Showing 69001 words to 72000 words out of 134562 words

Chapter 24 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

bataci komaiba duk gidan sun juya mata baya hatta Aliyu fushi yake da ita.


Shiko Hamma Umar a Abuja tunda sukaje bai samu sukuni ba haka yasa bai kirasuba sai dare daya kira Kuma sai akace Ummul tayi bacci hakan yasa basu gaisa ba koda gari ya waye ya kira duk woyoyin gidan basa shiga,
haka yasa suna dawowa ko gidanshi bai komaba ya kama hanyar potiskum d'in,
yana shiga cikin garin sai kuma yaji kewar Ammin shi da begen son ganin ta hakan yasa ya nufi gidan Ammin yana zuwa ya samesu ita da Inna da uncle ensu suna tsakiyar gidan suna ta hira,
kamar ko yaushe gaban ta ya zauna ya tonk'oshe k'afafun shi sannan ya cire hular kanshi,
itako Ammin ido ta tsura mai cikin murmushi da Happy tasa hannun ta kan gashin kanshi murya cike da k'auna tace,
"Allah yayi maka Albarka Allah ya tsaremin kai da d'an Uwanka Allah ya sanya alkhairi a rayuwarku ubangiji yayi muku rahama duniya da lahira".
Murmushi yayi cikin jin dadi yasa hannun shi ya dafa hannun ta dake kanshi yace,
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati Ammina".
sai kuma ya juya ya Kalli Uncle en cikin girmamawa yace,
"Uncle ina wuni ya gida".
"Lafiya lau Farouq ya hanya yanzu Ammin ka ke cemin jiya kazo ka sallameta zaka tafi Abuja".
"Alhamdulillah".
yace da uncle d'in sannan ya kalli Inna yace,
"sarkin surutu yau ya naganki shiru ko dan banzo da ogan naki bane".
dariya tayi sannan tace,
"ai kaima oganane".
kallonta yayi a hankali yace,
"kin Kama gaibu gwara miki Usmanun ki".
dariya sukayi duka shiko Hamma murmushi yayi sannan ya kamo hannun Ammin shi yace,
"Ammina farcenki ya d'an taru bari in yanke miki".
murmushi tayi tace,
"toh Allah ya ma albarka Allah ya tsaftace rayuwarka kamar yadda kake tsabtace min farcena".
"Amin Amin".
ya amsa sannan ya yanke matasu ya kankare mata,
bayan ya gama ne ya kalleta cikin karya wuya yace,
"Ammina yunwa nake ji kuma yau abin cikinki nake son ci".
mik'ewa Ammi tayi da sauri ta nufu kitchen,
abincin ta kawo mai tare da roban wonke hannun,
tuwan farar shinkafa da miyar ganye yasha man shanu da nama,
gaban shi ta ajiye mai a hankali tace,
"matso kaci ka d'ena zama da yunwa bana so".
"toh". yace sannan ya bud'e abincin murmushi yayi yace,
"Tab Ammi ai wannan yamin yawa gsky bazan iya cinyewa ba sai dai in zamuci tare zanfi jin dad'in cin".
murmushi Ammin tayi sannan ta matso sukaci a tare sannan suka dan yi hira Inna da uncle suna ta musu dariya,
sannan ya salla mesu ya tafita,
har yaje kofar gidan ya dawo ya kalli Ammin nashi itama shi take kallo a hankali yace,
"Na manta ban gaya miki ba na kusa na samowa autanki mata muyi mishi aure yafi zaman hakan matar zata kulan mana dashi".
murmushi tayi sosai sannan tace,
" toh Allah sanya Al,khairi".
"Amin Amin Ammina kiyiwa k'anina fad'a ya rink'a kula da kanshi".
"toh zan mishi kaima ka mishi ".
A haka suka sallami juna,
yana fita kai tsaye gidan Abban ya nufa.


Bayan yayi parking kai tsaye ya kutsa cikin gidan parlour Nenne ya wuce inda ya samu ba kowa har zai juya ya fita sai yaji sautin kukan Ummul a cikin bedroom d'in,
da sauri ya Koma cikin d'akin kan gado ya hangota konce tana ta rawan sanyi da kuka,
cikin sauri da furgici ya k'aroso gabanta hannu yasa ya d'agota ruggumeta yayi cikin kad'uwa yace,
"Khairi! Khairi na meke damun ki? Ina Nennen? ya gidan shiru basa nanne? ".
ruggumeshi tayi cikin kuka ta d'ago kanta,
da sauri ya tallabe kanta cikin tsoro yace,
"meya samu fuskarki inasu Nennen? ".
cikin kuka da tausayawa kanta ta, kwashe labarin abinda sukayi mata ta gaya mishi ta k'ara da cewa,
"Nenne ma bata min magana Abba ma fushi yakeyi dani ko Aliyu sun hanashi yamin manana ya Usman ma fushi yake dani duk basa sona basa zama kusa dani yanzu duk suna parlour Hajjajo".
hannun ta ya kamo cikin tsananin bak'in ciki da takaici waje ya fito da ita kai tsaye part d'in Hajjajo ya nufa da ita,
kicinb'is sukayi da ya Sadik a tsakiyar gidan,
yana ganin Sadik d'in yaja hannun Ummul d'in ya tsaya a gaban Sadik d'in cikin tarin bak'in ciki murya na rawa idanunshi sunyi jazir sai shek'in hawaye yakeyi cikin fad'a da d'aga murya yace,
"Zo nan".
jin muryarshi yasa gaba d'aya mutanen gidan suka firfito tsakiyar gidan dan basuma san ya dawoba,
shiko ido ya zuba musu d'aya bayan d'aya cikin rawan murya da fad'a yace,
"Sadik amman dai dama can haushina Kake ji ko? bazaka iya duka na bane shiyasa kai ma Ummul duka dan ka huce a kanta ko? ".
Gaba d'aya shiru sukayi ganin yadda jikin shi ke rawa dan basu tab'a ganin wannan bacin ran a fuskar shiba,
shi kuwa cikin fad'a yaja hannun Ummul zuwa gaban Adam baki na rawa yace,
"Adam ka tsani Ummul ko meyasa baza kayi min adalci da kawaici ba ka tsane ni shiyasa ka tsani Ummul tunda aka Aura minta ko?".
shi kam Adam da Sadik sai jujjuya kai sukeyi alamar a, a,
shiko k'ara jawo hannun Ummul d'in yayi zuwa gaban Nenne cikin rawan murya da k'ok'arin maida hawayen shi yace,
"Nenne ki rink'a ganina a jikin Ummul na tabbata a ko wanne hali kike zaki kulanmin da Ummul Nenne ya za'ayi kina ji kina gani a doki mutun hud'u Nenne Ummul a gareta Ammina a gareta d'an Uwana Usman a gareta d'ana da zata haifa a gareta ni kaina".
Nenne kam kasa cewa komai tayi.

shiko jawo Ummul d'in yayi gaban Abba dake tsaye a k'ofar parlour shi suka durk'usa cikin rauni da karya wuya yace,
"Abba kayi hak'uri abin ne yayi yawa gara in fad'a musu yadda nake ji in sun tozarta ta,
Abba nasan sonane yajanyo kai watsi da Ummul,
Ayyah Abba in dai soyayya tace to na rok'ek'a dan Allah ka kulanmin da ita ka hana su Adam dukan ta Abba kallifa da tsohon cikin nan suka daketa in sun mata illafa me zasu cemin".

ita kanta Ummul yau ta fara gano wani irin son da Hamma Umar ke mata hakan yasa ta cika da mamaki ziryan.

Shiko Hamma k'ara jawo hannun Ummul yayi ya tsaya a gaban Usman, cikin tuhuma ya kafe Usman da idanu sai kuma hawaye car-car na bin fuskarsa,
murya na rawa cikin kuka yace,
"Ashe Usman bazaka iya kula da iya lainaba in bana nan ?
Usman ashe baka damu da abinda ni d'an uwanka nake soba? shin in ban barmaka amanar Ummul ba wa zan barwa amanarta a wannan duniyar?,
wallahi wallahi bazan yafewa duk wanda ya takura min itaba hankalina bazai kwantaba,
Usman hakan yana nufun
kenan in nayi tafiya zatasha wuya a gaban ka?."
kai Usman ya rink'a kad'awa cikin kuka da tashin hankalin ganin yasa Hamman shi kuka cur-cur shima kukan ya rink'ayi yana matsowa jikin Umar d'in dan wani irin suka da zuciyarshi tayi a take jikin shi ya rink'a rawa,
shiko Hamma Umar kamo hannun Ummul din yayi yace,
"Khairi na mu tafi kai kuma Aliyu azatona ko kowa zai juyawa Ummul baya ai kai abokin kukanta ne dole ka lallasheta in kana son inji dad'i,
Nenne wallahi gata d'aya zakumin inji dad'i ku kulanmin da Ummul in bananan Adam! Usman! Sadik! wallahi da kunsan yadda nake ji a kan Ummul da ko hararta baza kuyi ba".
sai kuma yaja hannun ta ya nufi harabar gidan da ita tare da ce musu,
"Adam! Usman! Sadik! kuci gaba zata dawo in yaso saiku kashemin ita ku huta".
sannan yaja hannun ta suka fice
suko gaba d'aya bayanshi sukabi da sauri Usman yana kuka har jikin shi na rawa yace,
"Ayyah Hamma Umar kayi hak'uri ba hannuna a dukan Ummul Hamma bazan sake barin ayi mata komaiba kar kayi fushi dani d'an uwana ."

Bai kulashi ba sai bud'e mota yayi yasa Ummul d'in a ciki ya zagaya zai shiga kenan Abba ya matsoshi a hankali yace,
"Farouq kayi hak'uri".
girgiza kai yayi cikin sanyi da zubda k'ollah yace,
"a, a Abba raina nane ya b'aci kuma wallahi dazan iya tafiya da ita duk inda zanje da da ita zanje,
amman bazaiyuwu ko ina muje tareba anan kad'ai zan iya barinta amman sunk'i samamin konciyar hankali".
Sadik ne da Adam da Aliyu su kace,
"Hamma kayi hak'uri ka gafarcemu".
tsaki yaja ya bud'e motar zai shiga Kenan Usman ya ruggumeshi cikin kuka yace,
"in kayi fushi dani ya zanyi?".
shima ruggume Usman d'in yayi cikin rawan murya yace,
"Ba komai! ba komai! ba komai! Allah zai zama gatanta tunda dukanku kun tsaneta,
Kai kuma waya cema zan iya fushi da kai,
bani da kamarka fa duk duniya ina sonka d'an Uwana".
sai ya sakeshi ya shiga mota ya tafi yana juyowa yana kallon Usman shima Usman d'in binshi yayi da d'an sassarfa yana d'aga mai hannu alamar bye-bye tare da cemai,
"Hamma na ina sonka".
shima hannu ya d'aga mai yace,
"Usman ina sonka".
daga nan ya bar harabar gidan ya dauk'i hanyar damaturu,
suna isa
kai tsaye hospital ya wuce da ita yana zuwa shida kanshi ya duba lafiyarta a cikin asibitin sukayi sallah sannan ya dauketa suka wuce Restaurant abinci suka ci
suka sha sannan ya wuce gida da ita.

Bayan sun isane ya wuce d'akin shi yayi wonka ya fito kenan ita kuma Ummul ta shigo daga dukkan alamu itama tayi wonka,
a hankali ta tako tazo gabanshi cikin sanyi ta fad'a jikin shi murya can kasa tace,
"Hamma Umar ina son k..........



*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL, AMARI*

Page 2⃣8⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇






*A* hankali tayi taku cikin sanyi ta matsoshi ta fad'a jikin shi tayi lub a k'irjin yayin da ta manna kanta a kafad'arshi ido ta lumshe cikin yanayin sanyin zazzab'in,
shi ko Hamma Umar hannu yasa ya ruggumeta tsam a jikin shi sai ajiyan numfashi yake sauk'ewa ya lumshe idon shi yayi shiru yana jin bugun zuciyarta na harbawa kan nashi sai ya k'ara tallabo ta tare da shafa fuskarta,
lumshe ido tayi a hankali tace,
"Hamma Umar ina son kak'ira ya Usman ka lallasheshi,
ka ganifa yana kuka muka barshi,
Hamma kayi hak'uri karkayi fushi da ya Usman".
jawota yayi suka zauna tsakiyar gadon nashi sannan ya zauna ya d'an jingina da jikin kan gadon ita kuma ya jawota jikin shi sannan ya d'an sunkuyo kanta yana kallon fuskarta kallo mai cike da wasu yanayin a hankali ya fara magana cikin lumshe ido yace,
"Usman wani sashi ne na jikin Umar Usman rabin jiki nane Usman d'an uwanane da bani da madadin shi Usman aboki nane kuma amini nane kuma shak'ik'ina ne Usman wani babban jigone a rayuwa ta,
Ummul kin tab'a ganin mutun yayi fushi da d'an uwanshi Ummul indai zanyi fushi da Usman toh zanyi fushi da karan kaina kenan Ummul ba fushi nayi da Usman ba a a hannun ka mai sanda nayi mishi".
shiru tayi tana jin wani irin yanayi daya bak'onci rayuwarta tun sanda taga Hamma Umar d'in na kuka a gaban su Abba yana kuma yiwa su ya Adam fad'a,
haka kawai ta tsinci kanta da k'ara ruggume shi sai kuma tayi luf a jikin shi kamar maiyin bacci,
shima shirun yayi a haka har zuwa wani lokaci sannan ta d'an d'ago kanta ta kalleshi a hankali tace,
"Hamma ka kira ya Usman kaji kayi hak'ari shifa ya Usman baimin duka ba".
baiyi magana ba sai hannu yasa yajawo wayarshi dake kan dressing mirror sannan ya kira Usman d'in tare da sa amsa kuwa,
shiru sukayi suna jin yadda woyar ke ruri bai d'agaba,
a gida Kuwa su Hamma Umar d'in na fita Abba yayi tayiwa su Adam fad'a,
Hajjajo Kuwa gaba d'aya mamakin Umar take,
shiko Usman suna watsewa,
kai tsaye d'akin su ya nufa yana zuwa kan gado ya fad'a cikin tarin k'uncin zuciya da zafi haushin kanshi da kanshi yakeji tunda ya kasa samawa Hamman shi farin ciki mutumin da kullum burin rayuwarsa yasashi farin ciki amman shiko yau sai kuka yasa d'an Uwan nashi gaba d'aya sai yaji ya tsani kanshi da kanshi cikin kuka ya rink'a cewa, "Hamma na kayi hak'uri ka gafarceni Hamma na bazan sake yin abinda zai bata ma raiba insha Allah nima zan saka farin ciki".
yana cikin haka ne yaji woyarshi na suwa,
hannu yasa ya amsa kiran tare da manna woyar a kunnen shi, shiko Hamma yana jin a ya d'aga cikin sauk'e numfashi yace,
"B'iyaye na fushi kayi da nine?
toh kayi hak'uri kaji ko d'an uwana Usman ka gafarce ni."
kai Usman ya rink'a jujjuyawa tare dasa tafin hannun shi ya share hawayen shi murmushi yayi mai d'an sauti sannan yace,
"In dai zanyi fushi da Hamma na kenan zanyi fushi da mutanen duniya baki d'aya Hamma na ni zan nemi gafararka ba kai zaka nemi nawaba ka gafarce ni Hamma na karkayi fushi dani".
murmushi yayi jin dad'in Usman baiyi fushi dashi ba sannan yace,
"Ni bakayi komai ba na yafe maka kaima ka yafe min sannan ka samu Adam da Sadik da Aliyu kace su gafarceni nima na yafe musu".
dariya Usman yayi yace kai Hamma mune da laifi kuma mu za, a bawa hakuri har ka huce kenan".
murmushi yayi yace,
kai Usman da kana kusa dani da sai na rongwoshe ma kai na kuma matsema kunne tunda bakajin magana".
dariya Usman yayi sosai dan yaji dadin hucewar da Hamman shi yayi,
shiko Hamman a hankali yace,
"Usman inajin kunyar Nenne da Abba nayi ta fad'a a gaban su watak'il na b'ata musu rai,
dan Allah ka basu hak'uri kace su gafarceni".
da sauri Usman ya katseshi da cewa,
"Tab Abba fa da Nenne da katafi saida sukayi ta fad'a kamar su ari baki Abba harda marin Sadik,
sai kace badasu akayi wa Ummul d'in hukunci ba duk suka ware kansu laifi ya koma kan Sadik da Adam nima da Aliyu sai muka zille kanmu".
dariya sukayi baki d'aya sannan Ummul dake jinsu kuma tace,
"Ya Usman ba cin zalina kukayi ba duk kun tsaneni ba mai sona dan kunga Hammana baya nan kukamin halin yan ubanci".
dariya yayi yace,
"ai ked'in ce bakya jin magana".
ruggume Hamma Umar
d'in ta k'arayi da k'arfi sannan ta d'ago kai ta kalleshi baki ta d'an tura tare da cewa,
"ina jin magana mana ya Usman ka tabbayi Hamma shi yasan inajin magana".
sai ta kuma kalli Hamman a hankali tace,
"Hamma inada jin magana ai ko?".
ruggumeta shima yayi sannan yace,
"sosai ma kuwa Khairina tana da jin magana".
Murmushin jin dad'i tayi shiko Usman dariya yayi ya katse kiran,
ya kife kanshi cikin pillow numfashin sa na fuzga,
shiko Hamma Umar ganin yadda Ummul ke mak'ale dashi a hankali ya jawo blanket ya rufe musu jiki hannu yasa yana shafa cikin nata,
ita ko hannun ta ta kife kan kirjin shi tana d'an murza yatsarta a jikin shi,
a hankali yace,
"Khairi! Khairi! Khairi! ".
shiru bata amsa ba,
sunku yowa yayi ya lek'a fuskarta abin mamaki sai yaga tayi bacci tuntuni sai jikinta da ya k'ara zafi da zazzab'in haka yasa ya gyara mata kwanciyar ta a jikinshi sannan yayi musu addu'a ya shafa musu sannan ya d'auki woyarshi ya fara karatun qura'an,
a haka har bacci yayi awon gaba dashi.

washe gari lahadi da sassafe Hamman ya tashi kamar yadda ya saba ya kimtso komai sannan ya zauna da kanshi ya bata abinci Sauri-sauri dan duke da yau lahadi ne yauma zaije gidan govnr zai k'ara duba lafiyarsa,
9:20 Am ya gama komai ya fita kai tsaye gidan gomnatin jihar yana nufa.

Itako Ummul a gida Hamman nata yana fita ta koma d'akin shi ta zauna haka nan ta tsinci kanta da yin abinda bata tab'ayi ba duk da zazzab'in da take ji amman taji k'arfin guiwar jikin ta d'akin ta fara tattarewa ta kimtsa duk abinda ya watsa kafin ya fita zanin gadon ta canza mai ta nad'e wannan d'in sannan ta share ko ina ta goge komai ta killaci d'akin sannan tasa turaren wuta mai k'amshi daga nan ta koma d'akinta ta gyara ta fito parlour su har dinning area da kitchen nasu kab ta gyara komai sannan ta shoga kitchen d'in,
karo na forko kenan da tayi niyar tayi girki tare da rebon Hamma Umar d'in dan takanyi girki kam amman bata tab'ayi da rebonsa ba,
shiko in zaiyi itace forkon ci kuma duk inda yake zai dawo ya mata abinda zataci ko yana office yakan dawo yayi girki ta kuma ci,
amman yau da niyarta a cikin ranta zata yi girkin dan inya dawo ya huta,
bayan ta kammala aiki ne ta koma d'akinta wonka tayi mai rai da lafi sannan tana fitowa karano na forko a da ta zauna tayi kolliya na gani na fad'a sannan ta zira doguwar riga a jikinta duk ta feshe jikinta da turaruka tare da murje humra a jikinta,
k'arfe 2:00 pm ta fito parlour bayan tayi sallan azahar,
a k'asa ta konta kan carpet tayi matashi da pillows d'in kujerun
lokaci d'aya kuma gajiyar aikin da tayin ya rufeta sai mik'a takeyi,
shiko Hamma Umar a gidan govnr yayi sallan azahar ana idarwa ya koma ya sallamesu sannan ya nufi gida,
da saurinshi dan yana tunanin Ummul ba lafiya,
yana yin parking ya fito ya nufi cikin gidan a parlour ya sameta tana konce abun mamaki ko ina fes gashi ta raggad'a kolliya sai shek'i takeyi,
cikin mamaki ya zauna gefenta yana kallon dinning table nasu daya ga an shirya kuloli a hankali yace,
"Hmmmmm Halima ce tazo? ".
kai ta juya ba tare da ta fahimci manufar tabbayar ba,
shiko a zatonshi Anty Haliman ce tazo tayi musu wad'an nan aiyu kan,
k'ara matsota yayi yana shak'ar k'amshin jikin ta a hankali yace,
"Kinyi kyau Ummu na wannan kolliya haka duk ni akayiwa ko?".
hararan shi ta d'anyi sannan ta juya kai,
shiko matsota ya kumayi yace.
"Naga kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login