Showing 117001 words to 120000 words out of 134562 words

Chapter 40 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

ya Usman nata kiranta kuma bata son ɗagawa kar Ammi ta tashi,
tana buɗe datan
saƙon shi ta gani,

"ina jiranki a kofar Nanne ki fito mutafi kinga kowa yayi bacci".

Amsa tamaida mai,

"kayi haƙuri kaje ka kwanta saida safe".

"gaskiya bazan iya baccin ba kizo ki taimaka min in kuma bakizo ba kuka zanyi tayi har gari ya waye, daman ni nasani ba mai sona sai Hammana".

Jiki na rawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta lallaɓa dan kar Ammi tafarka ta fice,
a bakin ƙofar palour ta taddashi tana fita yasa hannu ya ɗauketa cak ya ruggume ta a jikin shi,
bai sauketa ko inaba sai sai akan gadon shi,
A hankali ya kontar da ita cikin wani irin yanayi ya konta gefenta a hankali ya jawota jikin shi yana maida numfashi hannun shi ya cusa cikin rigar baccin jikin ta yana mata wani irin salo mai taɓa zuciya a hankali yake sarrafata da salo mai cike da so da ƙauna haɗe bakinsu guri guda yayi yana mata wani irin tattausan kiss,
hannun shi nakan kirjin ta yana murzawa dukkansu sun rikice sunyi nisa cikin duniyar masoya a haka sukai ta fama har bacci ya ɗaukesu suna ruggume da juna cikin happy.

A zabure Ummu ta farka,
aiko tare suka mike yana daɗa matseta kamar zaa kwace mai ita,
"Ya Usman kabarni intafi kafin kowa ya farka kaga an fara kiran salla ".
Wani irin kallo yake mata kamar zai haɗiye ta baice komaiba ya saketa,
dasauri ta fice bayanta yabi da kallo badan yasoba banɗaki yashiga yayi wanka sannan ya fito ya fara nafilillin shi.


Gari na wayewa misalin 8:00 Usman ya shirya tsab yaje yagaida Abba da Hajjajo sannan ya shiga ɓangaren Nanne, a kitchin yaji motsin Nanne dan haka ya tsaya ya gaidata sannan ya wuce ɗaki, zaune yasami Ummul a kan sallaya Ammi kuma na bakin gado ta zuba mata idanu, kamar jira take ya shiga tana ganin shi ta zuba mai ido cikin son gano halin da ɗan nata ke ciki,
Shiko Usman a hankali yazo ya zauna a gefen ta yana gaida ta,
ɗago kai tayi tana kallonshi,
sai kuma ta sunkuyar da kanta ido cike da kolla a hankali ta fara zub da hawaye sai sautin kukanta dayake fita a hankali dasauri sukayo gabanta suka durkusa suna tambayar ta ko meya sameta suma idonsu tab kollah, cikin kuka tace,
" Usman wato wannan shine gatan da zakuyiwa Umar kenan ko Usman? sai ku taru kuyita mishi kuka?
An haɗaku aure dan a nazaton zaku samawa juna sanyi da sassaucin zafin rashi shi amman ashe bamu saniba hakan an baku damar ku zauna kuyi ta mishi kukane".
Usman ta kuma kalla da duk jikinshi yayi sanyi tace,
"Usman bakaso hankalina ya konta ko? Kasan bana son tashin hankalin ku kaida Ummu kuma shine kake ƙarawa ga yadda fuskokin ku suka kubbura,
Usman har sai yaushe zamu bar kukan rashin Umar?
Usman ai kukan rashin shi bazai kare manaba har sai randa muka konta damarmu daurewa zamuyi mubar zubda ƙollah muyita mishi Addu'a,
amman hakan ya gagara da sai ka tasa Farouq a gaba kaɓuya kayi ta kuka yanzu kuma Ummul zakake tasawa a gaba kana kukan kenan?".
Shiru sukayi cikin sanyi da yarda da nasihar Ammin,
A haka Abba da Adam suka shigo suka samesu suma suka ɗora tasu nasihar har saida sukaga sun sake suka je sukayi break cikin wolwola.


A ranar bayan sunci abincin dare ne suka zauna a palour Nanne dukkansu suna kallon news a tashar TVC News suna zaune kowa da abinda yakeyi amman ita Ummul gaba ɗaya hankalin ta na kan tv sai Aliyu dake zaune gefenta ta saman hannun kujerar da take zaune Usman kuwa yana gefen ta a kan kujerar
suna cikin hirar kawai sai sukaga Ummul
ta miƙe cikin tsananin razana da firgici gaba ɗaya jikinta sai rawa yake cikin gigita ta damki hannun Aliyu dake kusa da ita sannan ta nuna tv da hannunta ɗaya baki na rawa murya a hargitse take nuna tv tare da cewa,"
"Ammi gasu Ammi sune ya Usman kallesu wallahi sune Ammi sune suka k..".
Bata ƙarasa maganar ba tayi baya a sume ta faɗa kan Usman,
wanda ya taso tunda yaga yanda jikinta ke rawa,
dukkan su kanta sukayo kowa yana addu'a da jimamin damuwarta da gudu Sadiq yaɗebo ruwa ya mikawa Ammi jikinta na rawa ta yayyafa mata sannan ta shafa mata a fuska,
Lokaci ɗaya tayi wata irin ajiyar zuciya sai takuma razana tana ɗago kai idanu wanta a zazzare
cikin tsoro Ammi tace,
"Wai meke razanata ne haka fa in baku mantaba hakan yafaru da ita cikin azumi ta suma".
sai ta kuma kallon ta cikin tausayawa tace,
"Ummu na faɗamin me ke faruwa?".
Cikin firgici jiki na rawa tare da rera kuka mai cike da ƙuna a zuciya ta nuna fuskokin da ake nunawa a tv tace ,
"Ya Usman kallesu sune suka yankamin Hamma na a gabana sune suka kasheshi wallahi har abadan bazan manta waɗan nan fuskokin ba bazan manta fuskokin suba wallahi sune".
Gaba ɗaya jikinta na rawa,
sosai Usman yasake matsota ya tare mata fuskar ta daga kallon tv shima yana rumtse idanun shi da ƙarfi dan har abada bazai so ƙara kallon waɗannan mutanen da suka kashe mai Hamman shiba,
Adam dayake tsaye jikin shi yana rawa yafara musu bayani,
"Hakane cikin azumi wani azumi daya wuce ankama waɗanda suka kai harin bomb a Jos! Kano da Zaria a gurin da ake verification na malaman makaranta, an kamasu ne a hanyar komawar su a Daɗin Kowa ta jahir Gombe, wannan da take nunawa yanzu dashi a cikin su yanzu kuma dasune akayi musaya suka bada y'anmatan Chibok da aka sace sukuma aka badasu wa uƙiyar tasu".
Sadiq ne yakar ɓi zancen da cewa,
"Ammi waɗannan dukkansu y'an asalin nan potiskum ne fa wata ƙil".
Usman da tunda aka fara maganar baice komaiba sai addu'a da yaketa tofa mata,
ganin har yanzu bata dawo hayyacin taba yasa yamiƙe hankali itama ya ɗagota duk jikinta na rawa suka fita yanufi ɓangaren shi da ita tana makale dashi tana rawar jiki da zazzaro idanuwa,
Suko su Ammi da su Adam ɗin gaba ɗaya haka suka zauna sunata jajantawa da yiwa Hamma Umar ɗin addu'a.


A ɓangaren su Ummul kuwa kukan taketa yi a kiɗime,
ganin haka yasa Usman ya wuce da ita part nasu kan kujera ya jawota suka zauna
rarrashin ta ya rinƙayi amman ina ya rigada Ummu ta buɗe shafin kuku dan ganin fuskokin waɗanda suka kashe mata ɗan uwanta kuma mijin ta,
jawota jikin shi yayi a hankali ya tallabo haɓarta cikin sanyi da zubda ƙollah ya haɗe bakin shi da nata wuri ɗaya kissing ɗinta ya rinƙayi cikin salon son tsaida kukan nata daga nan ya gama rikitata da salon soyayyar shi mai tsanani duk da kuwa shima yanayi yana zubda hawaye,
haka suka kwana ranar ma yanata ririta ta da son sama mata nitsuwa,
sai dai duk yanda yaso daya samu damar raɓarta bata bashi damar kusantar taba shikuma baida niyyar takurata haka dole ya haƙura kamar yadda ya haƙura jiya,
Asubar fari ta tashi ta gudu kamar yadda tayi jiyan.




Usman ne yasami Abba da Daddy a safiyar litinin a palour Hajjajo yake sanar dasu cewa tafiyar shi zata kama cikin satin nan zuwa ranar juma a, kuma zaitafi da matar shi dakuma yaronshi Farouq duk da ba daɗewa zaiyi ba aiki ne kawai zaije na watanni uku yadawo,
Addu'a sukayi mashi cikin jin daɗi sannan Abba yace,
"Usman bazan hanaka ɗaukar matar ka da yaron kuba amma inaso ka fahimci hakan zai iya taɓamai karatu shi kada kayi tunanin dan yanzu yafara bazai sami matsala ba amma kaga ko zuwa kayi ka sakashi makaranta acan watanni 3 kawai zaiyi kasake ɗaukoshi kudawo kaga canje-canjen makaranta baida daɗi ga yaro dan haka kayi hakuri kutafi kubarshi anan yana zuwa makaran tar shi har kudawo ku sameshi ina ganin baza a sami wata matsalaba tunda daman yasaba da iyayen ku gakuma Adam da Sadiq sannan ga abokinshi Aliyu".

Kanshi a kasa idonshi yafara ƙollah ya daure ya danne halin da yake ciki gudun kada su Abba su gane a hankali yace,
"To Abba shikenan saimu barshi".
sai ya kuma ɗan gyara zama cikin sanyi yace,
"Abba dama Ummu tace min tana son zuwa gun AYSHA ALIYU GARKUWA marubuciyar dake rubuta labarin tannan to dama mun gama shiri kafin mu tafi Malesia sai munje garin su Garkuwar toh shine nake so in zamuje can ɗin kam a barmu mu tafi da Farouq dan itama Aysha tana son ganin Farouq ɗin".
Daddy ne ya ɗan kalleshi cikin murmushi yace,
" ba damuwa Usman Allah yayi muku albarka yasa ayi tafiyar a sa'a Allah ya kuma dawo daku lafiya".
Da "Ameeen duka suka amsa sannan sukayi ta tattaunawa kafin suka watse.


Ɗaki Usman ya koma yafaɗa kan gado yanajin wani irin zafi a zuciyar shi idanuwan shi na zubar da kollah a hankali yajanyo wayar shi yakira Ummul tana ɗagawa yace,
"Kisameni a ɗaki".
yana faɗin haka ya katse kiran,
jin muryarshi yasa jikinta yin sanyi dan ta fahimci akwai damuwa tattare dashi dan haka ba ɓata lokaci ta fita ta nufi ɗakin nashi.

Sallama tayi a parlour taji babu motsin shi dan haka ta murɗa kofar bedroom ɗin a hankali da sallama ta shiga,
kwance yake yana kife a haka ya amsa sallamar ta yaɗago hannu ya kamota sannan ya juyo ya janyota jikin shi zamewa tayi ganin ƙollah a idanun shi tasa hannu ta goge mai a hankali tace,
"Menene kuma?".
Shima tashi yayi ys zaune ya ɗora kanshi akan kafaɗarta duk ya narke a jikin ta cikin shogoɓa yace,

"ba komai Ummuna".

hannu tasa ta shafa sajen fuskarshi tare da cusa hanun ta cikin suman kanshi tana ɗan murza yatsunta a ciki murya can ƙasa cikin raɗa tace,
"Da komai kam ya Usman,
daman tunda naji Abba yaje yana faɗama Ammi da Nanne yanda kukayi akan tafiyar nan kuma naga kiranka sannan naji muryarka nasan abunda kake wa kukan".
Hannu tasa tashafi gefen fuskarshi tare da shafa wuyanshi zuwa ƙeyan shi ta ƙara manna kanshi a ƙirjinta cikin tattausan lafazi tare da sanyin murya tace,
"Yanzu saboda sunce kabar Farouq ne kake kuka?
Baka yarda da kulawar da zasu bashi bane? dan Allah ya Usman ka rege son da kakewa Farouq dan Allah kada kabari wani daga cikin iyayenmu yaga raunin zuciyarka akan wannan abun,
domin baza suji daɗi ba,
ni dakai zamuyi ƙoƙari mu danne damuwar mu musawa zuciyoyin mu haƙuri tunda ba rabamu dashi akayi gaba ɗayaba watanni 3 kamar yaune kadaure kaji ko? ya Usman na ko sokake nima nakasa jurewa nayi kuka har su gani?".
Ɗago kanshi yayi yana juya mata kai alamar a,a duk ya wani maraice mata tamkar yaro sai fama nuƙurƙusanta yake da salon sakalcin sa da Hamma Umar ya sakal tashi,
a hankali yasa hannu yakamo fuskarta ya zuba mata idanu sannan cikin karya murya yace,
"Nabari Noor ƙalbee na nadena zan jure badan raina yaso hakan ba Ummu bana son duk wani abu da zai nisan tani da Farouq".
ganin zai sake tada rigimar tasa yasa ta ɗan tureshi ya konta sannan ta ɗan kifa ƙirjinta kan nashi a hankali ta ɗan murza haɓarta a kan sajen shi cikin salon kawar mai da damuwar tace,
"Naji ka gayawa Abba zamuje garin su Anty Aysha ko?".
kai kawai ya iya gyaɗa mata dan tuni ta rikatashi ta yadda ko maganar zata bashi wuyan yi,
ita kuwa lips enshi ta kalla sannan tasa yar yatsarta tana zagaye lips en nashi cikin happy ta lumshe ido tare da cewa,
"To yaushe zamu tafi? in munje kwana nawa zamuyi?".
hannu yasa yana shafa bayan ta a hankali cikin cushewar voice yace,
"Hmmmm hahhhh gobe zamu tafi kuma kwana biyu zamuyi,
in muna dawowa zamu biya Yankari muyi kwana ɗaya in mun dawo da kwana ɗaya zamu wuce malesia".
murmushi tayi tare da subbatar lips enshi sai kuma tayi maza zata janye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login