Showing 99001 words to 102000 words out of 114909 words
ya zame mata dole tana yinsa ta ɗauko lil Minal ta bata nono sai da ta tabbatar ta koshi sannan ya kwatar da ita gabanta ita ma ta kwanta sai bachi.
Da dare takeaway yayi masu dan wuni tayi tana bachi shi kuma yana ganin tayi bachin ya sa kafa ya fita bai dawo ba sai bayan Sallah isha i,
Bayan ya shiga ɗakinsa yayi wanka ya dauko abinci ya nufo ɗakinta a bakin kofa ya tsaya ya sauke ajiyar xuciya sannan ya shiga da sallama,
Duk yadda yaso ya ɓoye damuwarsa dai ta gano dan idonsa take karantar halin da yake ciki ita kaɗai ta ci abincin sho bai ciba sai saka da yayi gaba yana kallo kamar tv,
Bayan ta kare cin abincin ya janye abubuwan dake gabanta ya matso kusa da ita ya rumgume ta, a nan ta kara fahimtar halin da yake ciki.
Haka suka kwashe kwana biyu ita da shi, ita ta kasa ta tambayeshi damuwarsa shi kuma ya kasa faɗa mata, sai dai kuma duk tsawon kwana biyu nan bai barta ta huta ba, kullum da salon da yake zo mata.
Yau ma bayan sun gama breakfast ya tashi kamar jiya ya nufi ɗakinsa, har yayi abunda zaiyi ya fito tana zaune a inda ya barta ganin yanayin shigarsa ya tabbatar mata da fita zaiyi. sai da ya kawo bakinsa daidai kumatunta zai mata kiss tayi saurin jayewa ya sake dawowa ɗayan gefen ta sake kauda fuskarta,
“Lafiya?”
Ya tambaya yana fuskantar ta, kallonsa tayi
“Bai kamata ace kana ɓoye min damuwar ka ba a tunani na yanzu ni da kai mun zama ɗaya”
shiru yayi sai kuma yaja kujera ya xauna ya kama hannunta,
“Matsalar Safiyyah ce take damu na saboda Momy da Gwaggo sun ce nine silar shigarta wannan halin hakan yasa yanzu Daddy shi ma ya kasa fahimta na”
Tasan me yake nufi tun da ta daɗe da sanin babu wanda Safiyyah take kauna irin Mijinta. sai dai kuma me su suke nufi har ya kai suna ganin laifinsa? ko aurenta suke so yayi? dan ta samu wannan amsar yasa tayi masa wata maganar.
“Toh ka aure mata sai ka wanke kanka”
Rumgume yayi yana dariya
“Funny girl ina ni ina Safiyyah bana mata kallon matar da zan iya aure ba zan iya zaman aure da Safiyyah ba sai dai kuma nima kai na tana bani tausayi sosai”
Wani sanyi taji ya tsara zuciyarta kara lafewa tayi jikinsa,
“To yanzu ya zakayi?”
“Oho gani ga Allah ni dai fata na kawai ta samu lafiya”
“Toh miyasa ba zaku sata under medication ba?”
“Gwaggo ce bata yarda ba wai kara firgita mata kwakwalwa za'ayi sai dai a nema mata na hausa”
“Ka barta ta nema mata na hausan wata kila a dace”
Sun daɗe a haka manne da junna sannan ya sake ta ya fice.
*** *** ****
Abu kamar wasa sai ga Safiyyah ta kwashe wata biyar da wannan lalurar tun ana ganin kamar sauki sauki yanzu abun ya fara wuce gona da iri, kuma duk da hakan Gwaggo taki yarda a kaita wajen maganin turawan ma sai an saci idonta ake bata,
Sannu sannu ake sabo yanzu kan Kairat ta san kan gidanta da kuma mijinta, ga kula da lil Minal da take sosai da sosai itama yanzu tayi kyau tayi wayo dan yanzu tana cikin wata na bakwai, in ka ganta kamar ka sace ka gudu.

Tana cikin kicin tana aiki taji an danna bell lil minal kuma ta kwala ihu saboda tsoro, da gudu ta fito tazo ta ɗauke ta,
“Ya akayi mi ya faru?”
Shiru tayi ta kalli kofar falo jin an sake danna bell ɗin, ɗauke da ita taje ta buɗe kofar, Da sauri ta rumgume Mummy ta welcomin ɗin ta.
“Ashe ma kinji sauki ce min akayi ɓaki da lafiya”
Mummy ta faɗa tana kunno kai cikin parlour,
“Naji sauki Mummy waya faɗa miki?”
“A shanun talla naji ina mai gidan naki?”
“Ya fita tun ɗazu Mummy ina Abbah na”
“Abbah ki? ai kinsan inda yake”
Murmushi tayi
“Haba Mummy ya kamata ace kun wuce wannan gurin tuni tun yaushe ake abu ɗaya dan Allah! haba Mummy ki amince masa mana Mummy yanzu ko dan karamcin da Abbah yayi miki ba zaki yarda ki aure shi ba”
“Yayi min ne saboda Allah dan Allah ki rufe min baki ko ruwa baki kawo min ba zaka ɗauko min wani shirme”
“Haba Mummy Abbah fa ko ke ko bake ba ya riga ya shirya aure a yanzu da aje a ɗauko mana wanda bamu sam halinta ba fa ao kara ke kuma kinga Hajiya ma da kanta ta roke ki miyasa kike son watsa musu kasa a ido ne? wallahi mummy sam bana jindaɗi in kina cewa Dr. Isma'il zaki aura ko dai dan yafi Abbah kuruciya ne?”
Mummy ta zaro ido
“Kairat zaki tashi ki kawo min ruwa ko sai na bar miki gidan ki?”
Tashi tayi tana dariya ta mika mata lil minal ta shiga kicin ta ɗauko mata drinks da yan kayan ciye ciye ta dire mata.
Sunyi kusan awa biyu suna fira, Mummy na batun tashi Saif ya shigo, yaji daɗin ganinta sosai dan rabonta da gidan har ya manta duk rashin lafiyar da Kairat take yi bata leko gidan ba har taji sauki, Cikin mutumci da girmamawa suka gaisa Mummy take tambayarsa ya mai jiki
“Jiki da sauki”
“Ta warke kuwa?”
“Aa har yanzu tana nan abunda dai sai dai hamdala”
“Allah ya sauwake amman da kun gwaɗa gurin Deen ko Allah zai sa a dace”
Kairat ta mere baki
“Wallahi Mummy nayi ta masa magana yaki yarda shi har yanzu yaki ya manta abunda ya faru”
Mummy ta kalleshi,
“Saif ba a son musulmi da riko, ka amanta abunda ya faru kuma ai ba wani abun zaka je nema ba sai lafiyar yar'uwarka kuma ba kyauta zai maka ba”
Kasa kasa ya watsa ma Kairat harara,
“Shi kenan Mummy zan gwada insha Allah”
“Toh Allah ya sa a dace ni kan bari na tashi kar baki da zanyi suzo ba su tararda ni ba”
Sallama tayi ma Saif, Kairat kuma ta rakata har gurin mota tana mata maganar Abbah ta, Mummy dai bata ce masa uffan ba taja motar ta ta rufe.
YAU MA SAI NACE VOTING AND COMMENTING?
55
Sai da taga ɓacewar Motar Mummy sannan ta juyo, tana shigowa Saif ya cafkota ya wani walkato ta ta juya ta juyo ta faɗo korjinsa, hannunta ya ɗan matse fuskarsa na kan kafaɗarta yayi mata magana kamar mai raɗa
“Wa yace ki daɗe?”
“Ba kowa ba”
Ta faɗa da dariya tana son kwace hannunta dan taji zafin rikon da yayi mata, shi kuma yaki sakinta sai kanshin turaren wuyanta yake shaka, suna haka Lil Minal ta rarrafo tazo ta kama kafan babanta hakan yasa ya saki Gimbiyar ya ɗauki yarsa yana murmushi, dariya tayi ta rika zallo Kairat kuma ta nufi kicin tana ɗan turo masa baki.
Bayan sun gama cin abincin dare Kairat take kara masa maganar Safiyyah, ta damu da ita a yanzu tsaɓanin baya da ba ruwanta da ciwonta ko dan yanzu taga abun yana damun Momy da Saif ne oho! Ita kanta Safiyyah yanzu ta zama abar tausayi bata magana kuma komai bata iyawa sai idan gwaggo ce tayi mata ko kuma yar aikin da ka ɗaukar mata, wani. Lokacin kuma bata komai saikin kuka, ga magani anyi nema har an gaji har yanzu shiru. Kansa ya shafa ya ɗan gunɗe baki
“You know how much I hate him”
War tayi da ido
“Oh my dear, kar wannan ya dame ka ai ba cewa nayi ka so shi ba lafiyar Safiyyah zaka nema ba wani abun ba ko dan Gwaggo da Momy and Kalbi babu abunda zai iya mana yanzu abunda yayi maka a baya zafin son ta yasa yayi maka haka tun da yana tunani zaka iya sakinta shi ya aure,
Kuma abunda ya faru a baya ai ya zame maka darasi yanzu wani ba zai kawo maka wani abun ka rufe idonka ka cutar da kanka ba”
Iskar bakinsa ya busar
“Fine amman shine zai zo ya same ni a nan”
Dariya tayi
“Haba dai wanda keso ba shi ke biya kuma wallahi kasan Deen ba xai kawo kansa gidan nan dan matsalar Safiyyah ba, karka manta yanzo ka hana n ganshi kuma ni yanzu ko number sa bana da”
“Me kike Nufi ke nan mune zamuje?”
“Idan mun je ai ba yada kai bane, kuma ka samu Momy ku tattauna”
Tashi yayi ya rika hannunta,
“Mu rufe babi wasu muyi na mu babin zo muje mu kwanta”
Tashi tayi tana wani irin yauki da jiki ta ɗora kan ta saman kafaɗarsa, hannunsa sarke da nata suka nufi upstairs.
Washe gari bayan ya tashi daga aiki ya biya gurin Momy, sai da yayi kamar yana yi sannan Momy ta sake dashi, dan fushi take dashi wai yau kusan kwana nawa bai leko gidan ba, shi dai hak'uri kawai yake bata yana dariya yasan ba dan komai bane sai dan Safiyyah zata ce ya daina kula da ita ne,
“Ya mai jikin?”
Ya tambaya yana kallon yadda zata amsa masa,
“Jiki yana nan yadda yake jiya Gwaggon ku tazo ta ɗauke ta wai zata kai ta wani gurin a gwada a gani”
“Wai ita bata gajiya da na hausar nn ne, ni da har nace ko mu kai ta gurin wani mai kula da masu irin ciwon mu gani”
“Toh ni ai lamarin ne yanzu na rasa gane ma kansa kullum abu ɗaya”
“Jarrabawa ce idan Allah ya kawo ma bawa sai hak'uri”
“Sai ka bari idan sun dawo sai muje gurin da kace ɗin Ya Kairat da lafiyar jiki?”
“Taji sauki sosai yanzu ai”
“Allah ya kara sauki amman nace Ba zata yaye Lil Minal ba? Kar tazo tasha ciki abu ya zama biyu gata tayi jikinta”
“Toh wai Momy Lil Minal bata saba da shan komai ba banda nono kuma kinga cikin ai wata huɗu ne yanzu kin ga akwai sauran lokaci”
“Aifa sai ka yi, wato har yanzu baku fara bata komai ba ko! Ko yar madarar nan ta yara ai kwai saba mata da ita”
“Za a bata”
Ya faɗa yana ɗan sosa kai, Momy ta taɓe baki
“ku dai kuka sani, idan ba a sharar masallaci ba ayi ta kasuwa”
Shi dai dariya kawai yake. Sai kusan la'asar ya bar gidan, Yana ɗaukar hanyar gidansa gabansa ya soma faɗuwa, sai jikinsa yayi masa ba daɗi cikin wani yanayi ya isa gidan, bayan yayi parking ma sai da ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito ya nufo cikin gidan,
Da sallama ya shigo jin ba'a amsa masa ba yasa ya zauna saman kujera yana
“Mom Lil Minal I'm back”
Shiru nan ya tashi ya leka kicin bai ganta ba, kai tsaye ɗakinta ya nufa yana tura kofar ɗakin da faɗin
“Madam ko bachi kike ne?”
Nan ma ba kowa a ɗakin sai Lil Minal dake bachi tana sauke ajiyar zuciya, da ala kuka tayi har ta gaji bachin ya ɗauke ta, bathroom ya buɗe nan ma bata ciki a nan ne hankalin sa ya fara tashi
_Toh ina ta shiga.?_
Ita ce tambayar da yayi ma kansa, a nan ya juya ya shiga ɗakinsa nan ma bata nan cikin sauri ya dawo parlour yana tunanin gurin da zata shiga ya dai san bata fita bata faɗa masa ba to ina ta shiga?, gurin mai gadi ya nufa yana tambayarsa, nan shima yace shi dai bai ga fitar ta ba, dawowa yayi cikin parlour ya danna mata kira sai kawai yaga wayar saman kujera tana ringing, ɗaukar wayar yayi yana dubawa can kuma ya aje ya nufi hanyar da zata sada shi da Garden,
Kwance ya hango ta kasa dafe da ciki, cikin sauri ya k'arasa yana kiran sunan ta, durkusawa yayi yana girgiza ta ganin bata motsa ba yasa ya ɗago ta ta ɗora ta saman kafafunsa,
“Lafiya mi ya same ki?”
Cikin firgice ya tambaya, hawaye ne yake mata zuba bata iya magana sai cikin da ta sa hannu ta dafe, hannu yasa gurin cikin yana dubawa
“Miya faru ciwo yake miki ne?”
Kai kawai ta iya ɗaga masa sai hawaye take, da sauri ya ɗauko ta ya nufo parlour da ita, saman jikinsa ya rungume ta, ita kan kallonsa kawai take tana hawaye, ganin abun banayi bane yasa ya ɗauke ta ya nufi asibiti da ita, yana isa aka wuce da ita Emergency taimakon gaggawa aka shiga bata, a waje Saif ya tsaya hankalinsa a tashe ya ciro wayarsa ya danna ma Mummy kira ya sanar da ita, bayan ya kashe ya kira Momy ita ya faɗa mata, yana kokarin zama Lil Minal ta faɗo masa a rai, cikin sauri ya ciro wayarsa ya saki kiran Momy, bugu ɗaya ta ɗauka
“Hello Momy na manta na baro Lil Minal gida a tura Lubna ta kula da ita yanzu Please”
“Okey gamu nan zuwa”
Bayan ya kashe wayar ya dafe kansa yana tunanin abunda ya samu matarsa haka, ba ayi minti goma ba sai ga Mummy ta iso gurin hankalinta a tashe,
“Ina take Saif?”
Shine abunda Mummy take tambaya cikin tashin hankali, gaishe ya fara yi ta amsa masa sama sama, tana kara tambayar sa ina take,
“Tana ciki Basu fito ba har yanzu”
“Toh wai miya same ta ne? ”
Bakin abunda ya sani ya faɗa mata dan shi kansa bai da takai maimen abunda ya same ta, zaunawa tayi a ɗayan kujerar tana kallon kofar ɗakin Kairat da take ciki. Bayan kamar minti arba'in likintan ya fito ɗaga ɗakin tare da wasu nurses guda biyu mata, da sauri Saif ya tashi da Mummy suna tambaya likitan ba'asi,
“Gaskiya ba mu gano ko minene ba a yanzu amman dai ko minene a cikin cikinta yake yanzu za muyi mata hoto ne sai mu bincika cikin nata”
Ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya,
“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un”
Shine abunda Mummy ta faɗa ta faɗi zaune saman kujera, Saif kuma yasa hannu sa aljihu yana kallon Momy da ta iso a yanzu,
“Lafiya miya same ta ne?”
Babu wanda ya iya amsa mata daga Saif har Mummy, likitan ya kalli Saif yana faɗin
“Ina son muje office kayi mana bayanin abunda tace tun daga safe zuwa yanzu”
Kai kawai ya ɗaga masa ya bisa baya jiki ba gwari, wani file ya karɓa hannun nurse ɗin bayan sun zauna Saif ya soma masa bayani
“Tea kawai muka breakfast da shi da safe da bread sai egg shima bana jin tace dan tun da ta samu cikin nan bata son kwai sosai sai, ni dai daga nan na fita ban sani ba ko a kara cin wani abun bayan fita na”
Bayan ya gama rubutawa ya mika masa file ɗin,
“Zaka sa mana hannu a nan”
Bayan yasa hannun ya kalli likitan yace
“Dan Allah kayi duk abunda ya dace Please”
“Insha Allah zamu yi duk abunda ya dace”
Juyawa yayi jiki ba gwari ya fice daga office ɗin.
Haka likitoci suka wuni akan ta suna bincikar ta, amman basu gano mike damunta ba dan ko hoton da kayi mata basu ga komai ba, abu ɗaya suka sani shine ko minene a cikin cikinta yake.
Sai dare Mummy ta kira Hajiya Suwaiba ta faɗa mata, ba ɗauka lokaci ba suma suka iso tare da kannen Kairat da kuma Nafisa yayar Kairat,
Abunda likitan ya faɗa musu shi Mummy ta faɗa ma Hajiya Suwaiba, babu wanda hankalinsa bai tashi ba ganin irin halin da take ciki kuma gashi likitocin sunce basu gano abunda yake damunta ta,
Duk yadda Mummy taso Saif yaje gida kiyawa yayi a dole suka kyale shi ya kwana asibitin tare da ita, lokaci lokaci ta kan buɗe idonta ta kalleshi sai kuma ta rufe kamar mai bachi duk maganar fa yayi mata ba zata buɗe idon ba, balle ta motsa ko tayi masa magana, a yanayinta ma kamar bata san inda take ba,
Har gari ya waye Saif ba rumtsa ba, a masallacin asibitin yayi sallah asuba, sannan ya sake dawowa ɗakin, kujera yaja ya zauna ya haɗa hannunshi da nata ya rik'e idonta taf da hawaye, ji yake kamar rasa ta zai yi,
“Allah ya baki lafiya i Love you so much”
Ya faɗa yana lunshe ido yana sauke ajiyar zuciya yana haka Mummy ta shigo, bayan sun gaisa ta tambayi shi jikin, yace mata da sauki hawayen da taga a idonsa yasa ta ɓoye nata hawayen, tana kokarin yi masa magana likita ya shigo ɗakin,
Bayan ya duba ta ya kalli Saif yace
“Za mu canja mata ɗaki kuma ba bukatar wani ya shiga ɗakin idan ba likita bane sai dai zaku iya ganinta ta windo ina fatar zaku bamu haɗin kai”
Ajiyar zuciya Saif ya sauke,
“Doctor ko dai mu fitar da ita waje?”
“Eh to ba zan hana ku fitar da ita waje ba amman da kun bar ta muyi mata irin na mu mi gani tunda kaga abun daga jiya zuwa yau ne wannan ɗakin da za'a kai ta za'a kula da ita sosai ka kwantar da hankalinka zata samu sauki insha Allah matsalar kawai mu gano abunda yake cikin ne”
Cikin zafin rai yace
“Dr ya za'ayi na kwantar da hankali na bayan kun kasa ku gano abunda yake damunta, tun jiya yarinya ba ta san inda take ba amman kun kasa yin komai”
Likitan ya dafa shi
“Muna kokarin ganin mun gano haka sai dai kuma ina son kasan lafiyar ta da ciwonta a hannun Allah yake ba a hannun mu ba, kuma kun fa ya kum sai Allah addu'a kawai ya dace kayi”
Buge masa hannu yayi ya tashi a fusace ya fice daga ɗakin, tsaban zafin rai ko Hajiya Suwaiba bai tsaya gaidawa ba ya nufi harabar asibitin, tsaye yayi gurin motarsa yana shafa kansa zuciyarsa na bugawa da karfi, oho me zai yi shi kanshi yasan addu'a ce kawai mafita tunda baya iya bata lafiya sai abunda Allah yayi,
“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un”
Shine abunda yake ta maimaitawa yana son haɗe kukansa, buɗe motar yayi ya zauna ya