Showing 18001 words to 21000 words out of 60308 words
dalubi ke har bautar qasa yasha zuwa States da dama na qasar nan duk a cikin aikinsa ne hakan shine yake bashi damar yin bincikensa cikin sauqi babu mesa masa ido bashi da yarda ko kadan kuma bashi da sauqi yanada zafi sosai Mainah Abdu dan rikici ne na qarshe da yana kirana daga baya kuma ya zubar da wayoyinsa amma na karbo number sa so shi wayarma ba dagawa yakeba saboda tsabar rashin yarda dakai Samhatu zan hadaki dai da yan'uwanki kuyi zumunci na lura suna sonki musamman Yasmin da duk zuwan da zanyi sai ta tambayeni kw har hotunanta tabani tace na kawo miki kuna kama sosai saidai ita farinmu tayo su dukkansu fararene zubin fulanin katsina mallawa kema kina yanayi dasu sosai fatarki ce dai ba irin tasu ba"
Lagwabar dakai tayi tace “ni nagaji da wannan lbrn da kake bani kullum Dad ka kasa kaini Katsina ni banma san hanyarta ba gashi har ana shirin turamu service Imo State" shafa kanta yayi yace “karki bata ranki zan kaiki kiga yan'uwanki sunada yawa Daughter wadannan da nake baki lbr dai sune shaqiqanki da babansu dani Babarmu daya babanmu daya" turo baki gaba tayi tace “ni bazanma ce ba tunda baka nunamin suba tun Ina qarama sai yanzu da kake shirin auraddani" dariya yayi sosai yace “yawwa dama wannan sakaran yaron Na'im yaxo da mgnr aurenku nace masa sai kin gama bautar qasa yace ya fasa aurenki saboda haka ki fitar da mijinki da kanki" rungumeshi tayi tana dariya shima dariyar yayi ta tashi ta shige kitchen ta dauko abinci ta zauna gaban Dad din nata tanaci tana bashi a baki itadai Mamy tana zaune tana kallonsu tana dariya tace “wlh Dad saika tashi tsaye akan Samha lamarin yaron nan data qwallafa rai akansa yana neman zautata" murmushi yayi ya lakace mata hanci yace “so abinki Yata ya cancanci asoshi na Allah dai yasa rabonki kine...." Dagowa tayi da sauri ta kalli Dad din kawai sai hawaye ya balle mata cikin damuwa ya janyota yana share mata hawayen yace “kici gaba da hqr zakiyi nasara my daughter hqr mabudin rabone kinji" daga masa kai tayi ta miqe ta shige dakinta ta kulle ya dube Hajiya Lubabatu yace “kinada matsala Hajiya na fada miki baa qwacewa yaro garma ki sakar mata da kanta idan ta sheqa taji babu qwaye zata zubar"
Haka kwanaki sukayita shudewa watansu biyu a gda cikin watannin Dr Mus'ab yazo Abuja yakai sau biyar tun tana zulle masa hardai ta rungumeshi hannu biyu saboda itama zuwa yanzun auren takeso da gaske shine yake cire mata kewar Abdul saboda yasan duk ta yanda zaiyi yabawa fulawarsa ruwa sosai.
Tunda kuwa yaga ta sake jiki dashi ya fara bijiro mata da mgnr aure yauma suna zaune a garden din gdan nasu cike da kulawa ya dago ya kalleta tayi murmushi tace “Sir yada kallone?" Ajiyar zuciya yayi yace “inajin tsoron wani ya kwacemin kene My love don Allah ki bani dama na turo magabatana asan dani a gdanku idan da halima a banike in yaso a tsayar da lkcn aurenmu zuwa lkcn da zaku gama bautar qasa in yaso sai ayi biki abani matata my love kada kicemin a'a don Allah wlh Ina buqatar aure shekaruna sun fara nauyi 37 year's ba aure haba Samha a tausaya mini mana kinga fa kema kina buqatar auren nan nasan dai kinfi 20 year's yanzu ko?"
Tunda ya fara mgnr idanunta suka ciko da qwallah inama ace Abdullah ne ke roqonta haka da taji dadi zamewa yayi daga kujerar da yake kai yace “don girman Allah kiyi hqr My love wlh bansan kalamaina zasu bata miki raiba da bazan fara ba nayi miki alqawarin bazan qara maki wannan mgnr ba harsai sanda kika buqata don kanki..."
Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tace “ba kalamanka ne suka batamin raiba hasali ma dadi naji na sani kuma na yarda kaidin masoyinane na haqiqa wanda nakeda yaqinin bazan taba danasanin rayuwar aure dashi ba na baka dama Sir na baka dama ka turo...." wani ihun murna ya saki yace “oh gud! Na gde my love naji dadi sosai insha Allahu zanyi miki adalci kuma zanci gaba da sonki har abada" janye hanunta tayi daga nasa ta miqe ta nufi cikin gdan da gudu tanaji yana kiranta amma taqi tsayawa murmushi yayi yanajin qaunarta na nunkuwa a zuciyarsa miqewa yayi ya fita ya samu taxi ta kaishi airport ya hau jirgi domin sanarwa da iyayensa kyakkyawan labarin.
Tana shiga ta fada gadonta ta fashe da sabon kuka shikenan yanzu ta tabbata ta rasa Abdul dinta? Mamy ce ta shigo ta zauna tana shafa gashinta cikin lallashi tace “meye yake damunki ne pretty?" Cikin kuka tace “Mamy na bawa Dr Mus'ab damar turo magabatansa yanzu shikenan na rasa Abdul Mamy shikenan na tabbata mallakin wani bashi ba" murmushin farin ciki Mamy tayi tace “nidai Ina tunanin shegen yaronnan asiri yayi miki Samha to wlh ki kiyayeni kinji na fada miki yaron kirki irin Mus'ab gashi babanshi me kudi ne ke nifa banason kaiki inda zaki wahala ke baki hutaba nima ban hutaba nafiso a fitar dake gdan arziqi akaiki gdan arziqi Mus'ab shine ya dace dake wanda yake sonki saboda Allah yo wancan wawan yaron idan kika kuskura kika aureshi ai kinshiga uku don ko ya sameki Varging yana tande zakin zaiyi jifa da kwalin tunda bake yakeso ba budurcinki yakeso shashasha dake da bakisan me sonki ba"
Tashi Mamy tayi ta fice daidai lkcn da wayarta tayi ring Dr Mus'ab ne yake fada mata yanzu zai hau jirgi sukayi sallama Kiran da akayi mata ta rinqa dubawa biyu na Rahmah ne uku na Abdul na Rahmah tabi saboda tana ganin kamar zaifi muhimmanci a gurinta nashi bai wucce gaisuwa ba da qaryar yana kewarta tana dagawa tace “wai Samha me yake faruwane?" Cikin rashin fahimta tace “game dame ba?" Sake katseta tayi da cewa “yanzu Dr Mus'ab ya kirani yake fadamin nayi masa gdy a bisa matsayin da kika bashi wanne matsayi ne?"
Ajiyar zuciya tayi tace “nabashi dama ya turo magabatansa gdanmu ayi mgnr aurena dashi ne kawai" hamdala Rahmah tayi tace “amma naji dadi sosai gsky ki godewa Allah Samha Mus'ab yana sonki sosai kuma zakiji dadin rayuwa dashi" hawaye ta share tace “inata qoqarin cusawa zuciyata soyayyarsa amma na kasa" rarrashin ta Rams tashiga yi tana bata kalamai masu kwantar da hankali nan take fada mata cewa ranar juma'a ana nemansu a makaranta zasu karbi posting latter su tace “nayi farin ciki da aka hadamu guri daya Samha" haka sukaci gaba da hirarsu bawai don tanajin dadin hirar ba saidon ragewa kanta tunani da damuwa sannan sukayi sallama tana sauke wayar a kunnenta wani Kiran ya shigo My Abdul tagani a saman wayar yana yawo tayi kamar bazata dagaba saidai wata zuciyar ta umarceta da dagawa ta kara a kunnenta tare dayin sallama ajiyar zuciya ya sauke tare da amsa Mata yace “laifin me nayi da kikaqi dagamin waya My Samha?" Cikin raunin murya tace “wataran dole zanbar iyayena da yan'uwana da qawayena na koma qarqashin mulki wani shiyasa na fara qoqarin sabarwa da kaina rayuwar kadaici" duk yanda yaso ya fahimci kalaman nata ya kasa dole ya nemi qarin bayani ta hanyar cewa ban fahimci abinda kikeso kicemin ba Samha" ajiyar zuciya tayi ta sake matse teddy bear din dake hanunta tace “ina nufin yau ta kasance rana ta musamman a rayuwata saboda yaune na bawa wani da namiji damar shigowa rayuwata ta hanyar qulla relationship na aure wanda ya kasance bakai bane Abdul nabawa Dr Mus'ab damar aurena...."
Cikin wata rikitacciyar murya yace “ya isa haka Samha banason jin wadannan munanan kalaman naki da suke neman tarwatsamin zuciya" harga Allah taji babu dadi amma data tuna irin wulaqancin daya rinqayi mata tsayin shekaru yana jizgata sai kawai ta share taci gaba da harkokonta zuciyarta cunkushe da damuwa.
Kwana biyu tsakani iyayen Mus'ab sukazo suka nema masa aurenta Dad yaji dadi kuma yasawa abin albarka suka tsayar da lkcn aurensu wata bakwai shima saboda service din da zasu tafi da bazaisa samada wata biyu ba wai ranar Dr Mus'ab kamar ya goyata saboda farin ciki yana wani marairaice mata waishi babu don babu yanda zaiyi ne amma lkcn yayi masa tsayi tayi dariya cike da tausayinsa tace “saurin me kakeyi Yallabai abinda baasa masa lkc bama zuwa yake ya wucce balle wanda aka sanyawa lkc tasha fama dashi kafin ya qyaleta ta kwanta da sharadin gobe shine zaizo ya taho da ita gurin Indection din.
Da asuba wayarsa ce ta tasheta ta daga ta kara a kunnenta tayi sallama ya sauke wata ajiyar zuciya yace “Wayyoh My love wannan sexy voice din take sumar dani zatayi" murmushi tayi tace “bancika son tsokana bafa” yayi dariya yace “babu tsokana gsky ce Allah my love duk lkcn dana ganki sai naji yanayina ya sauya dalilin da yasa na taba kiranki nayi miki nasiha akan ki rinqa suturtamin jikinki amma kika rufe idonki kika cinyemin mutunci tsaf" dariya tayi tace “kayy Sir nice na cinye maka mutuncin inama na ganshi balle na cinyeshi?" Dariya sukayi sosai yace “bazaki gane ba sai ranar da kika jiki a qasana Ina sukuwa a kanki sannan zaki fahimci inda nake Samha inasonki aduk yanda kike" duk sanda ya furta mata kalmar nan sai jikinta yayi sanyi tausayinsa da tausayin kanta abinda wanda takeso ya kasa yi mata a kenan sadaukarwar da Abdul ya kasa yimata a rayuwa kenan gata Dr Mus'ab yayi mata yana sonta a duk yanda take kalmarsa kenan kullum.
Wasu hawaye ne suka zubo mata tace “yaushe zaka taho?" Ya fahimci damuwa a muryarta don haka ya saisaita murya yace “yanzu wanka kawai zanyi na taho amma naji damuwa a muryarki meye ya kawota cikin rayuwar matata?" Ajiyar zuciya tayi tace “soyayyarka gareni itace take sanyayamin jiki da kuma bani mamaki ka tayani da addu'a Allah yasa nasoka kamar yanda kake sona Sir" numfashi ya sauke yace “ta daina baki mamaki kinji my wife ganinan zuwa yanzu ki tanadarmin breakfast dakanki nakeso kiyimin saboda ki fara samun ladan aure tun yanzu" murmushi tayi tace “angama ranka ya dade" sukayi dariya tare da ajiye wayoyin a tare.......
. *UMMUH HAIRAN CE...* ✍🏻
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*
*15*
9:00am Mus'ab ya sauka a garin Abuja lkcn ta gama shirya masa breakfast din a dinning din falon baqi ta koma dakinta tayi wanka ta sheqa kwalliyar ta cikin wani Lagos less purple mai masifar kyau da tsada wanda akayiwa dinkin riga da siket tayi kyau matuqa Mamy ce ta daura mara dankwali ta yafa mayafi purple komai nata purple ne Idan kuka dauke sarqa da dan kunnen azurfar datasa ta dauki zobbanta tasa ta dubi yatsunta wanda Abdul yasa mata ranar da zasu rabu shita zubawa ido tana kallonsa tana tuno kalamansa na rana Samha ki qaddara a ranki yayanki Abdul yana sonki komai nufine na Allah amma inaji a jikina zamu rayu cikin inuwa daya koban aureki yanzu ba wataran zamu kasance tare tabbas alaqata dake bazata tashi a banza ba akwai wani boyayyan abu tsakaninmu damu bamu sani ba"
Shigowar Mamy ne yasata janye idonta daga kan zoben ta janyota jikinta tace “dana yana jiranki a parlourn baqi yanzu idan kin tafi shikenan sai munzo Imo State gurinki zanyi missing dinki Pretty amma babu komai watarana ma sainayi watanni banganki ba kinacan gurin mijinki ko?" Ta fada tana dago mata da fuskarta sukayi murmushi lkc daya tare dayiwa juna kiss ta kama hanunta suka fita ita ta yafa mata mayafin sannan tayi murmushi tace “masha Allah kyakkyawata Allah yaci gaba da tsaremin ke kinji ki kula don Allah banason qawance da yayan talakawa da zasu dora miki ciwon kai"
Itadai daga kai kawai tayi tarasa meyasa Mamynta bata qaunar talaka bayan tasani har baban Mamy ya rasu wato kakanta a gdan darni suke a Maiduguri sai bayan rasuwarsa Dad ya gyara musu gdansu.
Shiga parlourn tayi da sallamarta ya dago fuskarsa ya zuba mata ido yana murmushi yace “masha Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan mata tawa kyakkyawa" murmushi tayi tayi qasa ta rusuna tace “ina kwana" dariya abin ya bashi sosai wai yau shi Mus'ab shine Samha take yima ladabi haka kamar wani ubanta harda rusunawa ta gaisheshi.
Dagota yayi yana murmushi ta zuba masa ido yana da kyau daidai nashi shima yanada haske da manyan idanu saidai bashi da dogon hancin sosai lebensa yanada dan fadi kadan baqi sosai kamar wanda yakeshan sigari amma halitta ce hakan don ko ashana bai taba qartawa ya zuqa ba lumshe idonta tayi tare da janyewa ta koma ta zauna tana hango fuskar Abdul dinta fari tas kyakkyawa me yalwar dogon hanci da qananun lumsassun idanu lebensa jane sosai sai gashin girarsa me gazarzar yanada zara-zaran gashin ido irin nata saidai ita idanunta manya ne.
Iskar da taji ya hura mata a idanunta ne yasata dawowa hayyacinta tayi ajiyar zuciya tare da jan flat ta fara zuba masa cheeps din ta hada masa ta zuba masa kunun mardan da Mamy tayi masa ta tura masa ya dauka yakai mata bakinta noqe kafada tayi yayi murmushi ya fara cin abincin yana yabawa da dadinsa shigowar Dad ne yasata miqewa ta nufeshi ya buda mata hanunsa ta shiga yayi kissing tsakiyar kanta yace “zamu tafi saikun taho mu mota zamu hau" ajiyar zuciya tayi tace “shikenan Dad zamu rigaku zuwa yau zakaga My Abdul dina" murmushi yayi ya kalli Mus'ab daya lura mgnr tata batayi masa dadi ba yace “ai yace bazai samu damar zuwa ba munyi waya dashi jiya yayan naki akwai shiririta" yana fadin haka ya fice.
Suna gama cin abincin suka miqe driver yakaisu airport suka hau jirgi sai Kanon dabo suna zuwa driven gdansu Dr Mus'ab yazo ya daukesu suka nufi cikin makarantar kamar hadin baki shima Abdul sun shigo shida Manson shine yake driving din zuciyarsa tana cike da farin cikin ganin Samhar saboda mugun kewarta yakeyi da tarin maganganu a bakinsa da shikadai yasan irinsu lkc daya motocin sukayi parking hakanan yaji gabansa yana faduwa ya zuba idanunsa kan motar da tayi parking kusa da tasu Dr Mus'ab ya bude ya fito yana dariya ya zagaya ta saitin inda Samha take ya bude mata gaban Abdul ya qara bada wani rass yana kallon qafarta data fara zurowa kafin daga bisani ta fito gaba dayanta wata uwar zabura yayi yace “Sam...Samha itace wlh Samha ce Mansoor da gaske auren mutumin nan zatayi?" Wani uban tsaki Manson yaja yace.
“To Ina ruwanka da wanda zata aura tunda dai bakai bane Mainah Abdu kace bakaso ta hqr ta cireka daga zuciyarta har ta bawa wanda yake sonta dama ya fito zasuyi auransu na qauna don Allah dubesu fah kai salon bai burgeka ba da gani kasan Allah yayi mawa yarinyar nan sauyi...." Wani uban mari ya zafga masa yace “zanci durun uwarka Mansoor ficemin daga mota ka fice nace...." Dariya sosai Manson yake ya bude motar ya rufe masa ya leqa ta window yace “kadai bi a sannu matar wani ce tariga tayi maka nisa" kifa kansa yayi a sitiyarin yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un oh my God" yana mgnr zuciyarsa na wani irin tiriri gashin jikinsa ya wani miqe saboda bala'in kishi nandanan qananun idanunsa suka qara qanqancewa suka kada sukayi jawur jikinsa har wani rawa yakeyi.
Ita kuwa Samha tunda ta dira a farfajiyar B.U.K take rarraba ido taga ta inda Abdul zai bullo amma babushi babu alamarshi wata sabuwar qaddara lkcn dataje amsar posting letter dinta saitaga an turata Katsina daga ita har Rahmah sosai iyayenta da masoyinta Mus'ab da Rahmah sukayi murna da sauyin da aka samu saboda dama bason zuwa kudun sukeyi ba amma ita haka kawai tunda tagani gabanta yake faduwa ta rasa dalili daga qarshe dai ta alaqanta hakan da cewa saboda asalinta ne da bata sani ba sannan garin masoyinta ne “shi ko Ina aka kaishi?" Tambayar data yiwa kanta kenan amma batada amsa hakanan ta yini raba ido domin ganinsa amma yaqi bari tagansa ta wucce ta gaban motarsa yakai sau uku yana kallonta haushin ganinta da wani ya hanashi yimata mgn yasan da alqawarin da yayi mata na idan sunzo zaije su gaisa da Dad dinta saboda yanda ta nuna tanason hakan amma kishi ya hanashi cika Mata wannan alqawarin ta kirashi a waya yakai sau goma amma bai daga ba da haushi ya ishetama jifa tayi da wayar ta koma ta kwanta jikin Dad dinta tace “yaqi dagawa Dad yaqi zuwa ku gaisa Dad kace zaka Saudi don Allah kayimin dawafi Allah ya mantar dani Abdul a rayuwata kowacce alfarma na nema a gurinsa bayayimin saboda ya tsaneni" Mamy ce tace “inda kinsan yanda na tsani yaron nan Samha dakin daina mgnrsa a gabana bantabajin kince yasaki farin ciki ba kullum quntata miki yake amma dake bakida hankali kinqi mantawa dashi"
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*
*16*
Kallon Mamy tayi tace “wlh Mamy bayin kaina bane addu'a kawai nake buqata daga gareku” haka iyayenta suka hadu sukaita rarrashinta hardai suka samu ta hqr gdan da Dad ya siya a Kano anan cikin unguwar sallari nan suka sauka ita kuma Rahmah ta tafi gda kwanaki uku tsakani Dad ya gama mata shirinsu tsaf har gda sukaje suka dauki Rams suka wucce garin Katsinan dikko dakin kara kunya gareku ba tsoro ba saida Dad ya gama yi musu komai sannan sukayi sallama a kusa da camp din ya kama musu gda ya zuba musu komai na buqatar rayuwa gda sosai ya tsara musu kamar na matar aure.
Saida sukayi hutun kwana biyu sannan suka fara zuwa camp din itadai Samha tunda tazo garin Katsina take fama da faduwar gaba haka suka yini a camp din sannan sukaje makarantar da aka turasu.
Sun fara aiki gadan²