Showing 15001 words to 18000 words out of 59144 words
Chapter 6 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel
na kara shigarta tsoki tayi tareda kashe duka Ac din tana kallon komai neat and intact basai an fada mata ba mai dakin is a neatness freak don yadda aka jera komai da muguwar tsafta
Ajiya kallon komai tayi ta shiga toilet dinshi wanda shima komai dark ne hatta towels dinshi dasu toileries dinshi
Bata wani bata lokaci ba ta shiga wankin toilet din cikeda kwarewa kuma da iyawa ba ha’inci sam a aikin Hurriya koda tagama wanke toilet din saida ta maida mashi komai inda ta ganshi ta fito.
Kallon yadda ya kwanta yana bacci tayi shiru tayi tana tunanin yadda zata tadashi tuna yadda ta tada Imad tayi ranar farko data fara aiki a wurinshi murmushi tayi a hankali don she missed them all Hamdan Amrah Imad and Ammar duka tayi missing dinsu harda liya da Neela she hope they are enjoying themselves in Heral palace obviously ma tasani
A hankali ta fara neman comb Everything intact duk inda ta duba bata gani ba sai da kyar ta hango comb din daukar comb din tayi tazo saitin gadon tareda hawa saman gadon kadan
Hurriya kamar tanajin tsoro ta fara zame duve din daya rufe kanshi dashi har saida ta sauke shi duka
Kallon yanda yake bacci very peaceful tayi yaune ta fara ganinshi a rayuwarta hé’s handsome and mysterious kallon dogon hancin shi mai kyau da daukar ido tayi sannan tazo har bakinshi bakar sumarshi agyara take wani irin kamshi yake wanda takejin shi har cikin kanta snapout Hurriya tace ma kanta sannan ta gyara natsuwarta
A hankali ta fara goga mashi brush din tun daga kanshi har fuskarshi kamar tana sosa mashi kanshi.
Khalifa wani kalar yanayi ya fara shiga yadda take sanya brush a saman gashin shi.
Da wani irin zafin nama Khalifa ya rike hannunta tareda bude idanunshi masu kyau da kwarjini Saidai bazata iya ganinsu ba saboda suna cikin glass din cikin wata deep strong voice dinshi yace how dared you touch my royal body Hurriya kam ta kasa cewa komai saboda yadda ta shiga shock how dare he touch her ta rasa mi zatayi mashi wanda zai kasance Daidai da yadda ya tabata Saidai ta kasa koda motsa hannun damanta don har yanzu Khalifa rike da hannunta yana binta da wani kallo
Hurriya dagewa tayi ta taro miyau mai yawan gaske sannan ta tsirta mashi a fuska
Da sauri Khalifa ya saki hannunta he never saw that coming miyau fa how dare her ?his filthy maid just spit at him Mad 😡
Hurriya kam ba wani remorse tattare da ita don wani deadly glared kawai take aika mashi don tabata da yayi Daidai yake da atsirta mata yawu acikin bakinta ko a fuskarta
Khalifa cikin zafin nama ya jawota da karfin gaske tare da fadowa saman jikinshi.
P.49
Shiru Khalifha yayi yana kallon gashinta da ya sagale a kunnenta ta zaro ido tunda take ba’a taba yi mata abu kalar wannan ba how dared he touch her with his filthy hand
Khalifha hannunshi zagaye da waist dinta cike da mugunta ya kara jawota tareda hade fuskarsu wuri daya don saura kadan bakinta ya shiga cikin nashi ya goge yawun data zuba mashi a fuskarshi da fuskarta sannan ya tureta ya mike tsaye cike da kyankyami ya nufi hanyar toilet dinshi .
Hurriya kam kasa yarda tayi da abinda ya faru yanzu tunda take a rayuwarta ba wanda ya taba yi mata rainin da wannan so called master dinta yayi mata she can’t believe how he Hugged her without her consent. rules dinta ba wanda yake tabata he’s the first male person that break her rule tunda take wani namiji bai taba kama koda hannunta ba face mahaifinta sai kuma kakanta sai kuma past dinta da batasan tunawa shiru tayi don sam ta kasa yarda da abinda ya faru that inhuman prince almost kissed her she can’t forgive him gaskiya.
Khalifha ya kasa yarda da abinda ya faru yanzu Ina ta samu audacity din dazata shigo mashi har dakinshi not dakinshi data shigo ma the way she woke him up and she dared to spit at his face bazai iya yafe mata ba
A hankali ya daura towel dinshi tareda fitowa kallon yadda ta gyara ko ina na dakinshi yayi wurin yayi fes fes kallon small figure dinta da gashin kanta wanda ya kwanta ko ina yayi ,wani Devil smirk ya fito mashi.
Har Hurriya tazo wurin vanity table bata lura da mutum ba don tazo zata goge madubi
Goge madubin tayi cikin yanayin natsuwarta da kwarewa a aiki saidai juyowar da zatayi suka hada ido da yarima Khalifha tsaye yana kallonta jikinshi sai kamshin shower gel yake sai wani ruwa da ya kwanta mashi a jikinshi sumar kanshi mai matukar kyau da daukar hankali
Hurriya kam wani kalar zare ido tayi tareda fasa wani kalar ihu ta rufe idonta da tafukan hannunta tayi hanyar kofa saidai ko tafiya bata fara ba ya tadiyeta tareda riko mata hannu ya dagota kallonta yake ta cikin glasses dinshi yana kallon zallar bacin rai wanda ya kasa boyuwa a fuskarshi cikin kokarin kwace kanta take Amman yaki barinta tayi hakan da kyar take hadiye miyau
Tunda take ba’a tabayi mata abinda wannan Khalifhar yayi mata ba.
Karshen cin mutunci yayi mata har sau biyu amman zatayi maganinshi.khalifha kallon idonta masu kama da zaiba yayi saboda hasken da suke fiddawa kwayar idonta mai masifar kyau don har wani gold gold gareta
cikin deep strong husky voice dinshi yace who send you ?
Hurriya idan zai bude zuciyarta to dole ya ruga saboda irin bacin ran da take ciki ta rasa mi zatayi mashi wanda zai saketa tunda baida mutunci baida kunya Khalifha kam ya tsareta da ido yana kallonta yana jiran amsarta
Hurriya ta rasa mi zatayi all her life ba’a taba mata jiki shine rule dinta na farko ganin baisan ido ba aiko ta duka ta ciji hannunshi da karfi wanda Khalifha ko gezau baiyi ba Hurriya ganin yaki sakinta ya sanya ta tattaro yawun bakinta ta kara watsa mashi a fuskarshi aiko da gudu ya saketa. A guje tabar wurin tana sakin ajiyar zuciya kallon hannunta tayi zuciyarta na bugawa duk inta tuno yadda ya riketa sai taji wani irin haushi da bakin ciki jerk Ass tace sannan ta fita.
Ba inda ta tsaya sai kitchen tana zuwa tace ma inna hanne ta zuba mata ruwan wanka inna hanne ba bata lokaci ta zuba ma Hurriya ruwan wankan
Hurriya ba inda ta tsaya sai toilet saida tayi wanka na mutunci don duk inda ya taba ajikinta saida ta wanke sannan ta fito tana dan jinta Daidai ,kamshin turarenshi da dakinshi duk ya cika mata hanci yana barazanar dagula mata lissafi hade dajin haushin Khalifha yake koma waye
Kaya ta sanya riga da skirt na English wears don skirt din Daidai gwiwarta ma ya tsaya sannan ta fito taje wurin Chamber din ayyo inda suke jiranta ba wani alamar sauki bare fara’a a fuskar Hurriya don gaba daya ko Khalifha yake or whatsoever ma ya gama bata mata rai
Zama tayi a saman kujera ayyo ta kalleta tace nayi magana da uwardakina tace za’a biyaki ko nawa kikeso indai kin tabattar bazai koreki ba
Hurriya daga mata kai tayi tace bazai taba korata ba kuma inda harna daina aiki sashen shi tohm sai kudaina biyana
Ayyo kallon Hurriya take don ko yanayin da take magana tasan ba karya take ba don a yadda ayyo ta shahara ko karya daya mutum ya fadi zata iya kamashi
Hurriya ta ajiye mata account numberta tace ina jira sannan ta juya tabar wurin .
Galadima ya kalli boka yace to yanzu mi za’ace mashi Boka dariya yayi yace akwai matsala babba kuma akwai maganin matsalar duka acikin masarautar galadima sakin baki yayi yana kallon boka domin yana bukatar karin bayani
Boka cewa yayi ka fada mashi akwai yarinyar da idan har ya sameta to ba sarki a masarautar Qamar ba kowace sarauta ta zai iyayi ya nemi yarinyar tanada matukar amfani a rayuwarshi.
Shiru galadima yayi tareda buga tagumi wata dariya boka yayi yace sai kun mike tsaye wurin fa neman yarinyar don nakasa gane wani abu a kanta amman ka dawo nan da sati daya zan kara bincike galadima godiya yayi mashi tareda kara tambayar shi makantar Khalifha fa?
Dariya yayi yace da kanku zaku gane idan lokaci yayi
Shima sai kun mike tsaye lokacin ka ya kare Galadima da yasan tunda ya fada mashi lokacin tafiyarshi yayi to ba abinda zaisa ya cigaba da ganawa dashi don haka ya fita tare da jimamin alamuran dake neman tun karosu
Duk da bai fada masu komai akan Khalifha ba Amman hakan bazai sanya su saki jiki ba Amman yace sai sun mike tsaye akan Khalifha sannan su nemo yarinyar indai har sarki Faizan yanaso ya cigaba da sarautarshi.
Galadima jikinshi ba karamin sanyi yayi ba Amman haka ya tuka motarshi har ta kawoshi masarautar Qamar ko hutawa baiyi ba yaje chamber sarki Faizan sannan ya warware mashi komai
Sarki Faizan sauke ajiyar zuciya yayi tareda kallon galadima yace to ya zamu fara neman yarinyar?bai fada mana ba Amman yace nan da sati daya In koma zai fada mana yadda zamu nemeta.shiru sarki Faizan yayi tareda shiga cikin tunani da fargaba kada fa dagaske Khalifha yazo ya amshe sarautarshi ne? Sauri yayi ya basar da maganar ba tareda ya yarda da abinda zuciyar shi keyi mashi waswasi akai ba.
Galadima ya kalli sarki yace maganar yanmatan da za’a kawo wannan shekarar. shiru sarki Faizan yayi sannan yayi murmushi yace wannan ai ba matsala bace jakadiyya zata shirya komai yanda ya kamata
Kuma ai an kawo mata cikin masarautarnan wannan shekara sosai har ance matan wannan shekarar sunfi na waccan shekarar kyau da komai Galadima murmushi yayi yace nima naji ana fadar kyawawan da aka samu a wannan sunfi na waccan shekara shekarar murmushi galadima ya karayi sannan ya hau yima sarki addu’a murmushi sarki faizan yayi tareda sallamar galadima.
Sarki faizan tashi yayi yanata yawo acikin makeken parlon shi wanda yake shake da abun more rayuwa.
Manage this please on &off nepa suka rinkayi mana.
Page 49&50
Sarki Faizan tunani kawai yake yanda zai tarbi abinda yake neman rusa shi gaskiya Khalifha ya mamayeshi sosai don baisan da dawowar shi acikin masarautar ba samm tunda ya tafi saida yayi shekara kusan 8yrs bai dawo ba sai yanzu ai da ya tanaji komai yanda ya kamata.
Zinariya tayi shiru tana kallon kuyangarta tana fada mata duk abinda ya faru data bar masarautar shiru tayi tareda daura hannunta akanta tana magana cikin zuciyarta wato duk kashedin da tayima subira bataji ba saidai fa kuma wanda baya jira yayi hukuncin shi kamar yadda ya saba wani murmushi tayi na gefen baki don tana hango kura cikin masarautar nan.
Hurriya duk yanda ta iya boye duk wani emotions da damuwa zaka iya hango damuwar dake kwance a fuskarta don wani tsoro tsoro takeji hankalinta duk yabar jikinta she need to leave masarautar Qamar as soon as possible don ko yau saida tayi mafarki marar dadi she need money she desperately needs money wani tunanin ya fado mata kodai tayi using kudin account dinta na Heral palace kwabar zuciyarta tayi da tabar wannan tunanin saboda tasan yadda har yanzu ba wanda ya manta da wanzuwarta acikin mutanane duk da cewar shekarun da suka shude
Sarkokinta ta kalla ko zata saida daya ne daga ciki ita kanta sarkar idan ta saida ba karamar matsala zata zamar mata ba abubuwan sun hade mata.
Bata kasance cikin mutanen wanda basu iya maganin damuwar su akoda yaushe ta kasance cikin mutanen masu kokarin magance damuwarsu duk girmanta .ta rasa minene mafita don bazata iya cigaba da aiki a Chamber Khalifhaba saboda watarana kilan zata mareshi ne kawai kuma duk aikin da tayi baza’a biyata ba idan tayi kuskure daya ko kuma a daureta and she don’t care.
Ta tsani bossing a rinka bossing dinta around tunda take rayuwarta ba wanda yake bossing dinta but seems like Khalifha tun daga dull color din da aka kawatashi a parlon yayi defining Khalifha
Ta riga tasan mafitar guda dayace shine tayima Khalifha aiki tanan ne kadai zata iya hada kudin da zata bar kasar nan.
Kallon kanta tayi a madubi fuskarta tayi fayau wandone jeans blue Amman baggy ne sai bakar riga jikinta tayi kyau na fitar hankali wasba ta kalleta cikin yanayin damuwa tace Aunty Hurriya mike damunki kwana biyu shiru Hurriya tayi don ko kallon inda wasba take batayiba tayi tafiyarta tanajin yadda wasba ta kwalla ihu alamar kukan shagwaba murmushi Hurriya na gefen baki tayi tace bratty ta fita abinta.
Bangaren Khalifha ta shiga wanda batayi gigin shiga dakinshi ba yau har an gama shirya mashi breakfast a full table dinshi mai kyau kuloli masu kyau da fararen plate sai cups masu kyau lokacin da Hurriya taje har angama jera komai a table din kallo daya tayi ma ma’aikatam da duk sukayi cirko cirko alamun mararsa gaskiya
Hurriya wani wuri ta samu ta zauna cikin kujerun parlon tana kallon news a Tvn
Tsaye yake a wani makeken daki wanda yafi bedroom dinshi girma dakin wani irin girma da kyaun gaske gareshi yana tsaye tareda kallon duk abinda yake faruwa a parlonshi ta na’ura.
Duk abinda masu aikin sukayi kafin Hurriya tazo yana kallonsu don sabbin note na kudi ya sanya aka aje mashi a parlon acikinsu ba wadda bata zara kudin ba face Hurriya data shigo daga baya.
Backward yayi tareda kallon yadda Hurriya take tafiya cike da yanga da aji cikin wata catwalk din da bai taba ganin wani yayi irinta ba tunda yake rayuwarshi.
Fuskarta a hade as usual har zaman da tayi a kujera ya kalla sai a lokacin ya ganeta itace yarinyar da aka hada hold up saboda ita har ya dauketa ya sanya aka kaita asibiti ta raising brows dinshi yayi sama yace interesting.
Wata slide door ce ya bude ya fito aininhin bedroom dinshi da yake kwana ya fito
dakin sai kamshin turarenta wuta mai dadi da tsada yake
Khalifha yanason turaren wuta sosai don da kanshi yake sayen turaren wuta masu matukar dadi da tsada.
Sanye yake cikin wata riga tight ta house of versace black wadda tayi mashi kyau kuma ta fito mashi da charisma dinshi ba karamin kyau yayi ba wandon shi désigner Na Ralph lauren wanda ya daidatu da shigar shi walking stick dinshi wadda take screaming danger ya rike sannan ya nufi downstairs.
Tun kafin ya ida saukowa daga saman bene ko ina ya cika da kamshin turarenshi mai dadi takunshi duk ya isar masu da sakon zuwanshi banda mutum daya wato Hurriya.
Wani irin shiru parlon ya dauka kamar babu kowa acikin parlon sai karar tv da ac kawai ke tashi
Hurriya hankalinta gabaki daya yana kan news din da akeyi na earthquake din da akayi a turkiya.
Karar plate cups da kuloli kawai kakeji a wurin duk an watsa su kasa katsam tartsatsa kawai kakeji
Batare da ta shirya ba kawai ta waigo domin karar ta shiga har cikin kwakwalwarta don kamar earthquake din da take kallo yanzu a tv yazo inda take haka taji
Natsuwarta tayi saurin nemowa saboda bata cika barin rashin natsuwa tattare da ita ba
Kallon saitin Khalifha tayi wanda yake tsaye da sandar shi fuskarshi babu alamun wasa don duk sun kusa rugawa masu aikin da suke kallonshi
You’re all fired bunch of useless ya fada da wani irin karfi da tsawa Dukansu cikin wani irin firgici suka fara kokarin guduwa harda masu faduwa acikinsu saboda tsabar rudewa kafin kace komai duk sun bace a wurin
Yasan tana a parlon juyowa yayi ya kalli saitin da take a hankali ya tako yazo wurin kallo daya tayi mashi tareda juyar da kanta .
Khalifha cikin strong voice dinshi yace what are you doing?Do you want to die Hurriya shiru tayi ba tare da ta kalleshiba bare ya sanya ran zata amsa mashi
Khalifha he was shocked saboda baya magana ba tareda mutum ya shiga hankalinshi ba
He control everything around him wealth,feeling,aura emotions,maids,employees seems like he can’t control the girl that is seating right in front of him
Cikin yanayin natsuwarshi ya sauke numfashi tareda kallonta she’s unparalleled beauty tanada kyau sosai saidai too bad he don’t like beautiful women Saboda most of them are cheaters
Hurriya saida taga dama tukunna tace I’m not fired I will serve you your highness zanyi aiki a chamber dinan and trust me ba wanda ya isa ya koreni.
Kallonta yake ta cikin glasses dinshi yana hango gaskiyarta a maganarta like she own the chamber wani Devil smirk yayi ya juya.
Tashi tayi tazo inda ya bata da abinci ta fara clearing tasha aiki sosai don saidata tabbatar da ta gyara duk inda ya bata Allah ya bata sa’a kam tana juyowa taga babu shi
Cikin zallar bacin rai yake waya muryarshi a kausashe yake maganar wadda kamar maganar business ce ta sanyashi magana cikin bacin rai shiru yayi don tabbas sai ya bar kasar nan yaje Germany da kanshi kuma baison ya tafi a irin wannan lokacin saidai gwara yaje da kanshi Because he can’t loose millions of dollars he values money saboda ya iya neman kudi duk daya fito daga gidan sarauta bai yadda yayi depending da arzikin masarautarsu ba don da kanshi ya nemi kudinshi kuma yayi making name a business world don a kasashen waje yake business dinshi he intimidates people by just his aura don haka duk wani business da zaiyi duk girman shi kuma duk wahalarshi da tsautsayi indai yazo wurin shi to ba komai bane a wurin shiru sai ya samu kudi with his hardwork and determination he had climbed far higher that a man intended to da kanshi yayi wahalar Neman kudinshi wanda idan yaso zai kwanta gida ba tareda ya fita nema ba kuma ba abinda zai ragu dashi indai arziki najin dadin duniya ne
Amman yasan banashi bane don haka ya nemi na kanshi sai yanzu kawai wani