Showing 12001 words to 15000 words out of 59144 words

Chapter 5 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel

26 Mar 2025

29936

bata extra care duk da Khalifha baice haka ba
Har yanzu wasba kuka takeyi Bintu da inna hanne hakuri suka rinka bata suna cewa Hurriya zata dawo kadata damu tayi hakuri suna lallashinta amman wasba sam bata ganewa saboda ba inda labarin abinda ya faru baije ba cikin masarautar Hurriya an zaneta Hurriya barauniya ce wasu sun yadda wasu kuma sunsan sharri akayi ma Hurriya.bintu da itada inna hanne kansu suna cikin damuwa kawai fada masu ne basuyi ba.
Yau ta kama kusan satin Hurriya biyu a asibitin ta warke sosai don duk ciwon da takeji ta warke saidai fa doctor din yaci wuyarta don baita ganin mutum mai kafiyarta ba kwata kwata ba’a taba mata jiki hatta nurses din bata barinsu ko a taimaka mata zuwa toilet but duk abinda tayi baiga laifinta ba her beauty is to be hold ba karamin kyau Allah yayi mata ba toh duk abinda tayi baiga laifinta ba
Hurriya jikinta ya koma kamar madara dan sati biyun da tayi a asibitin ba karamin kyau ta kara ba don kamar ta shekara a asibitin sai wani annuri take fiddawa ga wasu dogayen riguna abayas da chief of security ya kawo mata masu wani irin kyau da tsada idan ta sanya suna masifar yi mata kyau don ko gyalen bata yafawa don tunda ta fara samun sauki ta kwance kalabar dake kanta manya manya.
Doctor din tunda Hurriya tazo sau uku ya tabajin maganarta a karamar karya idan kuma zaiyi babbar karya tohm zaice baitaba jin maganartaba sosai yake jinjina mata don mutum sai ya dauka bebiyace ko kurma .
Yanzu haka zaune take ta mike kafafunta shirye cikin wata dark blue abaya wadda tayi mata kyau sosai gashinta a gyara yake ya zuba a bayanta idonta lumshe tana dan tsotsar bakinta tana kallon sarkokinta Wanda tunda ta damke su à hannunta har suka zo asibitin bata sakesu ba.
Jin alamar za’a bude kofar ya sanya ta maida sarkokin tana bata fuska chief of security ne yazo Kallonta yayi yace mutafi batayi mashi musu ba ta daga mashi kai shine ya daukar mata ledar kayanta ita kuma ta biyoshi yana kallon yadda larabawan Doctors din suka rinka binta da kallo duk inda suka wuce amman ita bai dameta ba
Kallonta yayi sannan yace ki rufe gashin kanki mana banza tayi dashi wanda kamar bataji ba Ganin yarinya yar rainin wayau ce don haka bai kara ce mata komai ba har suka iso masarautar Qamar . Suna zuwa a hankali ta bude kofar ta fita rike da kayanta da sarkarta
Duk inda ta gifta tanajin yanda ake kallonta Amman ko ajikinta don ta saba kuma ba bakon Abu bane awurinta and she doesn’t care 🤷🏿‍♀️ .
Dakinsu ta shiga inda ta iske inna hanne da Bintu duk sunyi tsuru tsuru wasba kuma tana Bacci....



Page 47&48
paid book gashi nan amana wanda yaci amana tsakaninshi dani kuma da Allah
Khalifha he’s not liking duk wasu masu aiki da ake kawo masa baisan miyasa mutane basu da gaskiya da tsoron Allah ba in fact shi bai yarda da kowa ba kullum sai an canza masu aikin chamber dinshi sai kuma idan an koresu suje cikin masarautar suna zagin khalifahn suna fadin dagaske shi Dodone don ba wanda yasan mai yake aikatawa sai yaje chamber Khalifhan hakan ya sanyawa mutane shakku da rudani Sosai alhalin basusan shi ake neman kashewa ba
Subira saida tayi lafiyayyun kwana uku tana prison don ba wani mutunci tsakanin su da ita ,ba princess bace ko Queen ce ba ruwansu Because they only follow their masters order don haka ba irin zuwan da Ba’ayi ba domin su saketa suka ki,
Sauro kuda cinnaka ba abinda ba cijeta ba karshen wulakanci da cin mutunci Uncle Khalifha ya sanya anyi mata don tunda take ba’a tabayi mata cin mutunci irin wannan ba kuma Duk masarautar ba wanda ya isa ya daga maganar hatta sarki Faizan mahaifinta saboda Khalifha baida sauki sam saida yasan punishment din da akayi mata idan ance gobe ta kara bazata kara ba tukunna ya sanya aka saketa.
Hurriya sati daya kenan daga dawowarta asibiti ta warke sosai sannan ta cigaba da aikinta kamar ko yaushe wasba kam kullum tare suke zuwa wankin don kamar Hurriya zata kara guduwa haka sukeji yanzu rayuwarsu gwanin ban sha’awa don Hurriya ta sake dasu Dukansu Sosai duk da bata da yawan magana amman ana yawan fira da ita haka zasu zauna karkashin wata bishiya da Bintu da inna hanne sai Hurriya da wasba ana fira mafi lokuta da dama itadai Hurriya bata cewa komai saidai tayi shiru tana kallonsu Amman tana bada hankalinta baki daya a wurin hakan kuma ba karamin dadi yake masu ba.
Khalifha kwance a wata doguwar sofa idonshi snye da glasses Sai sandar Shi Mai matukar tsada sai kyalkyali take chief of security alamomi sun nuna ya gaji da nemo masu aikin Khalifha kullum sai a kawo mashi mutane talatin amman basuyi ba yanzu bai tsayawa test din don kallo daya yake gane masu ,Don kusan duka kalar mararsa gaskiya garesu
Hurriya kallon uwar bayi tayi da take fada mata cewar zata koma aiki part din Khalifha tunda subira abinda ya fauru kenan .Shiru Hurriya tayi tana jin duk dokokin Khalifha din ita batada matsala aikinta kawai zai kaita ina ruwanta da wani Khalifha bullshit uwar bayi ta kalleta tace Amman fa zaki gana da Ayyo. Hurriya batace mata komai ba kuma itama Uwar bayi ta riga tasan bazata ce ba. Don haka ta fara tafiya Hurriya tabi bayanta har saida sukazo wani katon wuri chamber din babbace sosai don duk tafi chamber su Imad girma
Wurin an kawata shi da adon flowers tare suka isa wurin da uwar bayi aiko da sauri Uwar bayi ta fara Allah ya taimakeki tareda uwar dakinki Allah ya kara maku nasara tanata kirari da Addu’a Ayyo tayi murmushi tace Ameen Uwar bayi.kallon hurriya Ayyo tayi wadda kamar batasan da wata hallita biyu a wurin ba don hankalinta kacokam yana akan wayarta tana canza waka.
Ayyo kallon Hurriya tayi tun daga dogon gashinta har zuwa kafafunta mutum idan ba fada mashi akayi ba zai rantse da Allah ba ma’aikaciya bace a masarautar Qamar don wata red doguwar riga abaya ce a jikinta wadda tayi mata wani irin kyau gashin kanta kitso biyu ne wanda ta daureshi ya dawo kadan sumar gaban gashinta a kwance kamar ta yara sai kuma annuri da tsantsar kyau da fuskarta take fiddawa tunda Ayyo take bata taba ganin Mai kyaun yarinyar ba fararen idonta masu kama da zaiba saboda haskensu sai kuma golden brown eyes dinta da suke kara sanyawa ta zama unique acikin mutane Kallonta Ayyo kawai takeyi Because she has never seen someone with this kind of beauty tanada aininhin asalin kyau saidai mai take takama dashi a masarautar Qamar a yadda tayi ko uwar dakinta ba tayi mata haka .
Ganin kallon da Ayyo take mata ya sanya Hurriya ta dage girar saman idonta alamun lafiya kike kallona Ayyo murmushi tayi don bata taba ganin yarinya mai kwarinta ba don gaskiya yarinyar akwai confidence batasan ayyo bane ko kuma tasanta ne dagangan tayi hakan don ta burge ayyo kai gaskiya batasan ayyo ba da bazatayi hakan ba.abinda Ayyo ta gayama ranta kenan
Ayyo alama tayi ma Uwar bayi ta basu wuri da hanzarinta Uwar bayi tabar wurin kallon Hurriya tayi tace ta zauna Hurriya ba musu ta zauna tareda kallon ayyo cikin idonta tana dage gira irin make it quick I’ve things to do
Ayyo murmushi tayi tana karajin yarinyar a ranta don tabbas wannan itace zata taimaka masu wurin Ganin karshen Khalifha Qamar.
Aiki zakiyi mana inji ayyo zamu biyaki Hurriya kallon ayyo tayi don ita batada matsala da ko wani aiki tafison tayi aiki ko wani iri ne kuma wanda zai bata kudi don bata yadda da bara ko roko ba dom haka zatayi aikin.
Ahankali Hurriya ta kalleta sannan ta daga mata kai murmushi ayyo tayi tana ayyana abubuwa a ranta don wannan yarinyar daga gani baza tayi matsala ba don taga batada magana.
Kinaji shi wanda zakiyi ma aiki zaki rinka kula da duk wani motsi nashi abinda yaci inda yaje inda ya kwanta kuma har yanzu makaho ne ?
Sannan akwai magungunan da zakina barbada mashi kinaji ana biyanki dubu dari duk wata .shiru Hurriya tayi sannan tayi twitching bakinta ta kalleta sannan tace yayi kadan ,Da mamaki ayyo ta kalleta sannan tace dubu dari fa Hurriya cikin aji da natsuwarta ta daga mata kai jinjina kai kawai ayyo take don duk wanda suke sawa aikin basu taba cewa za’a basu dubu dari ba Amman sauran cikin so da kaunar hakan don kamar anyi masu albishir da zuwa makkah haka suke murna amman wannan dubu dari tace bazata amsa ba
Murmushi ayyo tayi don ta hango amfanin da Zatayi masu tace dubu dari biyu tayi?Hurriya kallonta tayi sannan ta dan ciji lebenta ta tashi tsaye tace make it 1M shiru ayyo tayi tana kallon bakinta da yake magana sannan tayi wata dariyar rainin hankali tace Miliyan daya fa kikace ?Hurriya daga mata kai tayi tana kokarin barin wurin don tagama magana bata amsar ko nawane idan bai kai 1M
Har ta fara tafiya ayyo tayi saurin dakatar da ita don ta hango alamomin nasara tattare da yarinyar sosai ma yawwa tohm miliyan daya duka kudin aikin ki? Hurriya tana kallon wayarta tace duk wata miliyan daya sannan tayi tafiyarta batare da ta kara bata second glance ba.
Uwar bayi tana tsaye tana jiranta har tazo inda ta tsaya kallon Hurriya tayi tareda cewa ya kukayi kun Daidaita shiru Hurriya Tayi mata.ita kuma ta kama bakinta bata sake cewa komai ba
Daidai inda sauran ma’aikatan suke nan suka iskesu sannan suka nufi inda chief of security yake kallon yan matan yayi yana Addu’a Allah ya sanya karshen wahalar kenan don tunda suka dawo yake wannan aikin shi kanshi Khalifhan ba yadda ya iya shike aikin Chamber da kanshi saboda tsaftarshi Amman yana bukatar masu aikin saboda girman Chamber dinshi yana fatar cewar Allah ya sanya wannan karan adace duk cikin zuciyarshi yake maganar.
Idonshi suka sauka akan Hurriya wadda fuskarta take a hade ba karamin kyau tayi ba cikin red rigar da ya kawo mata tana da kyau tanada aji duk a ranshi yake wannan maganar don zai iya rantsewa da Allah bai taba ganin mace miskila mai ajinta ba
Wata Dariya yayi a ranshi yana fatar Allah ya sanya Hurriya tayi ma Khalifa kuma babu cuta a ranta.
Kallonsu yayi sannan ya zabi wadanda zasu fara aikin kafin gobe ko jibi Oga Khalifha yayi firing dinsu don Khalifha kwata kwata bai jira.
Kallon sauran yayi yace kuyi hakuri sun isa Hurriya harta juya yayi sauri yazo wurinta yace kina cikin ma’aikatan Khalifa kema batace mashi komaiba kuma daman shima baiyi tsammanin zatace mashi wani Abu ba
Juyawa tayi ta shiga wurin ma’aikatan Khalifha murmushin da ba ko yaushe bane a fuskarshi chief of security yayi tareda juyawa ya farayi masu magana kamar haka don duk sharruddan Khalifha aka fada kuma ba wani aiki Sosai don ance banda sata banda cin Amanar oga Khalifha ta hanyar cutar dashi a abinci ku kiyaye duk wadda ta kiyaye zata zauna lafiya da Khalifha Qamar
Hurriya shiru tayi don kamar taso tasan sunan tunani ta fara sai a hankali ta tuna shine wanda ake gulmarshi a masarautar nan kenan
Palace and their issues duk tasan ire iren gulmace gulmacen da akeyi a masarauta don itama ansha maganganunta a masarautarsu
So he was the mysterious person that everyone in the palace was talking about . Shrugging tayi alamar I don’t care daman ita miye ya hadata da abinda ba ruwanta
Chief of security kallon Hurriya yayi yaji ta kwanta mashi arai saboda daga yanayin ta ita ba munafuka bace batada boye boye a yanayinta kaifi dayace don haka itace wadda ya kamata ta rinka kula da har wurin baccin Khalifa ya kamata ya huta shima khalifan
Zuwa yayi saitin Hurriya sannan yace aikin ki yafi na kowa Because you’re going to be his personal maid please kada ki cutar dashi ko nawane zan biyaki You’re going to take care of him Day &Night i will pay you ko nawane you just have to name your price kinji.
Shiru Hurriya tayi tana tunanin offer dinshi don Nigeria takeso ta bari shiyasa ma tace ma ayyo miliyan daya dazu ,ya kamata ta canza wuri saboda kawai she’s not feeling safe a masarautar Qamar din tanajin wani feeling na uneasiness kuma tunda ta fara jin wannan feeling din ya kamata ta bar masarautar saboda zuciyarta na bata cewar masu tracing dinta sun fara kokarin ganota ko kuma dai akwai abinda ke jiranta
Shiyasa take bukatar taje saudiyya tayi ibada hade da extending din kwanakinta acan kilan idan ta tafi saudiyya tayi shekara biyu acan idan ta gama shekara biyu sai ta samu Europe country mai sauki taje can ta cigaba da zama koda Canada ce tasan ba zata rasa abinyi ba yanzu a kullum wannan tunanin take she’s desperate to get money ta tafi her instincts is telling her to leave this palace soon idan ba haka ba tohm something big is going to happen she’s having this feeling these days.
Shiru tayi tana kallon cheif of security she can’t reject this offer ina tana bukatar kudi minimum 5mil maximum kuma 10mil she can do better she can do it ahankali cikin calmness dinta ta dage gira tace your conditions.murmushi yayi don yarinyar gaskiya tana burgeshi tanada aji ba kadan ba ga kyau na daukar hankali ga mulki ga miskilanci murmushi yayi sannan yace abinci sau uku a rana kuma ki tabbatar da duk abinda zaki bashi zaici sannan ke zakina gyara mashi daki ki hada mashi ruwan wanka hade da bedtime story idan yayi Bacci sai kiyi mashi addu’ar bacci and abu na karshe kada ki sake ki bari ya koreki saboda abinda yafi komai sauki kenan
Shiru Hurriya tayi tana kallonshi bata ko kyaftawa har ya kai aya sannan tace nawane zaka biya? Murmushi yayi yace name your price money is not my problem.hurriya tsotsar bakinta tayi tace 2.5M everymonth chief of security murmushi yayi yace indai zaki iya it’s a deal a hankali Hurriya tace Deal sannan yace mata thank you. Har ya juya ya dawo yace mata na baki nan da 3weeks ya fara cin abincin da kika dafa idan har 3weeks tayi baici ba tohm the deal is canceled duk idan bakiyi duty dinki ba tohm bazan baki kudin ba.Shiru tayi ba tareda ta kara cewa komai ba don abun will be very tough for her because after all sunanta Hurriya Faisait Hamood ba komai take tolerating ba rayuwarta Amman it seems like she will tolerate so much of shit this time around da takeso tabar masarautar Qamar.
Yau ta kama zata fara zuwa aiki part din Khalifha Qamar su dayawane ba ita kadai ba Saidai ita personal maid dinshi data zama aikinta ya bambamta dana kowa don haka da wuri ta tashi duk da daman yanzu ta rage makara sallahr asuba saboda idan wasba ta tashe ta a bacci tana komawa wasba zata cigaba da kukan karya har sai Hurriya ta tashi .Saidai ta kalli wasba din taje tayi alwala ta dawo tayi sallahr yanzu har ta saba.
Uniform ne ta sanya sunata kamshin turarenta tun wanda chief of security ya siya mata lokacin da ta kwanta asibiti gashinta a daure yake wanda ya cika sosai yayi yawa ga tsawo don haka ta tattare shi ta daureshi tare da cusa tikar gashin cikin gashin yadda bazata fito ba.
Tayi kyau sosai ba kadan ba don haka ta fito Daidai kofar ta iske uwar bayi wadda daman da alama Hurriyar take jira don haka tace mata Hurriya ahankali hurriya ta juyo tana kallonta Uwar bayi tace har an fito daga mata kai tayi.uwar bayi tace ayyo tana bukatar ganinki zaku ida maganar da kukayi jiya. Hurriya daga mata kai tayi sannan tace idan nagama aiki ta juya tabar mata wurin.
Tafiyarta a hankali Saidai yau ba earpiece a kunnenta har ta kawo part din Khalifha Qamar kusan kowa yazo duk da safiya ce kallon abokan aikinta tayi wanda sai dadi sukeji da alama
itama kallonta suka rinkayi kamar zasu cinyeta
Ba wanda ta karayi ma second look acikinsu ta haura sama inda take tunanin tanan zata iya shiga dakinshi wow kawai take fada a ranta data faracin karo da parlon shi na sama komai na parlon look mysterious don bata taba ganin an kawata wuri da dark color ba kuma dark color din yayi kyau irin parlon shi ba hatta fentin parlon dark brown ne sai kujerun da aka kawata parlon dasu brown and black everything is screaming rich and elegant and everything look so mysterious and dangerous color din parlon kadai yagama defining waye mutumin komai na parlon yayi mata kyau and she fall for the dull color don itakanta batasan dark color nada kyau ba sai yau Because ita tafison light color because of how neatness she was so tafison light color for the first time wani abu ya burgeta wanda ba nata ba a rayuwarta tunda take rayuwarta wani ko wata baya burgeta ko abun wani ya burgeta babu Saidai ta burge mutane ko akwaikwaye ta haka rayuwarta take.
Sauke ajiyar zuciya tayi ta bude dakinshi a hankali Saidai kamshin da taji ya sanyata lumshe ido duk da cikin kamshin tanajin irin danger da power da kamshin yake emanating dakin yayi wani irin dim Amman tana kallon yadda yake dukunkune cikin dark duve wanda ya rufe ko ina a dakin sanyin Ac dakin ya kaishi karshe duka Ac biyun da split da standing ac wanda sanyi ke ratsa ko ina a kashin mutumin .
Switch ta kunna na wuta tana kallon dakin in awe saboda haduwarshi don komai dark brown ne mai matukar kyau da tsada ajiyar zuciya ta saki sanyin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login