Showing 45001 words to 48000 words out of 134562 words
Chapter 16 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa
ba ko nasha maganin shi maganin abinda ya samu yake tayiwa in ya samu sauk'i sai ya k'ara sauk'i in ya samu ajali kuwa tofa ajalin yake tayiwa dan Allah Abba Hamma Umar ku maida ni gida bana son zuwa asibiti nan."
Haka dole ba d'an suna soba suka koma cikin gida dashi,
shi kuwa Umar Ummul ya ruggume sannan yabi bayan Abba dake tallabe da Usman,
kai tsaye part d'in Hajjajo suka nufa a parlour suka zauna kan 3 str Abba ya kwantar da Usman shi kuwa Umar ya kwantar da Ummul kan 2 str ,
ya Adam kuwa dama tuni ya fita ya d'auko doctor dake duba Usman d'in.
Bayan yazo ya duba shin yayi duk binciken da zaiyi ya gama sannan ya kalli Usman d'in dake konce a rigingine ya lumshe ido hawaye na bin fuskar shi sannan ya juyo ya kalli Hamma Umar dake zaune ya zuba mishi ido yana rik'e da hannun shi sannan ya kalli Abba dake k'ok'arin gyara wa Usman d'in konciya cikin kula doctor Ibrahim yayi ajiyan zuciya sannan yace.
"Alhaji Hassan ko kuna lura da Usman sannan kunsan meke damun shi akwai matsalar da yake boyewa a zuciyar shi sannan kuma yasan zuciyar shi bazata iya d'aukar nauyin ba Usman akwai abin da yake matukar so bai samu ba,
domin na duba na'urar dake cikin k'irjin shi tana zaune yadda ake so tana kuma taimakawa kamar yadda ta saba tana kuma harbawa jinin dai-dai misali kuma zataci gaba da aikin har nan gaba shekara 1 a lokacin zai cika shekara biyar da sata sannan za'a koma a canzata kamar yadda aka saba,
yanzu wata matsalar ce ta daban kuwa ke damun Usman kuma zata iya jawo komai a rayuwar shi."
yana rufe bak'in shi Usman ya bud'e idanun shi cikin salon sa na abin dariya ya fara magana cikin dariya da son badda matsalar tasa yace.
"Uhummm wai ina son wani abu,
toh niko mai zanso wanda Abba da Hamma Umar basu samamin shiba ni ba abin da nake so."
Ido Nenne ta tsura mishi cikin tsananin tunani lokaci d'aya kuma ta fara tuno wani abin,
Hajjajo kuwa ba abinda takeyi sai kuka,
shi kuwa Hamma Umar ido ya tsurawa d'an uwan nashi cikin sanyi yace.
"Me yake saka tarin da a man jini?."
murmushi yayi tare da d'an shafa sajen shi yace.
"You naga Anyi tayin maganin asibiti ba canji shine jiya naje na karb'o na wmzamai shine na jik'a nasha ,
sai gashi yana k'ok'arin fecewa dani barzaq."
Murmushi ya kuma yi sannan yace.
"Amman fa gsky naji sauk'i dana amayar da jinin."
haka ya rink'a shashantar da abin shi kuwa doctor Ibrahim ya tabbar akwai matsala tare dashi.
su ya Adam kuwa sun d'an samu nitsuwa ganin Usman d'in ya mik'e,
Hamma Umar kuwa har yanzu zuciyar shi na cike da fargaba,
Abba kuwa bayan doctor Ibrahim yabi suka fita tare yana k'ara mishi bayani,
bayan su Abban sun fita ne Hamma Umar ya d'an juyo kusa da Ummul tafin k'afafun ta ya kamo yasa hannun shi ya rink'a murzawa yana jan yatsun k'afafun nata tare da kiranta.
"Ummul ! Ummuuul !."
sai kuma ya dawo ta kanta hannun shi yasa ta k'asan wuyanta yana d'an murzawa,
nanma shiru sai ya manna hancin shi da nata sannan ya rufe bakinta da nashi,
cikin lumshe ido ya rink'a fesa mata numfashin sa sannan yana zuk'o numfashin ta bak'in ta gaba d'aya nashi numfashin ya rink'a fesa mata cikin sa'a tafizgo numfashin sannan a razane ta kamo wuyan shi baki ta bud'e da nufin zata sake k'ara,
sai yayi maza ya rufe mata bak'in da tafin hannun shi,
haka yasa ta bud'e idanun ta sannan ta rink'a kallon su d'aya bayan d'aya,
zame bakin ta tayi cikin sanyin muryar tace.
"Ya Usman ! ya Usman ."
ido ya d'an rumtse sannan yace.
"Na'am Ummul ."
jin muryar shi ta mik'e da sauri taku d'aya tayi ana biyun ta koma ta zauna ido na zubda k'ollah dan azaban ciwon da raunin jikinta ke mata,
cikin sauk'e ajiyan zuciya Hajjajo tace.
"Ke kuma meya sumar dake? sannan yanzu tafiya ma na gagararki."
batayi magana ba sai kawai ta kama kuka,
ganin haka Nenne tace.
"Toh sarkin kuka ya isa haka taso mu tafi kiyi wonka sai kici abinci kiyi bacci."
mik'e wa tayi cikin zubda k'ollah tafiya ta farayi cikin d'ingisa k'afafun ta tana d'an waresu tare da cije lips d'in ta,
ganin haka tuni Nenne tayi gaba dan ta gano matsalar yartata itama Hajjajo shiru kawai tayi dan ta fahimci matsalar,
shi kuwa Hamma Umar kanshi ya sunkuyar cikin tarin kunya da tausayin Ummul d'in sai hawaye yaji yana bin hab'arsa dan gani yake kamar ya gwada mata rashin tausayi tunda yasan yarinya ce,
kunya yakeji ta rufeshi kamar k'asa ta tsage ya shiga,
ganin hakan yasa su ya Adam duk suka zame suka fita itama Hajjajo kitchen d'inta ta shiga ta fara had'a wa Ummul had'in su na tsoffin shuwa'arab sannan tayiwa Usman d'in ma had'in shi na musamman ta kuma dafawa Usman abincin da zaici da kanta.
A part d'in Nenne kuwa suna shiga kai tsaye bedroom suka wuce kan gado Ummul ta konta ta kife kanta tana kuka,
ita kuwa Nenne toilet ta shige ruwan d'umi ta had'a mata mai k'unshe da sinadarai na gyaran jiki sannan ta had'a mata wani juk'o na musamman a cikin buta,
tana fitowa taje kusa da ita cikin kulawa da tausayawa irin ta uwa da yarta ta kamo hannun ta ta zaunar da ita kafad'an ta ta dafa a hankali tace.
"Ummul Allah ya miki albarka kiyi hak'uri mamana ki d'aure kinji ko ki denan kukan nan ya isa yanzu kin girma ya kamata kiyiwa kanki fad'a tashi kije kiyi wonka ki zauna cikin ruwan d'umin sannan kiyi amfani da ruwan butar nan."
kukan ta kumayi cikin shogwob'a dan ganin Nennen ta na lallashin ta,
da kukan ta shiga tayi wonkan sannan ta k'asa kanta lokaci d'aya taji jikinta duk ya wore,
tana fitowa ta samu Nennen ta jona borner a ajikin wuta tana fitowa ta zuba mata wasu turaruka masu tsananin k'amshi sannan ta kalleta cikin kulawa tace,
zoki tsuguna kiyi hayak'i da wannan."
"toh " tace sannan ta matso gaban borner ita kuwa Nenne ta fita parlour,
tsuguna wa tayi a kanshi hayak'in na shiga jikin ta wani irin k'amshi na ratsata,
tana mik'e wa ta Jita garau hakan yasa ta kimtsa sannan ta koma bak'in gadon ta konta cikin jin wani irin baccin gajiya,
Tana konciya Nenne na shigo wa had'in kaza ta karb'a mata wanda Hajjajo tayi mata sai ruwan tsumi mai dad'in sha,
ajiye wa Nenne tayi sannan tace.
"Taso kici abinci saiki kontan."
ba musu ta sauk'o taci tasha dan tana jin yunwa,
kuma yau tana jin dad'in yadda Nennen ta ke kula da ita wanda tunda ta nuna bata son Umar Nenne ta dena kulata sai yau d'in,
tana gamawa ta koma ta konta tana kallon Nenne dake shirin shiga wonka cikin sanyi tace.
"Nenne zazzab'i nake ji da ciwon kai."
ba tare da ta kalleta ba tace.
"Toh bari in gayawa Umar d'in yazo ya dubaki."
fuska ta tsuke dan bata son abinda zai had'a ta dashi inuwa d'aya kuma gashi ta jawa kanta,
bayan Nenne tayi wonkan ne ta shirya ta nufi d'akin Abba a tsakar gidan ta kalli Aliyu yana shirin shiga part d'in Hajjajo kiran shi tayi sannan tace.
"Jeka kira Hamma Umar d'in ku kace Ummul bata da lafiya yaje ya dubata."
"Toh" yace sannan ya nufi parlour Hajjajo yana zuwa ya samu Hamma Umar d'in yana zaune gefen Usman yana b'are mishi lemu,
gefen shi ya zauna a hankali yace.
"Hamma Anty Ummul bata da lafiya Nenne tace kaje ka dubata."
kai ya gyad'a sannan yaci gaba da bawa Usman d'in kulawa,
bayan ya gama bashi abinci ya bashi maganin sannan suka tafi part d'in su suna zuwa ya had'a mishi ruwan wonka,
har cikin bathroom d'in ya rekashi kamar zaiyi mishi wonkan,
murmushi Usman yayi tare da cewa.
"Hamma yau wonkan ma zaka min ne?."
"Kanaga ka girma ko?."
kai ya sosa sannan yace.
"Gaskiya dai Hamma na girma mai min wonka zai iya makancewa."
K'eyan shi ya d'an buga sannan ya fita,
shi kuma Usman wonkan yakeyi yana zubda k'ollah cikin tausayawa kanshi da d'an uwan nashi,
bayan ya fito Hamma Umar ya shirya shi sannan ya kontar dashi kan gado ya zauna gefen shi yana shafa kanshi cikin sanyi yace.
"Ammmi ta kiraka kana wonka nace mata kace min yanzu ka girma."
ido ya lumshe yana jin dad'in yadda d'an uwan nashi ke kula dashi k'aunar shi na ratsa mai zuciya,
ido ya lumshe cikin jin bacci yace.
"Hamma ?."
"Na'am Usman d'an uwana."
kai ya jinji na sannan yace.
"Ina sonka d'an uwana."
kanshi ya rink'a shafawa yana cewa.
"Usman duk duniya bani da tamkar ka ina sonka k'anina bani da buri a duniya daya wuce inga ka samu lafiya fatana a koda yaushe in ganka cikin farin ciki."
ruggume juna sukayi sannan a hankali Umar ya kontar dashi sannan ya rink'a yi mishi karatu qura'ani a cikin kunnen shi murya cike da rauni,
lokaci d'aya bacci ya tafi da Usman d'in,
shi kuwa Hama Umar a hankali ya gyara mishi konciya sannan ya fito kai tsaye harabar gidan ya koma motar shi ya bud'e ya d'auki magungunan Ummul sannan ya nufi part d'in Nenne,
yana shiga parlour ya samu ba kowa sai kuma yaji muryan Ummul dake magana da Anty Halima da woyar Nenne,
cikin yin sallama ya shiga yana shiga ya zauna gefen Ummul d'in sannan yasa hannu ya karb'i woyar ya katse kiran ,
ita kuwa a fusashe ta juyo gare shi a nufin yin tsiwa,
sai kuma tayi shiru jin yadda ya jawota jikin shi ya ruggume ta tsam a jikin shi sai sauk'e ajiyan zuciya yakeyi murya can k'asa yace.
"Kun bani tsoro keda Usman in na rasaku bansan makomata ba Ummul Khairi ina tsoron abinda zai rabani daku,
In babu Usman bansan ya rayuwa zata juya min ba."
sai kuma ya k'ara matsota jikin shi d'umin jikinta na ratsa shi,
ita kuwa tureshi takeyi tana k'ok'arin matsawa,
jawota ya kumayi a hankali ya tallabo kanta kissing d'in ta yayi da kyau sannan yace.
"Kiyi hak'uri my Khairi bazan sake wahala da keba."
shiru tayi tana jin yadda yake fidda numfashin da sauri-sauri a haka har ya fara sauk'e ajiyan zuciya a hankali nitsuwarsa ta dawo jikin shi sannan ya bata maganin ya kontar da ita ya shafa fuskar ta sannan ya fita.
A haka Hamma Umar ya wuni kula da k'anin shi da matar shi da derema haka ya kwana kula da Usman yayin da kewar Ummul ke cin jikin shi da zuciyar shi,
koda gari ya waye haka ya wuni kula dasu,
kuma Alhamhadullih duk sun mik'e musamman Ummul dan shi kam Usman k'arfin haline da son kontar da hankalin Hamman nashi,
bayan Anyi salla isha ne Abba yace Hamma Umar su tafi tunda duk jikin su da sauk'i,
bayan ya fita ne ya d'auko jakar Ummul ya bawa Aliyu ya kai mata cikin gida sannan yace .
"In kaje kace tazo."
"Toh" yace sannan ya nufi cikin gidan,
a parlour Nenne ya samu su ya Adam cikin mamaki ya Sadik yace .
"Jakar nanfa daga ina.?."
"Ta Anty Ummul ce."
Ya bashi amsa ya Adam ne ya kalli Ummul d'in cikin tsuke fuska yace.
"Ba yanzu zaku tafiba?."
Kai ta juya ido cike da k'ollah tace.
"A a ni bazan komaba bani da lafiya."
A hatsale ya bugawa Aliyu tsawa .
"Maza ka meda jakar cikin motar Hamma Umar d'in ke kuma tashi kibi mijin ki ku tafi."
shi kam Aliyu tuni ya juya da jakar ita kuwa hannun ta rink'a yarfa wa tana buga k'afafun ta tare da bud'e baki da k'arfi tana.
"Ai Hamma Umar d'in ya yarda kuma bani da lafiya shike nan dan an tsaneni sai ayi ta korata a gidan mu."
Kanta yayi da sauri yana zaro bel d'in k'ugunshi,
ya Sadik kuma cewa yake.
"Yauwa zaneta tunda bata jin magana."
Ihu ta saki jin sauk'ar bel d'in a jikin ta a guje ta fita tana kuka,
bayan Hamma Umar d'in ta tsaya tana tsalle da dire-dire tare da rik'e hannun shi ,
Abba ne ya fito dan jin kukanta yana zuwa ya kalli yadda takeyi sai murmushi yayi dan a fili yarintar Ummul take ganuwa,
shi kuwa Adam tsawa yake buga mata yana.
"Ki wuce ki shiga cikin mota."
Abba ta kalla dan ko zaice ta dawo sai kuma ta shiga motar ganin yadda ya had'a fuska yana kallon ta,
shi kuwa Abba cikin bada umarni yace.
"Farouq shiga ku tafi.
"toh."
yace sannan ya shiga,
Aliyu kuwa dariya yayi tare da d'aga tafin hannun shi ya saitasu da kanshi yana kad'a hannun tare da zaro harshen yana kad'awa Ummul cikin tsokana yace.
"Bana gaya mikiba yanzu ke ba y'ar gida nan bane yanzu dagani sai Nenne na."
ya k'arishe maganar yana rawa,
Usman ne ya d'an roggoshi keyarshi yace.
"Aliyu wato kaine d'an tada zaune tsaye ko."
ita kuwa kuka tasa tana cewa.
"Ya Usman ba kaga Aliyu ba."
Murmushi yayi yace.
"Muna sonki Ummul d'in mu ke y'ar gidan nance har Abadan."
K'ollah ta zubda tare da cewa.
"ya Usman kai kad'ai kake sona, nima ina sonka."
Ido ya lumshe sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
murmushi sukayi dukan su,
shi kuwa Hamma Umar hannun Usman ya jawo ya d'an sunkuyo kanshi a hankali yace.
"Ka kula da kanka d'an uwana ina son ka ina tsoron abinda zai cutar da kai."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Nayi lafiya fa."
Haka sukayi sallama suka tafi,
Ita kuwa suna fita harabar gidan ta bud'e sabon shafin kuka,
sunyi tafiya mai d'an nisa,
Hamma Umar yana tuk'in hankalin shi na cikin tunanin halin da k'anin shi ke ciki,
kamar a mafarki yaji Ummul tasa hannunta ta d'amk'o........
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2⃣0⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*H*annun ta tasa ta damk'o siterin ta rink'a juyashi tare da murza shi da k'arfi tana.
"Allah ka tsaya ni in sauk'a ehe,
ni bazan koma gidan kaba ka sauk'e ni a nan zan tafi gidan Anty Halima."
murza kan motar take da k'arfin ta,
tuni motar ta fara yawo a tsakiyar titi ga ababen hawa dake ta gaban su da bayan su da gefe,
gaba d'aya motar kanta ya kufce,
a firgice yace.
Innalillahi Ummul kin san abinda kikeyi kuwa?."
fizge hannayen ta yayi da k'arfi cikin tashin hankali ganin ya nufi kan wani mai a dai-dai ta yana k'ok'arin hawa kanshi ita kuwa tak'i sakewa sai murzawa take tana.
"Ka sauk'e ni a nan bazan koma gidan kaba bana sonka na tsaneka."
Ido ya zaro cikin tashin hankali ganin saura k'iris ya taka wani mai reke da yake gefen titin gaba d'aya mutanen wurin sai rik'e kai sukayi suna.
"Innalillahi subahanallahi."
shi kuwa Hamma Umar cikin firgici da tsoron ganin zata sashin kisan kai gaba d'aya jikin shi sai rawa yake yi,
cikin b'acin rai ya fizge hannayen ta sannan ya tura ta jikin sit d'in ta koma ta bugi jikin marfin motar sannan ta sake tasowa tana k'ok'arin sake rik'e kan motar,
tsawa ya buga mata cikin zafin rai ya ware tafin hannun shi ya zuba mata mari d'aya wanda saida taga taurari na yawa a sararin samaniya kunnen ta saida ya bada sautin kiuuuu sannan ta kuma jin yayi dum lokaci d'aya zanen yatsun shi suka taso a farar fatarta tuni fuskar tayi jazir gaba d'aya ta rasa ina take dan marin ya gigitata,
shi kuwa da k'er ya samu ya tsaida motar jikin shi na rawa zuciyar shi cike da tsoron karta sashi kisan kai yayi parking a gefen titin cikin sauri ya fito ya nufi gun mai reken da mai a daidaitan hak'uri ya rink'a basu,
da sun hatsala amman ganin yadda yake basu hak'uri yasa sukace.
"ba komai Allah ya tsare gaba a rink'a kula."
"Toh nagode."
yace dasu sannan ya koma cikin motar ya shiga ya zauna fuska a tsuke tamkar bai tab'a dariya ba,
jan motar yayi da gudu ya kama hanyar damaturun,
ita kuwa tunda ya zabga mata marin ta kife kanta kan cinyoyin ta ta rink'a kuka mai cike da takaici,
bai kulata ba,
ita kuwa kukan taci gaba dayi tana sheshshek'a,
a haka har suka isa cikin damaturu a inda suna shiga hadari na tashi iska mai sanyi ya rink'a busawa tako ina sai walkiya ake da d'an rugugi alamu irin hadarin karshen damuna ce,
suna isa yayi parking sannan ya koma ya zauna ya jingunu da jikin kujerar yana jin yadda take kuka,
a zahiri mamaki yake irin tsanar da Ummul ke mishi sannan itace da laifi itace da kuka kuma
har cikin ranshi yaji zafin marin da yamata,
ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yasa hannu ya d'an dagota ya jingina ta da jikin shi hannun ta ya kamo cikin sanyi ya cusa hannun kan k'irjin shi sai kuma ya kalleta a hankali yace.
"Kiji yadda kikasa zuciya ta bugawa dan tsoron karki sani nayi kisan kai Ummul nine ba kyaso amman k'iyeyyar har tana k'ok'arin saki in kashe wasu a banza."
sai kuma yayi shiru sannan yasa tafin hannun shi yana shafa fuskar ta a hankali yace.
"Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi sabida sai inga kamar na k'asa rik'e amanar dana d'auka ne kiyi hak'uri ki gafar ceni banyi niyar tab'a lafiyar jikin kiba."
tureshi ta rink'a yi tana janye hannun ta,
shi kuwa rik'e hannun yayi a hankali ya bud'e d'an durowan gaban motar wani d'an k'ara min kontena ya d'auko bud'e wa yayi sannan ya d'auko wani zoben Diamonds sai shek'i yakeyi tamkar tauraro yatsarta ya d'an d'ago a hankali ya zira mata zoben cikin sanyi yace.
"Kinyi kyau matata yatsarki ta haska zoben."
fizge hannun tayi dai-dai lokacin da ruwan sama ya fara sauk'a ,
bud'e motar tayi ta fice cikin kuka ta koma can tsakiyar harabar gidan ta tsaya tana kuka,
ganin haka ya fito ya rufe motar cikin sauri yaje gabanta hannun ta ya rik'o tare da cewa.
"Kiyi hak'uri zomu shiga cikin gida kar ruwan ya tab'a mu,
kinsan ni bana son ruwan sama ya tab'a ni zai sani zazzab'i."
cogewa tayi fir tak'i shiga daya kamo hannun ta sai ta dasa mai ihu,
ganin haka ya rufe gidan sannan ya wuce ya shiga cikin gida a zaton shi ko zataji tsoro ta biyoshi,
Abu kamar wasa ya shiga,
ita kuwa sai tsuguna wa tayi a wurin ruwan yana ta sauk'a a kanta duk ta jik'e tayi jilik sai d'iga takeyi ga tsawa da walkiya da akeyi,
parlour ya fito rik'e da leima ya nufi gunta,
yana zuwa ya jawota jikin shi cikin rawan sanyi yace.
"Khairi kiyi hak'uri mu shiga cikin gida kar mura ta kamaki d'an Allah mushiga ciki bana so ruwan ya