Showing 27001 words to 30000 words out of 59144 words

Chapter 10 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel

26 Mar 2025

29930

don convoy din da take fita dashi a lokacin ko convoy din shugaban wata kasar albarka then why the self defense ?Da mahaifinta da mahaifiyarta sune suka hanata sukace tayi hakuri she’s not stubborn sometimes Saidai fa stubbornness dinta irin na kakanta bata cika yi ma mahaifanta ba , Saidai wani lokacin idan ta kafe din ba wanda ya isa ya hanata sai Allah don ko Hamood da iyayenta din Saidai hakuri.
Mahaifiyarta is also from prestigious royal family of 🇲🇱 wadda Hurriya da ace ta dauko irin sarautar mahaifiyarta da ko maganarta ba wanda zai rinka ji saboda tsananin sarauta da iko da mulki nata Hurriya tana iya fin wata shidda bataji maganarta ba Saidai murmushinta wanda kullum yake dauke a fuskarta wanda yake nuni da irin zallah da soyayyar da take ma diyarta bata cewa uhm ko uhm uhm Saidai taita binta da kallo Amman bata cewa uffan idan Hurriya ta shigo har ta gama hidima da bidirinta bata cewa uffan.shiyasa ba wani sabo tsakaninsu Sosai tafi sabawa da kakanta akan iyayenta mahaifinta shima ba mutum bane maisan hayaniyaba saidai yana fira da da ita sosai don haka basu da damuwar komai tunda har mahaifiyarta tace ta daina takwendo itada kakanta ta bari don ranar taji doguwar maganar mahaifiyarta duk da a lokacin ta lura dacewar da kyar takeyin maganar ga dukkan alamu bata saba ba daurewa take don sosai tayi ma Hurriya nasiha tace you should stop doing that my dear you’re a girl kinji your father will always protect you and your husband kidaina kinji babanki bayaso kuma bayajin dadi.
Tun daga lokacin Hurriya bata karayi ba ko kokarin yin hakan don har Hamood saida ya tambyeta dalilin da ya sanya ta bari hakanan tace mashi ,yasan halinta na rashin son kutse sosai a rayuwarta don haka ya kyaleta da sai ya sanya an bincika mashi Saidai baisan ya bata mata Daidai da rana daya saboda irin tarin kaunar da yake mata.
Sauke ajiyar zuciya tayi ta kwanta tareda lumshe ido hoton mahaifiyarta da mahaifinta na dawo mata a idonta saidai batasan yawan tunani don haka tayi saurin cire abun aranta ahankali tace forgive me my dear parents Amman today she would show them aininhin Hurriya Faisait Hamood
Bintu kallon shaho tayi dashi da kaura jikinta duk a mace yanda bazasu iya gano wani shirin da sukayi ba gabanta yana faduwa sosai don tana tsoron suyi ma Hurriya wani Abu Saidai she trust Hurriya kaura ne yayi dariya yace ko kefa ai yanzu kinga ba wanda zai cutar da ita kayanta ne kawai zamu bincika sai mu duba abinmu mu tafi ko shaho
Shaho da banda cika da batsewa ba abinda yakeyi don yaune ranar fansar duk abinda ta tabayi mashi.cikin isa yace eh sannan ya kalli Bintu yace ke bace mana dagani ko kuma na fara ta kanki Bintu ai da sauri ta matsa ta nufi dakinsu.
Saida suka samu wuri suka zauna tareda jiran dakin yayi shiru yanda baza’a jisu ba.
Sun dade suna jira a wajen sannan suka shiga dakin inda bakajin motsin kowa sai wadanda aka hada baki dasu a mata sai kuma su shaho da kaura da suka shigo.
Hurriya tundaga kafafunta har zuwa wuyanta a rufe yake don cikinsu ba wanda baiyi mamakin shigar kirkin da tayi ba yau don ko dazu sunganta as usual da dan skirt na jeans iya cinya kilan batasan sauro ya cijeta sukayi tunani
Shaho ne ya kalli kaura yace shegiyar yarinyar akwai kyau. kaura kam lumshe ido yayi yace ga gashi ga kamshi don fa inajin kamshinta har a bakina murmushin mugunta yayi shaho yace yau zamu fanshe wulakancin da duk ta tabayi mana karshen jiji dakai da izza yazo.
Shaho yace ban iya jira sannan ya karkato kanshi tareda shinshina gashin Hurriya wanda banda kamshin mayukan Khalifa masu tsada ba abinda suke kamshin na bugun hancin shaho yace jar uba yarinyar nan yar gayu ce kaji wani kamshi da gashinta yakeyi wanda yake barazanar fasa mani kai kaura ne yace dallah ka ishi mutane da surutai muyi sauri muyi abinda ya kawomu mu kama gabanmu.
Shaho yace hakane sannan ya zura hannunshi saitin wuyan Hurriya. wani giggitaciyar kara ya saki don yadda Hurriya ta rike hannun tare da caka mai tsinke kitso mai tsananin tsini da zafi wanda ba zato ba tsammani don baiga tashinta ba Saidai saukar tsinke da yaji.
Cikin tsabar mugunta Hurriya ta murde mashi hannu tareda maida hannun baya sannan ta kai mashi wani duka ta mike tsaye
Dukewa yayi tareda rike cikinshi inda ta kai mashi duka yana gwanjin kukan azaba
Kaura da yayi tsaye yana kallon irin action din da yarinyar tayi tsoki yayi tareda kallon kankantarta
kuma da raina shaho da baiyi ta maza ba kalli fa yarinyar
Kaura bude kafada yayi tareda karya wuyanshi saidai ji kake kass kass sannan ya taimaka ya dago shaho tare da tsaida shi tsaye dayake shima shahon namiji ne ya dake kamar ba abinda ya faru.
Duk iya shegenta bata isa taci galaba akansu tunda su biyu ne Hurriya kam kallonsu tayi zuciyarta na tashi da bacin rai how dared they touch her royal body sunanta fa Hurriya Faisait Hamood the y really have messed with the wrong person nufota sukayi gadan gadan da niyyar dukanta tareda kadata ahankali ta juya ta dauko iccen data boye wanda basu lura dashi ba saida saukarshi da sukaji kowanne acikinsu .kafin su dawo hayyacinsu ta kara masu
Kaura ne yayi ta maza tareda rikota aiko rikon da yayi mata yayi triggering dinta ta caka mashi tsinke dake a hannunta sai jini shaho da yake kokarin guduwa aiko ta buga mashi iccenta a kafa wanda ya durkusa da sauri tareda rike kafar
Dukansu a durkushe kallonsu tayi wanda su kuma suka juya sun kasa kallonta
Kallon hannunta da yake sanye da safa tayi wanda ba abinda take bukata irin tayi wanka ta wanke najasar data taba a jikinta na wadanan jakunan.
Saidai ganin fa ba tabar masu tabon da zasu rinka tunawa da itaba batayi masu wani lahani wanda zata ga jini na fita ba ta tabbata sai taga jini na fita a kowanne daga cikinsu zata iya bacci yau ,daukar iccenta tayi sannan tazo inda suke zazzaune shaho da ya kasa magana alama yake mata da hannu tayi hakuri .har zata buga masu iccen wata idea tazo mata tsinke dake rike da hannunta ta durkusa sannan ta rinka caka ma kowa a gwiwar shi duka biyun aiko nan da nan jini ya fara fitowa saida ta tabbatar ciwon ya shiga jikinsu sosai sannan ta bugama kowanne acikinsu icce ta juya tayi tafiyarta
Ihu kara kururuwa ba wanda basuyi Amman kusan ba wanda yake jinsu saboda baccin da kowa yayi.
Bazata iya kwana hakaba batare da tayi wanka ba don haka kawai ta fito hannunta rike da fitilar wayarta da keys din part din Khalifha wanda aka aje mata saboda tana zuwa tana gyarawa.ba karamar doguwar tafiya bace tasha banda kukan karnuka ba abinda takeji
Har saida ta fara gifto Chambers din princes da princess din ta fara ganin securitys da tsirarrun mutane.
Bude kofar part din tayi tana shigowa ta lumshe ido tana maijin kamshin da parlon yake har cikin kanta, ba inda Hurriya ta tsaya sai dakinshi inda yake tsaff agyare banda kamshi ba abinda part din yake.
Toilet ta shiga sannan ta hada ma kanta ruwa mai dadi da kamshi sannan ta cire kayan jikinta ta sanya su watching Machine ta dade tana gasa jikinta tareda wanka sannan ta fito daure da bathrobe grey gashinta ta wankeshi tayi drying ya zubo a bayanta
Wardrobe dinshi ta bude ta fito da sabbin hoodie brown na bvlgari ta sanya hade da fesa turarenshi tana gamawa ta haye saman gadon Khalifa mai dadi wanda ya zama nata yanzu lumshe idonta tayi kaffn ace wani Abu bacci ya dauketa.


Short page

Tunda Khalifa ya fara cin abinci wurin ya dauki shiru Sosai
Ba wanda ya kara cewa uffan har saida suka gama Hurriya ce ta fara tashi kallonta Khalifa yakeyi cikin kayanshi data sanya a ranshi yace gaskiya batada kunya ba izini yar aiki ta bude maka wardrobe ta sanya kayanka kuma kamar batayi laifin komai ba
Bayan sun gama cin abinci Khalifa da maleek suka fita.hurriya saida ta tabbatar kowa acikinsu ya gama cin abinci tazo ta kwashe duka kayan datti fayrouz ya biyota ya rinka tayata komai yanayi yana mata labarai masu tsananin ban Dariyar duk yanda Hurriya take daurewa saida fayrouz ya kawo zance data kasa rikewa saida tayi dariya kadan a lokacin Fayrouz kam sumar tsaye yayi yana kallonta don wani irin kyau kawai yake gani dimples dinta hakoranta masu kyau wanda bai taba ganin irinsu ba sai adon dake tsakankanin hakoranta yaji dadi da yaga dariyar Hurriya don yasan yau abinda zai rinkayi mashi yawo kenan har yayi Bacci.saidai yaji dadi sosai da Hurriya ta zamana cikin mata mararsa dariya da kilan sai ya kusa mutuwa inda tayi Dariyarta yaga ana kallonta.
Hurriya ta dade a part dinshi tareda fayrouz sannan ta koma dakinsu tana zuwa tayi sallolinta da batayi ba.
Inna hanne ta iske da wasba aiko da murna wasba ta tarbeta tace tayi missing dinta jiya da daddare daga mata kai kawai Hurriya tayi inna hanne kallonta take da kayan Khalifa har zata tambayeta ta fasa saboda tasan ko wacece Hurriya zata iya bada shedarta
A wurin su inna hanne da wasba ta wuni bintu ma tazo ta zauna Hurriya idan ta kallesu tanajin wani irin nauyi azuciyarta duk da bata cika yadda wani abu yafi karfinta har haka ba don tasan bazata dade ba zata tafi.
Amman hausawa sunyi magana da suke cewa sabo turken wawa tasan cewar zataji ba dadi idan har ta tafi Amman ya zatayi haka rayuwarta tazo mata
Kwanciya Tayi bata wani dade da kwanciya ba bacci ya dauketa mai dadin gaske don ba itace ta tashi ba sai bayan magriba alamar period taji wanda tana fin wata da wattani batayi shi ba dan bata rai tayi sannan ta fita zuwa kitchen wurin inna hanne taje ta amshi ruwan zafi sannan ta nufi toilet ta gasa jikinta da ruwan zafi mai kyau
Saida ta sanya pad dinta sannan ta shirya cikin pink rigarta mai kyau iya gwiwa ta tsaya mata turare ta fesa sosai ta kara shafa ma gashinta mai sannan tayi ma wasba Bankwana wasba kallonta ta rinkayi don kamar ta bita haka takeji Allah ya dora mata soyayyar Hurriya
Tanaji tana gani Hurriya tabar dakinsu ta nufi dakin Khalifa Dukansu suna parlon ta shigo batare da sallama ba Saidai ganin mutum kawai sukayi wani irin kamshin dadi takeyi mai sanyi wanda ba wanda bai shiga hancinshi ba acikin mazan.fayrouz wani irin mugun kishi yakeji yanda take tafiyar catwalk wanda ta dauke ma kowa hankali a wurin banda mutum daya
Harta Khasheem saida ya kalleta ya kasa janye idonshi daga kanta
Kallonsu tayi sannan tace kallon na minene maleek basarwa yayi Khasheem ne yace girl can’t lie to you but you’re hot fayrouz ne yadan bugi kanshi yace please stop yana bata fuska Khalifa dai yanajin su Amman baice kala ba don tashi yayi ya haye sama ya barsu
Khasheem ne ya kalli Hurriya yace I’m Hungry please give us food dan kallonshi tayi tareda daga mashi kai sannan ta shiga kitchen fayrouz ne ya biyota ya rinka yi mata fira.
Koda suka gama suka jera table din Khasheem ya kira Khalifa ta landline yace yazo suyi dinner.
Bai wani dauki lokaci ba yazo da fararen kaya na Loro Piana wanda suka fito mashi da haiba da kyau banda kamshi ba abinda yakeyi don wurin duk ya dauki kamshin shi
Hurriya ita tayi serving kowa acikinsu sannan tayi serving kanta kamar ba yar aiki ba fayrouz kam dadi kasheshi ganin Hurriya ta zauna zataci abinci dasu they ate in silence don kowa yanaji da table manner dinshi
Wani karamin parlo suka shiga Dukansu su ukkun Hurriya kuma ta tattara duk abinda sukaci ta wanke a kitchen saida ta gyara ko ina da komai sannan ta dauki ledarta data sanyo items dinta da zata bukata ta haye sama
Dakin Khalifa kamar dakinta don tana shigowa ta shiga toilet tayi wanka mai dadi tanata wani irin kamshi kayanta ta sanya a washing machine din dake a toilet din ta wanke su tass sannan ta fito daure da bathrobe grey mai kyau
Saida ta shafa mayukanshi tanayi tana bata fuska don everthing there ,is for men nothing feminine raising browse dinta tayi sannan ta bude wardrobe dinshi ta zaro sabuwar jallabiya milk ta sanya wadda ta rinka yimata yawo ajiki turarenshi ta fesa sannan tazo saman kujerarshi ta zauna shiru shiru bai dawo ba ta dade tana zaune don har tafi awa daya ga wani bacci datake bala’en ji ga sanyi da yake shiga har cikin kashinta
Dabara ce tazo mata gwara ta kunna tv tayi kallo don tunda tayi wanka nan takejin wani irin bacci.
Kunna smart tv mai matukar kyau da tsada tayi katuwa ganin Netflix account ya sanyata shiga har zatayi logging asalin account dinta na hurain ta tuna kawai sai ta sanya YouTube wakar stability ta ayra star ta sanya kawai
Hurriya tafara enjoying wakar Amman tana cikin jin wakar batasani ba baccin gajiya ya dauketa.
Agajiye yake don sai karfe 1:00 suka gama rapping off na aikin da sukeyi ba abinda yake bukata irin ya kwanta ya Sauke gajiyarshi .
Yana shigowa toilet dinshi ya shiga tareda wanka bai tsaya wani kyale kyale ba kawai kayan bacci ya sanya yazo ya kwanta Saidai yana kwanciya yaji mutum ajikinshi tareda saukar numfashi da yake Khalifa ne ba tareda shakka bare tsoro ba ya bude idonshi tareda sauke matasu ahankali yake binta da kallo sannan yayi tsaki yace stubborn maid ya tashi ya bude screte room dinshi ya kwanta.
Bai wani bacci Sosai ba don karfe 4:00 ya tashi ya gabatar da nafila har asuba sannan yayi wanka ya fita sallahr asuba har ya fito sallahr asuba Hurriya na dukunkune cikin bargo tana baccinta mai dadin gaske.
Karfe 7:00 har yagama shiryawa haka ya fito falo inda duka abokananshi sun shirya kowa sai kamshi yakeyi ba karamin kyau sukayi ba don komai da suka sanya is screaming money don kallo daya zakayi masu ba lallai ka iya dauke idonka ba Saidai kwarjinin su bazai bari a tsura masu ido ba.
Khalifha hannunshi rike da walking stick as usual mai tsananin kyau da tsada haka suka jero su hudu aka bude masu farar limousine convoy dinsu ya dauka sai airpot.
Hurriya kam koda ta tashi mika tayi tana kallon dakin Khalifa mai tsari.

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



Page 56
Galadima ya kalli jakadiyya yace mata wacece waccan data wuce .
Jakadiya da take bin bayanta da kallo tace bansan taba don ban taba ganin taba galadima yace mata kiyi kokari ki nemota sai a hadata da sauran matan nan .cikin gamsuwa tace shike nan,
Hurriya har ta nufi dakinsu inna hanne na zaune idonta biyu da alama gyangyadi takeyi
Hurriya na shigowa ta mike a zabure ta rinka kallonta Hurriya itama kallonta tayi tace lafiya ?inna hanne sauke ajiyar zuciya tayi tace lafiya lau. Hurriya alama tayi mata ta zauna sannan ta mika mata ruwa saida tasha sannan ta kara sauke ajiyar zuciya don tasan abinda Hurriya take jira taji ayanzu bazai wuce miye ya hanata zuwa ta kwanta sannan damuwar miye a fuskarta
Murmushi inna hanne tayi tace kin tada mana hankali Sosai da bamu ganki ba wasba da kyar na lallasheta taci abinci tana gama cin abincin bacci ya dauketa gatanan kina ganinta ,Bintu ma da kyar na lallabata ta tafi ta kwanta
Hurriya data gaji da tsayuwa don wani irin mugun sarawa kanta yake mata Don har kafafunta karkarwa sukeyi inna hanne da tana kula da ita don tun shigowarta tasan bata lafiya don idonta sunyi wani kalar sanyi tareda canza launi da idonta sukayi
Murmushi inna hanne tayi ganin yadda Hurriya ke kokarin fada da ciwon don kada aga gazawarta don har ta zauna tareda jingina da yar katifarta wanda idan ba sanin Hurriya kayi ba idan ka kalleta zakace lafiyarta lau don yadda take kokari sosai wurin boyewar ciwonta
Ganin inna hanne har yanzu ita take kallo ahankali ta maida jikinta saman katifar tareda lumshe idonta tace bacci ya daukeni a Chamber Khalifha ku daina damuwa da abinda bai kai asa damuwa ba ,maganar ta fito da wani irin huci da zafi don inna hanne saida taji hucin Sosai mai dauke da kamshin mouthwash ya bugi hancinta
Inna hanne ba tareda tace mata komai ba tayima Hurriya saida safe ta fita Hurriya kam ko ida fita batayi ba ta sauke ajiyar zuciya sannan Bacci ya dauketa saidai wani irin nishi da shesheka kawai takeyi cikin baccin
Inna hanne datake labe bata tafi ba ta fito tareda shigowa wurin Hurriya hankalinta tashe data kalli yanayin da take ciki ai inna hanne da sauri ta fita taje ta dauko magunguna da kasko cike da garwashin wuta tazo da sauri ta barbada mata wani magani banda hayaki ba abinda ya turnike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login