Showing 108001 words to 111000 words out of 134562 words

Chapter 37 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

jaraba,
kuma ko a Shari'ance dama in gaya miki kisan irin mijin da zaki aura".
kanta ta sunkuyar cikin jin tsananin kunya hakan yasa ta kasa maga sai kai ta gyad'a mai murmushi yayi cikin tsananin jin dad'i yace,
"Dole in gwada miki farin cikina gaskiya kinyi na yaba miki al'k'awari kuma zan rik'e miki wurin zaman aurenmu wallahi bazan matsa mikiba zan sakaki a cikin farin ciki zuciyar ki na cire mata bak'in ciki da duk wani k'unci tunda kema kin yimin halacci domin kinyi rik'o da amana tunda kin amince dani".
ido ta lumshe cikin sanyi da jin kasala da kalaman ya Usman d'in nata,
a hankali tace,
"Lallai shak'uwa tana sanya yarda a tsakanin mu tabbas idan nace maka a zuciya ta kai na zab'a ka gaskatani ka bani dama,
amman in dai sone har gobe Hamma nane kawai nake so a raina ya Usman sai kayi hak'uri dani".
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya kamo hannun ta ya tsaida ita cikin mayen so da juyewar idanu yace,
"zan rayu dake cikin aminci son da kikeyiwa Hamma na ma kawai ya wadatar dani ko baki soniba ba matsala tunda kinso d'an uwana Kuma nasan nima wata rana zaki soni".

Haka suka kasance cikin hirar su ta soyayya duk da bakomai take amsamai ba amma saida suka raba dare suna hira sai k'arfe 3:15 ya rakata har bakin kofar d'aki ta shiga yanajin kamar kada su rabu sannan ya juya ya tafi part ensu.

Yana shiga bedroom ensu yasami Adam yayi d'ai-d'ai a gado yana baccin gajiya kasa hak'uri yayi yasa hannu yad'an bugi k'afar shi, da k'yar ya bud'e ido yad'ago kai yace,
"yadai?".
zama yayi kusa dashi a kan gadon yace,
"Tashi kasha labari naci zab'e Dr Bashir da Mustapha duk sun fad'i jam'iyata ta kafu k'ark'ashin jam'iyar Hamma na naci albarkacin d'an uwana duk da baya raye amman a sana dinshi nake farin ciki".
"a a dan Allah ka barni nai bacci na kaban labarin da safe".
Adam yafad'a yana gyara kwanciya,
da sauri shiko ya rik'oshi ya k'arasa zaunar dashi yana cewa,
"Gwarama ka tsaya kaji wlh dan bazan barka kayi baccin nan ba". Adam da yakeson yacigaba da bacci yace, "To menene?".
"Ummul ce". yace shiko katse shi yayi da cewa,
"ai dama nasani koyaushe maganar kenan".
hannu yasa ya toshemai baki yace,
"Kai ba irin wannan labarin bane,
yau da bakinta tace ta amince da aure na".
"congrat Allah sanya alkhairi". daga haka ya juya yaci gaba da baccin shi,
shiko mik'ewa yayi yaje yayi wanka da alwola yazo yayi ta nafiloli da karatun Qur'ani har aka kira sallah asuba.



Tunda suka fito daga masallaci sallah asuba Abba ya fahimci da magana a bakin yaron nashi dan yanata bin bayan shi yana sosa kai,
kamo hannun shi yayi suka nufi b'angaren Abban,
ya zauna a kujera shikuma yazauna k'asan kujerar ya ton k'oshe k'afa saida suka gaisa sannan yafara sosa k'eya kamar mara gaskiya,
"Haba d'an Abba ya aka yine ? ai babu wannan b'oye-b'oyen tsaka nin mu fad'amin me kakeso?".
K'ara sunne kai k'asa yayi yana murza yatsun kafar shi cikin sanyi yace,
"Daman mun gama magana da Ummul ne shine ".
Sai kuma yayi shiru dariya Abban yayi mai sauti ya dafa kafad'ar shi yace,
"To shikenan nagane anjima zamuyi magana da Ammin ku sai kuma insanar da Hajjajo inyaso idan Daddy ku ya shigo anjiman sai mu mik'a musu sadakin su kaga sai su samana rana ko?".
Baisan lokacin daya kamo hannun Abba ba yana cewa,
"nagode nagode". Saikuma ya saki hannu yana sosa kai.
"To jekai azkar d'inka".
"to ".
Kawai yace yamik'e a kunyace ya fice.


Shi kam Abba mamaki yake dan yana rena shekarun Usman gashi baida wani girman jiki amman ya lura yana son auren sosai,

Dr Bashir kuwa yau da wuri ya tashi dan zaizo yayiwa Ummun shi sannu da dawowa,
a gefen Mustapha ma harda Ummanshi suke shirin zuwa yau din suwa Ummul barka da dawowa Lafiya,

Shi kuwa Usman yana shiga part ensu a parlour ya zauna cikin jin bacci ya kira Ummil d'in
tana kan sallaya woyar na gefen ta juyowa tayi ta d'an kalli Ammi dake karatu,
a hankali ta yi mishi sallama,
yana jin muryar ta cikin,
wani irin yanayi yace,
"wash Noor Hayateeeeeeeeeh bacci nake ji kuma kuma b...........





*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣6⃣


*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*MOH ALLAH WUJI FURƊATA*



```A madadin Member's ɗina na Group ɗin
TABITAL FULAKU nake miƙa saƙon gaiduwar ta'aziya ta ga HALIMA Ummu Maryam kano tare Mu'allima Bauchi Allah ya jiƙan iyayen ku Allah yasa sun huta rabbi ya sanyayya konciyan ƙaburburansu Mu'allima Allah ya baki haƙurin rashin mahaifiyarki da kikayi a deren jiya Halima kema Allah ubangiji ya baki haƙurin maihaifiyarki da kika rasa shekaran jiya Allah yasa sun huta muko in tamu tazo Allah yasa mucika da imani```







*M*iƙa yayi cikin kasala da jin bacci murya can ƙasa yace,
"Washhh Ummu na bacci nakeji,
kuma begen ki ya hanani baccin,
gashi ina jin sanyi".
shiru tayi bata amsa mai ba a ranta kuwa mamaki ya Usman ɗin yake bata shi kuwa iska ya furzar a hankali sannan yaci gaba da cewa,
"Inama an daura mana aure Ummu na in samu d'umin jikin ki".
shiru tayi batace komai ba saidai cike take da kunya,
shi kuwa lumshe ido yayi yaci gaba da cewa, "Laisa liyal'huzni inkunti ma'ee=in kina tare dani bani shiga kunci, amma yanzu narasa yadda zanyi".
Dakaji yanda yake magana kasan bacci ke damunshi sai faman mik'a yake da hammah yana magana cikin shogoɓa yana maƙale da woyar yaci gaba,
"Uhhmmmm wash bacci nakeji Ummuna kuma begenki ya hanani lumshe ido".
A hankali ta buɗe baki cikin sanyi ta huramai iska a kunnen shi sannan cikin rad'a tace, "yanzu ina kake?".
ldo ya lumshe sannan cikin shogob'a yace,
"ina palour".
Murmushi ta ɗanyi jin yadda yake magana sannan a hankali tace,
"To tashi ka koma bedroom ka konta a hankali saika lumshe idonka".
Tashi kawai yayi yanufi bedroom ɗin yana shiga ya kwanta kan gadon ya lumshe ido a hankali ya furta,
"Nayi yadda kikace ɗin". Ɗan murmushi takuma yi shogob'ar shinna tana bata mamaki a hankali cikin raɗa tace,
"Gani a gefenka, ga hannuna ka riƙe". Hannu yasa ya damk'e filon da yake kai a hankali yafurta, "Shhhhmm Ummuna Insha Allah sana iyshu ma'aki ma'a habbah=insha Allah zan rayu dake tare da soyayya".
jin haka yasa tafara sauke numfa shi tana murmushi tana kuma hura mai iska a kunnenshi a haka yafara bacci ita kuwa taci gaba,
"Kayi bacci cikin nutsuwa hannuna na riƙe da naka kanka yana cinyata hannuna ɗaya na yawo a cikin suman kayin ka zuwa kunnen ka, ina son kayi bacci kar ya saka ciwon kai".
Shirun dataji dakuma jiyo saukar numfashin shi a hankali yasa ta kira shi ta tabbatar da yayi bacci dan jin bai amsa kiran da tayi mai ɗinba,
haka yasa ta katse wayar ta konta cike da tunani har bacci ya d'auketa.


Gari na k'arasa wayewa Ammi tazo ta tasheta dan tayi break saida tayi wonka tai kwalliya sannan taje tagaida Nanne,
bayan sun gaisa tace,
"Ga abincin Usman can ki ɗauka ki kai mishi".
Amsawa tayi sannan tajuya ta je ta had'a mai komai akan tire ta ɗauka ta fita hannun ta riƙe da hannun Faruq.


A ɓangaren Usman ma yana tashi yashige yayi wanka ya shirya tsaf ya feshe jikin shi da turaren hugo mai ƙamshi yana fitowa palour kunnuwan shi suka jiyemai abinda yafi son ji,
Sallamar da tayi ya amsa sannan ya buɗe hannuwan shi ya ɗan tsuguno da fara a fuskar shi yace,
"come on Daddy boy".
da gudu Farouq yaje ya faɗa jikin shi shima yamaida hannun shi ya rufe sannan ya ɗagashi sama yana kissing ɗinshi tako ina cikin ƙauna shima yayi kiss ɗin shi a kumatun shi cikin gwaranci shi yace,
"Ana Ubbuka Abee". Dariya yayi yana saukeshi ƙasa yasa hannu yana lakace mai hanci yace,
"Ana hubbuka ya bunayya".
Wucesu yayi yaje ya haye kujera yaɗau remote d'in tv yafara wasa.
Shi kuwa dawo da kallon shi yayi kan Ummul dake kokarin ajiye tiren a tsakar palour ya zuba mata manyan idanun shi, tana ajiyewa tasami guri a ƙasan a tsakiyar carpet tazauna sannan ta kalleshi ta ɗanyi murmushi yadda taga ya ƙure ta da ido dakai tamai alamar yazo ya zauna,
aiko kamar rakumi da akala yataho da hannu ta nunamai inda zai zauna,
saida tasa hannu taɗau flate tafara zubamai abincin sannan ta ɗan kalleshi cikin sanyin murya tace,
"katashi lafiya?".
Shima lumshe idanu yayi sannan ya buɗesu ya namata wani irin kallo murya can ƙasa yace, "Inafa lafiya Ummu na bayan a baccin ma zuwa kikayi,
kikayita jagolgoleni duk kin turmusheni kin sani cikin wani yana yin".
ya ƙarishe maganar yana kashe mata ido ɗaya da ɗan ɗaga mata girar sa,
kunya sosai maganar shin ta sakar mata sunkuyar dakai tayi ta ajemai abincin da tea data haɗa mai a gaban shi tace,
"Kacinye duka sai in baka kyauta".
Ɗan ɗago kai yayi yace,
"kefa?". kai kawai ta girgizamai alamar a a,
kallon ta yayi cikin tsigar so da ƙauna yasa hannu ya ɗauko ɗaya cup ɗin ya haɗa tea mai kauri sannan ya ɗan kurb'a cup ɗin ya miƙa mata a hankali yafurta,
"Ki shanye ba zafi sosai".
karɓa tayi tana kallon idon shi shiko lips d'inta da suka sha jambaki sai shek'i suke ya kurawa ido a hankali yace,
"Wannan janbakin dada hali zan tsotse shi dan ya rufemin pink lips d'inkin nan masu kyawun gani".
Baki ta ɗan tsuke tana ɗan yimishi kallon ƙasa-ƙasa bai jira tayi magana ba yace,
"l'ilam uhibbuki hubban azeem=kisani ina sonki so na hak'ik'a, bansan wanne irin murna zan yiba idan aka ɗaura mana aure,
bansan wsnne iri so nake mikiba Ummu na, Anti faƙat fee hayatee=kekad'aice a rayuwata".
Ɗan ɗago kai tayi tace,
"Kamar cewa nayi kaci abinci ko?
sannan ka tsaya surutu nikuma nafiso inga ka kaci abincin sannan kasha maganin ka".
Karya wuya ya ɗanyi cikin wani sabon salon shauƙi yace,
"Aaahhhh hubby zanci amma kinga wannan kallon? hmmmm". sai kuma ya haɗiye maganar da yayi niyar furtawan
sannan yaja flate d'in yafara cin abincin cikin nutsuwa,
Farouq daketa tsalle kan kujera ne ya sub'uce kamar zai fad'o dasauri suka tashi dukkan su sukayi gunshi hannu kowanne yakai dan riƙoshi aiko hannunsu ya haɗe wuri guda gun ɗaukan Farouq ɗin,
Shiko Usman haɗe hannun ta dana Farouq ɗin yayi ya riƙe ya na murzawa a hankali itako ƙasa tayi da kanta,
sun daɗe a haka sannnan suka koma suka zauna ya k'arasa cin abincin,
itako ta tattare kayan ta ɗauka suka fita tare,
suna fita suka haggo Dr. Bashir yafito daga motar shi,
Cikin gida Ummul ta shige b'angaren Nanne shikuma Usman ya k'arasa gurinshi riƙe da hannun Farouq,
suka gaisa ya tsuguna yakamo hannun Farouq ya ɗaukeshi,
Usman ne yamai jagora har palour baƙi yazauna yana wasa da Farouq shikuma ya juyo yafito yana fitowa yaci karo da Abba na shirin shiga palour ɗan russunawa yayi yace, "sannu da fitowa Abba".
Kallon shi yayi yace,
"Dr na ciki ko?".
"eh".
yace sannan yasake cewa,
"To ka jirani a palour Hajjajo zamuje gidan Daddy inna fito".
da "to". ya amsa yawuce parlorn Hajjajon.

Shiko Abba da sallama ya shiga palour suka gaisa cikin girmamawa, a hankali Abba yawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login