta yasa shi kisgota ta faɗo saman kirginsa suka faɗa saman gado. sunfi minti talatin a kan gadon yana aika mata da sakwannin ita kuma tana son kwace kanta amman ta kasa har ta gaji ta hakura. sai da yaji wayarsa na ringing sannan ya sake ta ta tashi tana duba wayar number Mummy ce baiyi picking ba dan yasan yana picking zata ce masa ya kawo Kairat. Bathroomƴa nufa, bai daɗe ba fito ya ɗauki keys ɗinsa,

“Saka hijab ɗin ki muje”

Da sauri ta nufi gurin da hijaban nata suke ta ɗauki wanda yayi kala da atamfar ta saka sannan ta ɗauki lil

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login