Showing 1 words to 3000 words out of 120027 words

Chapter 1 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 104...


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Ajay ya gaida Hajja da ta fito daga dakinta rik da bowl a rufe tana kallon sa da Khaleesat, bayan ta zauna tace "Kai kuma daga ina kama an jefo ka?" sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta cikin sanyin murya ta gaisheta, Hajja ta kalli direction dinta tace "Lafiya lau" Sai kuma ta kalli Ajay tace "Ita ce matar taka kenan" Shi dai Ajay bai ce mata komai ba, Haj tace "To Maa sha Allah, Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya" Daga haka bata sake cewa komai ba a parlon, bayan yan mintuna ta mike ta dau bowl din da ta ajiye ta fita daga parion, Jay taje ta sama a daki, bayan ta kulle kofar dakin ta karasa ciki ta zauna kan kujera tace "Na dauko maka dambun naman kuma ban same ka a parlon ba" Shi dai bai ce mata komai ba, ta ajiye bowl din tana kallonsa ta kwantar da murya tace "Kayi hakuri Jawwad, nasan kai me hakuri ne, bazaı ji dadi ba idan ka kullaci dan uwanka akan wannan abu, kun taso tare cikin so da kaunar juna kamar yan biyu rana tsaka wannan abu mara dadi ya gifta, ka fi kowa sanin halin dan uwanka ni ina da yakinin bai san da wannan aure ba shima sai bayan da sarki ya daura masa, sannan kasan yanxu haka in kace zaka sharesa damuwa zai saka ma kansa, ni naji ma kwata kwata yarinyar bata min ba wallahi' Sai a sannan Jay ya daga kai ya kalleta yace "Me ta maki?" Hajja ta hade rai tace "Me ta maki?" Hajja ta hade rai tace "Me ta min? Yarinyar kamar er jaraba gashi ta dalilint zumuncin da aka gina tale tale na neman rushewa tana neman shiga tsakaninku da dan uwanka, to kuwa ina amfanin irin ta a al'umma? Ai ta zama abar tsoro kenan, dole n sai an aurota cikin Family tunda auren bai yiw da kai ba ba sai a hakura ba, na meye sai an maida aure kan wani Junaid kamar ita din er gwal ce?? Wallahi da sarki yayi shawara da ni bazai aura ma Junaid yarinyar nan ba ko don saboda kai, in ma yace shi bazai zama karami mutum ba to gwara can ya aura mata Walid ko kuma Mukhtar, ko ya nemi wani a dangi ya aura mata, gaskiya ban ga alamar alkhairi tattare da yarinyar ba tunda ta dalilinta komai ya cakude na rasa ta inda zan fara gyaran nan kuma naga ma kamar halarabiva ce ko Idona ne Jay dai bai sake cewa komai ba, cikin nutsuwa Hajja tace "Nasan halin ka na kuma san halin Junaid, nasan Junaid bazai ki yi maka magana ba Jawwad don Allah idan yayi maka kar kace zaka ki kulasa, kayi hakuri ka bar ma Allah komai, kuma ba kowa ya ja sanadin faruwan wannan al'amari ba sai Aseeyah, Aseeyah ita ta ja komai kuma bata kyauta maka ba, amma a yanxu dai ina son ka saka ma ranka salama ka malda lamarin ka ga Allah" Hajja ta fi minti sha biyar a dakin tana kokarin kwantar masa da hankali tana kara jadadda masa kar yace zai yi banza da Junaid, shi dai yaki ce mata komai daga karshe ta bar dakin ta koma parlon ta, tun bata karasa ba take jin kamar muryar Aunty a parlon nata, tana shiga kuwa ta sameta tsaye da Hajlya Aisha suna ci ma Ajay mutunci ya ki ko daga kai ya kaliesu sai danna wayarsa kawai yake karnar ba da shi suke ba, Suna ganinta duk suka yi shiru, da mamaki Hajja tace "Lafiya? Me ke faruwa haka?" Aunty ta zauna kasa don gaida Hajja, Hajja tace "Me ke faruwa nace?" Cikin bacin rai Aunty zata fara magana Hajja tayi wani tunani sai ta dakatar da ita tace "Bana bukatar jin komai yanxu, kawai ke da A'isha ku tashi ku je" Aunty ta mike ta fita daga parlon Hajiya A'isha na biye da ita a baya, ita dai Khaleesat na zaune kamar an dasata inda take mamaki yaki barin ta, she was really shock don bata ga alamar mutunci ba kwata kwata, sosai jikinta yayi sanyi da wannan abu, is it she that will leave with this kind of people in the palace? Auren da har yanxu ba amsan sa tayi ba amma take ganin wannan abu, Hajja na kallonta bayan ta zauna tace "To ban san sunan kishiyar tawa ba" Khaleesat ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Sunana Halysaah" Hajja tace "Maa sha Allah, sunan kishiyar tawa ta yan gayu kuwa" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "Amma sunana Jiddah" Hajja tace "Maa sha Allah, kin ga mu mun fi gane wannan ai, you are welcome to the family Jiddah" Mikewa Hajja tayi da kanta ta kawo kayan ciye ciye ta ajiye a parlon sannan ta fita, can main parlor ta tarar da Aunty, Hajja na kallonta tace "Ke yanxu Hafsat saboda rashin kamun kai a gaban surka za ki zubar da mutuncinki ki nerr ki zubar da na gidan nan?" Cike da damuwa Aunty tace "Hajja tun da aka kawo yarinyar nan masarauta Junaid ke bude mata kofofin raina ni, tun kawota har yau yarinyar nan bata taba bude baki ta gaida ni ba kamar yanda sh ma sai ya ga ubansa yake gaisheni" Hajja tace "To ke ma ba sai kin ga uban nasa kike amsa gaisuwarsa ba? Duka duka yaushe har aka kai ta gidan da zata waye ki? Yarinyar da ko kwana uku bana tunanin tayi" Shiru Aunty tay bata sake cewa komai ba wani sabon bacin rai ya lullubeta, Hajja tace "To ki kama kanki, ba ruwana da abinda ke tsakanin ki da Junaid kar ki kuskura ki ce zaki zubar da mutuncin gidanmu a idon duniya, a gaban yarinya babu kunya ki tsaya kina kalaman banza da hofi akansa? Idan matar Walid ce za ki yi wannan iskancin a gabanta?" Aunty tace "Matar Walid ma bazata min haka ba Hajja" Hajja tace "To zageni Hafsat, kare min nima yanda kika kare ma Junaid al ba sabon abu bane" Shiru Aunty tayl sai kuma ta fara bata hakuri kai a kasa, Hajja tace "Aikin banza aikin Hofi kawai, a ko ina ke sai kin malda kanki karamar mutum, gaban yarinya kin zubar da mutunci da girman ki, ina amfanin haka wai kuma matar sarki? Dama haka matan sarakunan su ke? To sam mu ba mu yi haka ba, bama son duk wani abu da zai taba reputation dinmu da na gidanmu komin kankantarsa, amma ke kam taka haye ce ma a jinin sarautar Hafsat" Daga haka Hajja ta juya ta bar parlon, Aunty dai sai huci take tunani iri iri na yawo a ranta, lallai ta gamu da aiki ja wanda ko bacci bai kamata tana yi da ido biyu ba yanxu. Throughout ranan haka Khaleesat ta yini daga ita sai Hajja a parlor, ga 'ya ya da jikoki da mutanen arziki na ta zuwa gidan yi ma Hajja sannu da zuwa, in an gaisa sai Hajja tayi masu introducing Khaleesat dake gefenta, Khaleesat dai duk a masu zuwa bata ga wanda ya wani bata attention ba, duk kuma a nan ne taga yaran Aunty uku, wata me sunanta da ake ce ma Baby that is just a teenager sai yayyinta Maryam da Khadijah, gaba daya ko bin ta kan Khaleesat basu yi ba, ita dai tana zaune parlon ne amma Allah kadae yasan damuwan da ya cunkushe mata a rai, har take jin da zat: samu wajen da zata yi kuka ta samu relief, Babban damuwarta a yanxu shine wannan aure da aka mata da Junaid, secondly Jay da ta garni shigowar su daxu ya kara destabilizing dinta komai ya dawo mata kamar yanxu yake faruwa, thirdly Aunty, har cikin ranta taji take tsoron matar don bata mance mahaifiyar Abdul ba da abinda tayi mata, she is so afraid of the woman, further more gashi ta lura duk familyn babu alamar akwal wanda zai so ta, kllan sai Hajiya Shafa'atu kawai, duk sai sha mata kamshi kawai suke suna daga mata kai kamar sun ga kashi babu wanda ya bata attention a parion, hatta Hajja is just being neutral babu yabo babu fallasa ce, kuma duk zamanta a parlon sae ya kama Hajja ke mata magana although cikin mutuntawa zata mata maganar, kuma ko ita aka kawo ma abinci sae ta fara dibar me Khaleesat kafin ta ajiye. and the least among damuwarta Junaid, she don't know why he is being treated this way a gidan nasu, she don't even know ko hakan tausayi ya bata ko kuma she is just feeling for him, but for now dai duk ba shi ne a gabanta ba, damuwarta kawal Jay....
HALYSAAH PAGE 105

Khaleesat na komawa cikin gidan Hajja ta tarar da Hajja zaune parlor da Jay tana masa magana cikin kwantar da murya, Hajja ta daga kai ta kalleta da mamaki, Jay dai sau daya ya kalleta ya dauke idonsa, Hajja tace "Halan kin yi mantuwa ne Jiddah?" Khaleesat ta kasa kallonta ta gyada mata kai kawai, Hajja tace "To je dakin ki duba...." Hanyar parlon Hajja ta nufa tana tafiya a hankali, tana shiga parlon hawaye ya gangaro fuskarta ta juya tana kallon entrance din parlon kamar tana jiran taga ya shigo, she stood for almost 3 minutes a parlon daga karshe ta goge idonta kawai ta fita ganin ba shigowa zai yi ba, she was so heartbroken and sad, da kyar ta koma main parlor tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Hajja tace "Kin gani?" Ta gyada mata kai ba tare da tace komai ba don tana iya fashewa da kuka, bata ga Jay a parlon ba, a haka tayi ma Hajja sallama da kyar ta fita, Har suka koma masarauta Ajay bai kalli direction dinta ba ita ma haka, sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, suna isa bangaren sa taga ya bude daya daga rooms din dake bangaren ya shiga a maimakon part dinsa, ita dai tana tafiya a hankali ta shiga parlonsa ta zauna kan kujera wasu sabbin hawaye na zuba idonta, sai kuma ta kwantar da kanta kan kujeran tana kuka a hankali, Har aka yi Magrib Ajay bai shiga part din nasa ba, at this point, the whole situation is beginning to get him very angry, why is he even to be blamed? Shi adalci aka masa with this marriage? Yarinyar da is nothing but a burden to anybody around her..... Khaleesat na zaune parlor bayan ta idar da sallah kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai, tayi nisa tunanin da take taji an kwankwasa kofar parlon, a hankali ta juya daga inda take zaune tana kallon kofar bata dai amsa ba, bayan few seconds aka bude kofar Yakumbo ta shigo da sallama ta tsaya nan bakin kofar tana gaida Khaleesat cikin ladabi, Khaleesat ta sauke idonta ta gaisheta ita ma cikin sanyin murya, Yakumbo tace "Abinci ne za a shigo da shi ranki shi dade idan babu damuwa" Khaleesat ta gyada mata kai tace "To" Sai a sannan Yakumbo tayi ma ma'aikatan dake bayanta izinin shigowa parlorn with trays of different food a hannunsu, su ma duk suka gaisheta da ladabi sannan suka ajiye duk abincin har da kayan marmari bayan sun fita Yakumbo ta kara kwantar da murya tace "Babu wani damuwa dai ko ranki shi dade?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Ba komai, Nagode" Yakumbo tace "To maa sha Allah, sannan babu wani abu da zaki bukata da za a kawo maki?" Khaleesat tace "Eh ba komai" Yakumbo tayi mata sallama sannan ta nufi kofa ta fita, tsaye taga Ajay bakin kofar dakin da yake ciki don tun da yaji anyi knocking door din parlonsa ya fito don ganin waye a part din nasa, Yakumbo ta risina kai ta gaishesa ya amsa sannan yace "Idan kin gama ayyukan da kike zaki kwana nan bangaren tare da ita, akwai ɗan aikin da zan yi can anjima da daddare...." Da ladabi Yakumbo tace "To in sha Allah ranka shi dade" Juyawa yayi ya koma cikin dakin ya kulle kofa. Ana idar da sallahn Asuba Ajay ya shirya ya tafi gidan Hajja don tun ma ba ayi sallah ba kiranta ya shigo wayarsa don ta tunatar masa tana jiransa bayan anyi sallah, yana isa gidan bayan yayi parking ya fi minti goma zaune cikin motar daga karshe ya kashe ya sauka ya shiga gidan, direct ya nufi parlon Hajja ya sameta zaune tare da Jay, zaunawa yayi ya gaisheta calmly, Hajja ta amsa tana kallonsa, bayan kusan minti biyu tace "Ban ga ka gaisa da ɗan uwan naka ba Junaid" Ajay yaki ce mata komai kuma bai fasa kallonta ba, Hajja ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Jay dake danna wayarsa kawai, can ta sake kallon Ajay speaking with calmness tace "Junaid, you owe Jawwad an apology even though you are not at fault but for peace to reign you have to do that, don in batun gaskiya za a bi ba a kyauta ma Jawwad ba, things were never supposed to be done this way in an zurfafa tunani, bana son zumuncin ku ya taɓu akan mace, a ajiye duk wani circumstances da yayi leading to all this amma yana da kyau ku fahimci juna da ɗan uwanka, come to think of ur bond together, this is so pathetic...." Ajay dake ta kallonta yace "Apology for what in particular Hajja? Why is he trying to play the victim whereas nima tauye ni aka yi tunda ban bude baki nace ina so ba don ban hango future na tare da yarinyar ba, why is he playing the victim in this situation? Ni nace a aura min yarinyar?" Jay ya ɗaga kai ya kallesa calmly yace "That is a lie, idan da baka so babu ta yanda zaka yi accepting auren, stop fooling your self Man" Ajay ya mike yace "Then you do ur worst Jawwad, you think yanda ka nuna ma Mai martaba ba shi da 100% say akan ka sai yanda Mamin ka tace kana tunanin nima zan nuna masa haka, You think I can also disappoint him and make him look foolish in the eyes of people? Beside stick this to ur brain Jawwad... Abba bai yi shawara da ni kafin ya yanke wannan hukuncin da ya yanke ba tunda yasan ni ya isa da ni dari bisa dari" Mikewa Jay yayi ya nufesa yana kallonsa direct in the eyes carefully yace "Watch ur tongue, do not let me voice out all what is in my mind Junaid, do not push me" Ajay yace "So? Ya wuce kace idan naka Dad din ne bazai yi maka haka ba, ina ce iya abinda zaka fada kenan, wannan kuma ba ni zaka gaya ma ba kaje ka samu Mai martaba and tell him that, go meet him" Hajja ta hade rai ta mike ita ma tace "Bana son sake jin bakin kowa a cikin ku, ba wannan ne dalilin da yasa na hada ku a nan ba, what is all this nonsense???" A hankali Jawwad yace "There is nothing that will be said to me here da zai yi convincing dina or change my perspective of this whole thing Hajja, don haka kar ma ace min komai i am not interested, bana bukatar jin komai" Hajja ta saki baki tana kallonsa, zai fita daga parlon tace "Jawwad" Tsayawa yayi amma bai juyo ba, Ajay ya karasa har inda yake tsaye ya zaga gabansa yana kallonsa yace "Halysaah ko? Take a chill pill, she is urs.... It's just a matter of time, i am giving you my words" Yana kai wa nan ya fice daga parlon without turning back, Jay ya bi sa da kallo, Hajja was totally speechless a inda take tsaye baki bude, bayan few seconds tace "Allah ya sauwake, Allah ya tsare mu da wannan taɓara sai kace a garin gaɓa gaɓa, shi Jawwad din mahaukaci ne me kuma zai yi da matar da aka aura maka, ko kuma ita Halysaar er gwal ce? meye ma amfanin auro irinta cikin zuri'a tunda ta dalilinta gashi zumunci na neman samun tangarda, sam ni yarinyar ma bata min ba saboda abubuwan nan da ke faruwa babu kan gado, shi Jawwad din bashi da hankali ne? Me kuma zai yi da matar ka?" Jay ya juya ya kalli Hajja. Khaleesat ta fito daga Bedroom wajen karfe goma na safe jin sallaman Yakumbo a parlor, cikin kwantar da murya Yakumbo tace "Ranki shi dade yanxu Yarima ya kirani yace a sanar maki ki shirya za ku yi tafiya yau, ina fatan kin sani" Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can tace "To" juyawa tayi ta koma Bedroom din, rabonta da ganinsa tun jiya da suka dawo gidan Hajja da yamma, ta zauna kan kujera tayi tagumi tana kallon babban plasma din dakin, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda damuwa gashi har ta fara jin kirjinta na ciwo, tana ta zaune har bayan minti talatin ta ji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, bai ko kalli inda take zaune ba har ya shigo cikin dakin, ta bi sa da kallo har ya dau abubuwan da zai dauka zai fita daga dakin ta hade rai tace "Ina za mu je?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban sani ba" Daga haka yayi ficewarsa daga dakin, ta taɓe baki ta dauke kanta, bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login