Showing 57001 words to 59144 words out of 59144 words
Chapter 20 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel
da safe Khalifha ne ya shirya masu breakfast tareda gyara sama inda suke rayuwa don ya lura Hurriya kusan irin halinsu daya da ita ba’a peeping privacy dinsu don yagane hakan shi yasa komai ita takeyi idan ya danganci sama inda suke rayuwa
Lafiyayyen breakfast ya hada masu sannan ya shirya a table din sama lokacin Hurriya har tayi wanka ta shirya cikin wata abaya baka mai kyau idonta da kwalli wanda yayi mata wani irin kyau na ban mamaki da daukar hankali Khalifha kam murmushi yayi yazo ya dagata yace you look so beautiful and alluring my love murmushi tayi mashi wanda ya narkar mashi da zuciya tace thank you.
Shine ya zuba mata abinci sannan yanaci yana bata abaki yana kasheta da murmushi Hurriya kam mamakin shi takeyi wai daman Khalifha dan soyayya ne haka.
Bayan sun gama cin abincin ne yaga call din chief of security wanda bai saba kwata kwata kiranshi a irin wannan lokacin ba .Dauka yayi ya sanya a kunneshi yana kallon Hurriya da take lumshe ido alamar bacci takeji
Amsawa yakeyi cikin yanayi natsuwa da kuma kwarjininshi yana gama wayar ya kalleta yace zai fita sunyi Baki a masarautar, Hurriya rungumo shi tayi ta bayanshi tace zata bishi murmushi yayi yace mata okay.
Tare suka fito ita dashi wanda suka haska ina they look so perfect together haka suka taho
Khalifha da kanshi ya bude ma Hurriya mota yana tarairayarta kamar kwai convoy dinshi ne suke wani irin Gudu har sukazo inda ya kamata su tsaya acikin masarautar.
Taro ne yayi taro don harabar wurin cike take da hallitun dake cikin masarautar don tarbar sarki Hamood wanda ba’asan da zuwanshi ba sai yau an hallara an bayyana kuma anyi makeel
Khalifha kam koda ya bude ma Hurriya mota taga mutanen saida tayi mamaki don haka ta tambayeshi miyake faruwa murmushi yayi yace babban bako ne yazo masarautar mu murmushi tayi tadan lakuci hancinshi tace kaine ai babban bakon Khalifha dariya yayi tareda yi mata peck a hannu yace so you can joke?murmurshi Hurriya tayi tace I’m humaan too Dukansu dariya sukayi yanda tayi abun so childish.
Khalifha da kanshi ya samar mata kujera kusa dashi ta zauna inda iyalan Qamar kawai ke zama wurin.
Suna zama saiga subira tazo tana tafiya cike da izza da nuna isa Hurriya kallonta tayi sai kuma ta tuna abinda tayi mata zuciyar Hurriya bugawa saboda rashin daukar fansar da tayi sai kuma dazu ta tuna nasihar da Khalifha yayi mata na mutum ya kasance mai yafiya shima sai Allah ya yafe mashi tunawar da tayi kawai sai ta shareta
Nesa dasu subira ta zauna.saiga sarki Faizan ya hallara shida tawagar shi cikin shiga ta alfarma.Hurriya kam dan kwantowa tayi jikin Khalifha saboda wani bacci da tarinka ji yana dibarta murmushi Khalifha yayi
Mutane kam sai kallonsu suke zinariya ce data dawo daga tafiya wadda batasan wainar da ake tonawa a masarautar ba tace ke mi nike gani haka can yar aikinta tace hmmm ai baki nan ansha drama don ingaya maki Khalifha ya auri waccan yar girman kan zinariya wani irin fargaba ta shiga don duk tarin kaunar da tayi ma Hurriya ace Khalifha ya aureta kuma tasan halin Khalifha Daidai yake da kowa acikin masarautar don duk barikinta da tashar ta ba zataje tace tanason Hurriya ba daga gani sai hange.
Sanarwa aka farayi tareda kirari gafa sarKi ya iso kirari akeyi mashi kamar kamar mi tareda busa da waka.
Convoy ne na motoci masu mahaukatan tsada don security’s ne kota ina a motocin wasu kuma a mashina bike sai kuka sukeyi
Tunda suka nufo masarautar ake masu kirari kota ina family guda don akwai wa’inda suka taho dasu daga dubai daga jin cewar sarki Hamood zaije Masarautar Qamar kowa yace Zai bishi.
Hurriya kam runtse idonta kawai tayi tana shakar numfashin mijinta da kamshin shi, hayaniyar kidin ya isheta Khalifha kam lura da haka sai ya karkato yana mata fira ahankali don har suka iso batasani ba
Securitys ne kota ina suna ma sarki Hamood da iyalanshi clearing hanya manya manya security’s masu karfi.
Wurin shiru ya dauka don banda kamshi ba abinda ya dauka kamshin masu kudi.
Hurriya kam kamshin da bazata taba mantawa dashi taji cikin baccinta gyara kwanciyarta tayi tareda gargadar kanta akan yaudarar kanta datayi sannan ta cigaba da baccinta.
Kusan family guda ne kowa cikin gayunshi don ko su Neela irin gayun yan masarautar sukayi wato English wears sunsha kyau abunsu
Ba wanda bai rusuna ma sarki Hamood ba ta hanyar dukar dakai kadan sannan aka bashi kujera ya zauna
Sarki Faizan har inda yake yazo gaisheshi Khalifha ma dai hakan yakeso yayi yazo ya gaisheshi amman Hurriya ta hana don ta rikeshi gam
Galadima haka akaje ana faduwa ana gaishe da sarKi Hamood sarki Hamood hannu kawai ya daga mashi zoka ga dadi wurin Galadima don daga mashi hannun da yayi kawai ya sanyashi yaji wani irin farin ciki ya mamaye shi.
Kowa acikin family sun zauna saidai Hamood shima yana zaune saman kujera ta alfarma yana kallon kowa acikinsu wani irin yanayi yakeji saidai bazai iya fassara kalar yanayin ba.
Hamdan kam tunda sukazo yake dube duben inda zaiga Hurriya Amman bai ganta ba Hamood ne yace mashi ya kwantar da hankalinshi
Hamood yayi mamaki da Khalifha bai zo ya gaishe shi ba,saboda mutumin shi ne kallon ko ina yakeyi domin yaga Khalifha amman bai ganshi ba
Amrah ce ta hango Khalifha rungume da Hurriya wadda da kyar zaka iya ganinta
Amrah da sauri tabar wurin Hamdan ta ruga aguje ta haye Hurriya hade da rungumeta Hurriya kam cikin bacci taji wata mahaukaciyar runguma aiko da saurinta da zafin namanta ta ture amrah har tana faduwa aiko wani kuka da tayi saida yaja hankalin duk wanda yake kallon abinda yake faruwa.
Kowa yana mamakin Hurriya da al’ajabin abinda zai faru saboda agaban sarKi Hamood wanda yake kaka ga amrah ta ture ta .
Tabb ba Khalifha take aure ba kowa take aure yau tana ruwa don sarki Hamood bazai taba barin hakan ba.
Hurriya kam shigewa tayi jikn Khalifha taci gaba da baccinta tunda taga Amrah ce though taganeta kuma maganar gaskiya tayi missing dinsu Amman hakan bazai bata damar tashe ta daga Bacci ba.
Hurriya har ta koma bacci sai tace wait wai suwaye bakin ta fada cikin ranta kamshin turarenshi wanda saboda tsadarshi da kamshin shi bai taba boyu shine ya dawo mata gashi har gobe bata taba jin wani da kalar kamshin ba shikadai ta Sani da wannan kamshin indai hakane toh that means ya biyo grandchildren dinshi.
Dagowa tayi don ta tabbatar da hakan wanda cikin sa’a tana dagowa suka hada ido sarki Hamood kam ya kasa yadda da abinda idanunshi ke fada mashi cikin muryarshi yace Hurain Hurriya kam ta rasa mi zatayi don kafafunta suna neman gagararta daukarta
Cikin wani irin yanayi da sauri ta ruga ta rungumeshi kam Shima Hamood rungumeta yayi sosai wasu hawaye na taruwa a fuskarshi itama haka Hurriya idanunta suka cika taff da hawaye dagota yayi domin ya kara ganinta yace Hurain wai kece murmushi tayi mashi ta daga mashi kai tace nice.
Wurin duka shiru ya dauka yan uwan Hurriyar da sukazo kowa yana mikewa tsaye yana kallon ikon Allah.
Ma’aikatan masarautar kam kowa kallon ikon Allah yakeyi tareda mamakin yadda Hurriya ta kasance jikar Hamood jikar Hamood ai zata iya siyan masarautar Qamar da duk wata babbar masarauta dake amsa sunanta masarauta anan kusa.
Shine zatazo aikatau amman no wonder shiyasa takeda isa da kwarjini.
SarKi Hamood rike fuskarta yayi yace kina cin abinci daga mashi kai tayi tace kina cikin jin dadi daga mashi kai tayi sannan tayi murmushi tace I got married sarKi Hamood bata fuska yayi yace to whom saita nuna Khalifha wanda yake tsaye yana murmushi.
Hurriya dagowa tayi idanunta kawai suka sauka akan Qalbi Hera yana aika mata da wani kallo
Saidai abin mamaki sai kawai ganinshi sukayi ya fara cire kaya yana ihu zaizo wurin Hurriya
Da sauri securitys suka rikeshi yanata hau don kamar baida hankali
Wasu ihu ya fara yana maganganu sannan aka fitar dashi.
Ba wanda baiyi mamakin kasancewar Hurriya jika ga sarki Hamood ba masu tsoro naji masu bakin ciki nayi masu tayata murna nayi.
Fada ce mai matukar kyau duka yan uwanta suka hallara kowa shiru yayi yana jiran Hurriya ta fara bada labari
Labarin abinda ya baro Hurriya Heral.
Cikin natsuwarta tace lokacin da ina Mexico ina fashion school sai kuma zanje wani fashion show a paris lokacin tun ina Mexico Qalbi hera ya kirani yace daughter gani a Mexico zanzo mu gaisa cewa nayi uncle gaskiya nagama shiryawa yanzu zan wuce airport ina kuma za’a Hurriya sai na fada mashi France
Saida ya tambeyin gida zan sauka nace mashi Aa na fada mashi hotel din da muke sauka nida parent dina.
Kwana biyu nayi à Paris sai gashi ya Kirani yace ki fito ki amshi sako ban kawo komai araina ba na fita don saida na fito sosai tukunna naga black car
Tsayawa nayi nace nazo ya fito to my biggest surprise kawai sukayi abdicating dina
Nayi kuka sosai don wata kalar rayuwa mai ban wahala ya rinka bani anan naji cewar rasuwar iyayena is not an accident it was a murder
Ruwan sanyi haka yake zuba mani kuma yasan ciwona and everyday he want to sleep with me cizo ya kushi ba wanda banyi I hate body contact duk duniya ba abinda na tsana irin haka haka kullum.
Don ranar da bokanshi ya bashi ikon cewar he can sleep me ni kuma ranar na gudu don da karfinshi yazo saidai cikin ikon Allah self defense din da Hamood ya koya mun na samu damar kwatar kaina
Tunda na samu na fito na tattara komai nawa nabar Paris wanda kuma har wata letter ya karanta mani wai kaine ka bashi ya bani dana karanta sai nima na rubuto maka tawa letter.
Duk wasu kudina da nike dashi a wani account na samu na cire sai nayi tranfer ga wani sai ya bani dollars haka nayi har na samu nayi spending sati biyu saboda passport din dana karayi da komai da komai
Nigeria ce tazo mani saboda itace kawai nasan bazai taba tunanin ina nan ba.don bokanshi ne yace sai sun wulakantani da rayuwata shine nayi nisa da gida.
Sai tabasu labarin Khalifha Qamar da yadda shima aka biyata ta cutar dashi da har yanda sukayi aure
Kowa jinjina al’amarin ya farayi Sarki Faizan ne ya fashe da kuka shima ya fara bada labarin tuggun da sukayi ma Khalifha da asirce asirce wurin shiru ya dauka har yagama ya nemi gafarar Khalifha don baisan an makantar da Khalifha ba saida ga bayane mahaifiyar Faizan take fada mashi hakan.
Wurin shiru ya dauka Khalifha kam yace ya yafe mashi amman bazai taba yafe masu Galadima ba don yanzu Faizan yake fada mashi cewar ashe humain trafficking suke da yan matan masarautar.
Faizan ne ya kalli Hurriya da Khalifha wanda suka burgeshi saidai yayi saurin kauce kanshi don kada shedan ya raya mashi wani abu azuciyarshi
Cikin yanayi na karaya da nadama ya kara neman yafiya hada cire ma Khalifha glashi sai gashi idonshi sun fito tagaran murmushi yayi yace danuwa yanzu zan maida maka sarautar ka tunda tun asali takace.
Murmushi Hamood yayi yace Aa ai mijin Hurain ya girmi sarautar masarautar Qamar don haka saurata babba zaiyi wato sarautar Heral palace.
Bayan shekara Daya abubuwa da dama sun faru hada little Hamood da Hurriya ta samu ga kuma Bintu da aka sanya bikinta da chief of security ga sarki Khalifha Qamar mai adalci da yake tafiyar da sarautar Heral palace cikin adalci da kuma ilimi na addini.
Hurriya ta kara gyarawa sosai don bata yadda ta fita kanta bude karatun Al-Qur’ani shime yake koya mata d komai da komai.
Inna hannne Anyi mata gidan kanta da asibitin kanta.
Ba abinda Hurriya taji dadinsho irin wasba data kasance yar uwarta itama don uwarsu daya ubansu daya dasu Hamdan munafukar matar data saceta ita tazo ta warware komai.
Su Galadima anacam ana dibar abinda aka shuka dasu Qalbiher don Dukansu hauka sukeyi.
Alhamdullilah Anan muka kawo karshem masarautar Qamar badai hakan naso karshen ya kasance ba naso nayi komai daki daki Amman ramadan da yazo ya riskemu.
Abinda muka rubuta Daidai Allah ya bamu ikon aiki dashi wanda muka rubuta ba Daidai ba Allah ya yafemana
Ku yafeman Allah ubangiji ya karbi ibadunmu.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************