Showing 96001 words to 99000 words out of 120027 words
Chapter 33 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar
need for any questioning Jay na kallonsa yace "You are not mad to beat Walid that way, sai dai ko shaye shaye ka fara, me yayi maka that warrant such merciless beating?" Kin cewa komai Ajay yayi kuma yaki kallonsa yana jin tambayar ma na sa xuciyarsa ya fara tafarfasa, ganin yaki cewa komai kuma babu alamar zai ce komai yasa Jay bai sake cewa komai a parlon ba, suna ta zaune har na fin minti biyar, Jay ya mike without looking at him ya fita daga parlon, duk da ya ga Khaleesat that is almost near the door zata shiga parlon hannunta rike da tray din Hot chocolate da cookies a gefe amma haka ya ja kofar ya kulle yana kallonta yace "Wato ke me miji sau biyu kina ce min yana bacci whereas idonsa biyu ko?" Bata san sanda tace "Ehh, since he is always made to look like the black sheep and unwanted person of the family, no one is even willing to consider or reason with him, no one is giving him a listening ears, no one cares about his feelings, ban san offense dinsa ba, thank God title dinsa kawai aka rabasa da shi not his life, Kilan he will now be free from everyone's hate henceforth...." Muryarta na rawa ta kare maganar cikin zafi, Kallonta kawai Jay yake babu ko kiftawa, can ya juya ya bar wajen, ta bude kofa tayi shigewarta parlor ta kulle, Bata ga Ajay a parking ba ta karasa bedroom ta gansa zaune gefen gado gaba daya mood dinsa ya canza, tana tafiya slowly ta karasa har kusa da shi ta ajiye tray din kan beside drawer tana kallonsa tace "Baka ci abinci Jiya da daddare ba, i made you some Hot chocolate" Ya kalli tray din shayin da cookies sai kuma ya daga idanuwansa ya kalleta sosai taji gabanta ya fadi kuma bata cire idonta a nasa ba sai shi ne ya sauke idonsa a hankali, ya kai hannu ya dau cup din shayin yace "Ba kazanta ciki dai" Murmushi tayi tace "Ba dai yawa ne... Ya dan bude ido yace "What?" Ta langwabe kai tace "To cup din ne kawai ban wanke ba ai, kuma bayan na hada shayin i wanted to taste if the sugar is okay, ban san da zafi ba shi ne ya kona min bakina, ni kuma na juye na bakin a ciki da sauri, that is just it" Bai san sanda yayi murmushi ba don ba karamin dariya ta basa ba, ita dai kallonsa kawai take don murmushin look cute on his face, iya dariya kawai ta taba ganin yayi sau biyu kuma irin dariyar mugunta na Boss, ranan da ta yanke hannunta a kitchen suna Maryland Ikcin tana apartment dinta together with him, sai kuma a hotel room da zata cijesa, tace "Ko a zubar kawai?" Ya ajiye cup din kan tray din yace "Zai fi dai" Ta mike zata kai hannu ta dauka tray din ya jawota ta fado jikinsa ta sakar masa kukan shagwaba.... Wajen karfe bakwai da rabi Mami ta zo bangaren, Ajay ya fita zuwa parlor ya zauna ya gaisheta don tana zaune parlon, Khaleesat kuma na zaune kan Carpet bayan ta gaisheta tun shigowarta, Mami na kallonsa ta amsa gaisuwarsa tace "How was ur night?" Yace "Alhamdulillah" Sosai tayi mamakin ganinsa kamar babu abinda ya faru sabanin yanda tayi tunanin zata samesa sanin hali, he looks bright, shiru Mami tayi, bayan dan lokaci tace "Junaid, ka gaya min me ya hadaka da Walid?" Ya sauke idonsa a hankali don har ransa baya son ana masa maganar Walid don hakan kara saka masa wani radadi yake a zuciya barin idan ya tuna yanda ya zo ya samesa har ya gama cire belt, ya girgiza kai calmly yace "Mami abinda ya faru kenan na gaya maki jiya, we had issues in the mosque a sanda mu ke karatu" Ita dai Khaleesat kanta na kasa, Mami sai kallon Ajay take kafin tace "To amma menene yasa kai baka iya kai zuciyarka nesa ba? Yanzu meye amfanin irin haka?" Ajay dai yayi shiru, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kiyaye, kun gaisa da Mai martaban ne?" Ajay ya girgiza kai kawai, Mami tace "Ka tafi ka gaishesa" A hankali Ajay yace "A'a zan bari har sanda zai huce, zai ga na kara disobeying din abinda yace idan na je wajensa yanxu, and I know he won't take it likely Mami tayi shiru don tasan gaskiya ya fada, tasan yanxu dai kawai sai dai ayi jiran zuwan Hajja ranan talata don tun jiya da daddare ta kirata bayan ta bar fadan sarki, Mikewa Mami tayi tana kallon Khaleesat tace "Kin basa breakfast ne?" Khaleesat tace "Shayi ya sha kawai Mami tace "To ki zo ki amsar masa abinci na girka yanxu saboda shi.... Khaleesat tace "To Mami" Kofa Mami ta nufa ta fita daga parlon. Aunty na zaune dakinta idonta ya kumbura don kuka, Hajiya Nafisah dake zaune dakin bayan Aunty ta kirata ta taho tun daga Kano tace "Don girman Allah ki dena wannan kukan fulani kar ki tado Migraine headache din ki kinsan baya maki da sauki sai anje asibiti" Cikin kuka Aunty tace "Ta yaya zan daina kuka Nafisah ace duk effort dina ya tashi a banza kenan ya tafi in vain, mulkin ma sai kara nisanta zuri'ata yake fisabilillahi, wai Jawwad sabon Yarima? Me yasa Sarki zai min haka duk baya son jinina, wallahi ban taba kawowa zai ba Jawwad Yarima ba bayan ga dan sa na cikinsa, kawai ya maida min Walid dan banza kamar ba dan gidan nan ba ya maida shi kamar ba shi ya haifesa ba rikonsa ake a gidan, dama ba Allah ke shirya yaro wanda ya so ba? Ai bamu fidda rana Walid zai nutsu ba wataran, duka duka nawa yake da har baza ayi masa uxuri ba? Kowa fa da irin yarintarsa, ni dama can wallahi Jawwad din nan a tsane yake a raina ganin yanda Sarki ke fifita shi kamar shi ne dan cikin nasa na asali, ko Junaid baya sawa a lamarinsa yanda yake sa Jawwad, to gashi yayi me gaba dayan yanxu wai ya ba Jawwad Yarima, ba gwara ma Junaid din ba sau dubu tunda ina jin kamshin sarautan kusa da mu Nafisah? Wallahi gwara Junaid yayi ta zama a Yariman da dai wannan abinda Sarki ya min, na ma fi tsanar Jawwad din akan Junaid duba da yanda Sarki yafi fifitasa, kawai saboda Yarimancin ne yasa na sa Junaid a gaba maimakon shi" Nafisah tace "Fulani ki tsaya ki saurareni, ba fa wani abu bane na tashin hankali, aiki ne kawai zai dawo mana sabo ba wani abu ba, amma yanda Sarki ke passing passing title din Yariman nan haka nan zai passo shi ya dawo kan Walid ki sha kurumin ki, me yasa har yau ba a ci galaba kan Junaid dari bisa dari ba?? Ba don ance yana da ibada cikin dare ba, to kawar da Jawwad har wani wahala zai mana mutumin da sai in yanxu ya hakura da bacci?? Balle ma da bakin ki kike gaya min uwar tasa ma ya juya mata baya sai yanda matarsa tayi da shi, kuma kika sa aka maki bincike kika ga ba banza ba ashe Maimuna aiki take ta zabgawa akan er ta ta mallakesa tunda an ga irin shegun dukiyoyin da Marigayi Sarki Ahmadu ya bar masa, ai sai dai in ke kika ce kar a kawar da shi ne baza ayi irin aikin ba Fulani" Aunty na huci tace "A kawar da shi kawai ko nawa zan bayar wallahi, yau in babu shi ai dole Walid za a ba Title din tunda babu ta yanda za ayi Dethroning Junaid sannan a sake cewa za a mayar da shi kamar wasan yara... Walid din dai za a nada daga karshe" Nafisah tayi wani dariya tace "To an gama hasken idaniyan sarki, in sha Allah ina komawa za a fara aiki, sai dai don Allah ki saki ranki ki nuna kin yi murna sosai, ki nuna gwara da aka kwace hannun Junaid dama Jawwad ne yafi cancanta ta yanda babu shegen da zai zarge ki a Masarautar nan" Aunty da har taji wani irin sanyi a ranta tace "In Allah ya yarda Nafisah, zuwa anjima zan je in ma uwarsa Allah ya sanya alkhairi faram faram, sannan in nuna mata takaicin da nake ta yi dukan da Junaid yayi ma Walid duk tunanina sarki zai sa Dogarai su rama masa amma sai naga akasin haka shi yasa raina ya sosu sosai wato ya doki banza kenan, ga karaya biyu a hannu, ga hakorinsa daya na girgidi ya kusa faduwa, ga targade kusan biyar a kafa, hatta kwankwasonsa yau da ya tashi ya kasa zama wallahi yana can a kwance, jikin duk yayi masa tsami baya iya motsin kirki" Nafisah tace "Yauwa, haka za ki yi mata kawai, su ma tsinannun yan uban dake gidan nan ki nuna masu kinyi farin cikin dethroning din Junaid ko ba komai Jawwad yafi cancanta don ya fi sa hankali, ko kuma duk sun watse?" Aunty tace "Ina fa har yanxu suna nan, duk ana jiran Hajja wai tana hanya ranan Talata, baki ji yanda take ta fada ba ita ma tayi bakin ciki da wannan abu da sarki yayi ma Junaid, sai ta zo mu ga me zata yi" Nafisah tace "To ita Maimuna ya tayi?" Cike da takaici Aunty tace "Tana ta murna ita ga er iska har da hamdala da karfı a parlon Sarki wato sarauta nasu ne yanxu..." Nafisah tace "Ki Kyaleta, za ta dawo su yi bakin ciki, ke dai kawai yanxu kiyi abinda nace yanda babu wanda zai zarge ki" Wani makirin murmushi kawai Aunty take tana goge hawayen idonta.
HALYSAAH PAGE 143...
Khaleesat na kitchen da yamma tana dafa Jollof rice ganin kamar shi ne favourite din Ajay ko bazai ci ba dai at least she cooked don tun daxu ya fita, Yakumbo babu yanda bata yi da ita ta kama mata girkin ba amma taki yarda, hakan yasa take ta tsaye kitchen din take mika mata duk abinda taga zata dauka, tun karfe uku Aiav va bar gidan bayan........ da hukuncin da Sarki ya dauka kan Junaid, don ita ma kana ganinta kasan tana cikin damuwa jikinta yayi sanyi tun da abun ya faru, duk sonta da bada labari yau dai ba um ba um um, sai khaleesat ce ma ke mata magana jifa jifa, wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta gama girkin da take yi Yakumbo ta fara goge goge kitchen din tana tidying ko ina, Khaleesat ta gama wanke hannunta da wash a sink jin kamar an bude kofar parlor ta goge hannunta da towel ta fito zuwa babban parlon, tsaye tayi with shock tana kallonsu, bata san sanda ta tafi da sauri ta rungumeta ba cike da mamaki tace "Sophiee" Safiyyah sai washe baki take har kunne, Ajay dai ya wuce ciki ya bar su a parlon, Khaleesat ta koma baya tana kare mata kallo as if still wanting to pure Safiyyah ce, cike da farin ciki tace "Baki ce zaki zo ba ai, baki ma ce min kin dawo Nigeria ba Sophie" Safiyyah ta rike haba tayi kasa da murya tace "Yau sai gani a Great Emirate din Bauchi na zo wajen kawata, abun kamar al'mara, duk wannan parlon gari guda naki ne ke kadai kawata??" Khaleesat tace "Ni dai me yasa baki ce min zaki zo ba" Safiyyah tace "Tun yaushe nake maki magana baki online na kira wayar ma a kashe" Sai a sannan Khaleesat ta tuna da wayarta, ita in ta shiga damuwa mance da wani abu take wai shi waya, kama hannun Safiyyah tayi...... panom Ajay, uama uaxu ta yyara uakin na ud turaren wuta ta kunna a ciki, Safiyyah ta dinga bin dakin da kallo tace "Maa sha Allah matar Yarim-" Khaleesat ta sauke kanta bata dai ce komai L bayan ta ajiye akwatin hannunta tace "Ya Mama da Baba fa?" Safiyyah tace "Da kyar in gay maki aka bar ni, a haka ma sai da na lallaba Y. musty ya saka baki, kin san har da shi da matars muka dawo, to shi ne fa aka bani kwana biyl kacal, kaya kala uku ma na dauko, na hau wata rubabbiyar mota sau uku tana lalacewa a hanya ke kya ce Lorry na hau, muna kusa shigowa Bauchi ta karasa macewa taki tashi kwata kwata in gaya, da mijin ki ya kira ya tambayi ko mun karaso nace masa ai motar ma tayi condemn gaba daya, in gaya maki shi ne fa ya taho a babban motarsa ya daukeni amma fa na sha jira, ashe ashe tafiyar kusan awa daya da wani abu yayi kafin ya iso inda motar ta mutu, sai da muka dau hanya naga daga uwa duniya shi ma ya taho daukata" Khaleesat dai sai murmushi take amma fa hankalinta yayi kan ta tafi ta duba Ajay da ya shiga daki, ta sauke ajiyar zuciya tace "To sannu da zuwa kawata, i am soo happy to see you wallahi, yanxu ki shiga kiyi wanka, idan ma zaki yi sallah duk kiyi, bari in je in hada maki abinci a kitchen" Safiyyah ta cire mayafin jikinta tace "Ohh shkkn duk sanda nake son ganinki sai dai in taho Bauchi kawata??" .......ta gansa ya kunna laptop dinsa yana operating, ta zauna gefen kujera tana kallonsa ta marair ice tace "Shi ne baka ce min Sophie na hanya ba: Ya dan kalleta yace "Au, wai ita ce dama" Ta hara sa duk da dariyan da ya bata, yana ci gaba da abi, la yake yace "Ni ma a bakin kofa muka hadu ai z shigo" Ta sauke idonta a hankali tace "I made some food...." Ya daga kai ya kalleta calmly yace "Yau kika koyi girkin?" Er dariya tayi tace "To ai a America ma nayi ka ci baka sani ba" Yana kallon dimples dinta a hankali yace "In ur dream" Ta zaro ido tace "Wallahi da gaske" Kallonta kawai yake, tace "Ranan da ni da Safiyyah muke PS5 game a apartment dina before our exams ai mun cinye maka abincin da ka dafa shi ne nayi sauri na dafa wani kafin ka dawo" He was just staring at her, can kawai ya dan yi murmushi bai ce komai ba ya ci gaba da abinda yake yayi a laptop dinsa, mikewa tayi ta fita zuwa kitchen taje ta zubo masa abincin ta kawo masa tana ajiyewa yace "Later" Shiru tayi tana Kallonsa, can ta sauke idonta tace "Ohk" Mikewa tayi ta dau tray din ta fita.... Wajen karfe takwas da rabi Khaleesat na tare da Safiyyah da ke shan fresh fruits ga tulin tsire a gefenta ta....... Kalonta tace to da kin tsaya kina wanı yanga wal baza ki daura ba, ba gashi nan waist din ki har ya cicciko ba, ai shi jigida amfaninsa kawai ya ciko da kai idan ka saka kaya ya zauna maka das das, baki ga yanda ya kara maki shape ba" Khaleesat kamar zata shareta sai kuma tace "To ni ai noise din da yake making ne bana so, ko titi mutum ya fit-mutum yasan ka sa jigida?" Safiyyah tace "Haba dai me zai kai ki titi kuma kamar gantalalliya kina matar manya, titi ai sai mu, kuma ni yanxu waye yasan da jigida a jikina tunda ba tsalle tsalle nake a titin ba" Khaleesat bata sake tankata ba ta ci gaba da gyaran kayanta, Safiyyah dake ta kula da cewar Khaleesat na cikin damuwa amma tana ta bovewa tace "Ni fa duk yanda za kiin pretending as if everything is okay ba yarda za ba don nasan halin ki Khaleesat" Khaleesat ayi murmushi kawai don dama jira take ta gama ciye ciyenta tayi mata maganganun dake cinta a rai, Khaleesat ta dawo kusa da ita ta zauna, a han' tace "Sophie tun da muka dawo gidan nan issues upon issues, kuma issues ba kananu ba" Safiyyah ta matsar da tsiren kusa da ita tace "What issue kawata?" Khaleesat ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Different type of issues, daya daga issues din yasa har aka sauke sa Yarima jiya da ..... Baam aaya tajı nawaye ya cıka idonta, satıyyan da hankalinta ya tashi tace "Na shiga uku ki gaya min don Allah, kar dai Ajay kike nufi?" Khaleesat ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Safiyyah was shock and speechless ta dinga kallon Khaleesat babu ko kiftawa, a hankali ta dinga maimaita "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Bata sake cewa komai ba har na minti biyu a dakin don sosai labarin ya daketa, after a while tace "Khaleesat me ya faru haka? Kuma waye ya saukesa? Me yayi?" Khaleesat na goge idonta tace "It's not even worth speaking about it Sophie, Allah yasa hakan shi yafi masa alkhairi kawai" Sosai jikin Safiyyah yayi sanyi ba kadan ba and deep down her she felt happy ta yanda taga Khaleesat tayi showing genuine concern wato ta damu ba kadan ba da abinda aka yi ma mijinta, cike da takaici Safiyyah tace "Sai aka bama wa Yariman??" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Ya Jawwad" Da wani expression Safiyyah tace "Ya Jawwad??? Kuma ya yarda ya amsa? Amma ci amana wallahi, ba gwara ya gudu a nemesa a rasa ba da dai ya yarda a nadasa yarima, title din cousin dinsa fa?? ai ana barin halal ko don kunya, da wani idon yake kallon Ajay yanxu a gidan nan? Gaskiya ban ji dadin wannan han abun ba har cikin
Safiyyah tayi jimaminta sosai, bayan kusan minti biyar Safiyyah tace "Har naman ya fice min a rai wallahi, haba ta yaya za a cire Ajay Yarima it doesn't even make sense, wannan kuma rashin son zaman lafiya ne, bari ma in kwanta kawai da wannan takaicin dama na gaji ga kuma wannan labari mara dadi, duk yan gidanmu da yan unguwanmu na gama shelanta masu Kawata na auren Yarima me jiran Gado a Bauchi