Showing 105001 words to 108000 words out of 120027 words

Chapter 36 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar

kamata ka dinga tofa mata?" Sal a sannan Ajay yayi realizing abinda ya kamata yayi in the first place da yaga she is unconscious, da sauri ya sakar ma Mami Khaleesat ya shiga bandaki immediately zai debo ruwa, Kilishi ta bi sa da wani kallo baki bude ganin yanda duk yake a rikice ya daburce kamar ba shi da ta sani ba, dama akwai abinda ke rikitasa har gigice ya kasa boye hakan, haba ta rike tana kallon Khaleesat a ranta kuwa tana cewa har sun fara mallakesa kenan irin wannan gigicewa da rawan jiki kamar zai masu kuka, Mami dai sai gyara ma Khaleesat duvet din jikinta take bayan ta lura babu riga jikinta at the same time tana tofa mata addu'o'i, Kilishi ta tabe baki ta fara komawa baya a ranta tana addu'an Allah ya sa iskan su kara tashi ta shake Mami, ita banda Hajja da ta tasheta ta taho taga abinda ke faruwa da yake a bangarenta ta kwanta yau ai da baza ma tasan wani abu na faruwa ba a gidan, Hajjan ma tayi tunanin Hadiyah ce, Ajay ya fito bandaki da ruwa ya karasa kusa da gadon da sauri har ruwan na zubewa a hannunsa, duk tunanin Mami addu'a zai yi a ruwan ko wani abu, sai kuma taga ya zauna daya side din yana shafa mata a fuska, Mami zata yi magana Khaleesat ta fara juya kai a hankali, da sauri Kilishi ta koma can bakin kofa ta tsaya tana fatan ta makuro Mami a rasa me kwatanta, a hankali Khaleesat ta bude idonta da suka rine, Mami ta dafa goshinta cikin kwantar da murya tace "Sap Halysaah, sannu kin ji" Khaleesat ta kasa komai tana kallon Mami Kamar tana son tabbatar da ita din ce ko kuma idonta ne suke mata gizo, nan ta fara kokarin mikewa zaune amma ta kasa daga ko hannunta, gashi duk jikinta sai rawa yake, Mami zata gyara mata kwanciya tayi saurin kamo hannunta tana girgiza kai muryarta ko fita baya yi sai ga hawaye masu zafi na sauka gefen idonta a wahale tace "Don Allah ki tafi da ni Mami, don Allah ki tafi da ni" a nan ne idon Mami ya sauka kan bedsheet din kan gadon don a sanda Khaleesat take kokarin tashi ta janye duvet din da ya rufe wajen jini, shi dai Ajay ya mike a hankali ya koma daya bangaren dakin ya tsaya looking guilty, Mami tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, meye wannan?" Kilishi ma sai kallon kan gadon take da mamaki, Mami ta kalli Ajay da ya sauke idonsa kasa, sai kuma ta kara kallon Khaleesat that was still struggling to get up tana rike da hannun Mami muryarta na rawa tana cewa Mami ta tafi da ita don Allah, Mami dai sai rufa mata duvet din jikinta take ganin cirewa ma take kokarin yi gaba daya not minding she is naked, mamakin jinin meye a kan gadon Mami ke yi with confusion, gashi sai bin dakin take da kallo ko zata ga wani makami or anything sharp, Kilishi kuwa ta kasa daurewa ta kalli Ajay tace "Wannan kuma wai jinin meye haka kwance a kan gadon Junaid? Fada ku ka yi da matar taka ko me?" Ajay dai bai daga kansa ba, kawai suka ga ya nufi kofa walking slowly ya fita daga dakin don ji yayi kafafuwansa sun ka gaba da daukansa ga wani sanyi da yake shigarsa sosai, Mami ta bi sa da kallo cikin rudani, Khaleesat na kuka da kyar har Ikcn muryarta bai fitowa sosai tace "Don Allah ki tafi da ni Mami, pls take me away, wallahi mutuwa zan yi...." A hankali Mami tace "Ina hijab din ki?" Da sauri ta yunkura zata mike ta nemo hijab amma tayi wani kara me karfi ta rike Mami idonta kamar za su fito ta fashe da wani kukan tace "Bazan iya tashi ba wallahi...." Kilishi ta bude baki tace "Baza ki iya tashi ba? Yanka ki yayi da makami a kafar ko me?" Mami ta cire duvet din jikinta a hankali tana dubata, mamaki tayi sosai and she was shock at the same time amma fa ta rasa gane ma'anar hakan, after a while ta mike ta fice daga dakin ta fita har parlor, kofar dakin da ta gani a bude ta shiga ta gansa zaune gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, Mami na masa wani kallo tace "Meye haka kayi ma yarinyar mutane Junaid?" A hankali Ajay ya daga kansa yana kallonta da idanuwansa da suka kada sosai, sai kuma ya sunkuyar da kai yayi shiru, Mami ta daka masa tsawa tace "Ba magana nake maka ba, me kayi mata haka?" Dakewa yayi murya can kasa yace "Mami ba da gangan bane..." Mami tace "Ban gane ba da gangan ba, meye kayi mata ba da gangan ba?" Cikin sanyin murya ya daure yace "Ni ban san she is a virgin ba" Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa da wani expression tace "Virgin? Kamar yaya Vy Ajay ya kasa cewa komai kawai sai ga hawa idonsa, Mami tayi still a tsaye kamar an dasa ta a dakin tana kallonsa babu ko kiftawa virgin din da yace na mata yawo a kal, ta dade bata shiga shock irin na moment din ba, a hankali ta juya cikin rashin kuzari ta fita daga dakin, but how is she a virgin yarinyar da aka ce ta taba aure?? A corridor ta hadu da Jay da Hajja sun zo part din, Hajja tace "Aseeyah ke ma zuwanki kenan ko? ni wallahi na zata Hadiyah ce tun da ta saba ta kurma ihu ba gaira ba dalili saboda tabara" Hajja ta shiga parlon tana cewa "Ko dai iskokai gareta ne Jiddan? ina Ahmad din?" Jay bai shiga parlon Junaid ba yana kallon Mami yace "Me ya sameta Mami? Hope she is okay?" Mikewa Ajay yayi jin muryar Jay ya shige bandaki, Mami bata yarda ta kalli Jay ba tace "She is fine, I think she had a nightmare" Tana fadin haka ta shiga parlon ba tare da ta jira me zai ce ba, shi dai bai bi ta zuwa cikin parlon ba ya tsaya bakin kofar, Kilishi dake tsaye bakin kofar dakin Ajay taki zuwa kusa da Khaleesat ta fita parlor da sauri jin muryar Hajja a parlon, Mami dai ta wuce Bedroom ta bar su a parlon, Hajja ta kalli Kilishi tace "Na ji shiru shiru baki dawo ba, lafiya dai ko? Me ya sameta? Kuma ina Ahmad din? Halan tana da mutanen boye ne?" Kilishi tace "A'a ba lafiya ba Hajja, ina ganin Junaid dai fada yayi da ita, gashi can ya yanyanke ta wallahi, don saman gadon kaca kaca da jini, mun tambayesa me ya faru yaki bamu amsa ficewarsa, ita kuwa tana can kan gado" tashin hankali sosai Hajja ta dafa kujera tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta mutu??" Kilishi tace "Ga ta can dai a dakin, amma kam ta zubar da jini sosai, zanin gadon ya jike jagab da jini" Hajja tayi karfin halin karasawa cikin dakin jikinta na bari tana salati a zuciyarta, tana shiga ita ma idonta ya sauka kan zanin gadon tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Kallon Mami da ta fito daga bandaki bayan ta tara ruwan zafi a bath tub tayi tace "Aseeyah me ya faru?" Mami bata kalli Hajja ba, tana magana da kyar tace "Ta samu rauni ne Hajja" Hajja tace "Rauni? Wani irin rauni?" Karasawa tayi kusa da Khaleesat hankali tashe, Mami dai ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dauko gishiri hawayen dake makale idonta ya fara zuba, Hajja tayi shiru tana ta kallon stain din zanin gadon kamar warce ta fahimci wani abu, sai kuma ta kalli Khaleesat da ta rasa inda zata sa kanta cause she was soo weak and in pain, ta kasa kwanciyar haka zaman ma ta kasa sai Umminta take kira, a hankali Hajja ta rufe dai dai inda yayi staining a zanin gadon sannan ta kalli Khaleesat tace "Sannu Jiddah, Allah ya maki albarka....." Sai kuma ta juya ta kalli Kilishi tace "Idan Aseeyah ta kintsa ta a kawota sashi na komin dare" Hajja na kai wa nan ta fita daga dakin, Kilishi ta bi bayanta zuwa parlor with confusion, ba tare da Hajja ta kalleta ba tace "Wannan ai jinin budurci ne a saman gadon Kilishi" Kilishi ta wani gwale ido "Hajja ai ba budurwa bace wallahi" Hajja tace ко ma dai menene ga dai jinin budurci na gani akan gado, a linke zanin gadon a ajiye tukun" Hajja na kai wa nan ta fita daga parlon, Kilishi ta kasa barin inda take tsaye baki bude abinda Hajja tace na mata yawo a kai, jinin budurci kuma yarinyar da kowa yasan Bazawara ce, Mami ce ta shigo parlon bayan ta dauko gishiri a kitchen, da wani expression Kilishi tace "Aunty Aseeyah ki ji Hajja da wani zance wai jinin budurci ta gani a kan gado, wai dama boye ma Hajja aka yi bata san Bazawara bace yarinyar nan ashe?" Cike da karfin hali Mami tace "Abinda Hajja ta fada haka ne Kilishi, budurwa ce Halysaah.... Ga kuma shaida nan kan gado" Mami ta shiga daki ta bar Kilishi da sakakken baki a wajen, da sauri ta bi Mami zuwa dakin with shock tana kara kallon zanin gadon, ganin irin dagan da Mami suka yi da Khaleesat Kafin su je bandaki don ta kasa tashi tsaya wannan ya kara tabbatar ma da Kilishi gaskiya Hajja ta fada, Kilishi na jan kafa da kyar ta fita daga bangaren gaba daya, to amma ta yaya za ta zama budurwa bayan hatta iyayenta basu boye cewar Bazawara bace da aka je neman aurenta, ko dai wani salon yaudara ne wannan don su dena ce mata bazawara a gidan? Kai inaa yaudaran nan bai yaudaru ba don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata yarda ba, ta yaya warce kowa ya sani a Bazawara overnight ace ta zama budurwa kamar wani wasan kwaikwayo, wato su Junaid zai ma hankali tunda yaji yanda ake kiranta Bazawara now and then shine bari ya zo da plan, Jay was still standing outside of the main parlor don kawai ya kasa tafiya so yake Mami ta fito tace masa she is fine duk da Hajja da ta fito yanxu tace masa kawai iskokinta ne ya tashi ba komai ba ya tafi yayi kwanciyarsa she is fine now, shi kuma fin shekara daya da yayi da Khaleesat bai taba ganin alamar iskokai a tare da ita ba, don ko yaya ne ai da wataran za su tashi ko kuma su dan tabata barin lokacin da take cikin tension din Abdul, take cikin bacin rai kullum, why all of a sudden za ace tana da iska dare daya, bacci yake amma farat daya ihun da tayi ya tashe sa daga baccin kuma yasan sarai muryarta ne, kuma duk yanda ya so kin zuwa yaga if everything was alright ya kasa daure zuciyarsa, yana fitowa Parlonsa sai ga Hajja that was thinking Hadiyah ce don ita bata ma san Khaleesat bace, nan yace mata ba Hadiyah bace, shi ne suka taho part din Ajay tare, Kilishi ta fito daga babban parlon tana kallon Jay da ya juya yana kallonta ta karasa har inda yake babu kunya babu tsoron Allah tace "Jawwad wai don Allah wannan yarinya Halysaah take ko waye sunanta? Budurwa ce ko Bazawara? Ina ga duk wanda zai san matsayinta to a bayanka yake don da kai aka fara sanin yarinyar kafin Junaid Jay ya dinga kallon Kilishi still trying to process what she is saying, Kilishi tace "Dole ka kalleni haka Jawwad, mu dai mun san tun farkon neman auren yarinyar nan da kayi iyayenta basu boye matsayinta na bazawara warce ta taba aure ba, to wai kwatsam dare daya mijinta ya maidata budurwa zai raina ma kansa hankali ba mu ba, sannan ace duk tsawon watannin da suka yi tare sai yau ya fara saninta idan ba raina ma mutane hankali zai yi ba, to kansu suka yi deceiving da wannan jinin saman gadon da Hajja ta lakaba masa suna jinin budurci, na fi karfin yaron da aka haifa a gabana ya yaudare ni" Jay dai ya sauke Idonsa bayan ya gama jin duk abinda Kilishi ta fada, ta juya tayi wucewarta zuwa bangaren su Gimbiya Firdausi ta kai masu labari, Jay stood there for almost 20 mins sai ga Mami ta fito zata je kiran Yakumbo ganin ita kadai bazata iya da Khaleesat da taki bata hadin kai ba kwata kwata, Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta sauke idonta bayan sun hada ido, tace "Baka tafi ka kwanta ba?" Bai ce mata komai ba, tace "Ka je sai da safe, sun lafa mata ai tuntuni" Daga haka ta bar wajen ba ta ta kallesa ba.....

HALYSAAH PAGE 147...

Da asuba Khaleesat na dakin Mami a kwance tana bacci, wanda sai kusan karfe hudu da rabi na asuba baccin ya dauketa bayan Mami ta bata pain reliever har sau biyu a daren, kana ganinta kasan ba bacci me dadi take ba cause she is restless gashi sai firgita take ita kadai, Ita kanta Mami bata yi bacci ba daren don da ta so ma su je asibiti amma tayi considering ko waje bazata iya fita ba sai dai a zo gida a dubata kuma har Dr dinta sai da ta kira a daren bata sameta a waya ba, duk da tasan Gimbiya Firdausi babban likita ce ita dai bata je ta masu magana ba tunda babu wanda ya zo da sunan duba Khaleesat banda Hajiya Habibah ita ma tasan zuwan kwakwaf ne ba wai don Allah ta zo ba don tana zuwa tambayar da ta fara yi shine wai taji gida ya dauka Halysaah budurwa ce, kuma daga bakin Hajja aka fara jin wannan labarin, sannan banda shiri aka yi ta yaya ihunta zai karade gidan duk girmansa in dai ba waje ta fito tayi ihun ba sannan ta koma ciki, har da cewa su basu ma ji wani ihu ba kuma idonsu biyu a lokacin, Mami dai bata kulata ba, ta karaci maganganunta dake nuni da cewa babu wanda ya yarda da batun a gidan sannan ta fita... Mami na ta zaune kan darduma tayi nisa tunanin da take hannunta rike da carbi Hajja ta shigo dakin da sallama, Mami ta gaidata da ladabi, Hajja tace "Ya ba a kai ta can bangaren nawa ba bayan nace ayi Aseeyah?" Mami tace "Ai ko banda labari Hajja" Hajja tace "Kilishi na gaya ma haka ai, bata gaya maki bane?" Mami tace "Wallahi bata sanar min ba, da yake da wuri ta bar bangaren Junaid din ta bar ni a can, to amma bari in tashi mu je can din Hajja" Mami ta fada haka ne ba wai don Khaleesat zata iya tashi ba, da yaya ma suka zo part din nata don sai da Mami ta tausaya mata sosai, kuma da taimakon Yakumbo suka dawo part din nata, ta rasa wani irin zuwa Junaid yayi mata anya ma yana cikin hankalinsa kuwa yaje mata, kuma tasan dai babu abinda yake sha balle tace, Hajja tayi shiru bata ce komai ba don tunaninta kawai Mami bata yi niyyar kai Khaleesat can bangaren nata bane, dama ga maganganun da ta zo ta tarar kwando kwando a gidan akan irin yanda Mami ta dau karan tsana da tsangwama ta dora ma Hadiyah bata amsa ko gaisuwarta a gidan sannan ta hanata zuwa sashinta, wanda jira take yau ayi zama da Sarki ta ji dalili sai ga kuma issue din Junaid da Khaleesat, dama abu biyu ya kawota masarautar, Dethroning din Ajay da aka yi sai kuma tsangwamar da aka ce mata Mami ta dauka ta dora ma Hadiyah, a takaice Hajja tace "A'a ki bar ta a nan din tunda haka kika so, ya jikin nata?" Mami tace "Hajja Kilishi bata sanar min kince a kai ta can sashin ki ba, kuma ki kirata ki tambayeta ki ji...." Hajja ta dakatar da ita tace "Cewa nayi ya jikin nata?" Mami ta sauke kai tace "Bata samu bacci ba, kuma jikinta yayi zafi sosai yanxu haka duk da nayi ta bata pain reliever so nake idan gari ya waye na kira likita ta dubata ko ba wata matsala, ko kuma mu tati asibitin" Hajja dai tayi shiru don alamu sun nuna ba da hankali Ajay ya je ma yarinyar ba, ko kuma gardama tayi masa, ta juya ta kalli Khaleesat warce kana kallonta zaka san she is in pain duk da bacci take, Hajja ta karasa har kusa da gadon Mami tana kallonta ta kai hannu goshinta taji kamar wuta, numfashi ma da kyar take saukewa, duk da bacci take kana iya ganin yanda idanuwanta suka kumbura saboda kuka and she look pale, lebbenta suka dawo pure pink gaba daya, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya bata lafiya, amma naga ai Firdausi na gidan nan, me yasa baki mata magana ta shigo ta dubata ba?" Mami tayi shiru jin abinda Hajja tace, can kuma tace "To Hajja, bari ayi mata magana...." Mikewa tayi ta fita daga dakin, Hajja dai sai kallon Khaleesat take, can ta juya ta fita, bangaren Ajay ta tafi ta samesa kwance a parlonsa, ta karasa ciki tace "Kayi sallah kuwa Ahmad?" Sai da tayi tambayar taga darduma shimfide a parlon alamar yayi sallan, ganin yanayinsa ta cire abinda ya rufa da shi duk da bacci yake bai san ta shigo ba, nan ya fara sambatun da bata ma san me yake cewa ba idonsa a rufe yana kokarin juyawa tayi saurin cewa "Ahmad kar fa ka fado kasa, baka da lafiya ne?" Sai a sannan ya bude ido da kyar amma ya kasa barin idon a bude ya mayar kawai ya rufe, ta kai hannu forehead dinsa taji wani irin zafi don har yafi na Khaleesat zafi, she was quiet for some seconds tana ta kallonsa don ya bata tay sosai, sai kuma a hankali tace "Tashi ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login