Showing 51001 words to 54000 words out of 134562 words
Chapter 18 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa
tayi sallan maggariba da isha,
cikin kasala ta zame ta konta kan sallayar da nufin zatayi bacci ,
Amman sai ga wani sabon al'amari mai ban tsoro kuma,
bayan ta konta tayi Addu'a sannan ta lumshe ido a hankali bacci ya fara fizgarta,
lokaci d'aya bacci mai dad'i ya d'ebeta,
Amman cikin baccin sai taga Hamma Umar yana rik'e da jariri fari tas mai kyau yaron sai kuka yakeyi shi kuwa Hamma Umar sai ya mik'e mata jaririn ita kuwa sai ta ture ta juya ta gudu can gefen su,
shiko Hamma Umar d'in sai yasa yaron a kafad'an shi yana lallashin jaririn yana ta zirga-zirga shiko jaririn sai kuka yakeyi da k'arfi,
ganin haka ta tashi a firgice al'wala taje ta kumayi sannan tazo ta kumayi Addu'a sannan ta sake kwanciyar bayan kamar minti 30 bacci ya sake d'auke ta,
still cikin baccin ta sake ganin Hamma Umar zaune cikin jarirai sai kuka sukayi da k'arfi duk sun cika gidan da kuka,
a hankali ta rink'a ganin jariran sun dawo gareta sunata kuka shima Hamma Umar ya koma gefen su yana kallon jariran yana zubda k'ollah,
haka ta sake farkawa a firgice,
Toh fa haka Ummul take rayuwa ba bacci data rumtse idanun ta sai taga ana binta da jarirai suna kuka har abin ya fara zame mata ko a gyegyed'i takeyi sai tayi tajin kukan jarirai ga hannun ta kuma yamma nayi yake fara ciwo ta kuma k'i ta gayawa kowa Hamma Umar kuwa ko sabgarta ya dena shiga ,
sai ya kwana nafilfilin shi yana mai rok'on Allah ya azurtashi da haihuwa kullum Addu'ar sa Allah yasa Ummul ta samu ciki dan yana son haihuwa tare da ita
sai azumi da yake yawan yi dan ya rege k'arfin sha'awarsa tunda yasan ba kulawar Ummul zai samuba,
itako Ummul zuwa yanzu har tsoro take dere yayi da zaran yamma tayi bata da sauran kwanciyar hankali.
Yau juma'a tun safe Hamma Umar yake d'akin shi yana ta karatun qura'an har zuwa 12 sannan yayi wonka ya shirya sab cikin fararen tufafi sai k'amshin turaren shi na du'a'ul jannah yake yi sannan ya fito hannun shi rik'e da sallaya a parlour ya samu Ummul zaune cikin yanayin bacci dan yau koda safen da zaran ta rufe ido sai taga ana mik'o mata jarirai gaba d'aya baccin sai yasa mata ciwon kai ga hannun ta da takeji kamar ba nataba gashi dai ba kumbura yayi ba amman jin hannun take kamar dutsi,
tana ganin shi ta matso gaban shi cikin yin mik'a ido a lumshe tace,
"Hamma Umar a bani maganin bacci mana".
bai kalleta ba bai kuma yi magana ba har yaje bakin k'afa sannan yace,
" sabida me? zan baki maganin bacci?"
"Bana samun bacci ne shiyasa".
" baki da lafiya ne?"
"A a ni lafiya ta lau".
Juyawa yayi ya d'an kalleta sannan ya girgiza kai ya fice,
koda akayi sallan juma'a potaskum ya nufa kai tsaye gidan Inna ya nufa ranar ko lek'a gidan Abba baiyi ba dan tunda Usman ya tafi baya son zuwa gidan sosai,
yana zuwa ya wuni da Ammin su sunata hira ya kira Usman d'in ma a woya sun dad'e suna hira,
shine bai nufi hanyar damaturu ba sai bayan sallan ishah sannan ya kama hanyar,
ita kuwa Ummul gaba d'aya ta birkice bacci na shirin zautar da ita sai zirga-zirga takeyi da zaran ta konta in tayi baccin minti 30 dai toh sai mafarkin jarirai,
shi kuwa Hamma Umar yana isowa kai tsaye bedroom d'in shi kawai ya nufa,
wonka yayi sannan ya konta rik'e da woyar shi yana magana da Ammin shi yana shaida mata ya isa lafiya,
ita kuwa Ummul a hankali ta samu baccin ya saceta,
bacci mai nauyi cikin nisan baccin ta fara juyo kukan jarirai ba adadi kukan sai k'ara matsota yake har taga jariran sun cika kan gadon nata sai kuma taga hannu wani mutun ya yarfa mata mari sannan ya nuna mata wani fili mai kyau inda ta haggo Hamma Umar yana zaune rik'e da jariri yana ta kallon ta yana murmushi tana cikin mamaki ina Hamma Umar a samo yaron nan sai taji an kuma yarfa mata marin tare da buga mata tsawa,
" tashi kije ki karb'i d'an ki".
A firgice ta farka da jin marin tayi kamar a zahiri,
lokaci d'aya wani irin tsoro ya rufeta gaba d'aya jikinta sai zufa ke tsatstsafo mata hannun ta kuwa sai rawa yake kar-kar,
sai kuma taji kukan kululluka a saman d'akin ta,
haka yasa ta mik'e cikin tsananin tsoro da gudu ta fito parlour sai kuma ta nufi bedroom d'in Hamma Umar d'in tana shiga ta ganshi zaune kan sallaya hannun shi rik'e da qura'an da gudu taje ta fad'a jikin shi gaba d'aya jikin ta sai tsuma yakeyi hannun tasa ta ruggume shi da k'arfi kanta take ta cusawa cikin k'irjin shi tana to she kunnen ta,
da sauri ya kalleta cikin mamaki ganin yadda take boye kanta a jikin shi yasa shima ya k'ara ruggume ta sannan ya rufe qura'an d'in ya ajiye kan mirror ,
ita kuwa Ummul sai kuka takeyi cikin tsananin jin tsoro,
kanta ya d'ago a hankali yace,
"Ummul meke faruwa ne?"
baki na rawa tace,
"Hamma tsoro nake ji Hamma kullum bana bacci mafarkin jarirai nakeyi suna kuka suna hanani bacci".
Jawota jikin shi yayi ya kara ruggume ta cikin mamaki yace,
" jarirai kuma? toh banda abin ki Khairi kukan jarirai kuma me abin tsoro a ciki?".
K'ara mak'aleshi tayi tana, kuka tace,
"Suna da yawafa kuma yau har dukana akeyi".
ruggume ta yayi ya mik'e da ita kan gado ya kontar da ita sannan ya konta gefen ta ya ruggume ta yana shafa kanta cikin sanyi yace,
" kiyi shiru kibar kukan ba komai kinji ko".
Ido ta rumtse sai kuma ta mik'e da sauri ganin wani hannun yana sa wuk'a kan damtsen hanunta dai-dai inda akasa mata robar ,
hannun ta rink'a turawa Hamman tana kuka tana,
"Hamma ka cire min Hamma zasu yanke min hannun Hamma ka cire min".
Cikin mamaki ya kamo hannun yana duddubawa tare da cewa,
" Zasu yanke miki hannun kuma? me a hannun naki?"
shiru yayi dai-dai lokacin da yatsun shi suka sauk'a kan inda akasa mata robar,
d'ago hannun nata yayi da kyau ya duba wurin cikin rawan baki yace,
"Family planning kikayi ne?"
kai ta gyada mai cikin zafin da taji hannun yana mata,
tureta yayi da karfi lokaci d'aya idanu shi sukayi jazir gaba d'aya jikin shi sai rawa yakeyi murya a hargitse yace,
" fita min a d'aki ki koma can d'akin ki kisan hujjar da zaki gayawa ubangijinmu kisan yadda zakiyi da jariran dake binki suna kuka ki gaya musu dalilinki na hanasu zuwa duniya Ummul kiji tsoron Allah ki tuba ki koma gareshi tun lokaci bai k'ure mini ba".
sai kuma ya kamo hannun ya matse da k'arfi har saida tayi k'ara mai cike da gigita,
tureta ya kumayi sannan yace,
"Idan Allah yace ehh toh fa ke Ummul baki isa ki ce a,a ba ki sani idan Allah ya k'addara sai kin haihu dani wallahi wannan robar bata isa ta hana cikina shiga jikin kiba".
ita kam Umml sai zare ido take tana kuka,
gaba d'aya tsoron shi ya rufeta,
shi kuma murmurshin takaici yati wanda yafi kuka ciwo sannan ya nunata da yatsa yace,
" kina so kija da yin rabbi toh gashi kinga ishara tun ba'aje ko inaba kinga duk abunda kikeyi koni ban saniba Allah ya sani,
wallahi ki shirya me zaki cewa Abba da Adam da Sadik kome zasuyi miki bazan hanaba kuma zan gaya musu abinda kikayi zan kuma kaiki gabansu in sunga damage su tsireki ki kuma je ki samu mahaliccin mu tunda bakya tsoron Allah".
kuka ta kamayi sosai tana,
"Wayyo Allah na dan Allah Hamma ka rufa min asiri wallahi ya Adam zai kusan kasheni gashi ya Usman baya nan ba wanda zai ceceni kayi hak'uri wallahi bazan sake ba ya Sadik zai karyani Abbana zaiyi fushi dani Hamma wallahi bazan sake ba".
Cikin tsawa yace,
" ki dai ji tsoron Allah,
kuma ki shirya da sassafe zamu tafi abunki ya fara bani tsoro na lura baki da tausayi".
yana kaiwa nan ya fita ya bar mata d'akin,
binshi tayi a baya tana ta magiya da tuba,
bai kulataba ya wuce d'aya d'akin ita kuwa a parlour ta kwana tana magiya bata kuma samu ta rumtsa ba.
Washe gari bayan ya dawo masallaci yana shiga parlour tabi bayan shi murya a disashe tace,
"Ayyah Hamma na dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sakeba kaji na rantse dan Allah karka gayawa ya Adam".
bai kulata ba ya fara shiri ,
ganin haka ta lallab'a ta d'auki woyarshi ya Usman ta kira,
yana d'agawa cikin sanyin murya yace,
" Hamma na ina sonka yauma nayi mafarkin ka nayi kewarku zan dawo".
Cikin sanyi tace,
"Ya Usman dan Allah ka bawa Hamma Umar hak'uri karya kaini gida kasan ya Adam mugune zai karyani".
Hannun shi yasa ya dafe k'ahon zuciyar shi dake harbawa cikin sanyi yace,
" Allah ya d'aiyiba min k'anwata, me kikayi wa Hamma na har yasashi fushi yace zai hadaki da Adam Boss?"
Cikin sakarcin ta gayawa Usman abin da tayin,
tanayi tana kuka,
shi kuwa Hamma Umar ido ya zuba mata cikin tsananin bak'in ciki,
shi kuwa Usman gaba d'aya ranshi ya baci bai tab'a jin haushin Ummul ba akan batun auren su irin na yau rai a b'ace yaja dogon tsaki cikin fad'a yace,
"Ummul ki sani in kin cutar da Hamma Umar toh kin cutar da zuciyata duk duniya bani da kamarshi amman kike gaya min bakya sonshi bazaki haihu da shiba Ummul d'an uwana kikeyi wa haka,
bazan hanashi ba bazan bashi hak'uri ba ya kaiki duk inda zai kaiki kuma kiji a bakina,
nida kaina zan gayawa Adam da Abba".
jin haka saita kuma fashewa da kuka ta mik'awa Hamma Umar d'in woyar baki na rawa tace,
" Dan Allah Hamma Umar ka bawa ya Usman hak'uri dan Allah karku gayawa ya Adam".
Woyar ya karb'a cikin k'aunar juna suka fara magana,
Usman ne ya d'an yi shiru sana yace,
"Hamma yanzu forko dai ka cire mata robar daga nan kuma kayi abinda ya dace da ita".
A hakali yace,
" Me zan iya yiwa Ummul,
Usman duk hukunci da zanyi yunk'urin d'auka a kanta zai kasance na gaza rik'e al'k'awari da amanar dana d'auka".
shiru Usman yayi sannan yace,
"Toh ni zan gayawa Adam dan ajamata kunne".
yana kaiwa nan ya katse kiran,
shi kuwa Hamma Umar mik'ewa yayi ya yawo hannun Ummul d'in kai tsaye harabar gidan ya fita da ita, cikin mota ya sata,
sannan shima ya shiga yana shiga ya figi mortar kai tsaye ya kama hanyar potaskum,
tana ganin haka cikin tsoro ta kwanta kan.......
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2⃣2⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Ina kike ne Nana Fa'ad wannan shafi naki ne ke kad'ai ban had'a ki da kowaba gaba d'ayansa nasa d'aukar da shafin nan a gareni har kullum ke ta daban ce ina al'fahari dake🤝😍😘*
*Sisters kuyi hak'uri kwana biyu kun jini shiru banji dadine sosai Amman insha Allah zanke lallab'awa na rink'a yi mana typing ko kad'an -kad'an ne*
*T*ana ganin haka cikin tsoro ta kwanta kan cinyar shi ta kifa kanta a jikin shi hannun ta zagaye kan kugunsa tana "Wlh bazan k'araba kayi hak'uri karka kaini gun Abba wallhi Ya Adam zai karya ni". cusa kanta tayi a k'irjin sa tana wani irin kuka tana cewa "Ayyah Hamma Umar dan Allah kayi min rai wallahi nayi alk'awari bazan sake ba, kaji kaina karka kaini gurin su Abba bana son fushin sa kuma Ya Adam zai dake ni" tana mai k'ara narkewa a jikin sa, shi kuma Hamma Umar wani kasala yaji tareda mugun tausayin ta amma haka ya b'ata rai yak'ara murtuke fuska yana driving koh kulata baiyi ba, ganin hakan hankalin ta ya k'ara mugun tashi ta k'ara narkewa a jikin sa sai wani shege masa take ta ta cusa hannun ta cikin suman kansa tana mai masa sosa cikin kissa tana mai had'a sajen sa da fuskan ta tana wani iri kuka had'e da shagwab'a tana cewa "Wallahi Allah Hamma Umar ka yarda dani nayi al'kwari bazan sake ba, idan na k'ara without any second thought ka kai k'arana na yarda amma yanzu dan Allah kayi hak'uri ka yafe mini Insha Allah bazan sake ba" tana mai masa sosa kamar tafiyan tsutsa a hankali cikin sumar kansa, ganin tana neman rikita masa brain muddin tacigaba bazai ma iya tukin ba nan take yayi reverse da motar ya juya ya kama hanyan komawa damaturu, ganin haka ta sauke naunauyar ajiyan zuciya tareda hamdala cikin ranta tace "Nagode Hamma Umar Inshaa Allah bazan kara ba" shi kuwa koh kulata baiyi ba yacigaba da driving nasa ita kuma ta gyara zaman ta a seat tareda lumshe idanuwan ta.
Direct general Hospital dake cikin damaturu ya kaita. bayan yayi parking motar sa a parking lot ya kalleta yace " sai ki fito mu shiga ai", ba tareda ta musan tashiba ta gyara hijabin ta, mik'a mata farar hankerchief yayi wanda yake fitar da wani k'amshi mai dad'in gaske yace "Haka zaki fita salon a ganeh kinyi kuka koh? Maza karb'a ki goge fuskan ki" ba musu ta karb'a hankerchief d'in ta goge fuskan ta,bayan ta kimsa yace "Toh muje koh" ba musu ta sauk'o a motar suka jera suna tafiya abun sha'awa har office na abokin shi Doctor Nasir Fuskan tausayi tayi tana kallon shi tace
"Ayyah Hamma Umar fallasa ni kake sonyi? Salon abokin ka yasan abunda na aikata?". Hararar ta yayi ya bud'e office yashiga ita kuma tabisa a baya. Sosai Doctor Nasir ya amshe su yana mai zolayar abokin sa ango, bayan sun gama gaisawa Hamma Umar yace "Yawwa ina wancan Doctor'n take neh?" Cikin rashin fahimta Doctor Nasir yace,
"Wacce kenan?"
"Doctor Rukayya"
"Ohh tana nan bari na kirata tazo tayi assisting naku"
Ciro wayan sa yayi ya kirata tazo, dagan nan ya had'a su.
Bayan an had'a ta da Doctor'n tayi mata fad'a sosai tareda mata wa'azi tace "D'an adam kenan, wasu har kuka suke. Wallahi jiya wata mata da tazo shekarunta arba'in da biyar kuma tun tana shekaru goma sha tara tayi aure, bata tab'a family planning bata tab'a koh da b'ari ba. Jiya da tazo ta same ni sanda na zubda hawaye, kuka take sosai tana masifan son haihuwa kuma Allah bai bata ba, amma ke sai k'okari toshe ni'iman Allah kike bayan mijin ki naso, gaskia kin bani kunya kin ban haushi" Haka ta ta mata masifa har ta cire roban tareda bata wasu magani.
Bayan sun gama taje ta samu Hamma Umar a cikin motar sa yana zaune already daman sunyi waya ta same shi a cikin mota. Yana ganin ta da Doctor'n ya fita a motar sa ya mata godiya sosai tana mai k'ara basa hak'uri irin halin 'yan matan yanzu. daga nan ya shige motar sa daman tuni har Ummul ta shige ta kwanta a kan kujera tareda lumshe idanuwan ta,wani irin ciwon kai take ji dalilin kukan da tasha, tsantsan tausayin ta yaji ya shafa laulausar fuskan ta yace "Sannu kin gaji koh?" D'aga masa kai tayi ba tareda ta basa amsa ba, restaurant ya wuce ya musu odering abinci a take away yazo ya zuba su a seat na baya ya sake tsayawa ya siyo musu icecream dayawa daga nan ya kama hanyan gida.
Suna isa Ummul direct d'akin ta tashige shi kuma ya kwasa kayakin da ya siya ya shigar dasu, icecream d'in ya zuba su a fridge ya ajiye abincin dinning shima ya shige d'akin sa dan wanka.
Bayan ya fito ya saka jallabiyar sa ya fesa jikin sa da turaruka masu k'amshi gaske yaje d'akin Ummul, yana shiga ya ganta a kwance akan gado but da gani alama tayi wanka dan ta canza kaya, zama yayi a gefen ta yana mai shafan fuskan ta yace
"Ummul taso muje muci abinci tun safe fa ba abun da kika ci sai d'azu da kika sha coke a asibiti", ita kanta tasan tana jin yunwan haka ta taso a daddafe tace "Toh muje". Tasowa yayi shima ya kama kugunta suka fara tafiya har dinning, ya jawo mata kujera ta zauna, haka yayi serving mata abinci taci ta koshi,daga nan yace "Ummul bari naje masallaci kinji kinga yanzu za'a kira magrib bayan sallah'n isha zan shigo". d'aga masa kai tayi tace
"Toh sai ka dawo". Ganin yanayin da tayi magana da k'yar ya matso kusa da ita yace
"Lafiya kuwa Ummul? meke damunki?", wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta tace "Hamma Umar ciwon kai", kallon ta yake da tausayi fal kwance kan fuskan sa yace "Kinga illan yawan kuka koh? maza tashi ki shiga d'akin ki na kawo miki magani kisha"
Haka ta taso yana rik'e da ita har d'akin ta ya zaunar da ita kan bakin gado, ya shige d'akin sa ya d'auko magani ya had'o da faro ya mik'a mata, duk yadda yakai da batason magani ganin yadda ya tsareta da kallo ba yadda ta iya haka ta amsa maganin tasha,
daga nan ya wuce masallaci itama ta tashi tayi sallah a daddafe, ita bata tashi akan daddumar sallah'n ba har sanda aka kira sallar isha'i tayi, a yanzu dai ta d'an ji saukin ciwon kai d'in. Shiga toilet tayi tayi brush tabi lafiyan gado sabida tana wani irin jin bacci, cikin minti biyu bacci b'arawo ya d'auke ta.
Shima kuma Hamma Umar ana idar da sallah'n isha ya dawo gida, d'akin ta ya shiga ganin tana bacci ya k'aro rufe kofar yazo shi parlour ya had'a tea yana kallon news, shine bai tashi a gaban TV ba sai kusan k'arfe goma,
shiga d'aki yayi ya watsa ruwa ya canza kaya zuwa pyjamas da singilet tareda shafa turaren sa mai dad'in gaske du'u'rul jannah, zuwa d'akin Ummul yayi ganin tana baccin ta hankali kwance ya gyara mata blanket nata ya mata addu'a ya tofa mata had'e da mata peck a goshin ta ya fita ya ja mata kofar d'akin.
Kwanciya yayi akan gadon sa yayi addu'a, wani irin yanayi yafara ji yana zuwa masa ganin surar Ummul da yagani yanzu, yaso ya kau da tuninin amma hakan yaci tura, ganin bazai iya bacci ba ya taso ya