Showing 96001 words to 99000 words out of 134562 words

Chapter 33 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

aiwatar da abinda ya dace tunda dama ita Ummu tak'i kowa kuma inaga shak'uwarsu da Usman zatayi tasiri wurin sa ta amince dashi".
Ita love Hajjajo sunkuyar da kai tayi tana b'oye k'ollar data fito mata wadda ta fito da manufofi biyu tace, "namuku izini,
kuyi duk abinda ya dace,
Allah yai muku albarka yasa k'udirin mu yazamo alkhairi amman a nemi yardar Ummu dan yanzu ita ba budurwa bace ku bata dama tayi zab'in da ranta keso gudun kar a maimaita abinda ya faru a baya".
had'a baki sukai suka amsa da, "Amin".
sannan Daddy ya kuma gyara zama tare da cewa,
"Insha Allah baza a maimaita abinda ya faru a baya ba dan tabbas munga illar auren dole da illar auren cushe duk da muna da damar da zamuyi mata zab'i kuma mun mata amman zuciyarta bata soba gashi sai a k'arshe rayuwar ta katse mana cikin nadama ita kuwa sanin din kafiyarta ta d'auke farin cikin rayuwar".
cikin sanyi Hajjajo tace,
"Allah ya tsare na gama".
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa a tare, Matsowa Abba ya sakeyi kusa da d'an uwan shi yace,
"Hussain ina nemawa yarona Usman auren yarinyarka Ummulkhair". Hannunshi Daddy ya rik'o cikin jin dad'in yadda d'an uwan nashi kemai kara akan yaransu yace,
"Nabaku nabaku Ummulkhair bisa amana da k'auna Allah yasa ayi cikin sa'a kuma Allah ya sanya alkhairinsa".
Hajjajo da Abba suka amsa da, "Ameen".

Haka sukai ta tattauna yanda zasu tsara,
daga k'arshe Abba ya d'auko wayar shi ya latsa yasa a kunnen shi,
Usman dake zaune kan sallaya yaji wayarshi na k'ara yamik'a hannu Adam dake kan gado kwance yasa hannu yad'au wayar ya mik'amai dasauri Usman ya amsa kiran yasa a kunne ya russuna kamar yana ganin me kiran yace, "Assalamu alaika,
Abba ina kwana?". Adam dajin Usman yace Abba ya mik'e daga kwanciyar da yake ya zauna tsakiyar gadon ya zubawa Usman ido wanda ya saurara yana jin abinda Abban ke fad'a yana jiran karin bayani,
"To". Usman yace sannan ya sauke wayar ya kalli Adam yace, "Abba na kiranmu a palour Hajjajo".
daga haka ya tashi ya ajiye wayar yafice,
cikin happy yayi d'an k'ara tare da cewa,
"yes". sannan ya sakko daga gadon yafita cikin zumud'i da addu ar Allah yasa abinda yake zato ne.

A palour Hajjajo Usman yayi sallama suka amsamai yasami k'asa gefen Abba ya zauna sannan Adam ma ya shigo yasami gefen Daddy ya zauna,Usman ne yafara gaida Hajjajo sannan yakuma gaida iyayen nashi sannan Adam ma yayi tashi gaisuwar sai kuma suka saurara cikin nutsuwa Abba yafara magana dacewa,
"Usman banji dad'in yadda kuka waremu kaida d'an uwanka Adam kuke b'oye damuwarku ku kad'ai ba,
duk da nayar da komai lokacine kuma ga lokacin yayi dan haka inaso ka shaida sannan d'an uwanka ya shaida kamar yadda mahaifiyata ta shaida d'an ni mahaifinka na nema maka auren y'ar d'an uwana Ummul khairi".
sanyi, dadi, fad'uwar gaba gabaki d'aya suka ziyarci zuciyar Usman da haka ya kasa jin komai da gane komai da suke fad'a,
Abbane ya dawo dashi daga duniyar daya tafi ta hanyar dafa kafad'ar shi yace,
"Allah yamaka albarka Allah ya baka ikon kula da d'an d'an uwanka". Cikin nutsuwa da kwantar da kai k'asa Usman murya a sanyaye yace,
"Daddy nagode Allah ya saka da alkhairi". sai kuma yakai dubanshi ga Adam da dad'i ya cikawa ciki yanata murmushi yace,
"Adam katayani godiya gun Abba".
Shiko Adam washe baki yayi kai kace shi akaima kyautar matar yace,
"Daddy mun gode Allah ya k'ara girma".
Usman yasake matsawa kusa da Abban yai k'asa da murya cikin biyeyya da yace,
"Abba nagode Allah ya k'ara arzik'i,
amin godiya gun Daddy".
sai kuma ya d'anyi shiru kai ya kuma sunkuyarwa a hankali yaci gaba da cewa,
"Sannan inaso in nemi wata alfarma agurin ku".
Abba ne ya sa hannu ya shafa kan Usman yace,
"a shirye muke mu samar maka da farin ciki kada ka damu ka fad'i duk abinda kake so insha Allahu zamuyi maka danko munada yak'inin bazaka nemi abinda bazamu iyaba". sauke ajiyar zuciya yayi sannan murya na rawa yace,
"Abba dan Allah kumin alfarma kubani dama in nemi yardar Ummul,
da kaina kar ayi mata dole a bari ta amince dani da kanta,
Daddy inaso inganta cikin farin ciki sannan hakan shizai bani damar k'arasa kula da ita da yarona cikin jin dad'i, ina nufin zatafi jin dad'i idan anyi komai da yardar ta".

Shirune ya ratsa palour na y'an mintina sannan Daddy yai gyaran murya tare da cewa, "Usman Allah yayi maka albarka, hak'ik'a wannan kalaman naka sunkai ayi maka uzuri kamar yadda ka buk'ata kuma hakan ya dad'a tabbatar mana da cewa kaine kad'ai zaka iya dawo mata da farin cikin ta,
Allah yamaka albarka Allah yabaka ikon kulawa da iyalinka".
"Amin". Suka amsa sannan Abba yace,
"to duk abinda zance Daddyn ku yafad'a dan haka indai babu wata maganar sai kuje kuyi abinda zakuyi,
Allah yayi muku Albarka ya jikan yayanku yakai haske kabarin shi".
duka suka amsa da, "Amin".
Daddy yace to Adam kayi mana addu'a mu tashi,
daga haka taron ya tashi kowanne zuciyar shi na cikin nishad'i.

Suna fita Adam ya kama hannun Usman yace,
"congrat bros". Murmushi yayi yace, "nagode".
Adam yasake matse hannun Usman dake rik'e a hannun shi yace, "nidai naso kabari ayi auren nan kasan yadda Ummul take balle yanzu yaza ai kace saida amincewar ta".
a hankali ya janye hannun shi ya shafa kanshi ya kalli Adam cikin lumshe ido da sauk'e sassanyar numfashi yace,
"Adam hak'ik'a inason kasancewa da Ummul ina son rayuwa da ita k'ark'ashin inuwar sure, amma kasani a yanzu soyayya hud'u nake mata, nafarko inamata so irin na ma a bota soyayya da kauna wanda Allah ne ya dasamin hakan a zuciyata,
na biyu inason Ummul soyayya ta yaya da k'anwarsa, na uku itace abinda Hammana yafiso da k'auna, sannan itace tafara haifamin d'ana jinina,
kaga wad'annan suke jana kuma suke bani tabbaci da kwarin gwiwar insha Allah zanyi nasarar samar mata farin cikin data rasa a baya".
ajiyar zuciya yayi sannan yacigaba da cewa,
"Zan jure duk wata damuwa akan haka,
nasan burinka insami farin cikine amma inaso kacigaba da tayani addu'a Allah ya sanya sona a zuciyar Ummu".
Magan ganun Usman ne suka kashe wa Adam jiki ya sa hannu ya rungumo shi suka rungumi juna suka juya zasu tafi b'angarensu Keenan,
muryar Nanne c ta tsai dasu suka juyo inda take,
ita ko cikin jin dad'in ganin su a haka tace, "y'ay'an Abba me kuka samu ne? na ganku a cikin nishad'i".
K'asa sukai suka tsuguna a tare suka ce "ina kwana".
Ammice ta amsa da, "lafiya lau". Kasancewar indai Ammi naguri Nanne bata amsa gaisuwar da za ai daga farko,
sannan suka sake gaida Nanne ta amsa cikin sakin fuska tace, "kuje abinku muma zamu gaida mai sunan Ummul ne".
Da haka suka shige sukuma suka kama hanyar b'angarensu.

Dab da zasu shigene Usman yasaki hannun Adam daya rik'o yace, "kaga jeka ni bazan iya komai ba saina dubo Noor hayati name da my son".
dariya Adam yasa harda rik'e ciki,
shiko Usman ko kallo bai ishe shiba ya juya yai tafiyar shi.

Hargowar Farouq yajiyo tun kafin ya shigo,
yana k'arasowa ya sauke idanuwan shi kan Ummul dake zaune a bakin gado rik'e da rigar Farouq a hannu ta shagwab'e fuska kamar zatai kuka,
inda take kallo shima ya kalla Farouq ne tsaye ya mak'ale kafad'a ya turo baki gaba yana zare ido, abin nasu dariya yaso bashi amma saboda gudun rigimar Ummul ya b'oye dariyar yazauna bakin gadon kusa da Ummul yace, "meya had'aku ne?". Kafin tai magana Farouq ya taho yafad'a jikin Usman yace,
"Abee imma ne".
k'ara rungume shi yayi a jikin shi yace, "Ummuna wai menene?".
Itama k'ara shagwab'e fuskar tai tace,
"tun dazu kowanne kaya na d'auko sai ya gudu yace bashi ba ni har nagaji".
Murmushi Usman yayi yana jinjina aikin gaban shi na rarrashin y'an shagwab'a biyu sannan yasa hannu yakarb'i rigar daga hannun Ummul yace,
"yaron kirki yi hakuri kasa wannan yanzu anjima kad'an sai in canja maka wasu ko?". d'aga kai yayi yace cikin gwaranci, "ambuma". hannu Usman ya mik'o ya mak'ale yatsu guda biyu yace,
"e". aiko dariya Farouq yasaka sannan yasa yatsanshi tsakanin na Abeen nashi ya raba yatsun da Usman d'in ya had'a,
sannan ya mik'a kai Usman ya sakamai rigar yajuya ya fice da gudu,
ido suka rakashi dashi sannan Ummul tasuke ajiyar zuciya tai k'asa da kai tace,
"Ina kwana".
Ido ya zuba mata na tsahon 20 second sannan yace,
" waya ce maki a haka ake gaida masoyi?".
d'an turo baki tayi ta turo lips d'inta gaba ta mik'e zata fice daga d'akin,
cikin zafin nama ya rik'o hannunta abinda yajine ya ratsa dukkan sassan jikin shi yasa yayi saurin sakin hannun nata itako tacigaba da tafiya,
ganin hakan ya dafe kirjin shi da hannun shi d'aya yace,
"washh". da sauri ta juyo ta dawo kusa dashi ta zauna tad'ora hannunta akan nashi tai rau-rau da idanu kamar zatai kuka tace, Ya Usman meke damunka? k'irjin ko? ". zame hannun ta yayi daga nashi yace,
"so, soyayyarki ce take damuna Ummul soyeyyar kice take son min illah a zuciyata da jikina". Yanda ya kafeta da idanuwan shi masu zuba kasala yasa tai k'asa dakai ta marai raice fuska cikin sanyin murya tace,
" dan Allah kadena min haka kaga kaban tsoro nazaci ciwo kakeji". murmushi yayi cikin jin dad'i tare dayi mata wani solon kallo mai cike da k'auna sannan yace, "Ummuna bakyaso inji ciwon ne?".
Dakai ta amsamai alamar "eh".
sannan ta tashi zata fice,
da sauri ya taso yasha gaban ta ita kuwa ta rink'ayin baya-baya har ta isa jikin gini,
ido ya tsura mata cikin laso lips enshi murya can k'asa yace,
"Ina sonki so mai tarin yawa ina son rayuwa dake da Farouk na wuri d'aya ki kijik'ana ki tausayawa tuzurun yayanki Ummul na gaji da zama ba mata na matsu da yin aure ki tausayi min nida Farouq kar muyi maraici biyu ba Hamma na kema kuma kiyi nesa damu baza muji dad'in rayuwa ba".
k'ara matsowa kusa da ita yayi cikin yin k'asa da murya yace,
"Ummuna ina son aure wallahi na fa gaji da zaman gidan ina son mace kusa dani hak'uri na ya fara gazawa kiyi hak'uri ki yarda dani ki bani dama zan dawo miki da farin cikin ki kinji Ummuna".
rab'awa tayi gefen shi cikin jin tsananin kunya da tsoron ya Usman d'in dan ta lura baida sauk'i ficewa tayi ta barshi a d'akin,
shiko murmushi yayi yamik'e yafice.

A ranar bayan ya tashi daga aiki,
kai tsaye ya wuce Ahlul bhait communication ya seyowa Ummul d'inshi waya k'irar Iphone 6,
sannan ya nufi gida yanajin farin ciki sosai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login