Showing 84001 words to 87000 words out of 114909 words

Chapter 29 - Babban Goro By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

6127

windo ganin shi ɗin ne ya kara mata jindaɗi,
   Da sauri ta dawo ta buɗe jakar ta ta ɗauko wani kwalli ta buɗe maciyin ta kira sunan Saif sau uku ta tofa sannan ya shafa. daman haka yace mata duk zata shafa ta kira sunansa dan da sunan akayi aikin.
     
Tana gama shafawa ta mayar a jaka ta nufi madubi ta dauki hoda ta shafa ta gyara jan bakinta ta buɗe wata durowa ta ɗauko wani turare daga ganinsa kasan na magani ta shafa, sannan ta juyo jiki na rwa ta nufo parlour.
   Ta koyi sa'ah tana saukowa yana danno kai cikin parlour, yana sanye da shada sky blue tayi masa kyau sosai kansa ɗauke da bakar hula.
wani fari tayi masa da ido ta sakar masa mirmushi

“Ya Saif sannu da zuwa”

A maimakon ya amsa sai kawai ya wanke mata fuska da mari.



Kuyi Hakuri da wannan Anjima Wani Zai Zo Amman Ban Muku Alkawarin Mai Yawa Ba.😀
just keep voting and commenting on every single line. Stay bless Candy Love you from the bottom of her heart.😍

MY QUESTIONS.

TUN FARKON FARA KARANTA LITTAFIN NAN ZUWA YANZU ME YAFI BURGE KU?

INA YAFI BAKU HAUSHI?

INA YAFI BAKU TAUSAYI?


48

Ja tayi baya da sauri ta dafe junco dan ba karamin mari yayi mata ba,

“Lafiya mi tayi maka haka?”

Momy ta tambaya tana tashi tsaye, sai a lokacin ya lura da Momy, juyar da fuska yayi ya ɗan haɗe rai. A nan ya shiga neman dalilin marin nata da yayi ya rasa, shi kan shi bai san dalilin marin nata dayayi ba shi dai kawai ya samu kansa da jin haushin murmushin da tayi masa da magana.

“Momy parking tayi ba dai-dai ba gurin da nake aje mota na take ta aje”

Ya faɗa yana kokarin kare kansa, tunawa da yau gurin da yake parking yaga motar ta fake,

“Haba dan Allah dan Annabi sai kuma kayi mata wannan mari haka? Sai kace karamar yarinya, ai sai kaje kace ta ɗauke motar ko.? Ba ma ita ra fita da Mota ba Lubna ce”

Shafa kansa yayi yana ɗan yatsinar fuska ya zauna saman kujera, kallonta yayi kamar yace tayi hakuri sai kuma yaji ba zai iya ba, ya kalli Momy data ranta ya ɓace ya ce

“Na ɗauka ita ce sorry Momy”

Banza Momy tayi dashi tana kallon Safiyyah da ta rufe ido tana hawaye, juyawa tayi kamar kazar da kwai ya fashe ma ta nufi ɗakin.

“Ni Wallahi halin naka ya fara isa ta bana son abunda kake yima yarinyar nan ko kaɗan”

Momy ta faɗa tana jan tsaki cike da ɓacin rai. Kallonta ya sake yi

“Momy kiyi hakuri”

“Wane irin nayi hakuri fusabilillahi abun da kake mata kyautawa ne? Ko kuma dan tana zama nan gidan sai ya baka damar yi mata duk wulakancin da kaga dama”

“Momy mistake ne fa”

“Wane irin mistake daga shigowar ka ka fece yarinya da mari kace mistake haka ake mistake to Wallahi daga yau sai yau ko Kallon banza karka sake mata balle ka ɗaga hannu ka dake ta”

Momy na kawai nan, ta tashi a fusace ta shige ɗakinta. Gashin kansa ya shafa ya ɗaga kansa

“Oh my goodness Momy ba zaki saurari abunda nazo dashi ba akan na mari Safiyyah, ya salam!”

Ya faɗa yana girgiza kai.

***          ****        ***

“Assalamu Alaikum”

Yayi sallamar yana kokarin kunno kai cikin parlor, cikin taku irin nasu na manya. Dr Salamatu ce ta amsa masa Kairat kuma ta karasa gurinsa a guje ta rumgume shi

“Sannu da zuwa Abbah”

Ta faɗa cikin wani irin jindaɗi tana dariya, shina dariyar yayi yana faɗin

“Yauwa yar Salamatu ya gidan naku?”

“Gida lafiya kalau”

Ta masa yayin da take ɗago kanta daga jikinsa, hannunta ya rika suka nufi three sitter suka zauna.

“Ina wuni Salamatu”

Abbah ya gaishe ta ganin yadda ita ɗin ta kasa masa magana sai wani abu take kamar ba ta jidaɗin ganin shi ba. Daker ta asa tana ɗan murmushi. Kairat ta tashi cike da zumuɗi

“Abbah bari na kawo maka Abinci yanzu muka gama ni da Mummy”

“Toh yar Mummy ba sai kin kawo min ba ruwa ma ya isa”

Kicin ɗin ta nufa tana faɗin,

“Toh Abbah”

Bata daɗe ba ta fito ɗauke da ture mai drinks da cup, a gaban sa ta dire ta ɗauki lemu ta zuba masa ta mika masa

“Gashi Abbah kasha lemon gidan mu”

Karɓa yayi yana murmushi ya kurba kaɗan ya aje sannan yayi ma Mummy kallon natsuwa.

“Gurin ki nazo ke da yarki”

“Allah yasa ba laifi muka yi ba”

Mummy ta faɗa tana ɗan murmushi, Abbah ya gyara zaman sa

“Jiya ne iyalan Alhaji. Bashir bature suka zo gidana akan maganar Kairat sun ce min daga nan aka turo su kuma yace da amincewar ku, haka ne?”

Kairat tayi saurin yin kasa da kanta cikin kunya ta mataa gurin Mummy, Mummy kuma tasa dariya tana shafa kanta

“Eh haka ne daga nan na tura su can”

Abbah yayi dariya

“Ance Saifullahi ne mijin margayiya”

“Eh. Haka ne sun daidaita dashi da ita ne sai nace idan har da gaske yake yaje can ya same ka ashe ya je”

“Eh sunje Jiya, ni kuma nace ba zan ce komai ba sai naji ta bakin ku, amman naji daɗi wannan abun sosai Allah ya tabbatar mana da alheri”

Mummy ta amsa da

“Amin”

Abbah yayi dariya yana kallon Kairat

“Toh ke kina son shi dai ko?”

A gudu ta tashi ta shige ɗaki tana rufe ido. Abbah ya kalli Mummy da ta bita da kallo ya ce

“Sai a samu su rana kenan?”

“Eah a sa musu amman kayi shawara da Hajiya tukuna”

“Nayi mata magana ai tace nazo nan na same ki ai kece uwarta”

Shiru Mummy tayi tana nazari, ke hakan yake nufi kenan? Babu ruwanta da lamarin auren ko muma me? Maybe bata ji daɗin haɗin auren da aka yi ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Abbah

“A sa musu kuma inda hali kar asa da tsawo saboda Babyn ta kasan an kusa sallamo ta daga asibiti kuma kasan ita ce zata shayar da ita”

“Masha Allah amman kunyi tunani mai kyau gaskiya dan ba kowa bane zai iya yima ma rokon gaskiya ba, Bari na saka muku wata ɗaya yayi?”

“Wata ɗaya bai yi nisa ba?”

“Toh bari aka muku sati biyu”

“Toh ina madallah da hakan Allah yasa albarka”

“Amin”

Shiru ne ya biyo baya kowa hankalinsa ya koma kan tv, zuwa can Abbah ya kalleta

“Toh ni kan zan wuce inda wata matsalar zaki iya sanar min, duk da akawai wata maganar da nale son yi dake amman ina ganin sai an gama wannan hidimar ta Kairat”

Mummy ma tashi tayi ganin ya tashi tace

“Na gode sosai ka gaida Hajiya”

Ta basar da wacan maganar, murmushi kawai yayi dan yasan da gangan tayi hakan, ya nufi kofa ita kuma tayi masa rakiya har gurin Mota.

   Kuka Kairat ta samu kanta dayi lokacin da ta shiga ɗakinta kuka marar dalili dan itama kanta bata san dalilin kukan nata ba, ita dai kawai taji kuka yazo mata ba kakkautawa.
     Kusa da ita Mummy ta zauna lokacin dats shigo cikin ɗakin ta kalleta cikin damuwa

“Kairat bana nufin cilasta ki, bana burin kiyi auren da baki so ban roke ki ki auri Saif sai dan ansan akwai ɗigon son shi cikin zuciyarki, na haɗa ki da girman Allah karki auri Saif matukar kina tunanin aurensa zai zame miki matsala ko kuma tursasawa daga gare ni”

Dagowa tayi ta ɗora kanta saman cinyar Mummy,

“Wallahi Mummy ni kaina ban san dalilin wannan kukan nawa ba, kawai dai ina jin wani abun ne daban, babu cilastawar ki ko ɗaya a wannan auren ni naji zan iya kuma nasa kai na karki taba zargin kanki”

“Amman Kairat bana jindaɗin wannan kukan da kike yi yana kuna min zuciya”

“Ba zan sake ba Mummy insha Allah”

Ta faɗa tana share hawayen ta, Mummy ta shafa kanta.

“Allah yayi miki albarka ya biya ki”

“Amin”

                               ☆ ☆  ☆     ☆ ☆ ☆       ☆ ☆ ☆

Cikin satin Abbah yasa yanka musu sadaki ya kuma duk wani abun da yace uba yayi ma yarsa, cikin satin kuma akayi komai cikin har da kawo tufafin da Kairat zata saka, Saif yasha mayar nu gidan yana tambayarta ko da wani abun datake bukata tace masa a a. duk wani abu da yan mata suke yi ita kinyin tayi ciki har da kin raba katin aurenta, walima ma dan Mummy ce ta shirya ta shiyasa kawai zata halarta. babu yadda Mummy bata yi da ita ba akan ta ɗan yi wani event ko da ɗaya ne amman taki.
   Safiyyah kan tattarawa tayi ta koma gidan Gwaggonta wai ba zata iya zama a gidan Momy ba dan ba zata iya jure yadda Saif yake disgata ba, gashi yanzu abu ɗaya da biyu zai sako maganar Kairat ko lil Minal.
   Duk wani abu da ya dace ya tayi ma yarta sai da Mummy tayi ma Kairat shi, tun daga gyaran jiki zuwa tufafi har kan abunda za a saka mata a ɗakin. hakan sai yasa Kairat ta zama yar gata dan Hajiya ma irin nata gatan take nuna mata, Abbah ma duk abunda aka siyo sai ya nuna mata ya kuma tambaye ta abunda take so, amman hakan bai taɓa sa taji daɗi ko da sau ɗaya ba.
   Ana saura kwana biyu a ɗaura aure Hajiya Suwaiba ta zo gidan, Mummy taji tsoron ganin ta dan bata san da wace tazo ba, tunawa da zuwanta na karshe a gidan, Murmushi dake fuskarta yaba Mummy karfin gwuiwar yi mata magana

“Sannu da zuwa Hajiya Allah dai yasa ba laifi muk yi ba”

Hajiya ta zauna tana murmushi tana kokarin zaunawa,

“Ya gida ya hidima”
  
“Alhamdulillahi ya naku?”

Mummy ta faɗa tana kallon Fusakarta.

“Masha Allahu na fito gidan Ramatu ne nace bari na biyo tun da ku baku zuwa ga shirye shirye yayi nisa”

Dariya Mummy tayi suka cigaba da fira sai dai kowa bai sake jikin kasancewar Mummy tunanin da wace tazo, ita kuma tana jin nauyin Mummy akan abunda tayi masa.

       
           RANAR ASSABAR.........
Rana ce da da dandanzon mutane suka shedi ɗaurin auren KAIRAT IBRAHIM AHLAM da SAIFULLAH BASHIR BATURE, anyi taro kosai tun daga kan yan'siyasa yan kasuwa sarakauna malamai da kuma daidai kun jama'ah, Daga  garuruwa daban daban, bayan ɗaurun Auren mutane suka ɗugun zuma zuwa gurin liyafar cin abinci.
        Bayan gama liyafar Saif ya nufo gida tare da wasu abokaninsa, Kallo ɗaya zakayi masa ka ganr shine angon duba da yanayin shigarsa da kuma yadda fuskarsa ke annuri kanshi turare kan ba a magana, kallo ɗaya Safiyyah tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da kallon tv tana wasa da makulin hannunta,

“Sannu Ango Allah ya bada zama lafiya”

Shafa ta faɗa tana murmushi, Safiyyah ce ta amsa da amin kamar ba komai, sannan ta kalli Lubna take da zuba da Nasir tana faɗin

“Ke suda muje ni dai akwai gun da naƙe son zuwa”

“Ina zaku?”

Nasir ya tambaya yana kallon Lubna dake tsaye kusa dashi ta rike masa hula

“Yauwa Ya Nasir muje ma ka kai mu gidan Ya Saif zamu je ɗakin Lil minal zamu gyara”

“Ita lil Minal ɗin har an mata ɗaki?”

Tayi wani fari da ido,

“Taf tun yaushe yau ɗin ma wasu kayan zamu kara sakawa”

“Toh masu abu su keci da rana kuna shagalin ku”

Duk suka sa dariya har Safiyyah, a nan Luban ta tirsasa shi tasa shi gaba a dole ya kai sai da yayi driving ɗin su har gidan a mota in banda tsokanar Lubna babu abunda yake har ta saka masa kuka.
Dukan su sun yaba kyau gidan da kuma yadda aka gyara ɗakunan musamman ɗakin Lil Minal sasancewarsa ɗakin yara yana da ɗaukar hankali idan an gyara shi.  A tare suka shiga jera sauran kayan ganin aikin nasu ba mai karewa bane yasa Nasir yayi tafiyarsa yace idan sun maga su buga masa zai zo ya ɗauke su. Ai ko Safiyyah ta jidaɗi sosai yana fita itama ta fita daga ɗakin ta nufi gurin da aka dasa itace dan kwaliya, hannu ta kai ta kalli wani ɗan karamin ice ta duka a gurin tana gina, wani abu naga ta ɗauko ta saka cikin karamin ramen ta rufe waige waige take har taƴi ta gama tana Allah Allah kar wani ya ganta, Tashi tayi tana karkaɗe jikinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya can kuma ta buɗe ta nufi cikin gidan.
       wani kallo Shafa tayi mata mai alamar tambaya ita kuma ta ɗaga mata kai, sai ko wannenasu ya ɗauke kai suka cigaba da shirya ɗakin.

      Nasiha Sosai Mummy tayi ma Kairat bayan Abbah da Hajiya sunyi mata nasu, Kuka sosai Kairat ta rikayi kamar ranta zai fita kwaliyar da akayi mata duk ta bace Mummy ma ba karamin kuka tayi ba, saboda tunawa da auren Minal da kuma ganin za a barta ita kaɗai. daker aka ɓanɓare hannun Kairat a jikin Mummy, Motar ma daker aka saka ta, sai wani abu take kamar mai aljannu. ko kuma nace wanda za a cire ma rai, har wani numfashi take saboda kuka.
            Har a ka isa da ita gidan angonta kuka a motar ma ba karamin yaki akayi ba wajen fitowa da ita a shiga cikin gidan ba, a ɗakin aka wuce da ita kowa sai yaba kyau gidan yake da kuma kayan da ka zuba ma Kairat, masu ɗaukar hoto nayi an video camera ma nasu aikin suke. ita kan bata kula komai ba kuka take har abokanin ango suka shigo dashi. zolayarsa suka rikayi shi dai in banda murmushi babu abunda yake shima kana gani zaka san bai kai zuci ba, Nasir ne kawai ya ware kansa daban yana musu nasiha irin ta zaman aure da kuma hakuri, har sauran abokanin suka rika janshi wai sai kace shi ɗin aure ne dashi. sai da suka canye lokacin su har suka shiga na amarya da ango sannan suka bar gidan bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da.

    Gyara zamansa yayi ya kalleta yana sauke ajitar zuciya, shi kansa ba wani farinciki yake ji ba, jinsa yake daban yana tuna rayuwar aurensa ta baya, motsin abun warwaronta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ya sake kallonta a karo na biyu

“Godiya ta tabbata ga Allah wanda cikin ikonsa da amincewarsa da rahamar sa ya nuna mana wannan rana, wanda yau gani ga ki a masayin miji da mata, wannan lamarin na Allah ne shi kaɗai yasan abunda ya tsara mana da kuma wanda zai tsara mana nan gaba”

Ita dai har lokacin kanta na kasa cikin mayafi.

“Sai ki tashi muyi ma Allah godiya”

ta shi tayi ta nufi kofar bathroom ɗin tana wata tafiya kamar ta faɗi, bayan ta ɗauko alwala ta fito shima ya shiga yayi ya fito.
   A tare suka gabatar da Sallah raka a biyu suka yi addu'ah, sannan ya juyo ya kalleta

“Ga abinci nan nasan baki ci komai ba, ni zanje ɗakina na kwanta”

Bata ce masa komai ba shima ɗin bai jira tace masa ba ya tashi ya nufi ɗakinsa. aiko tana jin rufewar kofar ɗakinsa wani sabon kuka yazo mata ta tashi ta koma saman godon ta kwanta tana rera kuka a hankali. da haka bachi yayi gaba da ita

               WASHE GARI.......
Sai tara da rabi Saif ya fito daga ɗakinsa, yana sanye da jallabiya baka tayi masa kyau sosai kamar ba wanda ya tashi daga bachi ba, ganinta tsaye gurin dinning yasa ya karasa gurin yana ɗan murmishi kamin yace wani abu tayi saurin dukawa ta gaidashi cike da ladabi

“Lafiya kalau kin tashi lafiya”

Cikin jindaɗi ya amsa mata. ita kuma ta amsa masa cike da jin kunya,

“Ga abincin ka nan”

Ta faɗa tana kokarin barin gurin.

“Kinci naki ne?”

“Aa a ɗaki zan ci”

Oka kawai ta faɗa yaja kujera ya xauna, bayan ya kare ya koma ɗakinsa ya shiga bathroom yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin wata shadda Lemon green yasa hula baka ya nufo ɗakin Kaoeat sai kanshin turare yake.
   zaune ya tarar da ita gefen gado sanye da babban hijab wanda ya suturce mata dukan jikinta, da alama ita wankan ta fito kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai

“Ni zan ɗan shiga gari idan kina bukatar wani abun sai ki kirani ko kiyi ma mai gadi magana”

Kai ta ɗaga masa ba tare da kalleshi ba, shi kuma ya juya ya fice daman daga bakin kofa ya tsaya.
    Wunin ranar mutane ne suka rika zuwa gidan tun daga ɓangaren Momy har zuwa yan'uwanta da abokanin arziki, masu zolayarta suna yi masu mata nasiha nayi mata. sai kusan insha kowa ya watse aka barta ita kaɗai aiko taji kamar ta fasa ihu ko kuma ta bisu amman ina ba dama yanzu rayuwa ta sauya.
       Bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa black and white ta saka bakin hijab ta nufo dinning dan jera kulolin abincin da aka kawo, Tana cikin aikin raji an buga kofa a hankali, sau biyu zuwa uku. yi tayi kamar ba taji ba har sai da aka sake yi sannan tace

“Wanene?”

Shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta nufi kofar ta buɗe, ga mamakinta sai bata ga kowa ba babu ma mutun balle alamunsa. mai da kofar tayi ta rufe ta juyo zata kunno kai cikin parlour,
   Buga kofar da akayi yasa ta sake juyowa babu kwankwanto ta buɗe kofar da bismillah.
    Minal ce tsaye bakin kofar sanye da bakar riga gashin kanta har godon bayanta tana kallon Kairat da wasu irin kalar idanu manya manya, fuskarta ba yabo ba fallasa. Ba shiri Kairat ta buɗe baki, ta zaro ido tana kallonta numfashinta na kokarin ɗaukewa jikinta kuma ya shiga rawa kamar mazari.

GUESS WHAT?😱  Please keep voting and commenting on every line 😘bohot bohot shukuriya 🙌 love you all guys 😍



49

Ji tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login