Showing 87001 words to 90000 words out of 120027 words
Chapter 30 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar
ta kai mata, har kusan Magrib Khaleesat na bangaren Mami a zaune, tana son komawa part din Ajay amma tsoron haduwa da Walid ko a hanya ya hanata tafiya, Har sai da Ajay ya shigo da Drugs da ya siyo tun da rana, ta sauke ajiyar zuciya ganinsa, bayan ya nuna ma Mami prescription din drugs din yayi mata sai da safe, Mami ta kalli Khaleesat tace "Ki tashi ku je sai da safe, Nagode" A haka suka bar parlon Mai martaba kansa a kasa, Sarki dai sai kallonsa yake tun bayan da yaji abinda ya kawosa, after almost a minute sarki ya numfasa yace "Ka koma zuwa ina kenan?" Ajay bai dago kansa ba yace "Ko a nan garin ne ranka shi dade...." Sarki yace "Ohk, kawai dai ya zamto baka cikin Emirate kake nufi ko?" Ajay yayi shiru bai ce komai ba, Mai martaba yace "Isn't it?" Ajay ya gyada kai a hankali yace "Haka ne ur highness" Sarki yace "Ohk, amma meye dalilin ka? Ko don saboda abinda ya faru recently?" Ajay yace "A'a dama ina da wannan intention din in har zaka amince min zan koma daya daga gidajenka na cikin garin nan in zauna" Calmly Sarki yace "To ban amince ba Ahmad, don bana son kayi nisa da ni, kafin ka zo da wannan batu Jawwad ne ya fara zuwa min da shi kuma na hanasa, ina son ku duka biyu a kusa da ni, and i will make sure ur wife lives comfortably in this Emirate if that's ur fear Ahmad" Ajay ya girgiza kai da sauri yace "A'a ranka shi dade ba don abinda ya faru bane, dama tun asali kasan i prefer staying outside of the Emirate" Mai martaba yace "Learn to love staying inside of the Emirate Ahmad, babu zancen barin ka cikin gidan nan, i won't be king forever, I won't rule forever, wataran dole ka gaje ni, and you will rule this great Emirate in sha Allah" a hankali Ajay yace "Allah ya huci zuciyarka, ur wish is my command in sha Allah, a gafarce ni idan na bata maka rai da batun nan" Sarki bai kara cewa komai ba, bayan minti daya yace "Kuma yaushe zaka koma bakin aikin ka?" Ajay yayi shiru don babu inda tunaninsa ya tafi sai kan Khaleesat and how she will Cope in the palace idan ya koma aiki, A hankali yace zan zauna a gida. I know that, ko ka zauna gida naga ba shigowa fada kake yi ba ake yin komai da kai, baka involving kanka a abubuwa da yawa da suka shafi masarautar nan, it is as if you are not even in the House, to me yasa sai kayi shawara kafin komawa bakin aikin ka?" Ajay ya sauke idonsa yace "Ranan Litinin in sha Allah zan koma" Sarki yace "Allah ya taimaka" Ajay na ta zaune parlon har bayan wani dan lokaci Sarki dai sai kallonsa kawai yake, dai dai sanda Walid ya bude kofar parlon ya shigo, yana ganin Ajay a ciki har ya fara komawa baya zai fita sai kuma yaji yana ma Mai martaba sai da safe, hakan yasa ya tsaya, ai bai san yana ciki ba tun daxu da tuni ya tafi bangaren sa wajen Khaleesat, Ajay ya mike ya nufi kofa ya fita Walid ya bi sa da kallon gefen ido sannan ya karasa cikin parlon. Ko da ya koma part dinsa ya tarar da Khaleesat har tayi bacci a bedroom dinsa, yala kan kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran ya lumshe ido, bai yi tunanin Sarki zai yi turning down request dinsa na barin Palace ba and he really felt bad about it, yayi tunanin sarki zai yi considering abubuwan dake faruwa ya basa go ahead din barin gidan even if it's just for a while, ga kuma maganar aiki da zai koma ranan litinin and today is Thursday, ji yayi kansa ya kulle gaba daya, bayan abubuwan dake faruwa gidan babban dalilinsa na jin bai son zaman masarautar saboda Jay ne don bai son suna haduwa in anyway ta haka kadai ne zai iya concentrating.... Washegari da asuba Ajay na tafiya masallaci Khaleesat ta je ta kulle kofar babban parlon ta ciki kamar yanda ta saba, tana idar da sallah ko azkar bata gama ba taji ana knocking kofar parlon, mamaki tayi don in ya tafi sallah sai karfe bakwai da rabi wani lokacin har da minti arha'in yake dawowa nart din ranta va hata hra all to open the door tace "Waye?" Yace "Bude min kofa" A hankali ta murda kofar ta bude tana kallonsa ya shigo parlon ya wuce parlonsa, ta kulle kofar ta juya ta bi bayansa har zuwa parlon, kafin ta shiga har ya shige Bedroom still ta bi sa, ta gansa tsaye yana kokarin cire jallabiyarsa alamar kwanciya zai yi, tun bai gama cirewa ba ta koma other bedroom din zata karasa azkar dinta sannan ta shiga wanka, Ajay ya fasa cire jallabiyan bayan ya tuna zai duba jikin Mami ya juya ya sake fita daga dakin zuwa part din Mami, Khaleesat ta daga kai jin kamar fita ya sake yi, after few minutes ta mike ta fita daga dakin, sai da ta kara shiga bangarensa ta duba don tabbatar da fitan yayi sannan ta fito ta nufi babban parlor da nufin kulle kofar da makulli taga an bude, tsabar shock kasa kwakkwaran motsi tayi a wajen ganin Walid, can ta juya da gudu ta koma daki da nufin saka makulli amma taga Ajay ya cire makullin, cikin rikicewa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Tuni ya shigo har cikin dakin yayi kasa da murya yana bin ta tana komawa baya yace "Babu wani Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, duk ke kika jawo, da kin bani hadin kai tun a America da duk ba a zo nan ba amma ke me taurin kai kika ki bani co-operation, to yanxu dai mijinki na can masallaci suna karatu da sarki da wasu fadawa kuma shi da fitowa daga masallacin nan dai sai kusan karfe takwas, don haka kawai ki sallameni in kama gabana, kin ga kafin nan ma har mun mance mun yi wani abu, idan kuma kika ce yau ma taurin kai za ki min ko kuma ki min ihu wallahil azeem sai in kashe ki in kashe banza, bar ganin an samu CCTV camera part din Mami, nan babu ko normal camera ki ji in gaya maki halle cctv" Randa rawa hahu ahinda iikin Khaleesat ya hau rawa kamar mai jin sanyi, shi ko fisge hijab din jikinta ya fara yi kamar yasan ihu take da niyyar kurmawa ya shake wuyarta da hijab din yanda zata san da gaske fa yake sai ya iya kasheta idan bata basa hadin kai ba, hakan bai sa ta fasa kururuwa ba tana basa hakuri duk da muryarta bai fita sosai saboda shakar da yayi mata, a haka ya yage hijab din jikinta da karfi tun daga wajen wuya har kasa sannan ya jefata saman gado, da sauri ya fara cire belt dinsa jikinsa na rawa ganin alamar kayan bacci ne ma a jikinta, dai dai sanda aka bude kofar dakin, da mugun shock ya juya suka yi ido hudu da Ajay dake tsaye bakin kofar, nan ya fara mayar da belt dinsa da sauri yana zare ido, Khaleesat kuwa kuka ta dinga yi tana rufe jikinta da hijab dinta da ya yage ta sauka daga kan gadon ta tafi gun Ajay jikinta na rawa tana kuka sosai, Walid sai gwalo ido yake bayan ya gama saka belt dinsa yana kallon window din dakin ko zai samu hanya, a nan kasan dakin Ajay ya jefar da wayar hannunsa ya karasa ciki ya fincikosa yana kallonsa da idanuwansa da suka yi ja, ya fito da shi har zuwa Main parlor, ya fara masa wasu mugayen kulli a ciki, Khaleesat na ganin haka ta saka wani hijab ta taho parlon da sauri ta riko Ajay tana girgiza kai tace "Noo plsss, don girman Allah kawai kayi reporting dinsa...." Hankadata Ajay yayi sai ga ta kan kujera ta fadi, Yana jan Walid ya bude kofar parlon suka fita daga part dinsa gaba daya har suka yi nisa da bangaren nasa, Walid na kokarin guduwa Ajay yasa kafa ya kwashesa kasa sannan ya lankwashe hannunsa daya ya take da karfi, Walid ya kurma wani wagegen ihun azaba don sai da hannunsa yayi wani kara bayan Ajay ya take hannun, Ajay ya dagosa ya hau sauke masa wasu arnayen kiss ta ko ina yana yana jin wani irin yanayi ya dena ganin fuskarsa sam ya dena ganin fuskarsa saboda jinin da ke zuba a goshinsa, tuni mutanen gidan suka fara fitowa jin ihun Walid, hakan kuma bai sa Ajay ya fasa dukansa ba yana bugasa da bango yana punching dinsa, Cikin tashin hankali su Hajiya A'isha da Kilishi da Ummi suka dinga cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, mun shiga uku mun lalace, kashe sa zaka yi? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, jama'a ku kawo agaji zai yi kisan kai" Daga nesa Aunty ta tsaya with shock tana kallon dukan da Ajay ke ma Walid jikinta na rawa, ta fashe da kuka ta taho da sauri ta cakumo Ajay tana jijjigasa tace "Kashe min dan nawa zaka yi Junaid? Kashe min Walid din zaka yi?" Ko kallonta Ajay bai yi ba bai kuma fasa dukan da yake ba, su Maryam da Khadijah sai rusa kuka suke, da sauri Ummi ta tafi ta saka ayi kiran Mai martaba dake Masallaci, Dogar Dogarai biyu suka zo kwace Walid hannun nun Ajay bayan Kilishi ta tafi ta kirasu.... aika anyı kıransu also stood in shock yana kallon scene din, ya karasa wajen cikin sauri ya finciko Ajay da karfi yace "Are you out of ur senses? What is this u are doing? shaye shaye ka fara??" Mukhtar da shi ma shigowarsa kenan yayi saurin Janye Walid shi da wani Dogari bayan Jay ya finciko Ajay ya hadesa da bango, Ajay ya fixge hannun Jay daga rikon da yayi masa yana huci kamar zaki, dai dai sanda Mai martaba ya karaso wajen yana kallon Ajay babu ko kiftawa, Ajay yaki yarda ya kallesa ya kauda kai yana sauke numfashi, can kuma ya juya ya bar wajen kamar zai tashi sama ya tafi part dinsa, Sarki ya bi sa da kallo, duk sauran mutanen wajen ma haka suka bi sa da kallo, Aunty na koke koke ta bi bayan wa enda suka fita da Walid su Ummi duk suka bi bayanta da sauri, Mami dai na tsaye bakin kofar part dinta ta kasa cewa komai.
HALYSAAH PAGE 140...
Ajay na shiga part dinsa ya sa ma kofar key, tsabar yanda Khaleesat ta girgiza har Ikcn bata tashi a inda yayi dumping dinta ba a babban parlon, ko Kallonta bai yi ba ya nufi parlonsa kamar zai tashi sama, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa zuciyarta na wani irin bugawa, kawai taga ya juyo ya dawo parlon yana kallonta Strictly yace "Do not say anything to anyone duk tambayar da za a maki Yana kai wa nan yayi wucewarsa parlonsa taji yayi banging kofar, Khaleesat ta fashe da kukan tashin hankali ta zamo abar tausayi, kuka kawai take a parion kamar ranta zai tita, daga karsne ta mike tana tafiya a hankali ta tafi parlonsa bugun zuciyarta na tsananta, ganin yana Bedroom ta karasa ta murda kofar taji ya sa makulli, ta juya hawaye na sauka idonta ta koma parlor ta zauna tayi tagumi, knocking din kofar parlon taji ana yi ta mike a tsorace duk da kofar a kulle yake, muryar Mami taji a bakin kofar, hakan yasa ta karasa zuciyarta na bugawa ta bude kofar, Mami ta shigo tana kallonta tace "Ina Junaid din?" A hankali Khaleesat tace "Yana daki" Mami ta nufi cikin parlonsa Khaleesat ta bi bayanta bayan ta kulle kofar parlon, knocking kofar dakinsa Mami tayi tana kiransa, After a while ya bude kofar, ya ki kallon Mami, Mami ta shiga dakin tana kallonsa tace "What happened Junaid? Me ya hadaka da shi haka??" Ajay yayi shiru bai ce komai ba kuma bai daga kansa ba, a fusace Mami tace "Magana nake maka ko baka ji na ne" Ya dago idonsa a hankali yace "He is just daring me in this house, dama kuma tara sa nake, ko shekaranjiya a gaban Mai martaba ya gaya min maganar banza" Mami tace "Shi ne zaka masa irin wannan duka Junaid? Ko dai baka da hankali ne?" Ajay ya ki cewa komai, Mami tayi shiru tana ta kallonsa, daga karshe ta juya kawai ta fita daga dakin Ajay ya mayar da kofarsa ya sa makulli, Mami na kallon Khaleesat tace "Me ya masa yau din yayi masa wannan duka haka?" Hawaye na sauka idon Khaleesat ta girgiza ma Mami kai kawai alamar bata sani ba tunda ya mata warning kar ta fadi komai, Mami ta nufi kofa ta fita daga bangaren, Khaleesat ta tafi ta kulle kofar ta fashe da sabon kuka ta sulale wajen, Walid dai tuni aka yi asibiti da shi hannu a karye. Tun bayan da Mami ta tafi Ajay bai sake fitowa daga dakinsa ba, Khaleesat dai na ta zaune parlor tana tunanin wannan wane irin bala'i haka, sai lokacin sallan juma'a Ajay ya fito daga bangarensa sanye da fararen kaya kamar ba abinda ya faru zai tafi masallaci, sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "Have you eaten?" Duk da bata ci ba kawai ta gyada masa kai, ina taga nutsuwar cin abinci ita kam, yana fita parlon taji ya kulle daga waje, bai je masallacin da ya san Mai martaba da mutanen gidan ke zuwa ba, yayi tafiyarsa masallaci me nisa. Bayan isha'i Ajay ya nufi fadan Mai martaba tare da Khaleesat dake biye da shi a baya zuciyarta na bugawa, tun safe Mai martaba ya sanar da zaman, Ajay ne karshen shigowa ya tarar da kusan duk familyn gidan zazzaune a babban parlon, hatta wa enda ke nesa duk sai da suka amsa kiran Sarki suka zo, tun daga iyaye har 'ya ya da jikoki, Walid ma na zaune parlon da katon bandage an nann kansa ga hannunsa da aka daure saboda karyewan a da yayi, fuskarsa duk a kumbure, ga targade kashi kashi a kafafuwansa, bakinsa ma yayi suntum, Aunty dai na zaune idonta duk sun kumbura don kuka jira kawai take taga hukuncin da Mai martaba zai dauka kan Ajay kafin ma ta ce komai don tun safe taki magana a gidan, Ajay bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya zauna kusa da Mukhtar ya sauke kansa kasa, kowa na parlon kallonsa yake banda Sarki, Khaleesat jiki a sanyaye ta tafi ta zauna kusa da Mami, ita ma aka bi ta da hararan tsana, for 5 mins babu abinda Sarki yace a parlon, ko ina was absolutely silent, in da sabo duk sun saba don sarki sai ya iya bata kusan minti goma bai yi magana ba kamar dai yana nazarin abubuwan da zai furta before saying anything, daga karshe Sarki ya sauke ajiyar zuciya dama an riga an bude waien da addu'a tun Ajav basu karaso ba tunda haka ne sai mai martaba ya fara magana cike da nutsuwa da kuma dattako... ina da labarin abinda ya faru a gidan nan yau da safe, which is so unfortunate, bana kuma tunanin akwai wani abu da Ahmad zai fada da zai yi justifying abinda yayi ma dan uwansa ignoring my few days ago warning akan duka a cikin gidan nan, don haka Ahmad is not and will never be capable of ruling this Emirate one day one time, babu ta yanda za ayi a ba madambaci mulkin masarautar nan, shi ne naga yana da kyau in tara ku nan in fara sanarwa tun daga cikin gida cewar Ahmad Junaid Yusuf is hereby dethroned as the prince of this great Emirate, daga rana irin ta yau na sauke sa a matsayin Yariman wannan masarauta...." Ajay ya daga kai a hankali yana kallon Mai martaba babu ko kiftawa kamar yanda kowa na parlon ke kallon Sarki with utmost shock, Khaleesat ta daga kai hawaye cike idonta tana kallon Ajay, Aunty sai gyara Alkyabbar jikinta take tana kara kallon sarki da idanuwanta kamar za su fito don sai taga kamar mafarki take ba daga bakin Mai martaba hakan ya fito ba ko kuma ita ce bata ji da kyau ba, Jay ma sai kallon Mai martaba yake babu ko kiftawa, Mami ta sauke idanuwanta a hankali, the announcement came as a shock to everyone in the parlor babu wanda ya kawo wannan hukuncin sarki zai yanke kan Ajay, Sai da sarki ya bari kowa ya gama processing abinda ya fada sannan ya ci gaba cikin nutsuwa yace "And from tomorrow in sha Allah Ahmad Jawwad will be crowned the Prince of this great Emirate through all proper rite" Sai da numfashin Aunty ya dauke na yan dakiku, ta dinga kallon sarki babu ko kiftawa, duk tunaninta Walid zai nada sabon Yarima tunda Walid ne second blood son dinsa, kowa na parlon was in a shock da jin wannan hukuncin na mai martaba. Daga can Fulani Aseeyah ta bude baki ta fara magana "Amma Allah ya taimake ka...." Dakatar da ita Sarki yayi yace "Ban bukaci Opinion din kowa ba, and this is disrespect to the king Fulani Aseeyah" Mami tayi shiru, Hadiyah ta kalli Ummi da farin cikinta ya kasa boyuwa sai kallon Mai martaba take unbelievable, hawayen farin ciki ne ya hau sintiri fuskar Hadiyah ta dinga ganin abun kamar a mafarki wai mijinta ne Yariman Masarautar nan yanxu, Mai martaba ya ci gaba yace "Na saka Makama ya sanar ma masu sarautu, tun daga Hakimai, dagatai da sauransu duk su hallara a fada gobe su shaida wannan sauyi da aka samu sannan a nada sabon Yarima, and mind you all... no one is in the rightful place or position to question the decision of the King in anyway, and as for you