Showing 30001 words to 33000 words out of 60308 words

Chapter 11 - Adandi By Oum Hairan

15 Dec 2025

7029

ba dole sai gdanta ta koma.
Sai dare sosai suka shiga Abuja dake tafiyar mota ce suna zuwa Samha ta tarar gdan babu kowa wai Mamy ta tafi Maiduguri yar yayarta ta haihu dakinta ta shige tayi kwanciyarta duk sanda ta tuna yanzu itafa ba budurwa bace sai tayi kuka kamar ranta zai fita ta qara jawa Abdul Allah ya isa.




Haka kwanaki sukayita tafiya saida Mamy tayi sati ta dawo lkcn Samha ta qara warwarewa cima me kyau ga kulawar mahaifinta har tayi qiba tayi shar da ita babu abinda takeyi saidai tayi wanka taci abinci tayi sallah a cikin kwanakin ne Dr Mus'ab ya kirata sau daya yake fada mata zaizo zasuyi wata mgn akan shirye²n bikinsu tunda Dad ya yarda an sauko dashi yanzu haka bikin saura sati uku lkcn da yazo ta jima a daki a kwance kafin tayi qarfin halin miqewa ta fito a garden suka zauna suka gaisa tun daga yanayinta ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya kalleta sosai yace.





“Nazo da tawa damuwar kuma sai na fahimci kamar taki tafi tawa Samha meye yake faruwa ne kusan sati hudu kenan banajinki a yanayin dana saba jinki kin daina sakin jiki dani kin daina bani kulawa sai na kiraki sau uku baki dagaba meyene?" Hawayen da take boyewa ne suka gangaro mata tace “bansan wanne kallo zakayimin ba idan na fada maka ainihin abinda ya faru Mus'ab rayuwata taqi tafiya kamar yanda ta kowa take tafiya Mus'ab Abdul yayimin tabon da bazai taba gogewa a zuciyata ba na tsaneshi Mus'ab na tsani Abdul wlh na tsane don Allah Mus'ab ka janyewa aurena" dagowa yayi ya kalleta da sauri yace “kamar ya na janyewa auranki Samha?" Cikin kuka tace “ina nufin ka hqr dani kace da Dad ka fasa aurena wlh nafi buqatar rayuwa ni kadai bansan irin kallon da zakayimin ba duk ranar daka fahimci nidin ba budurwa bace wani ya lalata min budurcina ta hanyar zalumci Mus'ab don Allah kace ka fasa..." Rufe mata baki yayi memakon taga alamun bacin rai ko damuwa a tattare dashi sai taga yayi murmushi yace “abinda yasa kike qara burgeni kenan Samha qarya bata cikin tsarinki wlh tun washegarin ranar da abin ya faru aka turomin saqo da wata number da yake nunamin abinda ya faru dake a ranar saida nazo Katsina haka na gama bulayi na ban samu ganinki sai bayan na gaji na koma na kama hotel ina hutawa sannan saqo ya kuma shigowa wayata akace min dama kayi hqr Samha tayi maka nisa Samha a cikin saqon har gargadina akayi cewa kada na kuskura nace zan aureki ke matar Yariman Katsina ce sannan aka qara tabbatar min cewa harma cikinsa gareki kuma yanason kayansa nayi qoqarin bayyanawa Dad wannan saqon sai kuma naga rashin dacewar hakan saboda ya kamata ace ya zama sirrin mu saboda mune zamu rayu tare kodan rufuwar asirin yayanmu amma wani abu nima da yake damuna har yasa na sauko da aurannan namu Samha Hajiyata tace saidai na aureku ku biyu keda yar qawarta bama wannan ba Samha abu daya dana boye miki shine inada mata da yarana biyu...."





Dagowa tayi da sauri cikin tsananin mamaki tace “kana da Mata harda yara biyu amma Sir baka taba fadamin ba meyasa ka boyemin hakan..." Saurin katseta yayi da cewa “aa ba haka bane lkcn dana fara neman auranki banida mata mun rabu da ita so wata uku kenan data dawo gdana itama Hajiya ce tasa na dawo da ita wai a cewarta dana auro mata ke da muka hadu ADANDI gara na da Maryam matar data nemi kasheni kawai saboda taga hotonki a wayata".....




_Kuyi hqr da wannan sisters_ 🙈🙈


********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************



*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/13, 8:26 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




*23*




Miqewa tayi ta nufi cikin gdan yayi saurin shan gabanta yace “ki fahimceni Samha kada kiyi fushi saboda gudun irin wannan yasa na boye miki gsky" tsaya ta saurareshi ba ta shige gdan daidai lkcn da Dad da Mamy suke sakkowa daga sama Dad ya tareta da sauri yace “lfy meye ya faru Aishatu?" Cikin kuka tace “na hqr da dauren Dad wlh bazan aureshi ba Dad ya yaudareni ya munafurceni dama Abdul ya fadamin Mus'ab yana boyemin wasu abubuwa Dad kabashi kudinsa don Allah Dad kada ka takuramin na aureshi...."



Riqeta Mamy tayi tace “Waime yake faruwa ne meye ya faru tsakaninki da Mus'ab din?" Cikin kuka tace “yanada aure Mamy kuma wai mu biyu zaya aura yanzu Dad Mamy Mus'ab bashida gsky" wata uwar zabura Mamy tayi tace “yana da Mata kuma ku biyu zai aura kambu wannan rashin mutuncin ba anan ba wlh bazai yuwu ba" shikam Dad zama yayi yana nazarin abun bai iya cewa komai ba ya miqe ya fita ya tarar da Mus'ab a tsaye ya kama hanunsa yace “Aishatu tazomin da wani zance na yarinta Mus'ab mene gskyr lamarin nan?" Sunkuyar dakai yayi alamun rashin gsky ya fara sosa kai yana zayyano masa kamar yanda ya fadawa Samha gwauron numfashi Dad ya ajiye ya jinjina kai yace “shikenan kaje zan nemeka"




Yana fadin haka ya juya ya shiga gdan lkcn Samha ta shiga daki so Mamy a tsaye tanata huci ta tareshi tace “ya kukayi dashi?” ajiyar numfashi yayi yace “abinda ke akwai kenan" kallonsa ta kumayi da sauri tace “kawai ka mayar masa da kudinsa tunda dama gobe ake shirin kawo lefe sai kawai ya hada ya kaiwa waccan din amma yata bazata iya wannan auren ba Mata biyu ita ta uku ina laifinma daya ita ta biyu Ina da sake wlh da sake Dad bafa zai yuwu ba nifa idan babu dama yaronnan Na'im ya dawo satin daya wucce ma har tsaraba ya kawomin da kuma atamfofi har uku kawai ka bashi dama ya turo ayi mgnr amma wlh yata bazata taba auren irin Gdan sarautar Katsina ba na tsani ahlin Sa'eed kuma azan taba hada jinina dasu ba..."




Dafe kuncinta tayi da sauri saboda baqon abinda bata taba sani ba a gurin mijin nata ya nunata da yatsa yace “kina haukanki Lubabatu nine da dangina muke da iko da Aishatu bakeba kuma daga rana irin ta yau zan fara gwada ikona akanta bandama rashin kara irin taki harni zaki kalli tsabar idona kice bakyason dan dan'wana wanda mukazo duniya tare to bari kiji da Sa'eed da Sa'ad abu dayane kuma dole ki hqr da tsarin masarautarmu don bans tare da masarauta ba yana nufin nabarta kenan ba so Samha ta Mainah Abdu ce kuma tunda abin naki yazo da rashin mutunci wlh babu abinda zaa canza yanda akasa da Mus'ab haka zaayi da Abdu ko kinaso ko bakyaso ni dake maga wanda zaibi wani" juyawa yayi ya fice daga gdan zuciyarsa na tafasa yana fita ya kira Mai martaba ya sanar dashi abinda ke faruwa ya tura masa number waliyin Mus'ab a take Mai martaba ya kirashi ya sanar dashi shine waliyin Aishatu yanason ganinsa washegari kuwa sukaxo garin Katsina sosai sukayi mgn ta manya dole Mai martaba yace to babu komai amma fah yarinya tana neman canza raayi saboda haka suzo sati me zuwa zai daura auren Samha da Mus'ab wannan abu ba qaramin citta yabawa Mus'ab ba nandanan ya fara shirye²nsa.




Shikuwa Abdul tunda ya rasa Samha ya shiga wani hali lamarin har tsoro ya fara bawa Mai martaba duk ya susuce bashi da aiki sai kuka yaje garin Abuja yafi sau goma haka zai gama yawonsa ya dawo duk ya rame yayi baqi bashi da aiki sai tunani yakan kulle kansa a daki ya bai leqo ko farfajiyar gdan sarautar ba Fulani Amina ta shiga damuwa da lamarin dan nata da soyayya take azabtar dashi gashi baimasan inda zai samu yarinyar da yakeso ba yauma suna zaune ta kawo masa ziyara dakinsa kansa yana saman cinyarta tana shafa sumarsa tana share masa hawayen fuskarsa yace “Fulani Samha tasoni fiye da duk yanda kike tunani ta dauki amanar kanta ta bani ta yarda dani kuma ta nunamin qauna amma naqi yarda da soyayyarta gareni naqi gasqata gskyrta yanzu gashi ta tafi ta barni wlh fulani da nasan inda Samha take zanje tayimin duk hukuncin da take ganin ya dace dani indai zata aminta ta aureni wlh bazani iya rayuwa da kowacce mace ba idan ba Samha ba ita nakeso itace burina fulani naqita saboda ina tunanin bazan taba samun budurcinta ba sai gashi da kaina na rabata da budurcinta a lkcn dabai dace ba na cutar da ita yanzu kallon danakeyi mata a baya shi mijinta zaiyi mata idan ya gane itadin ba varging bace meyasa taqi ta bani damar gyara barnar da nayi da kaina?" Numfashi Fulani ta sauke tace “na fada maka kaci gaba da addu'a idan Samha rabonka ce zatazo gareka ko kai kaje amma kayi qoqarin fitar da mata kasan halin mahaifinku tunda yariga ya sakoka a gaba to saiyayi maka garama ka kawo da kanka kafin ya waiwayeka nasan yanzu hidimar bikin Gimbiya Aysha ne ya dauke masa hankali amma tabbas zai waiwayeka" ajiyar zuciya yayi ya share hawayensa yace “gobe zan sake komawa Abuja idan na dace na sameta zan dawo idan ban sameta ba zan wucce England zanyi wani aiki na wata takwas bazan fadawa Mai martaba ba saboda nasan bazai barni ba zaice sai nayi aure sannan na tafi"......





_Don Allah kuyimin hqr kaina ke ciwo Allah ya bamu alkhairi_







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/14, 9:08 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*



*24*



Washe gari tunda yayi sallar asuba bai koma gdan sarautar ba kasancewar tun dare ya hada kayansa yakai gdan Manson qarfe takwas zakara ya bashi saa yabar garin Katsina inda ya dauki hanyar Abuja zuciyarsa cike da zulumi yanabin address din da Rahmah ta bashi harya isa layinsu Samha amma saidai kashhh yana zuwa sojojin da suke gadin gdan suka tabbatar masa da sun tafi garinsu bikin Samhan saura kwanaki uku a daura mata aure rashin sani da akace yafi dare duhu ashe gda dayama suka kwana da ita kasancewar shigar dare sukayiwa birnin Dikko.



Ba qaramin girgiza yayi ba da yasamu wannan mugun lbr ya jima a zaune a cikin motar yana tunanin abinda ya dace yayi zuciyarsa na bugawa da qarfi yana Kiran sunan tare da neman agajinsa cikin gaggawa saura kwana uku auren Samha da Mus'ab? Ya tambayi kansa tare da juyawa ya nufi airport saboda baiga amfanin zamansa a 9ja ba da yake dama yayi booking bai samu matsala ba jirginsu ya tashi bayan ya kira yayansa Farooq yace yazo ya dauki motarsa a filin jirgin saman Abuja wannan kenan.


*****


A bangaren amarya Samha kuwa hidima ta kankama ta biki duk wani abu da akeyiwa amaryar gdan sarauta fulani Amina tasa anyi mata sunje lalle ita da Yasmin tare da gyaran gashi Rahmah ma tazo tare suketa kaikawon bikin qasan zuciyar Samha fal da zulumi Allah ya sani don dai shima mahaifinta umarni yakebi ne amma da babu abinda zaisa ta auri Mus'ab mutumin da ya boye mata wasu bangarori na rayuwarsa daya kamata ace ta sani.
Da wannan tunanin akaci gaba da shagalin biki itadai Samha bata wani nuna farin cikinta da auren nata Yasmin ce takeyi mata tsiya takance “wai saikace ba auren soyayya ba Princess Aysha duk kin wani takurawa kanki da koke koke ai kawa ki saki jikinki abune daya zama dole a gurin kowacce mace keda zaama keta hazo dake abar qasar dake kodai kinada wanda kikeso ne?"




Takan kada mata kai tace “aa kawai dai inajin zuciyata bata na'am da auren nan ne Yasmin" hakadai zasuyita tausarta harta dan saki jikinta aketa hidimar da ita Mamy kam tananan sai quncin rai takeyi ita a dole Gidado Sa'ad yayi mata laifi ya dauko biki ya kawo garinsu yan'uwansa sai wani gani-gani sukeyi mata shidai bai kulata ba duk da lura da rashin walwalarsa da tayi bata tambayeshi baasi ba shima bai fada mata ba.
Ana gobe daurin aure ne fah salon biki ya canza bushe² da kade kade suka qaru a gdan daga Samha har uwarta har fulani Amina da Yasmin babu wanda yasan meke faruwa kawai dai hidima suketa yi Mamy kam ko bangaren fulani Amina bata taba zuwa ba tunda sukazo fulani Amina dake mace ce me sauqin kai ko a jikinta saidai idanma wani abune ta karya billenta taje ta tambayi Mamy tana yatsina tanashan qamshi zata bata amsa bata wani damuwa tunda dama tasan ba dasawa sukeyi ba fulani Hadiza itace makira irin Mamy saboda haka tunda Mamy ta iso suka jorner kasancewar me martaba matansa biyu Fulani Amina itace babba kuma itace me Yaya hudu Mainah Abubakar shine babba sai Mainah Farooq sai Mainah Abdullah wanda suke Kira da Abdu sai kuma Gimbiya Yasmin sai fulani Hadiza itace Mata ta biyu bata taba haihuwa ba hakan ne yasa ta dauki karan tsanar duniya ta dorawa yayan gdan musamman Mainah Abdu wanda shi yafi kowa fada gurin ubansu saboda miskilancinsa da izzarsa ga uwa uba rashin barin ta kwana baya daukan raini a cikin masarauta shiyasa ya zama gagarabadau na masarauta kowa ya debo raininsa a waje yake zubarwa ciki kuwa harda Fulani Hadiza baya raga mata ko kadan shiyasa take mugun tsoronsa wannan yasa data fahimci tsananin qiyayyar Mamy gareshi dalilin marin daya taba tsinka mata tun yana yaro saboda ta zagi babarsa yasa fulani Hadiza shigewa jikinta saboda su samu damar gamawa dashi cikin sauqi.



Ranar asabar ta kama ranar daurin auren Samha da Mus'ab kamar yanda kowa ya sani qarfe 12:00pm akasa saboda dangin ango da suke da nisa ilai kuwa kamar yanda aka tsara din hakace ta kasance sha biyu daidai maroqan fada suka fara shela suna fadin “Alhmdllh zumunci yayi albarka rayuwa tai albarka a yau mun shaida daurin auren Mainah Abdallah Sa'eed Dandoki da Gimbiya Aysha Sa'ad Dandoki akan sadaki mafi daraja...”



Tashin hankali wata uwar zabura da Mamy tayi ta miqe ta qunduma wata uwar ashar tace “idan na yarda Allah ya tsinemin albarka wlh bazai taba yuwuwa ba ni Lubabatu ni zaayiwa rashin mutunci a rasa wanda zaa aurawa yata sai dan iskan fitsararren yaron nan wanda uwarsa tai cikinsa da rana aa bazai taba yuwuwa ba dole da sake bama fa zai yuwu ba" babu kunya saiga fulani Hadiza nan ta shigo da gudunta ta riqe kafadar Mamy da taketa mazari saboda bala'i tace “wai da gaskene abunda nakeji Abdallah suka bawa Ayshatu..." Cikin qunar zuciya tace “barni dasu Hadiza zanyi maganin matsiyata da daidai duk munafurcin na shegiyar matar nan ne itace take shirya komai nikam makircinta bazaiyi tasiri akaina ba da yata wlh ni Lubabatu ban haifawa Mainah Abdu matar dazai kwanta da itaba ina qaryane wlh"




Daidai lkcn Dad ya shigo parlourn yanda yaga ta nufoshi gadan² yasashi tsayawa ya zuba mata ido tana zuwa ta damqi kwalarsa tana girgiza qugu tana fadin “baka isaba Gidado wlh kayi kadan Samha yatace nice na haifeta saboda haka bazata zauna da dan iskan tujararren yaron ba dolene a warware auren nan kafin na gwada maka kalar haukana" murmushi yayi ya cire hanunsa daga wuyansa yace “to Lubabatu bismillah haukanki wanne irine ban sani ba auren Aisha da Abdullah ne yariga ya dauru babu abinda ya isa ya rabashi saboda haka kiyi hqr kawai haka Allah ya tsara" ficewa ya juya yayi ya nufi bangaren fulani Amina saboda tunda sukazo Samha tabar bangarensu ta koma can yana shiga ya tarar da ita a jikin fulani Amina a kwance tanata gursheqen kuka tana cewa “meyasa Dad zaiyimin haka meyasa bazai barni na kawo wanda nakeso da kaina ba Fulani kice su janye aurennan don Allah banaso wlh banaso bansan wacce irin karba Mainah Abdu zaiyimin ba bazai taba yarda dani ba kuma bazai taba aminta da abinda zan fada masa ba..." Dagota taji anyi ta fada jikin Dad tace Dad meyasa haka meyasa zakayimin haka Dad banasonsa meyasa zakuyimin auren dol..." Rufe mata baki taji anyi ta baya ta sake bude idonta tar ta saukeshi akan Abdul dake gyara tsaiwarsa cikin hawaye yace “qarya kike Samha kina sona don Allah ki daina furtamin wannan kalmar haka ki fahimceni ki fahimci iyayenmu"........






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/14, 3:50 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*



*25*



Kamota yayi ya rabata da jikin Dad yaa qoqarin hadata da jikinta ta turje tare da cewa “ka sakeni Abdul ka sakeni na fada maka banasonka na tsaneka macuci fasiqi azzalumi Allah ya is..." Rufe mata baki yayi ya durqushe a gabanta yana kallonta cikin tsananin damuwa yace “duk abinda zaki fada akaina na cancanta babu abinda zaki fadamin da zaikai girman kalmomin Dana fada miki a baya Samha bakida wata kalma da zaki fadamin da zata goge tabon da nayiwa rayuwarki amma Ina neman alfarmar ki daina ciwa bakya sona nasani bazaki taba daina sonaba har numfashinki na qarshe...." Qarya kake makiri munafuki qaryane kace yata bazata daina sonka ba tama daina Wlh indai nice na haifi Samha to qarya takw ta rayu dakai" cewar Mamy dake shigowa tana zuwa ta finciko hanun Samha ta dage ta sharara mata mari tace.




“Dama wannan dan iskan fitsararren tujararren yaron shine Abdul din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login