Showing 42001 words to 45000 words out of 59144 words
Chapter 15 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel
kallo wani tunani ne yazo mai sai yayi murmushi ya tafi don bayan sallahr azahar ne da angama za’a daura auren hannunshi rike da takarda har ya iso masallacin
Bayan angama sallah ya mika ma liman takarda ba bata lokaci Faizan ya zama walliyyin ango wasu na amarya shidai chief of security ya zamana hurriya Don rike yake da sadakinta haka aka daura aure aka gama
Chief of security wani irin farin ciki da annashuwa yakeji don ko angon yasan bazai kaishi farin cikin aure nan ba don ji yake kamar ya sauke wani nauyi babba Alhamdulillah Alhamdulillah ya rinka fadi kawai.
Page 65
Babu Khalifha a wurin sune suke kdin su suke rawar su chief of security kam ya kasa rufe baki he hope auren nan da Khalifha yayi da Hurriya ya kasance aure na har abada saidai baisan mi yarinya take tunani ba don Kamar auren da tayi da Khalifha is to her own advantage saidai zai kasance yana masu addu’a kuma bazai fasa yi masu addu’a ba
Galadima ne yake gaisawa da mutane daya daga cikin yaranshi ne suka zo ahankali yaja Galadima tareda rada mashi wata magana wadda firgici da ihun da yayi ya jawo hankalin mutane dayawa suna kallonshi.
A wani zabure ya fito ba inda ya tsaya sai wurin chief of security cakumo wuyanshi yayi yace uban waye ya sanya acanza sunayen da na bada wato kaine munfukin ko chief of security nan take murmushin da yake kan fuskar shi ya dauke ya dawo sak irin fuskar oganshi wani irin kallo yayi mai wanda Galadima ya saki kwalarshi tare da zaginshi a wurin
Chief of security dannah bacin ranshi kawai yayi saboda yau rana ce ta farin ciki agareshi wanda ya rasa miye dalilin hakan don haka kawai ya juya ya bar wurin.
Hurriya wani irin faduwar gaba takeji tunda ta maida sunanta maimakon sunan diyar Galadima anya abinda tayi ta kyauta ma kanta kuwa? Aure fa Hurriya Faisait Hamood got married to her blind Arrogant boss shiru tayi tana safa da marwa tanason tayi tunani mai kyau tunani da tayi sosai tayi na’am dashi don auren is not a forever marriage that’s the only way da baza’a iya checking dinta ba shine kawai if not asirinta tabbas ya tonu but now they can’t dared to touch her royal body tana gama tunani ta nufi dakinsu
Ba karamin kyau tayi ba fuskarta tayi fayau sosai haka ta shiga dakinsu cire gyalen kanta tayi wanda takejin kamar an daura mata duniya saboda nauyin shi da ta rinka ji
Kwanciya tayi tareda rumtse idonta wani bacci mai nauyi ya dauketa.
Shagali akeyi ba kama hannun yaro don wani busa akeyi mutane daga manya manya masarauta sunzo
Masarautar Qamar yau ta kasance very busy sosai don shagalin da akeyi ya dauke ma dubanin jama’a hankali sosai
Khalifha kam yanzu ya dawo daga Meeting da wasu japnese don a wani irin mugun gajiye yake sosai ba abinda yake bukata irin ya kwanta ya huta saidai suna shigowa yaga hakan ba lallai ya faru ba don shagalin da akeyi da mutanen dake wurin ya tabbatar mashi da hakan
Cewa yayi calido sauya akalar concoy din akayi aka koma can baya inda wani katafaren building yake wani irin ginin ne irin na turawa wanda zaka rantse ba’a masarautar yake ba saboda tsari da kyaun ginin da sauri driver dine ya bude mashi mota ya fito yana mai tafiya da karfi ginin ba karamin kyau da daukar Hankali yayi ba don everything is screaming danger and opulence kusan komai na gidan dark color ne as always his favorite kenan
Wani katon daki ne mai matukar kyau da girman gaske don yafi dakin part dinshi girma sosai cire kayan jikinshi kawai yayi tareda sakar ma kanshi shower wanka yayi hade da dauro alwala shiryawa yayi cikin jallabiyya sannan yayi sallah yana gama addu’a ya linke carpet sannan ya kwanta tareda kara Ac
Wani irin bacci ya daukeshi cikin Baccin shi sosai ya rinka jin ringing wayarshi kamar bazai dauka ba saidai karar wayar ce ta dameshi don haka ya dauka tare da kangawa a kunnenshi chief of security ne yake mashi magana with so much respect tareda rokon shi alfarma da yazo hawan kilisar da za’ayi .
Shiru Khalifha yayi yana sauraren abinda chief of security yake cewa wanda yayi mamakin farin cikin dake kwance a maganar shi hada shi da Allah ya cigaba dayi domin hallartar kilisa da za’ayi na bikinshi yau Khalifha daya manta da wani aure nashi duk da taron da yaga anayi bai taba samun chief of security cikin farin ciki irin na yau ba don abun har mamaki yaso ya bama Khalifha saidai da yake shi bamai yawan shiga abinda bai dameshi bane don haka Jawa yayi shiru tare da cewa toh da wani irin murna a bakinshi yace thank you Kayl and please ka sanya kayan hausawa tareda alkyabba wani slight murmushi Khalifha yayi ganin yadda chief of security ya saki jikinshi dashi yau Because tunda suke bai taba kiran sunanshi ba Khalifha sun dade tareda chief of security don shekaru ne akayi tun ba’a gama girma ba
Kusan tare suka taso mahaifiyar chief of security itace jakadiyyar mamanshi sun ta rike Khalifha tsakani ga Allah kuma taso shi tsakani ga Allah don lokacin tun mahaifiyar shi na da rai
Lokacin chief of security daga kauye yake yana wurin ubanshi saidai kishiyar uwa ta rinka gallaza mashi har aka dai kasa abun karshe sai ya hakura ya dawo masarautar don haka tun lokacin shine yake ma Khalifha ban ruwa na flowers a part dinshi a lokacin he’s calm and baida hayaniya kamar Khalifha saidai yana respecting Khalifha saboda irin kyautatawar da yake mashi tun daga lokacin yayi alkawarin baida wani uban gida face Khalifha mahaifiyar Khalifha ba karamin dadi taji ba lokacin da taji alkawarin da chief of security yayi mafari kenan kuma duk dadewar da sukayi tare banda girmamawa da ba abinda ke ya tsakanin Khalifha da chief of security duk yanda Khalifha yaso ya daina kiranshi da sir ko wani suna da yake nuna shi ogane amman sam yaki yaune ranar da yaji kirashi da kyal kuma hakan ba karamin dado yayi mashi ba
Cikin shine yayi kuka Ahankali ya shafa shafeffen cikinshi tsoki yayi tunawa yayi da baici abinci ba abun yana damunshi wai miye damuwar shi da abinci stubborn maid dinshi don kwata kwata yanzu cikinshi basu gane ma fruit saidai abincinta tsoki yayi tareda shiga toilet ya sakar ma kanshi cold shower
Banda kamshi ba abinda yakeyi kugunshi daure da wani grey towel gashin kanshi da na jikinshi duk sun kwanta sai wani haske da annuri yake yi
Haken fatarshi ya wani fito yana haskaka ko ina kamar rana,
Saida ya shafe mai da deodorant ya sanya inner wears sannan ya shirya cikin wani dark blue yard mai matukar kyau da tsada ba karamin kyau sukayi mashi ba don sun fito mashi da tsawonshi da giant dinshi don wani irin kyau yayi Sosai
Yana fitowa parlo ya iske chief of security da sauri ya dan rusuna mashi tareda mika mashi wata Leda sai kamshi take yi Khalifha da mamaki yace what is this murmushi chief of security yayi yace your wedding gift please into it Khalifha kallonshi yake da mamaki wedding gift daga mashi kai chief of security yayi da wani irin pleading eyes yace please ka sanya I put so much effort
Khalifha kamar bayaso haka ya dauki ledar ya shiga da ita dakinshi fito da kayan yayi farar shadda ce mai kyau da tsada don tsada ba kadan ba sau wata alkyabba mai masifar kyau da tsada hula da takalmi duk masu kyau haka suke
Khalifha kamar bayaso haka ya canza kayan jikinshi zuwa fararen kayan da chief of security ba karamin kyau yayi ba daya kalli madubi don bazai iya tuna when last ya sanya kaya masu haske haka ba
He looks calm and handsome hular ya sanya hade da alkyabba
Kamshin turarenshi ne ya sanar da chief of security zuwanshi don haka tare suka fito.
Hurriya cikin Bacci ta rinka jin hayaniya bude idonta tayi ta murza su saidai su Galadima ne cikin dakin don Galadima idonshi har wani jann bacin rai sukayi don tijara ce da azalzala kawai ke a idonshi
Bincike Hurriya suka zo yi wadda ta tashi daga bacci yanzu.Yaran Galadima ne suka zo zasu tabata cikin yanayi natsuwa kuma da isa da mulki tace are you mad tana watsa masu kallo wani takadari ne acikinsu yazo zai finciketa muryar chief of security yace Do you want to die?
Durkusa mata yaran Khalifha sukayi kowa yanata Allah ya taimake ki Allah ya baki nasara Galadima bakin shi bude
Hurriya kwance samam gadon Khalifha da dare bacci ya dauketa shigowa yayi tareda kallon saitin da take shikam har yanzu ya kasa amincewa da abinda chief of security yace mashi wai she’s among his wife
Kallon small figure dinta yayi wanda take Bacci hankali kwance zuwa yayi saitin da take kwance domin ba abinda yakeso yanzu irin tayi mashi bayanin dalilin aurenta.
Page 66
Yanason yaji miye ba’asin maganar don bayan sun fito shida chief of security dazu shine yake yi mashi albishiri da cewar wai ai Akwai Hurriya cikin matan shi tambayar shi yayi wacece haka da murmushi chief of security yace mashi your personal maid
Nan take Khalifha ya ganeta wato wannan yar rainin wayaun mai aikin tashi he wondered what is her motive don ya tabbata akwai dalilin da ya sanya ta aureshi he promised zai gano koma wani dalili ne kallon cheif of security yayi da Question mark sannan yace Are you the one instigated the idea girgiza kanshi yayi sannan yace I’m not the one sir but I hope the marriage idea will work out shiru Khalifha yayi sannan sukaje ya zauna a kujerar da aka tanadar mashi kusan kowa yana zuwa yayi Allah sanya alheri amman ba don Allah ba don wasu san ba inda auren zaije don ba yau bane aka fara daura mashi aure ba saidai kusan kowa yasan zancen da sun tare suke cewa a raba auren
The event was cheerful anci ansha saidai Khalifha duk a takure yake
Hurriya kam abunda ya faru jiya tunda taga Galadima yazo da mutanen shi ta tura ma chief of security urgent text yazo aiko ba’a wani dauki lokaci ba suka zo suna bata girmanta shida yaran Khalifha masu firgita mazaje
Ba karamin mamaki da rudani mutane suka shiga ba da jin cewar Hurriya matar Khalifha ce don abun sai ya zama kamar show manya manya mata da kananun mata suka zo suna kallon ikon Allah da yawa kam sun rasa bakin magana don bakin ciki ne ke cikin ransu zalla wasu kam sun san cewar tana cikin wahala ta rasa wanda zata aura sai dodo wanda yake tsorata mutane tareda firgita su don haka abun bai kai suyi mata bakin ciki ba da kanta zatayi kuka
Galadima kam irin tashin hankalin daya shiga ba’a sanya mashi rana don yarinyar nan ta mamaye shi sosai Khalifha fa ta aura ta ture diyarshi taje a matsayin mace ta hudu ba kalar shirin da basuyi ba wannan karon don ganin cikar burinsu don makudai kuma miyagun kudade ne suka kashe masu yawan gaske duk saboda irin wannan rana wadda zatazo masu da cikar burinsu shiyasa yace ma sarki Faizan da ayi ma Khalifha aure saboda nashi burin Amman ace hakane ya faru
Bazai taba zuba ma hurriya ido ba don alkawari ne ya daukar ma kanshi sai ya kasance da ita kuma tareda yi mata wulakanci mafi kaskanci acikin masarautar da ita lallai dashi take magana
Yanaji yana gani anata girmama ta don gani yayi kamar daman can asalin jinin sarauta ce don yadda salon tafiyarta da jiji da kanta ya canza baisan cewar dama can haka take ba ko kuma ya manta da hakan
Cikin wata zukekiyar ferrari chief of security ya bude mata hade da convoy din Khalifha suka tafi
Ainihin Chamber dinshi ya kaita wanda tana sallah ta kwanta don wani bacci dake idonta .
Kallonta Khalifha yayi maganar gaskiya he is tantalized don she’s beautiful gashin kanta da duk yadan sauko ya gyara mata ya cigaba dayi mata kallo marar dalili jira yake ta tashi daga Bacci yaji dalilin auren shi da tayi ahankali kuma yace ma kanshi are you sure is that the reason smirk yayi sannan ya tashi sai kuma ya dawo
Wani siririn gashi ne ya sauko mata a fuskarta wanda ya sanya shi stop hannunshi masu kyau da laushi kamar na jarirai ya sanya ya janye mata wanda yayi Daidai da bude idon hurriya tarr a a nashi idon kallonshi tayi sannan tayi frowning face dinta tace how dared you touch me Khalifha kallon bakin da yake maganar yayi shidai yana mamakin rashin kunyarta da rashin tsoronta Amman bai taba kulata duk abinda takeyi mashi ba kawai
baisan mike damunshi ba but he just want to played along or try to annoy her don since ranar daya fara saninta yasan miye bata so a rayuwarta so he will make sure he annoys her today
Kallom yanda take frowning fuskarta tayi in an annoying way matsowa yayi kusa da fuskarta gaf da gaf Hurriya kam matsawa ta farayi har yanzu ba tareda ta daina bata fuska ba Khalifha kam yanda takeyi ma ya kusa ya bashi dariya don kamar taga kashi haka take bata fuska but she look so cute and beautiful har matsowa ya cigaba dayi itama tana matsawa har suka kai fuskar gadon wadda babu wani space da zai tareta wani kallo yake binta dashi wanda takejin idanun shi Sosai akanta duk da idonshi rufe suke da glasses shikanshi Khalifha baisan mi ya sanya yake yawon kallonta ba kwana biyu bai gajiya kwata kwata da kallonta har yana rasa dalilin hakan
Hurriya kam tasan halinshi ta karance shi don tasan miyake da niyyar aikatawa right now aiko bata ida tunanin abinda take tunanin ba saidai ki tayi ya jawota ta fada saman jikinshi wani kallo banza takeyi mashi tace how dare you touch me shima murmushi yayi sannan yace how dared you married me shima yayi raising brow dinshi guda he really is cute she will admit that saboda yanda yayi
Hurriya sauri tayi ta daina wannan tunanin tareda kokarin kwace kanta a wurinshi
Amman ya gagara don Khalifha is not her mate cikin muryarta da accent dinta mai dadi tace kabari Please it’s disgusting please tace mashi kallon yanda tayi da bakin yayi ahankali kam ya fara matsowa da bakinshi saitin bakinta Hurriya kam kallon abin yake kamar a mafarki this blind man is trying to kiss her fa subahanallah tace tareda buga mashi goshinta da dan karfi kusan atare suka ce ouch don duka sun bugu
Khalifha kam glasses dinshi ne ya cire wanda idanun shi masu matukar kyau da kwarjini suka fito Hurriya kam bakinta ta bude tana kallonshi da wani irin mamaki tace you’re not blind
Shima kallonta yayi tareda frowning face dinshi irin yanda tayi yana imitating dinta she’s the first person acikin masarautar Qamar da tasan he’s not blind and why was he not reacting she knew his secret but he’s not ready or willing to react why?
Kallpnta yake da lafiyayyun idanunshi masu kyau da kwarjini hurriya itama kallonshi takeyi tana admiring dinshi yanada idanu masu kyau haka why would he pretend to be blind gaskiya he did injustice to his eyes kallonshi ta rinkayi wanda shima kallonta yakeyi ba ko kyaftawa saidai idanunshi sunyi mata yawa akanta ahankali ta sauke idonta tare da cewa please let me go ahankali ya zare hannunshi daga nata ya saketa ta sauka daga kan gadon
Kallon kayan dake jikinta yayi shiru yayi har yana kallonta tabar dakin shi.
Ba inda ta nufa sai dakinsu wanda su Bintu suke zaune suna jiranta domin jin dalilin auren wasba ce ta rungumeta bata fuskarta tayi what’s wrong every one in this place they really love skin contact janyetq tayi a jikinta sannan ta kalli bintu , inna hanne data shigo yanzu a kitchen taji labarin abinda ya faru ba wanda ya kaita jin dadi labarin abinda ya faru don tasan yarima shi kadai zai iya boye mata sirrin ta sannan ya taimaka wuri kareta daga sharrin masu sharri a masarautar nan.
Jakadiya ke hidima wurin tarewar amaren Khalifha Dukansu acikinsu ba wadda ba daga prestigious family ta fito don iyayensu masu kudin gaske ne kuma cikinsu ba wadda ba mai kyau bace Amman abin mamaki miye suke nema a duniya wanda basu dashi sun sha jin cewar aure Khalifha sam baida dadi kilan they want to see it in person abinda yake faruwa din
Jakadiyya da sassy beauty a great makeup artist sune suka shiryasu ba karamin kyau kowacce acikinsu
Ba karamin canza masu kamanni sassy beauty tayi ta hanyar fito masu da wani irin kyau da talent dinta na kwalliya ba don kamar kasace su ga kayansu masu matukar tsada da aman kudi haka kowacce ta sanya alkyabbarta acikinsu
Cikin Zuka zukan motoci akazo aka dauki kowacce acikinsu aka kaisu Chamber din Khalifha.
Jakadiya da duk duty dinta ne tasan yanda abun yake don dakunan daman an gyarasu anyi sabbin funitures masu kyau Dukansu ko wacce dakinta akasa yake anan kowa ta shiga acikinsu
Jakadiya ta fada ma chief of security angama kallonta kawai yayi tareda girgiza kai,what are they achieving by doing that sun san cewar kusan 8yrs duk auren da Khalifha yayi ba taba working ba kuma duka auren baida choice a matan Dukansu baya sonsu Amman ake daura mashi aure dasu saboda kawai su bata mashi suna
Abin haushin wato shine da matan basu daddara they are mongers they don’t want anything except for fame wanda duka iyayensu sunada abinda