Showing 24001 words to 27000 words out of 59144 words

Chapter 9 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel

26 Mar 2025

29934

batace komai ba don Komi za’ayi a wurin ba zatace uffan ba indai ba gamacin abincinta tayi ba.
Khasheem ya kalli Khalifa yace Kayl join us I’m sure you will like the food haka shima fayrouz yace cmon gee join the food da dadi saida suka rinka magiya sosai sannan ya zauna yayi bismillah ya faraci.
Kallonshi suka rinkayi da mamaki don basuyi tunani zaici so easily haka ba.
Hurriya wani irin dadi taji they really did help her in this battle don batasan ta yanda zata fara a cewa yaci abincinta ba, yau za’a sanya mata 2.5m ta riga tayi deciding tabar kasar with 3.5m tasan cewar kudin zasu kaita saudiyya.





Page54
Kallon dakin Khalifa mai tsari da kyau tayi sannan ta sauko ahankali ta shiga toilet saida tayi activities dinta sannan ta tara ruwa a bahon wankanshi cike mai kamshi tayi wankanta mai dadi.sannan ta ziro dogayen kafafunta da banda silbi da salki ba abinda sukeyi cikin bathrobe dinshi da suke hang ta dauki sabuwa ta sanya sannan ta fito saida ta bude wardrobe dinshi ta samu kaya masu rashin nauyi kuma da alama zasuyi mata ta sanya
Gyara dakin tayi tass tareda wanke toilet ta sauko kasa sannan ta shiga katon kitchen dinshi tayi yamrita da coconut milk masu dadi har tagama komai tayi arranging ba wanda ya fito shrugging kafadarta tayi irin I don’t care ta zauna ta zuba komai kadan kadan kuma dai dai cikinta a hankali ta rinka cin komai har tagama tana gama cin abinci ta shiga kitchen ta wanke kayan data bata sannan ta gyara kitchen din.
Wani takarda ta gani a saman kitchen island ahankali takai hannunta ta dauka note din fayrouz ne yace mata tayi hakuri baiyi mata Bankwana ba they’re gone for a business a in Mexico she should take care of herself for him sannan yayi mata kalamai masu nuni da zaiyi missing dinta Hurriya kam cikin dustbin ta sanya takardar.
Saida tayi bacci wanda ya isheta sosai sannan ta fita jikinta sanye da kayan Khalifa wanda duk inda ta gifta kallonta akeyi.
Daidai zata sha kwana taga shaho da kaura suna kallonta kallonsu tayi sannan tayi tafiyarta.
A bakin kofa tagasu Hansa’u da su barira da wasila da suwaiba Dukansu dai. Hurriya kam kallo daya tayi masu ta shige daki while su kuma sun kura mata ido tunda ta taho har ta bace masu dagani.
Ahankali ta zauna sannan ta kalli wasba da take kwance tana bacci Hurriya kallon kamanninta takeyi don ko zata tuna dawa take mata kama Saidai hakan ya gagara, gashi gareta wasba sosai kuma baki mai kyau da cika irin na Hurriya
Hurriya batasan ya akayi ba kuma batasan garin ya hakan ta faru ba Amman tanajin tsananin kaunar mutum uku a masarautar Qamar ko kuma mutum biyu saboda ai Bintu tun akauyensu take jin kaunarta har cikin ranta.
Bata shirya ma hakan ba saboda tasan kalubale da sarkakiyar datake cikin rayuwarta kuma tasan cewar itadin ba mazauniya bace ako wani lokaci zata iya canza wuri Saidai ya zatayi itama she got heart like every human being she have feelings and emotions Saidai barrier dasuke dashi ta riga ta dakatar dasu yanda bazasu taba kawo mata cikas ba a rayuwa.
Bintu ce ta shigo ta zauna kusa da Hurriya tana kallonta cike da so da kauna don babu abinda Hurriya batayi mata ba.Tayaya zata fara tunanin cin amanar Hurriya bayan tasan yadda Hurriya take kaunarta duk da bata nunawa idan har taci amanar Hurriya tabbas amanar Allah zata cita ina bazai yiwu ba .
Hurriya kallon Bintu take tanaso ta karanci damuwarta don banda ramewa ba abinda takeyi kuma damuwa tsoro da alamar firgice duka ya nuna a fuskarta. Bintu kam duk ta tsargu sosai da irin kallon da Hurriya takeyi mata ba abinda take tsoro irin Hurriya ta tambayeta miye matsalarta don Hurriya nada matukar kwarjin idan kana kallon idonta bakasan lokacin da zaka fada mata gaskiyar lamarin ba.
Bintu da sauri tace Hurriya bari naje na amshi aikina na kitchen ban karasa ba nazo nan.
Daga mata kai kawai Hurriya tayi don ta lura da ita so take ta tsere mata.shiru Hurriya tayi trying to figure out what was bothering her friend Saidai to no avail ta rasa minene Amman zata gano da kanta.
Bintu na fitowa a firgice kuma a tsoroce Saidai ganin da tayi masu kaura da shaho yafi firgita ta don batayi tsammanin ganinsu ba anan.kallonta Dukansu suka rinkayi irin muna jiran bayaninki ganin Bintu tayi shiru kamar bazata basu amsa ba shaho da baida hakuri yace ke malama kin zuba mata ko baki zuba mata ba.shiru bintu tayi cikin wani irin zafin nama ya wanka mata mari yace magana fa nike maki
Bintu da wani irin rude ta dafe kai tace mashi zan zuba mata à abincin da dare yanzu tana kallona ne shiyasa ban sanya ba kaura ne ya kalleshi alamar ya kyaleta Bintu kam ajiyar zuciya kawai ta saki sannan ta dukar da kanta suna barin wurin ta samu wuri ta zauna
Su barira ne da Hansa’u suka zo sukace shawara ta rage taki yarinya ki zuba ko karki zuba munafuka
Barinta sukayi da sakin baki.
Galadima kanshi akasa ya mika mashi farin kyale da zanen wani abu ajikinshi mai martaba Faizan ya kalleshi alamar yanason yaji karin bayani
Allah ya taimake ka yace tana acikin masarautar nan Saidai har yanzu ya kasa ganeta Saidai wannan zanen tabbas ajikinta akwai wannan zanen don ba karamin aiki yayi ba kafin ya samo wannan zanen saboda akwai kariya tattare da ita sarki Faizan kallonshi yayi tareda mika hannunshi ya amshi handkerchief yana kallo wani murmushi yayi na gefen baki tatoo ne na Heral palace dole ake cewa wanda ya sameta zaiyi sarauta kowace iri.
Galadima yace yawwa maganar da kayi man nayi ma jakaddiya magana tace ayi sauri ayi kafin Khalifa ya dawo
Shiru sarki yayi yana nazarin abinda Galadima yace don tabbas a irin wannan lokacin ya kamata ayi abun nan don yadda Khalifa yabar masarautar ,don yanzu yana cikin shakka saboda yadda Khalifa yazo ba tareda ya sanar da kowa ba yasan zai dawo ba tare da ya sanar da kowa ba kuma koda yake sarki yasan Akwai abubuwa da dama da bazai iyayi ba agaban idon Khalifa ba saboda yasan waye Khalifa and what he’s capable of doing.
Sarki yace ku samo matan kamar yadda akeyi ita kuma yarinyar ya za’ayi mu ganeta inji Sarki Faizan
Galadima yace Saidai a sanya jakadiyya ta duba manah sai asan mi za’ace masu a masarautar. sarki na’am yayi da hakan sannan Galadima yayi Bankwana ya fita.
Hurriya wayarta ta dauko tana budewa taga alert din 2.5m as promise don tun ranar da Khalifha ya faracin abinci chief of security ya cika alkawarinshi ya tura kudin ajiyar zuciya ta sauke don bazata wani bata lokaci a masarautar nan ba saboda kwata kwata zuciyarta na bata akwai matsala
Kallon kudin dake cikin account dinta tayi 3.5m don su ayyo sun sanya mata kudin Amman batayi aikin ba ita bama wannan ba exist permit din da zata fita masarautar shima kanshi wani Abu ne batasan inda zata samo ba. Da ace chief of security yana anan da tayi mashi magana ya samo mata Saidai sam bata ganshi ba kwana biyu.
Inna hanne tare suka shigo da Bintu bayan isha’i lokacin Hurriya har tayi wanka ta kwanta don yau wani irin bacci taji tanaji sosai inna hanne tace Hurriya ma har tayi bacci ashe, ga abincin da na kawo mata kuma,
bintu ce tace ki ajiye abincin nan idan zan tafi sai intada taci. Inna hanne batayi tunanin komaiba ta ajiye abincin ta juya ita kanta wasba tana gama isha’i ta kwanta alamar ta gaji don wasba akwai hidima da yake batada aiki kwata kwata daga nan sai tayi nan kullum aikinta kenan ta tsokani fada ba wanda yake biye mata don kusan duk wanda ya kwana ya hantse yasan wurin wadda take zaune a wurinta don Hurriya ta zame mata uwa da uba ba kalar gatan da bata nuna mata duk abinda takeso najin dadi indai tanaso Hurriya bata taba gajiyawa wurin sai mata harta kudi zata zo tace ma Hurriya tana bukata haka Hurriya zata zaro ta bata Saidai wasba ta rinka dariya da murna taje ta kashe kudin
Duk da Hurriya bata wani nuna alamar soyayya ko tayi magana dasu Amman kallo daya idan kayima inna hanne Bintu da wasba zakasan they’re very dear to her don yadda take kashe masu kudi take kyautata masu kamar batasan ciwon kudinta ba.
Don ba’afi kwana hudu ba saida ta sanya aka dinka ma bintu da inna hanne sabbin hijabai masu kyau haule reza ta bama kudin aka dinko masu na Daidai karfinta harda sabbin takalma don taga Bintu batada wasu takalman kirki sai ta sanya aka siyo masu itada inna hanne gabaki dayansu koda aka kawo haule reza ta sanya ta kai masu aiko sukayi ta murna suna sanya mata albarka hade da addu’oi kala kala don sun san ba aikin kowa bane sai na Hurriya duk da tana nuna bata ita bace ba Amman ankare suke da ita acikinsu.
Bintu kallon Hurriya ta rinkayi da take bacci peacefully kamar batada wata damuwa a duniya murmushi bintu tayi wanda yafi kuka ciwo tace ko bacci kike kedin mai kyau ce kuma mai kyawawan halaye duk da cewar kin ki bari muga kyakkawan halinki kin boyesu kota ina kamar yadda kika boye kanki ta ko ina ta yadda ba wanda zai iya fahimtar ki ko ya gane kedin wacece Amman Hurriya ke ta daban ce a rayuwarmu kin taimake mu alokacin da muke bukatar hakan kin kwatar mana yanci a lokacin da rayuwa take barazana a garemu anya zan iya aiwatar da abinda su shaho suka umarce ni ?anya ba kaina na zalunta ba ?don laifin dazan aikata bazan iya yafe ma kaina shi ba.
Kuka ne yaci karfin bintu tana kallon Hurriya data dan sha lips dinta masu kyau da daukar ido long eye lashes dinta da suke kwance kamar ta sanya mascara double eyelid dinta wanda ya taimaka sosai wurin shaping idanunta sai dogon hancinta mai kyau wanda ya tafi kamar an zanashi she’s beautiful everything about her is beautiful don mutum ko shine karshen hasadda to sai yayi hakuri ya kyale Hurriya don duk bala’en hassadar mutum da kishi sai ya barta
Bintu duk cikin ranta take karanta hakan a hankali ta jawo kular da baba hanne ta kawo mata sannan ta barbada maganin dasu shaho da kaura suka bata,saida ta tabbatar ba’a gane mi ta sanya don duk ta dan cakula shi don tasan yadda Hurriya take da kaifin basira da gane abu Hurriya is very smart daga kallo daya takan karanci abinda mutum yake tafe dashi tasha ganin yadda take dealing mutane sosai so she have to be very cautious
A hankali ta fara ambatar sunanta shiru shiru bata amsa ba Bintu kara daga muryarta tayi yadda zatayi ringing cikin kwakwalwarta aïko hakan ta faru don cikin alamar bacci tace Bintu ya akayi ?
Hurriya ki tashi kici abinci tun dazu inna hanne ta kawo kina bacci nace bari na tadaki tunda ta fara maganar Hurriya take binta da wani irin kallo Bintu tsarguwa Tayi tace kodai na kawo maki ruwa ne ki wanke hannunki Hurriya daga mata kai tayi aiko Bintu wadda takejin kamar tana saman kaya saboda irin kallon da Hurriya ta rinka jefo mata mai wuyar fassarawa bata wani dauki lokaci ba sai gata da ruwa da uban yawa a kwano tace gashi
Tashi Hurriya tayi zaune har lokacin idonta bai bar kan Bintu ba saida ta wanke hannunta sannan ta janye idonta ta jawo kular Bintu banda faduwa ba abinda gabanta keyi Bintu Hurriya dagowa tayi ta kalli Bintu da tayi zugum don kamar za’ace mata arr ta arce sannan takai 1spoon.





Page 55
Ahankali takai 1spoon Daidai saitin bakin Bintu tana kallonta alamar ta bude bakinta taci abincin a zabure Bintu ta girgiza kanta tareda ja baya tace na koshi Hurriya na koshi fa. Hurriya shiru tayi sannan tace inci?bintu wasu irin kwalla suka rinka zubo mata masu zafi tana kallon Hurriya tace kada ki ci abincin
Hurriya kallon bintu takeyi wanda duk wanda yaga kallon zai tabbatar da cewar she’s broken sannan ta girgiza kai .bintu kallon irin disappointing look din da take bata wanda bata taba ganin irinshi a wurinta ba ya sanya da sauri ta durkusa mata hawayenta nakara yawaita kamar an kunna famfo tace na tuba ki yafe mani Hurriya ba yin kaina bane bansan ya zanyi da raina ba kiyi hakuri don Allah tanayin maganar da wani irin tsoro da kuma tunanin irin hukuncin da Hurriyar zata iyayi mata kuka Bintu takeyi mai taba zuciya tareda narkar da rai tana rokon Hurriya gafara Amman shiru batace komai ba kallonta kawai takeyi
Kiyi hakuri don Allah Hurriya kallonta Hurriya takeyi don ba abinda takeso taji ba so take taji miye dalilinta na cutar da ita saboda tasan Bintu ,wani Abu bazai taba sanyawa tayi tunanin cutar da ita ba indai ba babban Abu bane.
Bintu kamar tasan bayanin da take bukata kenan don haka tace Hurriya lokacin da suka kirani wai zasu biyani har kaura yace yana sona zai aureni haka nace masu babu abinda zasuyi man wanda zaisa na yaudareki ko naci amanar ki sun dade suna bijiro man ta haka Amman naki basu hadin kai sai wani dare da suka tareni a lungu da wuka a hannunsu sukace indan har ban zuba maki maganin ba to idan suka tashi kashe ki zasuyi tareda wasba duka sai sun kasheku sai idan har na zuba maki maganin shine soyayyar da zan iya nuna maki don shine bazasu taba kasheku ba
Kaura ne yace bazai taba bari wani abu ya sameki ba wannan alkawari ne yayi man ba abinda zasuyi maki kawai suna so ne su duba wani abu ne idan kinyi bacci Amman duk da alkawarin da sukayi man na kasa aikatawa share hawayenta tayi zuciyarta na karewa tareda shasheka a muryarta tace ba irin tsoratarwar da ban shiga ba bani iya cin abinci bani iya bacci duk saboda abinda suke fadamani na tsorotarwa
Sai jiya da suka mareni dare nayi sukazo sukayi man gargadi da cewar idan har ban zuba makiba bazanji da dadi ba. Hurriya banda niyyar cutar dake Saidai niyyar kareki don Allah kiyi hakuri.
Hurriya kallon Hawayen dake zuba a idonta take har muryarta ta fara sarkewa Hurriya alama tayi mata da tayi shiru ya isa yanzu ba lokacin kuka bane kinji na hakura inji Hurriya tana sakar mata dan karamin murmushi
Bintu kasa yadda tayi yadda tasan halin Hurriya ya za’ayi tayi hakuri har da sauri haka Hurriya daga mata kai tayi alamar ta hakura ai da sauri Bintu tazo ta rungumeta.hurriya bata rai tayi tareda dagata sannan tureta Hurriya ta kura mata idanunta masu matukar haske da kyau tace mata Amman miyasa baki fadamin ba? bintu saddar da kanta kasa tayi don ganin wani kwarjin da Hurriyar ta karayi mata yau.
Bintu tace ina tsoron yadda zan fada maki ne .hurriya wani genuine murmushi tayi mata sannan ta sassauta kallonta zuwa mai sanyi da sauki wanda tana dadewa batayi irinshi ba tace fatma ahankali Bintu ta dago tana kallon idonta wanda har wani maiko suke tsabar kyau da sanyisu abinda bata taba gani ba bintu tunda take da Hurriya shine irin wannan kallon mai kyau da sanyi.
Murmushi tayi ganin mamaki kwance a fuskar bintu sai kuma ta daina murmishin tace kada ki kara haka kinji idan wani Abu ya sameni You’re not to be forgiven for the rest of your life koda na yafe maki Hamood bazai taba yafewa ba kinji .Duk abinda zai faru tell me ki fadamin we will face it together and fight it together abinda kike kokarin yi is betrayal koda kinyi shi da ace kinyi shi da niyyar protection don cutar dani sukeso suyi , don’t ever try something stupid kinaji.
Bintu ta daga mata kai don wasu maganganun batasan inda ta dosa ba Amman tabbas abinda tayi kokarin aikatawa cin amana ne wanda ba wanda zai taba considering niyyarta da ace wani abu ya sake ya samu Hurriya da yanzu ya zatayi.bintu daga mata kai tayi tareda yin na’am sannan tace yanzu abinda zakiyi kije ki fada masu naci abincin zaro ido Bintu tayi tace kada suyi maki wani abu Hurriya tace ba abinda zasuyi man kidai fada masu cewar naci kinji ta ida maganar tare da lumshe idonta masu kyau.bintu daga kai tayi tareda hanyat kofa don isar da sakon Hurriya.
Hurriya tasan abinda ke ranta it’s been a while since she played a dirty game wannan karan is not a dirty game she’s playing,it’s action.
Itadin tayi takwendo lokacin da tana masarautar Heral kuma kakanta ya koya mata tareda cewa self défense ne ko an kawo Mata Hari she will be able to protect herself she always enjoyed the action don ta dade bata taba defeating kankanta ba who’s very strong and destructive don ranar da tayi defeating dinshi saida ya bata babbar saraauta wadda akayi shekara da shekaru ba’a bama wani sarautar ba saboda irin muhimmancita sai gashi ya bama yar karamar yarinya Hurriya , tareda wata babba chambre à palace dinsu yayi mata kyautar golds da diamonds da dawakai harda gaggarumar dinner ya hada mata damar she was always his favorite granddaughter and she knew that she would forever be his favorite.Hurain Faisait Hamood kenan bestfriend dinshi kuma jikarshi wadda yake jinta kamar shine ya durkusa ya haifeta
Saidai ko a lokacin iyayenta basu san wasan da suke da kakanta saboda haka suke fada mata ita mace ce kuma they believe that nothing will hurt her saboda Akwai security’s ko ina a Heral palace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login