Showing 36001 words to 39000 words out of 59144 words
Chapter 13 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel
don shima badao kyau ba don a wurin shi subira ta dauko kyau
Yace mata you can pay me now Hurriya tsotsar bakinta tayi sannan tace I don’t have anything to pay for now sarki Faizan cewa yayi just promise me with anything i ask daga mashi kai kawai tayi cewa yayi be my friend kallonshi tayi mamaki fal a fuskarta amman babban mutum zai zama friend dinta girgiza mashi kai tayi alamar aa sai yace mata you already promised me,so you can’t take back your words
Zama yayi a swing din dake opposite dinta sannan yace mata kada ki damu I can be a father and also a friend at the same time daga mashi kai tayi Because he doesn’t look like someone da zai iya cutar da ita saidai batasan cewar sarkine zaune da kanshi
Fira ya rinka janta dashi saidai abun mamaki bai taba ganin miskilin mutum irinta ba ta bashi duka attention dinta Amman hardly yaji tayi magana amman tabbas hankalita na akanshi kuma tanajin duk abinda yake fada saida bata cika magana ba,
Saida firan yazo karshe tukuna ya farajin maganarta jefi jefi ta fahimce shi sosai ta magana ,kamar yana fama da damuwowi dayawa she knew alot of people like them they just need a shoulder to cry and a friend to rely on,she understands all the pain that he’s going through ,ta conversation dinsu shiyasa ta rinka kokari wurin tana taya shi magana.
Sun dade suna magana saida call ya rinka shigowa wayar sarki Faizan non stop saidai yaki dauka Hurriya tace ya dauki wayar sai yaki ganin haka tayi mashi Bankwana may be he needs his privacy but trying to be kind itakam ina ruwanta
Koda tabar garden din ba inda ta nufa sai dakinsu don duk yau bataje ba kada hankalisu ya tashi don tasan halinsu da sanya ma rai abu hada wasba kullum Hurriya takan zauna tayi tunanin yanda ta canza sosai kamar ba ita ba she réa do change alot don da bata barin damuwar kowa ya dameta ba abinda ta Sani irin kanta amman yanzu komai ya canza ba kamar da ba
Galadima ne yake kiran sarki Faizan wanda baijin dadin hakan ba don ya kashe mashi firar da yake da his little fairy cikin tashin hankali Galadima yace aikin wuka yayi aike yace muyi sauri mu gano wannan yarinyar saboda masu nemanta sun yawaita gab wani abu yake da niyyar faruwa sannan kuma ya bada sako a fada maka Khalifa yana gani
Sarki faizan wani irin fargaba da zullumi da tsoro kawai ya shiga abubuwa sunyi mashi yawo damuwa itace kullum abinda yake kwana yake tashi da ita kamar ya fashe da kuka yakeji kamar ya hakura yabar ma Khalifha sarautar kowa ma ya huta haka yakeji.saida ya dade kafin yayi magana sannan ahankali cikin yanayi na nagaji Sosai daga wannan sai wannan yace ma Galadima ku nemota ai akwai zanen tatoo din ko?Galadima cike da girmamawa yace ehhh sannan sukayi ban kwana
Galadima wasu irin manya manya security’s da dogarai ya tara kamar za’aje wani fada ko yaki sannan suka nufi cikin masarautar inda masu aiki suke da niyyar neman Hurriya Faisait Hamood.
Page 60
Manage this page please banajin dadi sosai
Banda ina lillahi wa'inna ilahi raji'un ba abinda inna hanne takeyi a kitchen don yanzu taji abinda haule reza take fada wai ana neman wata yarinya Saidai ta jikinta kawai za'a iya ganeta saboda zanen dake jikinta tabb hmmmm inji haule baku ga abin ba kamar yaki ko kuma nace sata don runduna guda suke yawo da ita
Inna hanne banda salati ba abinda takeyi don tasan anzo wurin da ba'ason azo, Hurriya na cikin matsala don ta tabbata ita ake neman wannan wani irin tashin hankali ne da ba'a sanya mashi rana subahallah kawai take fada don ta kasa cigaba da motsa shinkafar dake kan wuta banda kai da kawo ba abinda takeyi hasbunallahu wani'imal wakeel kawai take karantawa ita yanzu mafita kawai take nema wadda zata iya fidda Hurriya daga masarautar saidai a bakin haule taji ance curfew akeyi baza ashigo masarautar ba sannan baza'a fita ba toh minene ma fita.
Saurin karasa abincin da takeyi tayi sannan ta fito daga kitchen din da wani irin sauri don yanzu ba abinda take bukata irin taga hurriya don haka dakinsu ta zarce aiko sai cin karo tayi da Hurriya wadda take kwance hankali kwance don tayi crossing legs dinta hannunta biyu ta dora saman kanta ta baya gashinta ya kwanta sai wani uban flat tummy dinta wanda mutum zai dade yana tunanin ina abincin da takeci? don cikin a shafe yake flat dinshi fuskarta na fidda wani kyau na bacci wato sleeping beauty
Inna hanne cikin wani mugun firgici tazo tana kallon Hurriya da take kwance alamar bata da wata matsala a duniyar don ana cikin wannan halin tana bacci kallon Hurriya take da wani irin mugun tausayinta tana mamakin yadda karamar yarinyar kamar ta har take iya rayuwa a ko wani hali na rayuwa abubuwa sosai sun faru da ita a rayuwa wanda idan har mutum yanada karanci Imani Amman she’s always strong babu abinda ke girgizata ko ya tsorata ta. Inna hanne cikin dubara ta samu tabar wurin Hurriya don batasan ta tasheta a barcin.
Hurriya a hankali ta bude idanunta wanda suke nuna alama ta gajiyawa wai ita har yaushe zatayi rayuwa irinta ko wani dan mutum miye ta tsare ma mutanen da sunki su rabu da ita a rayuwarta shiru tayi tsoro da fargaba duk ya cikata don ta hango storm din dake akwai nan gaba ako da yaushe tana mamakin yadda za’ace wai mutumin da bai san Allah ba wanda kuma ta kanji cewar babu wanda yasan gaibu sai Allah a wurin babanta yana yawan fadar haka sai kuma ace mutumin da baisan Allah baisan komai ba yazo ya Gaya maku abinda zai faru sannan ku yarda don takanyi wannan tunanin so dayawa a rayuwarta kuma hakan yana bata mata rai.
Sai dai fa she made a vowed she promised to protect herself no matter what bazata taba bari wani yasan itace Hurriya ba koda kam za’a kasheta tagaji tagajei she’s tired of these things abinda tafi bukata yanzu rayuwarta shine ta huta ta manta da duk wata damuwa a rayuwarta tayi moving on she deserve to be happy again ya kamata ace itama tayi farin ciki kamar kowa saidai yanzu tunaninta bai fi ta yanda zata fara ba kuma ya zatayi ta magance komai don zuciyarta na gaya mata asirinta ya kusa tonuwa don wani irin feelings takeji irin wanda ta rinka jinshi kwanakin baya tayi tunanin cewar kafin matsala ta afka mata zata iya tsere ma matsala but everything seems inevitable don tanajin a jikinta kota tsira ko kuma ta durmiye saidai abu daya tasani insha Allah zata tsira sunanta fa Hurriya Faisait Hamood the one and only Hurriya Faisait Hamood from heral palace and masarautar Qamar she can survive this
Bintu ne suka shigo tareda wasba sai hamma wasba takeyi Bintu ta kalli Hurriya wadda ta kalli gabas.
Page 61
Bintu shiru tayi tana kallom yanayin Hurriya Mai tsoratawar don idanunta sunyi sanyi kamar banata ba kodai batada lafiya ne shine abinda Bintu take fada aranta cikin kulawa tace sannu Hurriya naga kamar bakida lafiya ne shiru Hurriya tayi mata ta tashi ta fita Bintu murmushi tayi saboda hakan ba bakon abu bane a wurin Hurriya wasba ma shiru tayi don sai taji wani iri da taga Hurriya cikin wani yanayi Dukansu zama sukayi sukayi shiru suna kallon juna
Hurriya kam inda take wanki da can taje ta zauna tana wasa da icce tana kallon nature a masarautar masu sanya mutane nishadi ahankali ahankali ta saki ranta she believe that they will never get what they want from her after all ita fa jikar Hamood ce
Rashin mutumci kawai su Galadima sukeyi don da manya manya Guards wadanda suka kasance abun shakka ko wanne da bindigu acikinsu sai dogarawa wanda hannun su ke rike da zabgegiyar dorina fuskarsu babu wani annuri bare alamar sauki
Sai manya mata wadanda suka kasance suke yawo tare dasu wanda suma dai babu sauki a tattare dasu koda ga kallonsu , su jakadiyya sune ke wani irin bincike mata tareda wulakanci da rashin sanin darajar yan mata don sai mutum ya cire kayanshi dagashi sai zani sannan a duba bayanshi agaban mazan daman bayan kawai ake dubawa don boka ya fadi inda za’a samu zanen ajikinta saidai ya kasa ganin fuskarta don wani irin bishi bishi takeyi mashi ta yadda koda shine bokan da yafi kowa iya tsafi bazai ganeta ta haka ba.
Galadima wanda sun gama da dakin bayi ne don haka Hurriya ce ta fado mashi arai wata dariyar mugunta yayi don yasan yanzu ne zai iya zuwa ya dauki fansanr abinda tayi mashi,
Har sun kama hanyar wani daki yace masu bana nan zasuje ba yace ga inda zasuje.ba wanda ya musa mashi haka suka jero kowa idan ka kalla acikinsu sai yan hanjin cikin mutum ya kusa kadawa
Basu wani sha tafiya ba Sosai saiga su adakin su Hurriya wanda yake sosai da mutane aciki saidai tun kafi a ida yi masu iso kowa acikinsu ya natsu ya shiga taitayinshi
Dakin shiru yayui don kamar babu numfashin biladama aciki
Kallon matan yayi yace ku fara aikinku da kakkausar murya .Daya daga cikin dogarawan yace suyi layi ba musu suka jera layi
Cikin sauri aka rinka zuge rigar uniform dinsu ta baya ana dubawa don da an duba naki sai ki koma gefe haka aka rinkayi hadasu bintu da wasba akan layin ba wani bata lokaci suke komai wasu kam hada mari matan ke kai masu
Galadima shiru yayi tareda mamakin rashin ganin Hurriya a wurin don ga dukkan alama gashi har an kusa gama searching bata nan saidai tun kafin yagama tunanin da yake yaji wata acikin matan da yazo dasu ta bude Baki tana kallon kofa tace wacece wannan aiko kamar hadin Baki suka juya suna kallon yadda take tafiya in all her mighty
She looks fierce and confident don wani jeans ne jikinta shima crazy wandon duk ya fashe saidai shi ba kamar wanda ta sanya rannan bane don wannan gwiwar ne yafi fashewa gashin kanta kitso ne guda hudu gashin ta nanadeshi ba karamin kyau kitson ya karayi mata ba don ya sanya ta kara looking very unique and classy yanda take tafiya kanshi abun kallo ne with so much mighty don kamar tana da sarautar rabin duniyar haka take takawa she’s beautiful tana da asalin kyau wanda idan akace ta zana kanta iya abinda zata iya yi ma kanta kenan inda ace zata fito gasa kyau toh tabbas Akwai 100% possibilities din dazata iya ci Because her beauty is beyond perfection
Kamar an dauke wuta an kawo haka ta haska wurin kallonta kawai sukeyi they were all in awe don cikin mazan harda matan suma sun kasa janye idonsu daga gareta .
Cikin wani irin confidence ta iso wurin saidai idan zaka bude zuciyarta fargaba ne fal da tsoron makomarta saidai tasan ta riga tazo bazata iya juyawa ba saboda sunanta Hurriya Faisait Hamood ba abinda ke firgita ta bare ya tsorotata jikar sarki Hamood ce fa.
She knew that she would never allowed anyone of them to touch her with their dirty fifthy hands saidai batasan mi zatayi ba.
Jakadiya kallon tafiyarta da izzarta tagama how could they not see that tuntuni ai basai an fada masu ba wannan Hurriya itace yarinyar da ake magana daga Heral palace why are they so blind that they couldn’t see that since, tafiyarta cin abincinta miskilancita rainin wayonta yayi solving equation din it’s not a coincident she must be the girl they’ve been searching for
Galadima gabanshi banda faduwa ba abinda yake yi irin tunanin jakadiya ne shima ya darsu a zuciyar shi sadai dayar zuciyar shi tafi rinjaya da haba ba ita bace bazata taba zama jikar sarki hamood ba duk da alamamomin a bayyane suke Zata iya zama jikar tashi.
Da sauri manya manya matan sukazo zasu taba Hurriya kallonsu Hurriya tayi tareda dage gira babu alamun tsoro bare kuma fargaba kallon su tayi ahankali sannan tace cikin muryarta mai dadi tace mi kukeso wani acikin dogarin yayi karaf ya amshe tareda cewa ubanki mukeso shegiya yar matsiyata,Hurriya ahankali ta dan ciji bakinta sannan tace ubana kakeso kallonshi tayi cikin idonshi idanunta cike da rashin tsoro da kwarjin tace ubana yafi karfin kaskantaccen mutum irinka sakarai wawa irinka har ka gama rayuwarka baka isa ka taka inda mahaifina yake ba sannan tace ko karen mahaifina baka isa ka bashi ruwaba bare kuma gugar takalmi har ka kai inda zaka ganshi kace shi kakeso raising brows dinta Tayi in a mocking way tace bawa kamar ka bai isa ba ta ida maganar cikin mulki gadara da jan aji
Wurin kamar ita ake jira ta fara magana don har wani extraordinary shiru ya kara dauka wurin sosai har takai aya muryata kawai take fita cikin sautin amo mai dadi da kuma iya shirya kalamai
Cikin zafin bakin ciki da kufula dogarin yace ni kike gayawa wannan maganar yau zaki gane waye matsiyaci tsakani na dake ,kallon matan da suke duba bayan yan matan yayi yace kuyi maza ku cire mata rigar ya matso saitin su hannunshi rike da bulala abinda ya Sani yau mai rabashi da Hurriya yau sai Allah don sai ya wulakanta ta ya kaskanta mai muni cikin bainar jama’a don yanda tayi mashi maganar banza sai ya huce akan jiknta don yanzu ya daukar ma kanshi alkawarin bazai iya Bacci ba idan baiga bulalarshi akan jikinta ba.
Galadima yasan mi dogarin yake shirin yi amman bazai hanashi ba saboda shima cike yake fam da yarinyar she always gets on his nerves don shi baiki ta wulakanta ba wulakanci mafi muni
Dogarin ya kallesu yace wai mi kuke jira tsoronta kukeyi manya matan masu duba bayan yan matan suka kalli guards da sauran dogarawan daga masu kai head of security din yayi alamar kuyi aikin ku kada ku fasa shima haka galadima ya nuna saidai kallo daya zakayi ma Hurriya kasan cewar batayi na’am da wani ya taba mata jikinta ba don wani irin kallo take watsa masu in a warning way wanda kallon cike yake da gargadi da kashedi
Galadima kallonsu yayi yace mi kuke jira dallah ku dubata muyi mu tafi akwai sauran inda zamuje aiko yana gama maganar sukazo zasu taba Hurriya da zafin nama ta ture daya daga cikinsu da tayi sa’ar sanya hannunta saman wuyanta wani irin fury bacin rai kawai ke fita daga fuskar Hurriya
Basu daddara ba mutum biyu suka karu suka cike hudu sukazo suna kiciniyar cire mata riga jakadiya acikinsu Hurriya wani irin murda takai ma hannun jakadiya da sauri ta saketa how dared you touch me with your stinky hands inji Hurriya ta fada tareda turesu wanda cikin muryarta zaka iya jin zallar bacin rai da kuma bakin cikin hakan da akayi mata
Tunda tabar Heral palace bata taba samun ranar bakin ciki irin ta yau ba wasu matsiyata kazamai suke kokarin su tabata not just to touch her ma they’re trying to undress her this is unforgiving itace Hurriya Faisait Hamood nobody dared to touch her even in their palace except for 3people that was her father,her mother and her grandfather except them,nobody would tried that because they knew the outcome don bata da sauki don a Heral palace ace mistakenly cousin dinta ya matso kusa da ita da niyyar ko kai hannu kan yatsanta don ta daukeshi da mari sannan akawo mata ruwa agabanshi ta wanke hannunta ba komai bane,
Sai a masarautar Qamar wanda basu kai ta hada hanya dasu ba ma wadanda ba blood relatives dinta ba sune suke tabata da kazamin hannunsu if her grandfather is were to hear this tasan da kilan yau masarautar Qamar tazama labari don kilan sai ya sanya an rusheta
Cikin kulewa Galadima kuma ba tareda tunanin abinda zaije ya dawo ba yace ma Guard din su cire ma Hurriya riga now ya buga masu tsawa,
Hurriya kam ba karamin gajiya tayi ba don sarkin yawa yafi sarkin karfi sosai don bataci abinci ba duk yau ga abinda ya faru itakam batada karfi don karfin daya rage mata kadan ne
Fargaba ne da tsoro fal acikin ranta saidai bazaka iya ganewa ba saboda bacin rai daya rufe mata fuskarta,Dogarin da ta gama gaya ma magani shine ya kutso kai tareda jan rigarta Hurriya kam ta riga ta hakura tayi nata fadan yanzu saidai ta zuba ma sarautar Allah ido saboda karfin daya rage mata kadan ne da wani irin zafin nama da bakar keta yaja rigar saidai ji kake tass tass
Sakin baki kowa yayi tareda kallon saitin Khalifha sanye yake cikin wasu hadaddun suits na Hermes wanda suka amshe shi tareda fito mashi da haiba da kwarjini he looks so dangerous and scary don aura dinshi da ta cika wurin mutum bai isa yagane yanayin fuskar shi ba,
Hurriya wadda take neman faduwa idonta har rufewa sukeyi da sauri ya tallabota ta fada jikinshi yana mai riketa gam
Kowa kallon shi yake da mamaki yanda akayi ya iya ganeta yana makaho da yawa a wurin suna cikin fargaba da tashin hankali saboda basu san Khalifha ba sai dai suna jin labarin shi don duk wanda ya kwana ya tashi masarautar yasan labarin shi wanda ako dayaushe cewa ake baida dadi sam.
Rungume yake da Hurriya sannan ya juya ya kalli cheif of security yace mashi take care of them
Wurin ba wanda baiji hantar cikin su ta kada ba don ba kowa ke son shiga harkar shi ba.
Page 62
Khalifha cikin bayan motar shi ya sanyata sannan driver ya bude mashi