Showing 15001 words to 18000 words out of 60308 words
murya tace.
“Dama iyakar tunaninka Dr kana tunanin qaddarar haduwa dakai ce ta kawoni B.U.K matsayin dalubar Spychology? Uhm to kayi saurin sake hasashe domin falsafarka ta fada maka qarya nace qarya zuciyarka take fada maka mallam so dayane tak kuma na riga na bayar dashi ga wanda ya cancanta saboda haka kayi gaggawar mayar da kalamanka inda ka fito dasu na barka dasu basu da guri a zuciyata”
Tana kaiwa nan ta juya ta fice da sauri tana hada numfashi kusan a makance take tafiyar har tazo daidai faculty dinsu Abdul din haka kawai zuciyarta ta rinqa umartarta data shiga koda zai daketa batare da tsayawa shawarar me hakan zai haifar Mata ba ta nufi cikin gurin zuciyarta na bugawa da qarfi kan wata kujera ta hangeshi shida abokansa ya dora hanunsa a kansa kamar wanda ya tafi duniyar tunani.
A nutse ta qarasa tare dayi musu sallama suka amsa mata tare da kallonta ta fahimci kallon da sukeyi Mata na tausayi ne amma banda Nasir data fahimci kallon mara zuciya yakeyi mata murmushi tayi saboda ita kanta batasan bata da zuciya ba sai akan Abdul tace “kuyi hqr ko zaku iya bani aron abokinku don Allah" murmushi Ja'afar yayi yace “keda mijinki waye zai shiga tsakaninku yaji kunya"
Maye gurbin inda Ja'afar ya tashi tayi tare da saisaita muryarta tace “My Abdul" sauke hanunsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya ya zuba fararen qananun idanuwansa a kanta qasa tayi da idonta wasu hawaye nasu zafi suka zubo mata tayi qarfin halin cewa.
“Ya jikinka dazu Rahmah take fadamin kayi fama da ciwon kai" a gajarce ya amsa da cewa “da sauqi yana qoqarin tashi ta ruqo hanunsa bata damu da irin kallon da yake Mata ba tace “bazanyi maka dole kasoni ba My Abdul amma nasani ko bayan Raina idan soyayyarka tayi nasarar halakani zakake tunawa dani a matsayin masoyiya ta haqiqa wadda ta qaunaceka domin Allah na yarda da naqasun tarbiyyata daya zamemin katanga da samun farin cikina na yarda ban cancanci zama matarka ba kamar yanda ka fada amma inaso koda zaka yanke alaqa dani din girman Allah ka cireni daga matsayin daka ajiyeni wlh niba karuwa bace bantaba zina ba ka yarda dan...."
Fuzge hanunsa yayi yana qara maida hankalinsa ga kallonta yace “taya zan gasqataki Samha bayan kina shaye² nasani kuma maye babu abinda baya sanyawa shiyasa aka haramtawa duk wani musulmi na qwarai shan wani abu da zai gusar masa da hankali Samha kiyi gaggawar cire mgnr so tsakanin mu idan ba hakaba zan yanke igiyar zumuncin dake tsakanina dake kuma kamar yanda na fada miki a farko abokaina sune suka roqeni naci gaba da zama a matsayin yayanki kuma malaminki kamar yanda kika buqata" cikin kuka me ciwo tace “hakan ma na gde indai zan sanyaka farin ciki to zanyi biyayya ga umarninka koda kuwa zan rasa duk wani haske na rayuwata amma Ina neman alfarmar kaci gaba da zama a matsayinka na malamina kuma yayana My Abdul jahilcina ga abinda ya shafi addinina shine ya haifarmin da shiga halin da nake ciki a yanzu don Allah kada kabada qofar da wannan tawayar zaisa wani yaqi qanwarka kamar yanda kaima kaqini My Abdul please..."
Sosai kalaman nata na qarshe suka daki zuciyarsa zuba mata ido yayi yanason gano aibin yarinyar da zuciyarsa taqi amsarta a matsayin abokiyar rayuwa yanda take kukan riqe da qafarsa ya sanyashi jin wani mugun tausayinta baisan sanda ya sanya hanunsa ya dagota ba yasa yatsansa ya share mata hawayen yace.
“Insha Allah bazan gaza ta wannan bangaren ba kinji qanwata" daga masa kai tayi tace “na gde da hakanma"
Tana fadin haka ta juya ta fice daga faculty din yabi bayanta da kallo zuciyarsa na bugawa da qarfi yanajin ninkin tausayin yarinyar a zuciyarsa tabbas da zai iya daya daya karbi soyayyarta amma yasan bazai taba iya auren macen da tasan maza ba yanada yaqinin qaryane abinda take fada masa na cewa bata taba zina ba.
Daqyar ya iya daga qafarsa ya nufi teather din da zasuyi lecture ya zauna Mansoor ya kalla yace “tausayin yarinyar nan yana neman karyamin burget Manson wlh dazan iya dana karbi soyayyarta amma bazan iyaba bazan iyaba Manson” Khamal ne ya magantu da cewa “tausayi matakin farko ne na so Abdul na tabbata abinda kakeji game da Samha ya wucce tausayi ko ka yarda ko kada ka yarda zuciyarka ta kamu da son yarinyar nan" miqewa yayi zai fita Khamal ya ruqosa yace “ba dole nace ka yarda ba amma ni na sani kanasonta...."
Daga masa hanu yayi yace “ya isa Khamal nagaji da sauraron wadannan yan iskan kalaman naka me zanyi da ita Khamal idan na amince da wannan ballagazar yarinyar me zata bani me zan karba a gurinta da zai zamemin abinda zanke dubawa nayi farin ciki a darenmu na farko babu ta rabar muku komai Khamal qila kaima ka taba dandana ko dolene a gurina na zabawa yayana uwa tagari mezan fada musu idan suka taso sukaji tarihin uwarsu karma akai ganan wlh tallahi Khamal ba Samha danasan halinta ba ko watace da bansanta ba na aura nakai mata samartaka ta nikuma najita ba budurwa ba wlh a daren saina yanke igiyoyin aurena uku a kanta ko wacece ita to kuma menene zaisa nayi abinda zai dameni ina sane"
Yana fadin haka ya juya ya zai fice daga Hall din Ja'afar ne ya daga murya yace “dama nasan tunaninka kenan Abdullah amma ka sani sona gsky baya duba cancanta akan dauko mace ADANDI ma a sata tayi istubura'i kuma a aureta a zauna da ita zama na soyayya balle Samha da duk wanda ya kwana ya tashi a skull dinnan yasan bata zina"......
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*
*13*
Jinjna masa kai tayi cikin qoqarin sanyawa zuciyarta dangana Abdul bazai taba sonta ba bazai taba tausayinta ba balle tasaran zai bata soyayyarsa zuwa yanzu ya kamata tayiwa kanta fada ta hqr da soyayyar da babu nasara a cikinta shekara kusan biyu kenan tana fama dashi amma yaqi bata hadin kai janye jikinta tayi daga nasa ta koma ta kwanta tace “shikenan kaje na gde" cikin tsananin mamaki yake kallonta miqewa ta kumayi ta qarasa gabansa tace.
“Kaje nace Abdullah na gde da gundummawarka cikin rayuwata na gde da taimakonka gareni zanyi yanda kakeso duk da nasan zuciyata bazata taba daina sonka ba saboda Kaine na farko dataso kuma takeso har abada amma zanyi qoqarin samun madadinka wanda zai soni saboda da Allah wanda zai qaunaceni domin Allah zai zauna dani a yanda nake kuma zai karbeni da raunina Abdul bazan fasa fada maka ba inasonka amma qaramar qwaqwalwarka ta kasa fahimtar bambamcin karuwa da yar maye nasani a baya nidin yar maye ce shekara biyu data wucce amma bazan fasa sanar dakai niba karuwa bace bantaba zina ba kuma ko badon kaiba Ina neman Allah ya tsareni daga gareta kamar yanda kake ganin kai wayonka da dabarar ka ne ya tsareka daga rudin zamani uhm Abdul wayo ko dabara bai Isa ya tseratar dakai ba Allah ne ya tsareka nima kuma tsarewarsa nake nema kuma Ina qara gde masa daya tsareni kuma ya tsaremin zuciyata duk da tantiranci na na tsare addinina tun kafin na gama fahimtarsa na gde Abdul ficemin daga daki ka ficemin daga gda banson ganinka Abdul..."
Tana kaiwa nan ta zube a gurin tana wani irin kuka me ban tausayi daqyar ya iya bude bakinsa zaiyi mgn ta daga masa hanu tace “banason jin komai daga gareka ka fita a dakina nace" a matuqar sanyaye ya juya ya fita daga dakin cikin tashin hankalin da baisan meye ya kawo masa shiba daqyar ya iya mayar da kansa makarantar yana zuwa ya shige dakinsa ya kwanta a katifarsa yana fitar da wata iska me zafi a bakinsa ransa mugun ciwo yakeyi zuwa yanzu ya fara yarda yanason Samha to amma yasan koda ya aureta bazai iya yimata adalci ba saboda zaike kallonta a matsayin wadda tayi kantafi da mutuncinta har ya zube tayiwa maza da yawa abinda zatake yimasa a matsayinsa na mijinta.
Saurin miqewa yayi yana jinjina kai yace “ina wlh bama zai yuwu ba kawai kuma sai ake kallona matsayin mijin karuwa ballagaza wadda ta gama tallan kanta da surarta ga wasu mazan ga mazan kwararo? Sake kwanciya yayi yana tuna yanda ya tarar da ita kwance a dakinta yana raya cewa “bafa nine na farko dana fara ganinta a haka ba maza da yawa sun ganta a haka kafin ni yanayin yanda surarta take da kyauwun kallo na sani babu namijin da zai ganta a haka ya kawar da kansa kamar yanda nayi qoqarin hadiye tawa qwalamar maza da yawa sun dade sunajin abinda nakeji yanzu game da ita" da wannan tunanin yayi qoqarin samawa zuciyarsa salama ta hanyar daukar system dinsa ya fara duba aikin project dinsa.
Cikin yan watannin kawunan dalubai ya dauki charge sosai tayi iyakar qoqarinta wajen ganin ta tursasa zucciyarta wajen cire Abdullah a cikinta amma ta kasa duk da haka tayi namijin qoqarin tursasa gangar jikinta yimata biyayya wajen qauracewa duk wani abu dazai hadasu koda kuwa sun hadu to iyakarsu gaisuwa yanason janta da hira amma babu fuska ya lura gaisuwar ma tanayine saboda musulumci daya hadasu babu yanda zatayi dashi.
Matakin sam baiyi masa dadi ba sosai yake azabtuwa tare dajin zafin abinda takeyi masa gajiya yayi da zaman doya da manjan da sukeyi ya yanke shawarar zuwa ya bata hqr suyi abota kamar yanda ta buqata tun farko yaqi amincewa.
Koda yaje ma bata saurareshi ba tace masa tana da uzuri baiyi tsammanin haka daga gareta ba ranar har hawayen takaici yayi yarasa meyasa rashin yarinyar ya addabi zuciyarsa Mansoor ne ya dubeshi yace “Sone Abdullah ko ka yarda ko kada ka yarda kanason Samha kaba dakai bori ya hau kaqi Ina qara tabbatar maka Idan ka sake Samha ta kufce maka haqqinta zai dade yana bibiyarka saboda kaqi tausayinta kaqi yimata adalci sannan zaka dade kana kukan zuci harma dana fili wlh samun masoyiya irin Samha a zamanin nan abune me wahalar gaske ka cire kishi ka kalli gaskiya da maslahar taka rayuwar Abdul dan'uwa nane kai kuma abokina tunda muka taso kake haduwa da mata masoyanka amma bantaba ganin soyayya irinta Samha ba batasanka ba batasan waye kai ba kawai nagartarka da kyawawan dabi'unka sune suka fara daukar hankalinta harta fada soyayyarka sannan a lkcn da tauraruwarta take haskawa kaf new site sunanta ake ambato mgnrta akeyi manya da yara a daidai lkcn ka fado rayuwarta ka canzata cikin qanqanin lkc ka mayar da ita nutsattsiyar mace take binka sauda qafa duk abinda kakeso shi takeso koda baiyi Mata dadiba bazata taba nuna maka ba kawai don kada ranka ya baci haba Abdul ai Samha ta cancanci yafiya daga gareka koda kuwa abinda kake zarginta dashi gaske ne ta aikata”
Wasu hawaye ya dauke masu dumi bai taba tunanin Samha zata canza masa lkc daya haka ba yace “nasan inajin sonta a zuciyata amma kishinta yana damuna fiye da sonta Manson bazan iya zama da ita ba a duk sanda na tuna Samha a baya matar kowace nakanji wani kunci a cikin zuciyata naji dama banzo B.U.K ba England na tafi nayi karatuna acan" miqewa Mansoor yayi yace “tawayarka kenan a rayuwa kishi da zargi amma ni nasan duk munin halin mutum baya rasa hali daya na yabo Samha tanada uku kyawawa na yarda batasan namiji ba saboda ni nasan mata duk macen da tasan namiji kana kallonta zaka ganeta Samha bata less sannan Samha bata qarya shiyasa ake cewa tanada wauta saboda bata iya boye boye ba idan tayi abu kai tsaye zatace tayi koda kuwa zaa kasheta Idan batayi ba kuwa bazata taba amsa tayi ba na yarda da ita dari bisa dari kaini inajin Samha fa a jinina wlh wani lkcn har fusgar kama sukemin da Yasmin qanwarka"
Lamarin Dr Mus'ab kuwa yananan akan bakansa kullum sabon salon qauna yake bullo Mata dashi tun bata kulashi hardai ta fara saukowa tana sauraron sa saboda tausayi yake bata batason wahalar dashi kamar yanda Abdul yake wahalar da ita a haka sukayi final Exams dinsu cike da farin ciki zuciyoyin dalubai sunata daukan hotuna wasu suna yiwa juna alqawarin zasu hadu a bautar qasa amma banda Samha da Abdul itakam tunda ta fito daga Hall din da sukayi Exam ta nufi motarta ta shiga ta kifa kanta a sitiyari tana kukanta me ciwo tana kiran sunan Allah"
Shima cikin tashin hankali ya fito daga nasu Hall din ya nufi nasu Samha saboda ko a pepar sa bai rubutu abin arziqi ba har booklet aka canza masa saboda na farko yana tashi inda zaisa admission number sa sunan Samha ya rattaba daqyar aka canza masa yayi abinda yazo kansa ya fita da sauri daga abokansa har supervisor din sun fahimci baya cikin nutsuwarsa yana fita yaje ya tsaya a Hall dinsu Samhar Zainab ke fada masa ta fita tun dazu nan fa ya kama zagaya faculty din har yayi katarin ganin motarta ya nufi gurin da sauri ya bude motar ya shiga bataji shigowarsa ba saida yakai hanunsa ya dago fuskarta yaga yanda idonta ya kada yayi jawur gabansa ya fadi yayi saurin fadin “ya salam ki...kiyi hqr Samha wlh Abdullah yana sonki Samha banason muyi irin wannan rabuwar dake bamu da tabbacin sake haduwa ki yafemin abubuwan da suka faru wlh da idana iko da zuciyata da tuni na cire Mata zargi da kishin da takeyi akanki ta karbeki ta aminta tayi rayuwa dake amma kisa a ranki yayanki Abdul yana sonki"
Yana fadin haka ya dora bakinsa saman nata ya tura harshensa cikin bakinta yana zaqulo nata harshen ta rintse idonta tana qoqarin qwacewa amma yaqi barinta ta qwace din yaci gaba da tsotsar bakinta yanajin wani tausayi da qaunarta na kwaranya a zuciyarsa bai ankara da abinda yakeyi ba saida yaji shassheqar kukanta yayi saurin janye bakinsa daga nata ya matso sosai ya hadata da jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali cikin wata kasalalliyar murya yace “ina tare dake har abada My Samha ki qaddara komai nufine na Allah shikadai yasan meye ya boye tsakanin mu Samha ko ban aureki yanzu ba inaji a jikina zamu zauna inuwa daya inaji a jikina akwai wani boyayyen sirri tsakanin mu damu bamu sani ba"
Yana mgnr muryarsa na rawa yanyewa tayi daga jikinsa ta jingina da kujerar tanaci gaba da kukanta mgn takeson yi amma ta kasa haka har Rahmah tazo ta riskesu ya cire wani zoben azurfa dake qaramin yatsansa ya kama yatsanta na tsakiya ya sanya mata ya bude motar da sauri ya fice ya nufi tasa motar ya shiga bikin graduation din da dukansu babu wanda yayi kenan ficewa sukayi daga makarantar zuciyoyinsu cike da zulumi abun da ya faru tsakaninsu ya kasa gogewa a zuciyoyinsu idan ya rintse idonsa hangosa yake rungume da ita yana tsotsar Sweet lips dinta.
A ranar yabar Kano ya wucce garinsu Katsina har sukaje baiyiwa Mansoor magana ba ya kifa kansa a tsakanin cinyoyinsa zuciyarsa sai tafasa takeyi yanajin haushin kansa.
Itama Samha a ranar Dad dinta yazo ya tafi da ita a mota suka tafi yanata satar kallon yar tasa ta rame sosai tayi baqi gashi kana kallonta kasan tana cikin damuwa bai takura Mata da tambaya ba har suka isa gdan ta shige bangarenta ta kudundune saboda sanyin da takeji akan lamarin daya shafi Abdul babu wuya zazzabi ya rufeta Mamy ce ta shigo ta zuba mata ido bayan ta yaye bargon data rufe jikinta dashi wani takaici ya kamata tace “kin hadu da shiga uku kuwa Pretty akan wani dan iskan almajirin yaro kin dorawa kanki hawan jini idan zuciyarki ta buga ai kin huta to waima meye wannan sakaran yaron yafi Na'im ne Na'im dan gata kamarke dan arziqi gdansu gdan arziqi ki fita a arziqi ki komawa arziqi amma kin tsaya kina wahalar da kanki akan mutumin da baisan darajarki ba" miqewa tayi zaune tace “yace yana sona Mamy don Allah ki dubani ki gani nasan namijine bansan ya zanyi na gane ba Mamy bantaba zina ba amma Abdul yaqi yarda Mamy kinsan bambamcin Varging da Disvarging don Allah ki dubani Mamy ki gani wlh idan har ni ba budurwa bace na hqr da Abdul har abada amma idan ni budurwa ce zanci gaba da adana budurcina saiya karbeshi da kansa Mamy wlh bantaba sex ba ko Na'im da yaso yin sex dani qi nayi saboda burina na kaiwa mijina budurcina amma Abdullah yace banida shi......."
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*
14
Kallonta Mamy takeyi cikin tsananin mamaki da tsoro tace “au cewa yayi keba Varging bace to ubansa ne ya budamin ke da zaice keba Varging bace kinga Samha ki rufawa kanki asiri kifita daga sabgar taqadirin yaron nan idanma bazaki auri Na'im ba to kibawa malaminki dama yazo kigani idan yayi miki mana ki manta dashi nifa banga ribar son abinda baya sonka ba" tana gama fada mata haka ta miqe ta fice ita kuma taci gaba da kukanta sai dare sannan ta fitar parlourn Dad dinta ta tarar zaune yana aiki a system dinsa ta zauna kusa dashi ta dora kanta a kafadarsa tace “Dad ko missing dina ma bakace kayi ba"
Murmushi yayi ya tallafo fuskarta yayi kissing kuncinta yace “nayi missing dinki sosai daughter love amma kece naga kamar bakiyi murna da dawowa garemu ba jiya naje Katsina naga yan'uwanki Yarima Farooq yanata tambayarki nace kina mkranta shine yace idan ya dawo daga Rasha zasuzo da Mainah Abdu tunda shima ya gama project din daya kaishi Kano ne ko Kaduna tsakanin B.U.K da A.B.U dai yake kinsan dake jami'in leqen asiri ne na qasar England amma yana musu aiki anan yafi yi musu aiki a makarantu cikin dalubai yakan samu department din da yakeso yayi register dasu ya shiga a matsayin