Showing 39001 words to 42000 words out of 59144 words

Chapter 14 - Masarautar Qamar Book 2 Complete Hausa Novel

26 Mar 2025

29931

mota suka tafi ahankali ya kwantar da kanshi jikin kujerar motar sannan yayi kasa da kanshi yana kallonta kallon dogayen lashes dinta wanda suke kamar tayi fixing dinsu ,sajenta ya duba sannan ya karkata wurin kallon gashinta
Fuskarta a daure wani slight murmushi yayi sannan yace stubborn bai daina binta da kallo ba don haka kawai yaji yanason kallonta
Baisan dalili ba Amman kawai yau ya samu kanshi da yawan kallonta ahankali ya gyara mata gashin daya sauko mata ya rufe mata fuska.
Lumshe idonshi yayi kamshin turaren motar yana shiga hancinshi yana mai jefashi cikin wani yanayi.
Suna isowa aka bude mashi mota ya shiga ya fito hannunshi rike da ita kamar baby.
Part din an gyara shi tsaf don ko ina sai kamshi yakeyi ba inda ya kaita sai katon bedroom dinshi ya dorata saman gadonshi don zaman da yayi da ita ya gane yanda take kaunar dakinshi ruwa ya debo sannan ya shafa mata ahankali a fuskarta
Hurriya a hankali ta bude lumsassun idanunta wadanda suke cike da gajiya kallonshi take bata ko kyaftawa wanda shima haka nashi fannin baya ko kyaftawa wurin kallonta ,wani irin kallo suke bin junansu dashi wanda acikinsu ba wanda yasan ma’anar kallon da dan’uwanshi yake mashi
Hurriya kam tsoki tayi sannan tace what is he doing in my dream tace maye tadan murguda bakinta kadan ta rufe idonta sai bacci
Khalifha wani murmushi yayi yace my stubborn little maid saboda ai little ce don inda yayi auren wuri rayuwarshi kilan da first born dinshi ta kusa girmanta saboda he’s about 40
Khalifha kam tashi yayi tareda nufa dayan dakinshi wato secret room yana shiga ya cire kayanshi ya daura farin towel ya lumshe idonshi Toilet ya shiga sannan ya kunna cold shower ruwan yana shiga kota ina na jikinshi wani irin sanyi ke ratsa shi wanda ya taimaka wurin kwashe duk wata gajiya tashi.
Hurriya kam bacci ta rinkayi mai rai da lafiya don saida tayi baccin sauke gajiya don duk saida gajiyarta ta sauka sannan ta tashi ahankali ta bude idanunta sannan ta kalli dakin Khalifha wanda banda kamshin shi ba abinda dakin yake
Hurriya kamshin Khalifa ne yake dawainiya da duk jikinta don kamar shine a kusa da ita takeji frowning face dinta tayi sannan tace wannan kamshin fa ?ganin batada amsa ne ya sanya ta tashi da niyyar shiga toilet ahankali ta tashi Saida kafarta taji tadan amsa ahankali tace what caused this sai a lokacin ta tuna abinda duk ya faru gabanta ne ya fadi don wani fargaba da tsorone ya cikata don tuna halin da take ciki
Sai a lokacin tagane cewar Khalifha ne tagani ba mafarki tayi ba daman she wondered why would she saw him in her dreams while he’s nothing to her cizon lebenta tayi tareda tashi ta shiga ciki toilet din wanka tayi da ruwa masu zafi sosai sannan ta fito daure da bathrobe dinshi cikin sauri take komai Amman komai yana tafiya da natsuwarta bataga ta zama ba yau ya kamata duk wata hanya tabi yanda zata tsere ma wannan bakar masarautar don ga dukka alama sun shirya mata sosai don sam baza su barta ba, don haka gwara taje tayi facing abun kuma tayi fighting dinshi bazata mika kai ba sai tabar masarautar nan safe and sound ahankali ta kalli sama tace In Sha Allah don lokacin da tana a Heral babanta yakan ce insha Allah acikin magana watarana ta tambayeshi ma’anar insha Allah aiko yayi mata bayani da kuma nuna mata girman hakan kuma da tabbatar mata cewa indai tace Allah zai mata abinda takeso kalmar ta fado mata a rai tareda fatan Hakan ya tabbata
Kayan khafha ta sanya masu kyau kuma designers ko mai bata shafa ba ta fito ta nufi dakinsu aiko tana zuwa su Bintu suka taso da wasba da sauri ta kauce ma kowa acikinsu don ta tabbatar rungumeta zasuyi nan da nan suka fara tambayar lafiyarta lau ba abinda ya sameta ko ?daga masu kai tayi wasba ce ta share Hawayenta tace don Allah kada ki kara tafiya ki barmu kinji daga mata kai Hurriya kawai tayi Don tunanin da takeyi yanzu yanda zata bar masarautar nan
Sarki Faizan sai kai da komowa yake da jin zancen Khalifha ya dawo hankalin shi kwata kwata ba’a Daidai yake ba ga tunanin yarinyar nan da baisanta ba da yabi ya dami kwakwalwar shi abubuwa da yawa duk sun hade mashi ya rasa miye yake mashi dadi
Galadima ne ya shigo jikinshi na wani irin rawa yana bar bar don shi kadai ne ba’a tafi dashi ba cikin mutanen dake wurin don kaf harda su jakadiya an tafi dasu gidan yarin Khalifha abinda ya sanya bai tafi dashi ba chief of security saboda alakar dake tsakaninsu da sarki Faizan da kuma Khalifha shi yasa ya kyale shi amman Dukansu suna prison
Sarki Faizan yana ganin shi yasan cewar ba alkhairi bane tattare dashi don yadda ya shigo a kidime aiko hakan ta faru bakaken labarai ne ya fada mashi guda biyu daya na dawowar Khalifha da kuma yanda ya sanya aka tafi da dogarai da security’s din shiru sarkin yayi don ya rasa abinda Zai fada kafin ya dawo daga tunanin ya kara daga mashi hankali da sakon boka don yace duk yanda za’ayi su nemo yarinyar nan ciki kwanakin nan idan ba haka ba akwai matsala
Shiru yayi don ya kasa tunani sarKi Faizan don yasan bai isa acigaba da nemanta ba Khalifha na cikin masarautar nan
Galadima ne yace Allah ya taimake ka ga wata yar shawara tawa mu gwada mugani ko zatayi daga mashi kai sarKi Faizan yayi wani irin murmushi yayi sannan yace mai zai hana kawai Khalifha yayi aure kamar yanda ta rinka faruwa dashi da
Shiru sarKi Faizan yayi sannan yace Aa kasan duk wadda ya aura ranar take cewa saidai ya saketa Amman bazatayi auren ba ka canza wata shawara
Galadima shiru yayi yace wannan ita kadai ce shawarar idan akayi auren da an fara shagali hankali mutane yadan dauke sai mu cigaba da dubata ana shagali ana dubawa.
Sarki Faizan duk yanda yaki yadda saida Galadima ya rinka insisting har dai yace akai ma Khalifha takarda da sauri Galadima ya daga kai ya fita akayi rubutu ya kawo ma sarki yayi stamp yakai part din Khalifha
Khalifha yana zaune a falo kafa daya kan daya yana amfani da iPad dake hannunshi don duka hankalin shi nakan iPad din saida akayi ma chief of security iso sannan ya shigo hade da sallama
Galadima sallama ya karayi mashi Khalifha ba tareda ya dago ko bare ya kalleshi ba ya amsa sallamar shi bayan sun gama gaisawa wanda Khalifha cike da tsantsar mulki yake maganar don har lokacin bai kalli inda Galadima yake ba
Galadima cikin yar kyarma don duk yanda kake kazo wurin sai kaji dar don powerful aura dinshi duk ta cika wurin , fara karanta takardar da sarki ya sanya akawo mashi yayi inda yake cewa gobe akwai daurin auren Khalifha da za’ayi bayan azahar kuma mata hudu zai aura
Khalifha bai ko kalleshi ba ya tashi yabar parlon don ba abinda ya dameshi idan an tashi adaura mashi mata dari ya san cewar a ranar kowacce acikinsu zata nemi sakinta zasu gudu baisan miye ake turo mashi ba Amman koma miye bai damu ba sune suke auren kuma sune suke raba auren
Galadima kam ya shaka lokaci kawai yake jira zai bama kowa mamaki acikinsu daga sarki Faizan din har Khalifha duk zasu dawo atafi hannunshi lokaci kawai yake jira.
Koda dare yayi inna hanne tazo taga Hurriya ba karamin dadi taji ba ganin ba abinda ya faru da ita don ta saki jikinta Sosai tunda gashi tana kallonsu Bintu sunata cin abinci kowa yayi shiru baya yin magana inna hanne murmushi tayi don tasan aikin Hurriya ne zama tayi itama bayan sun gama cin abinci suka taba yar hira sannan tayi masu Bankwana ta tafi ta kwanta
Saida ta tabbatar Bintu ta tafi ita kuma wasba tayi bacci sannan ta tashi ahankali ahankali ta fita don ganin ko akwai inda zata iya samu ta gudu
Cikin sanda takeyin komai har tazo taron wasu yan iskan dogarai suna zaune suna shaye shaye aiko suna ganinta suka taso kowa acikinsu a buge yake yana cewa ina aka samu wannan kyakkawar yarinyr
Hurriya kallonsu tayi don kyankyamin su Dukansu takeyi wani acikin su ne ya kawo hannu zai taba mata gashi ne aiko yaji an rike hannunshi Hurriya kallon wanda ya rike mashi hannu tayi shiru tayi tareda zuba mashi idanunta masu kyau wanda ke kara jefashi cikin kaunarta da sauri ya janye idanunshi daga nata sannan ya kalli dogarawan yace ku wuce ku bama mutane wuri,da sauri Dukansu suka bace a wurin
Kumurci kasa kallonta yayi ita kuma kallonshi kawai takeyi
Cikin natsuwa yace mata kinason fita ne Hurriya saida ta dauki lokaci as always sannan ta daga mashi kai murmushi yayi ganin ji da kanta har yanzu yana nan ba wanda ashe ya ladabtar da ita.
Kallonta yayi sannan yace muje na taimaka maki Hurriya daga mashi kai tayi sannan suka fara tafiya duk inda suka gifto da anyi mashi magana sai yaje wurin ma’aikatan ya basu wani Abu sai su wuce saida suka zo Daidai bakin wani gate din da zai iya fiddasu palace din tace na manta wayata
Kumurci kallonta yayi da mamaki ganin tana Neman komawa bayan duk wahalar da suka sha ahankali yace mata kiyi hakuri da wayar mana.Girgiza mashi kai kawai tayi sannan ta juya ta koma saida tayi tafiya mai nisan gaske ta fara hango dakunansu ga dare
Kunnenta akwai ji don tana tafiya daga nesa taji ana waya ana cewa dole mu nemo yarinyar nan gobe ko a ina ta makale cikin masarautar nan don boka yace duk wanda ya sameta zaiyi sarauta ko dai na aureta kona kasance da ita
Ai saboda auren Khalifha da za’ayi ba zai zargi kowa ba ko yayi tunanin Akwai Abu ke faruwa a masarautar don haka ba wata matsalar da za’a samu







Short page 64
Har ta shigo daki tana tunanin abinda taji a waje yanzu ,frowning face dinta tayi ganin yadda aka matsa mata it almost made her laugh wai they will marry her or sleep with her
Shin ita har batasan mi zatayi ba don tasan yanzu koda ta koma hardly ne a barssu su fita daga masarautar shiga dakin su tayi wanda har wasba tayi bacci saboda dare yayi bakajin kara komai sai ta tsuntsaye ahankali ta kwanta tareda rufe idanunta batayi tunanin zata iya Bacci a irin lokacin ba saboda tunanin abinda ke faruwa wanda ba abinda ba taji ba saidai she’s always calm
Ba notice bacci barawo ya dauketa Mai nauyi hade da gajiya.
Khalifha kam ranshi ba karamin baci yayi ba saboda yunwar da yake ji baisan miye yake damunshi ba Amman safa da marwa kawai yake a tankamemen parlon shi tsoki yayi ahankali don abun ya dameshi Sosai amman ya rasa gane dalilin shiga damuwarshi saboda abinci ba wani damunshi yayi ba don yakan gama zaman da zaiyi wata da watanni a masarautar Qamar baici abinci ba sai irin su fruits cookies da junk sune ke rike shi tsoki yayi ganin yana damun kanshi for no reason
Kitchen ya shiga da tsalelen daren ya hada ma kanshi coffe sannan ya fito parlon tare da kunna tv yana kallon News ya dade yana sipping yana lumshe ido sanye yake cikin wasu hoodie Wanda suka fito mashi da tsantsar kyau gashin kanshi a gyara yake sai fitar da wani kamshi yake jikinshi alamar hutu da jin dadi duk ya bayyana don farar fatarshi kamar ta baby haka take haskakawa
Ahankali ya tashi ya hau sama saida yayi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe din da Hurriya ke sanyawa idan tayi wanka
Wani irin kamshi yakeji na daban ko ina na jikinshi ya dauka lumshe ido yayi sannan ya shirya cikin ash jallabiya saida yayi shafa’i da wutiri sannan ya nufi gadonshi ya kwanta saidai komai na dakin ya canZa mashi don wani irin kamshi na daban gadonshi yakeyi wanda saidai he’s really enjoying the new scent addu’a yayi sannan Bacci ya dauke shi .
Hurriya sai karfe bakwai na safe ta tashi brush dinta ta dauka sannan taje wurin inna hanne ta amso ruwan zafi
Saida tayi wanka sannan tayi alwala hade da brush lokacin har kusan 8 sannan tayi sallahr asuba bayan tana gama sallah taji wayarta na ringing cikin natsuwarta ta dauka ta kanga a kunnenta ba tareda tace uffan ba chief of security ne ya gaisheta amsawa tayi tareda sauraren abinda yake cewa har saida ya gama sannan tace okay sir
Ta dade kafin ta yunkura ta shirya don wani irin faduwar gaba takeji tunaninta kam bai wuce abinda taji ba jiya tsoki tayi kallon kanta tayi a madubi cikin wata black doguwar abaya wadda tayi masifar mata kyau don cikin kayan da chief of security ya bata ne
Rigar is screaming rich and elegant and sai ta taimaka wurin kara fito da cramela luminous skin dinta
Kallon gyalen mayafin tayi kawai ta dauka ta yafa ma kanta ba karamin kyau tayi ba cikin bakar abayar ba kamar da ta yafa mayafin don sai kananan gashinta wanda suka kwanta suka fito suka kwanta mata a goshi gashinta kam kamar tayi acuci yanda yayi
Takalmi ta sanya ta fito tana tafiya cikin catwalk dinta wasba wadda take shigowa Hurriya kuma tana fita ta kalleta tace wow Hurriya kinyi kyau
Kallonta ta rinkayi cikin mamaki ganin yadda tayi shigar musulnci yau shiru Hurriya tayi ba tareda tace mata komai ba ta raba gefenta ta wuce .
Part din Khalifha taje shiru parlon ya dauka banda sanyi Ac da kamshi ba abinda parlon yakeyi
Aikinta ta fara cikin kwarewa takeyin komai har tagama sannan ta hau sama saida ta fara gyara parlon sama sannan ta shiga dakinshi cikin sa’a baya cikin dakin don haka ta gyara dakin fess tareda wanke toilet sannan ta kunna waau turaren wuta masu wani irin dadin kamshi
Khalifha da ya shigo dakinshi yanzu wani irin lumshe ido yayi saboda dadin kamshin da ya bugi hancinshi ahankali idanunshi suka sauka gareta tana gyara abubuwan turaren wuta
Wani irin kallo yake binta dashi wanda baisan ma’anar hakan da yakeyi ba don duk yanda yaso ya janye idanunshi daga gareta ya kasa
Hurriya juyowa tayi itama tareda zubaida mashi idanunta masu kyau cikin muryarta mai dadi yace lower your gaze banza yayi da ita wanda kamar baiji ta ba amman sarai ya jita ya fara takowa zuwa inda take Hurriya kam ganin yana nufota itama ra fara tafiya da baya da baya don tasan mi yake kokarin yi she knew he will annoy definitely don haka ta rinka tafiya
Dukansu kallom juna suke batare da sun janye ba Hurriya kallon idonshi take ta glass wanda glass din yake da haske sosai shima ita yake kallo
Saidai yana mamakin yadda take tsayawa very comfortable around him don mutane dayawa basu iya tsayuwar minti daya a inuwar shi saboda irin kwarjinin shi
Amman ita ba kallo ido cikin ido duk da idonshi rufe yake da glasses he really hope watarana ya cire gilashin yaga ko zata iya kallon cikin idanun shi
Hurriya juyawa tayi tareda kallon inda take nufowa cikin sa’a kam toilet ne kusa da ita tayi sauri ta bude tareda shiga
Wanke toilet din tayi tsaff sannan ta fito bata iske shi ba a dakin don haka ta sauka kasa sannan ta shiga kitchen ta hada mashi breakfast chips ne tayi da liver sauce sai sosage data soya mashi,ta hada coffee
Arranging komai tayi a table sannan ta dauko plate da cups tayi arranging dinsu.
Kamshin turarenshi Mai dadi da tsada ya cika parlon Hurriya kam ko kallon inda yake batayi ba don ta riga tasan ko waye turarenshi da aura dinshi ta gama fada mata da zuwanshi
Khalifha daya daga cikin kujerun yaja ya zauna sannan yayi serving kanshi Daidai abinda yasan zaici Hurriya kallon yadda yake cin abini tayi cikin natsuwa sannan tace not bad zai iya cin 90/100
Ahankali itama taja kujera sannan ta zauna ta shiga zuba abincinta cikin tsari taje komai
Ba wanda yace ma dan uwanshi kalma daya har suka gama cin abinci
Khalifha ya fara barin dining din sannan ita don ya rigata cin abin don saida ta dade kafin tagama cin abincin bayan tagama cin abincin ne fa ta shiga kitchen ta wanke duk kayan data bata tanayi tana tunanin irin makomar da zata koma don tabbas yau saidai wani iko daga Allah amman sai sun nemota
Tunawa tayi da chief of security aiko tayi saurin daukar wayarta ta kirashi cewa tayi tana bukatar yazo tanajin hayaniya sosai inda yake
Acikin kujerun kitchen island ta zauna tana jiran isowar chief of security bai dauki wani lokaci ba Sosa ya iso
Kiranta yayi awaya ta fito kallonta yayi sannan ya sakar mata murmushi yace Hurriya ya aiki amsa mashi tayi da fine kallonta yayi Ganin Kamar akwai magana bakinta tambayarta yayi mi takeson tace??
Hurriya shiru tayi tana naZarin whether to asked him for her exist kodai ta kyaleshi ta rasa abinda zatace har ta bude baki zatayi magana taga takarda a hannunshi kallon takardar tayi taji cewar kawai tanason taga abinda ke cikin takardar
Ahankali tace mashi miye anan in gani,chief of security haka yace ohhh sunayen matan da Khalifha zai aura ne ,Hurriya kallonshi tayi irin wani Khalifha din , ya daga mata kai
Kallon takardar kawai tayi wata idea ce ta zo mata kallonshi tayi sannan tace did you have extra sheet please daga mata kai yayi tareda mika mata,Hurriya amsa tayi sannan amshi pen sunayen mata guda hudu ne rubuce a takardar Hurriya rubuta guda uku tayi tsaff sannan ta sanya sunanta ana hudun ta mika ma Galadima.
Galadima kallon sunan kawai yakeyi Hurain Faisait kara kallonta kawai yake yana binta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login