Showing 81001 words to 84000 words out of 114909 words

Chapter 28 - Babban Goro By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

6105

na kawai ina son kiyi shawara ne ke da ita ki kuma nuna mata abunda ya dace”

Yana kawai nan ya tashi tare da zuba hannayensa cikin Aljihu

“Na barki Lafiya Mummy sai naji daga gare ki”

Nasir da tun ɗazu mamaki ya kashe shi ya tashi shima yayi mata sallama ya fice.

    A Mota Nasir yayi ta yima Saif magana yaki ya amsa masa sai tukinsa yake har suka isa gida sai da yayi parking sannan ya kallesa

“Dan mi zakayi min haka Nasir? wannan ba shine karo na farko da kake min irin wannan katsa ƙandan ɗin ba ban san miyasa kake min haka ba!”

Tuntsurewa yayi da dariya

“Ba gashi ka faɗin abunda yake ran ka da kanka ba ni ai soso maka gurin da yake kaikayi ne kawai nayi. Kuma Saif in bakayi auren nan yanzu ba yaushe kake tunanin zakayi shi? kai fa ba yaro bane kasan abunda ya dace”

Saif dai bai sake ce masa komai ba ya buɗe Motar ya fice.
ganin haka yasa shima ya buɗe motar ya fita. a tare suka shiga parlour Nasir na ta jan Saif da maganar shi kuma ya masa shiru kamar ba dashi yake ba.
  Guri ya samu ya zauna yana kallon Momy dake kallonsu ya gaishe

“Momy an wuni lafiya?”

“Lafiya kalau ina kuka fito haka? tun ɗazu na aika a kira min kai akace ƙa fita”

Ta karasa faɗa tana kallon Saif,

“Eh mun ɗan fita ne”

Ya bata amsa yana kallon Dinning dan yasan ba zai wuce maganar abinci ba, dan yanzu ta mauda shi kamar karamin yaro ganin baya son abinci.

“Gidan Dr. Salamatu muka fito Momy”

Kamar wanda aka matsi bakinsa haka maganar ta fito a baki Nasir yana ɗan Murmushi

“Me kuka je yi ko maganar Lil Minal ne?”

Nasir ya nuna shi

“Zai miki bayani ni yunwa nake ji”

Da kallo Saif ya bisa har ya zauna saman kujerar dininning yana mamakin yadda take aron bakinsa yana ci masa albasa,

“Lafiya dai ko?”

Momy ta tambaya ganin yayi shiru baice komai ba sai hararar Nasir yake. Sai a lokacin ya kalli Momy yana mata wani murmushi daya kara fitar da ramarsa, zaiyi magana Sallamar Safiyyah da Lubna suka katse su.
Haɗa baki sukayi da Momy gurin amsa musu sallamar Lubna ta zauna kusa da shi yayinda da Safiyyah ta zauna kasa tana kallon tv.

“Ina jinka”

Momy ta faɗa tana mai hankalinta gurinsa

Sai da ya nisa sannan ya fara kora mata bayani,

“Momy akan maganar shayar da Lil Minal ne, toh shine Mummy tace ba zata bari ta shayar da ita ba tunda ba ta da aure. kuma nima ina goyon bayan hakan tunda gaba sai iya zame mata matsala”

“Oh yanxu ta fasa shayar da ita kenan?”

Momy ta tambaya,

“Eh toh ba wai ta fasa bane ita tana son ta shayar da ita matsalan ba daga gare ta bane, Toh shine Nasir ya bani shawarar na aureta kawai ta yadda zata iya shayar da ita tana matata kuma karkashin iko na tun ni daman ba son nake Lil Minal tayi nisa da ni ba.”

Annuri ne ya cika fuskar Momy ta jidaɗin maganar sa sosai, daman abunda yake da munta a yanzu kenan dan gani take idan yana da mata wannan damuwar da yake ciki zata ragu.

“Kayi tunani mai kyau Saif hakan na nuna ka fara yarda da kaddara kenan. kuma kayi sara kan gaɓa, jiya fa muke magana da Abbah ka yake cewa ya kamata ka samu matarm aure ta yadda zaka rage wannan damuwar”

Murmushi Saif yayi

“Momy ai yarda da kaddara waji bi ne ga duk musulmi, kawai dai sabo ne da kawa zuci irin na ɗan'adam”

Lubna ta rika hannunsa tana murmushin jindaɗi,

“Wow Yayana ya kusa zama ango Allah ya tabbatar da alkhairi amman Yaya zakayi mata mai mutunci wallahi ana yabon Kairat da tarbiya nima yarinyar tana burgeni. amman Yaya ta yarda?”

“Yardar nata dai nake nema duk da nasan abun zai zame mata wani iri”

“Gaskiya kan sai taji daban sai kayi hakuri da ita”

“Ko kuma ita tayi hakuri da ni ba”

Ya mayar ma Momy da amsa yana ɗan taɓe baki. tashi Safiyyah tayi tana kokarin ɓoye kukan ta, ta nufi ɗakinta. Duk suka bita da kallo har ta shige.
    Maida kofar ɗakin tayi ta rufe wani irin kuka mai karfi ya zo mata, bata son ta fasa shi su jita duk da tasan sai sun zargeta ganin bata sa bakinta ba, gashi kuma ta taso ta baro musu ɗakin.
   Makullin Mota ta ɗauka tare da waya ta shiga bathroom ta wanke fuskarta sannan ta nufo downstairs.

       Ko da ta sauko Momy da Nasir kawai ta tarar sai kuma Saif dan Kairat bata gurin Momy kawai ta kalla

“Momy zan ɗan fita naje gidan Gwaggo”

“Toh ki gaishe ta Allah ya tsare”

Bata amsa mata ba kai kawai ta ɗauke ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga Parlour. Nasir ne ya bita da Ido har ta fice, sannan ya kalli Saif dake aikin dannar waya ya ce

“Ina jin maganar auren nan da kayi ne yasa taji ba daɗi”

Kafaɗunsa ya ɗaga ya taɓe baki, alamar bai damu ba ya cigaba da abunda yake. Momy ta sauke ajiyar zuciya

“Wallahi yarinyar nan tana son ka Saif ni wallahi har tausayi take bani da zaka bi shawara ta da ka aure ta”

Sai a lokacin ya aje wayar dake hannunsa ya kalleta

“Momy da zan iya auren Safiyyah da tuni na aure ta yun da ba bakuwar fuska ta bace a nan gidan fa ta tashi”

“Toh ai ko ɗan haka yaci ace kayi mata wannan halaccin, ina fa maka tsoron kar kaima kaje ka samu mai yi maka haka gaba kayi aure na ɗaya ka barta ka kara wani ka barta yanxu ka zo da maganar wani ai mutane ma sai su zargi abu cewa za'ayi dan ita ba yata bace yasa kake mata haka gashi taki ta tsayar da Miji”

Nasir ya ce

“Kar hakan ya dame ki Momy nan gaba kaɗan xata fito da mijin aure dan kanta”

“Ni abun har mamaki yake bani wallahi wai mace da aka sani da kunya ita zata fito kiri-kiri ta nuna tana son ka ni bana son irin wannan rayuwar”

Saif ya faɗa yana taɓe baki Nasir ya karɓa masa

“Aiko yanzu mata yawancin su duk haka suke sai ɗaiɗai ku su suke kai tallar kansu da kansu gurin maza musamman in suka ga wanda yayi musu”

Momy ta ɗan ɓata Fuska

“Toh. miye haramun ne? ai Annabi yace duk abunda kake so ka ce kana son shi, sannan a zamaninsa ma an samu mace da taje tace tana son Annabi (S.A.W) balle yanzu da zamani ya canja”

“Momy ai ana barin halal dan Kunya, irin wannan can daban irin wannan daban wannan baya jawo komai sai rage ma mutun kalama da mutunci a idon namiji”

Saif na kaiwa nan ya tashi ya nufi dinning area.

         Kacar  Safiyyah taga ta isa gidan Gwaggo, aiko tana shiga faɗi falonta ta fashe da kuka dan fashe kurjin da yake mata ciwo. da gudu Gwaggo ta fito daga kicin tana tambayar

“Lafiya? wani ne ya mutu?”

“Da mutuwa ce Gwaggo da yafi min sauki”

“Miya faru haka ne Safiyyah?”

“Gwaggo Saif aure zaiyi”

Ta faɗa cikin kuka har muryarta na rawa,

“Oh shine kike wannan kukan ? yau kika saba ganin Saifu yayi aure ne? tashi ki share hawayen ki da yarda Allah kece amaryar”

Cigaba tayi da rairai kukan tana faɗin

“Gwaggo ba zaki gane ba”

“Na gane mana Safiyyah babu abunda Saifu da Mahaifiyarsa keso sai ki mutu. ai tasan ta yadda zata iya sashi ya aure ki amman taki kuma tsan yana sonki da yanzu kece baki sonsa cillas ta miki aurensa zatayi. matar nan ko dan tashin da kikayi a hannuta yaci ace tayi miki wannan karancin. amman batayi ba dan tsabar mugunta”

Cikin kuka Safiyyah ta kalleta,

“Wallahi Momy bata so na Gwaggo bata tausayi na rayuwar yayanta kawai ta sawa gaba ko dan taga bana da uwa ba uba shiyasa take min haka”

“Na sani Safiyyah ai matar ɗan uwa ba ɗan uwa bace shiyasa nake son ki daina kuka lokacin kuka ya wuce kamata yayi mu tashi tsaye muyi abunda xai fitar da mu”

“Toh Gwaggo me zamu yi? bana ganin akwai wata mafita”

“Akwai mafita. nasa abinci ka min wani malamai kwararin kuma an samu mo min ta hanyar su zamu bi har bukatar mu ta biya”

tashi Safiyyah tayi tana share hawaye,

“Gwaggo yaushe zamu je?”

“Ba sai mun je ba su da kansu zasu zo nan gidan zan zuba kuɗi a ɗauko min su daga duk inda suke suyi min aiki”

Rumgume ta Safiyyah tayi tana kuka.

                 Kairat ta tashi zaune tana kallon Mummy idonta cike da hawaye

“No Mummy ba zan iya ba”

“Zaki iya Kairat Saif yana da mutunci yana ɗa karamci bana jin zaki samu matsala a zaman ku dashi”

“Ba shi nake nufi ba Mummy ba zan iya auren Mijin Minal ba, ba zan iya auren wanda bana so ba”

“Ta wannan hanyar ce kawai zaki iya share min hawaye na ta wannan hanyar ce zaki wanke ni daga zargi, ta wannan hanyar ce kawai zaki iya shayar da yar ki cikin kanciyar dan duk namijin da kika aura ba zai yarda ba taɓa yarda ki shayar da yar wani ba ba kuma zan barki ki shayar da ita kina budurwa ba”

“Mummy....”

Mummy ta tari numfashinta

“Kairat ina son kiyi tunani ki kuma yi shawara amman mummy ki ba zata cutar da ke ba”
           
Kai Kairat ta ɗaga mata tana lasar bakinta idonta kuma cike da hawaye, Mummy ta shafa kanta ta tashi ta fice.

    Wayarsa ce take ta ringing alamar kira, shi kuma yayi kamar bai jita ba sai tunane tunane yake, sai da aka masa kusan kira biyar sannan ya tado kai ya kalli wayar dake kan mirrow. ɗauka yaƴi bayan ya danna picking ya kara a kunne, shiru yayi bai yi magana ba hakan yasa mai kiran yin magana

“Hello Saif....”

Muryar Huda ce cikin kuka ta kira sunan nasa. Dafe kai yayi ya ɗan yatsina fuska

“Ya a'akayi?”

Ya tambaya kamar baya son magana, ta ɗan daɗe kamin ta sake cewa wani abu

“Na kira ne naji muryar ka na kuma roki gafarar ka a zaman da mukayi, nasan munyi samun taɓani kuma naci amanar ka dan Allah Saif ka yafe min har abada ba zan taɓa samun miji mai hakuri da juriya irin ka ba Kayi min halacci ta ko ina kayi min adalci Saif baka taɓa cin amana ta ba baka taɓa tauye min hakkina ba ina rokon Allah ya haɗa ka da mata ta gari wanda ba zata ha'ince ka ba Allah ya raya maka abinda Minal ta bari. karka manta da soyayyar Huda a zuciyarka ina Huda na son ka sosai Saif karka manta da wannan.....”

Da sauri ya kalli wayar jin kiran ya katse. wani dogon numfashi yaja ya lumshe ido, maganganunta suka tsaya masa a rai. damuwarsa ta karu yana cikin wacan tunani yanzu kuma ga wani dafe kansa yayi jin yana masa wani sara. babu abunda ya faɗo masa a rai sai Happy Island tashi yayi ya ɗauki keys ɗinsa cikin yan mintuna ya bar gidan.

                             ***      ***      ***

“Allah sarki Sweet Friend wai ke da niyarki sai zama zaki yi sai ranar da yazo yace yana sonki? ai an daina wannan yayin yanzu idan kawai kika ga wanda yayi miki zuwa kawai zakiyi a asirce shi shikenan sai yadda kika yi dashi”

Shafa ta faɗa tana wani rausayar da kai,

“Toh ai ni ba zuwa gurin bane kar sa ka kauce hanya ka kwasar ma kanka zunubi”

“Ah lallai sabuwar shiga ce kwace hanyar na yaushe ai tunda kika ce baki yarda da kaddarar son da Allah ya ɗora miki ba na son Saif kika ki hakura kin daɗe da kwance hanyar.
   Zunubi kuma na nawa? ba ke kika shiga kika fita ba har sai da kika kulla zargi tsakanin mata da miji zama ya gagare su kika ɓata amintar aminai ai kin daɗe da tara wannan zunubin sai dai kawai indan munyi wannan sai mu taru mu tubar ma Allah”

Shiru Safiyyah tayi bata ce komai ba kamar mai tunani,
hakan yasa Shafa taɓe baki

“Ba zai fa taɓa sonki ba tun da kika nuna kina sonsa, bama kece gabansa ba ai maxa sun gware a wannan fannin arkinki ɗaya wannan ba ɗan duniya bane da sai dai yace yayi amfani da wannan damar ya nemi lalata ki”

Ajiyar zuciya Safiyyah ta sauke

“Toh yanzu ni dai yaushe zamu je?”

“Ni idan zaki yarda yau ɗin nan zamu je ba sai gobe ba akwai wani boka a kauyen abujar nan yana aiki sosai kamar hankan wuka sannan ko wane irin aiki yana yi sai dai fa kuɗi”

“Toh ko zamu je can ne kamin Gwaggo ta gwada nata? kuɗi ba matsala bane matukar akwai biyan bukata”

“Ni kuma nace miki matukar akwai kuɗi to akwai biyan bukata, idan kin shirya kawai ki tashi muje”

Tashi tayi tna faɗin

“Bari na ɗan watsa ruwa.”

                              ***         ***        ***

        Magana take da kanta tana safa da marwa can ta samu guri ta zauna ta dafe kai tana dauke ajiyar zuciya,

“Innalillahi wa inna ilaihirraji”

Shine abunda ta furta tana lumshe ido, bata buɗe ba duk da tafiyar da take ji a bayata har sai ta taji anyi mata magana

“If you need someone to talk to I'm here”

Juyowa tayi da saurin jin kamar muryar Saif, shi ko ne ba kama ba ya rumgume hannayensa yana kallonta

“Me kazo yi a nan?”

Kallon gurin ya shigayi kamar bakonsa

“Na kan zo nan wani lokacin dan samun natsuwar zuci. tun lokacin da Minal ta faɗa min nan ne gurin zuwanta sai na samu kai na da sha'awar na kasance a gurin ko da yaushe,
    Kamar yadda kema nasan hakan ne ya kawo ki dan naga yadda kika shigo hankalin ki ba kwance ba”

Yawun dake bakinta ta haɗe ta kalli itace dake gurin, shi kuma idonsa na kanta Yana karantar damuwarta

“You can trust me Kairat”

Ta Kalle shi

“Why should I?”

“Cos I'm the only one you can trust”

Dauke kai tayi hakan yasa ya zagoyo gefenta ya zauna yana kallon tsuntsayen dake gurin ya soma magana a hankali

“Kaiyrat babu ta yadda zaki iya shayar da lil Minal sai kina da aure miyasa ba zaki yarda kiyi auren ba idan har da gaske kike kina son Minal kina kuma son abunda ta bari, taya kike tunanin tarbiyantar da Yar Minal ba tare da ta girma a hannun ki ba? ko kin manta wasiyar Minal ne Kairat?”

“A a ban manta ba, naji ba zan iya shayar da ita ba sai ina da aure amman kuma ba zan iya auren Mijin Minal ba, i can't”

“Ba Mijin wata zaki aura ba mijin ki zaki aura uban yayanki”

Ya faɗa yana kallonta ita, ma shi take kallo. hakan yasa ya kara fuskantar ta

“Kairat bana son ki ra a ranki zamuyi wannan auren ne dan so da kauna kisa a ranki zamuyi wannan auren ne dan sadaukarwa.
   Zakiyi hakan dan Mummy da lil Minal kinsan me? a lokacin da Minal zata rasu ta faɗa min na aure ki na saki cikin farinciki, even on her bed dying ta kula da farin cikin ki misa ke ba zaki iya kula farin cikin yarta ba? ya kike tunanin lil minal ta girma ta buɗe ido taga mahaifiyarta ba raye ba?”

Kai ta girgiza idonta cike da hawaye

“Ba zan iya auren ka ba, ba zan nuna ma lil Minal bani na haife ta ba”

“Taya zaki nuna mata hakan bayan baki auri mahaifinta ba.? banyi wani dogon zama da Minal ba Kairat abunda kike tunani ba shi bane nasan zakiyi rika ga yadda na saba rayuwata da minal ke kuma nayi rayuwa dake no ba haka bane kanun Minal ina da wata matar kin tuna kuma na zauna da ita mukayi tamu rayuwar daban ki sa a ranku saurayi zaki aura wanda bai taɓa aure ba ke zaki koya masa rayuwar aure ki karantar dashi naki karantun a makarantar ki”

Kallonshi take tana mamakin yadda waɗannan kalaman ke fita bakinsa kamar bashi ne yake maganar ba sai kuma ta girgiza kai

“Still ba zan iya ba Saif ya duniya zata kalleni...? i just can't.”

Murmushi yayi mai sauti murmushin da ya kara fitar da kyau da kuma kamalarsa,

“Duniya zata rik'a ɗaga ki ne, mutanen cikin ta kuma su rika kallonki karkace kiyi ta tafiya haka har baki ankara ba lokaci ya k'ure miki baki yi abunda zai amfane ki ba. Nasan yadda kike ji Kairat I feel the same way”

Hannu ta kai ta ɗauki handbag ɗinta ta rata ya

“I need to go home”

tashi shima yayi tsaye,

“Yes go home Kaiyrat kije kiyi tunani mai kyau kiyi abunda zai fidda ki karki manta da baya Kaiyrat karki cutar da kanki karki cutar kar kuma ki bujirewa Minal”

Cikin kwayar idonsa take karantar abunda yake fita bakinsa, kallon kallo suka rika yima junan su kowanne ta tasa sakar a zuciya. ita ce ta fara yin jihaɗin ɗauke nata idon daga nashi ta haɗeye yawun karamin bakinta ta, taka a hankali tana tafiya kamar mai tausayin kasa.

    Da ido ya bi ta yana mata kallon da shi kansa bai san na minene ba? sha'awa, tausayi, so, ko kuma kauna! wani kalar yanayi nake jin kansa ciki yanayin da bai taɓa jin kansa ciki ba wani kalar yanayi ne mai wuyar fassara.
   A hankali ya kai hannu ya shafa kyakyawan gashin kansa ya tada kai yana kallon itace dake gurin yana lumshe manyan idonsa a hankali.
Mamakin kansa yake yadda yake rokonta ta aure shi bayan bai taɓa yi ma wata mace hakan ba. wani gurin kuma gani yake yana da gaskiya saboda wasiyar Minal da kuma lil Minal.

                        ****           ***      *****

BAYAN KWANA BIYU....

      Safiyyah ce kwance ɗakinta fuskarta ɗauke da murmushi sai juyi take ta kafa tana jindaɗi. yau ne zata fara gwada maganin da malamin ta ya bata kuma ta yarda zaiyi mata aiki. tana jin fakawar Motar Saif ta tashi ta sauri ta leka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login