Showing 132001 words to 134562 words out of 134562 words

Chapter 45 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

Daddy ko?". Tana ɗaga kai tace,
"Abokin Farouq nagane shi ai yana yawan zuwa gun Farouq yana son Farouq sosai ko yaushe sai yazo ya daukeshi wani lokacin ma in Farouq na kuka sai kaga shima yana kuka,
in Ammi na mai fad'a ya dena kuka,
sai yace yana tausayawa Farouq ne".

Ajiyar zuciya Usman yayi yasa hannu ya shafa kanta sannan yace,
"Kinsan yana universty maiduguri, to ɗazu Sadiq ya kirani inagun aiki yake cemin ɗazu yaga yaron yake tambayar shi baije registration ba yaga tare suke tafiya da Aliyu,
shine yake cemai daman Hamma Umar ne ya samar masa admission ɗin kuma shine yake biyamai kuɗin dan haka yanzu ya hak'ura saboda mahaifin shi bashi da k'arfi bazai iya biya maiba shikuma baya aikin komai balle yaci gaba da d'aukar nauyin karatun shi da kanshi".

Shiru sukayi dukkansu naɗan lokaci sannan yaci gaba da cewa,
"Ummu kinga Hamma baitaɓa faɗamin yana wannan aikin alkhairin ba,
yayi tsakanin shida mahaliccin sa,
dan haka shine nace Sadiq yacewa Adam yamai komai gobe ya tafi makaranta".
Sai lokacin tasa hannu cikin dabara ta goge k'ollah daya zubo mata ta tana daga kwance jikin shi tace,
"Ya Usman nima Hamma Umar bai taɓa faɗamin ba saidai ina mamakin yanda Garba yakeson Faruoq kuma kullum sai yaje gun shi ya ɗauke shi, amma dan Allah inaso kaimin wata alfarma".
ido ya lumshe tare da manna hancinshi kan nata yace,
"Kinfi k'arfin komai a gurina Hubby".
Kissing k'irjin shi tayi tace,
"Dan Allah kabarni in k'arasa aikin da Hamma na ya fara, kubarni inci gaba da biyawa Garba komai na karatun shi".
ta k'arashe maganar murya na rawa,
gyara kwanciyar shi yayi itama ya gyarata ya kwantar da ita sosai a k'irjin shi yasa hannu ya rungumeta a hankali kamar me raɗa yace,
"To daman ai yanzuma ke kikayi,
kinsan kece Hammana kuma kece ni,
nikuma yanzu komai nawa kece kuma nakine".
hannu yasa yana shafo k'irjinta yana lumshe ido yanason kawar da maganar dan kar Ummul ta fara tunani da kuka a cikin rad'a yace,
"Irin wannan kayan gara da daɗi da kike bani ai dole komai nawa ya kasance naki".
Dukan k'irjin shi tayi sannan ta rungume shi tana dariya,
Dama abinda yakeso kenan ya ganta cikin Happy dan haka ya lumshe ido yaja bargo ya rufesu,
hannu tasa a hankali tafara wasa da kan niples ɗinshi tana ɗan murzasu tare da sauk'e mai kasala,
kamar a mintsine shi ya d'anyi zillo yasa hannu ya rik'e hannunta murya can k'asa yace,

"kwaɗayyeyiya kawai".

d'ago kanta tayi taga yayi kamar bashi yayi maganarba ya tsareta da idanu shogoɓe fuska tayi tana murza k'afafuwan tana ɗan dukan k'irjin shi da hannun ta gaba ɗaya ta rikita shi ta tasomai da fitinar daya kwantar mintina kaɗan dasuka wuce dakyar yasa hannu ya matsota jikin shi murya na rawa yace,
"To wai menayi Kuma?".
bata dena abinda taken ba tace,
"bakai bane kacemin kwaɗayeyyiya ba". dariya yayi mai sauti sannan yace,
"Ke bakiji maganar a dai-dai bane kwaɗayeyye nace fa,
aidai kinsan indai zaki taɓamin niples ɗina to kwaɗayina saiya tashi koda yanzunnan na kaudashi,
to da kika taɓa nefa sai naji abin na motsi shine nacemai kwaɗayeyye, ni badake nakeba nine makwad'aicin".
Yana gama faɗar haka ya janyota ya tusa hannun shi a k'irjinta nan da nan tabada kai bori yahau suka koma aikin da basufi awa biyu da gamawaba.

Haka rayuwa taita tafiya Usman na ririta matar shi da babyn cikinta yana bata kulawa ta musamman hakan yasa hankalinta yafara kwanciya wanda har takan iya wuni guda batare da tayi kukaba.

Watanni ukun da zaiyi suka ciki dan haka sukai shiri komawa gida Nigeria cikin aminci da d'an cikin ta da ya fara girma.

A gida kuwa kowa na murnar dawowarsu Abba da Daddy kuwa tuni sun k'awatar masu da gidansu dake kusa da gidansu komai yakammalu kowa na farin cikin dawowarsu musamman Ammi da tayi kyewar y'arta da shogoɓarta Hajjajo da Inna ma sai Happy suke da d'okin ganin jikokin nasu,
Adam da Sadiq ne suka ɗaukosu daga Abuja kai tsaye gida suka kawosu inda auka tarar da duk familyn su na nan suna jiran isowarsu,
Kowa yaji daɗin ganin yanda Ummul ta gyaru tayi kyau tak'ara cika ga haske da shek'in da fatarta keyi ga d'an cinkin ta ya taso,
Usman kuwa yana manne da Farouq dayaketa zubamai surutu cikin gwaranci sa,
shiko Usman yanayi yana satar kallon matar shi yana k'arajin k'aunarta na ratsa duk jikin shi.
Haka suka wuni cikin y'an uwa anata raha da hira.

K'arfe tara na dare Ammi ta tashi Ummul data fara bacci a palour tace ta koma bedroom ta kwanta badan Usman yasoba shima yaje ya kwana ɗakin Adam amma yakasa bacci sai juyi yake yana missing matar shi.

Washe gari diTun bayan sallah asuba malamai suka fara karatu dan sauk'e qur'ani a gidan Usman dake kusa da gidansu domin neman kariya dakuma samun albarka a gidan, basu wuce 12pm ba suka kammala akayi addu'o'i. Sai bayan sallah isha'i sannan Ammi da Hajjajo da Aunty Halima sai Anty Aysha Garkuwa suka raka Ummul gidanta.

Satinsu guda da dawowa aka shirya bikin buɗe makarantar da suka assasa kafin su tafi mai suna
*Dr Umar Faruq learners academy* dake tudun wada layout daura da masallacin juma'a na jibwis k'ark'ashin kulawar k'ungiyar Fityanul Islam ta jaha reshen k'aramar hukumar potiskum. bikin yasami
halartar manya daga ma'aikatar ilimi ta jaha dakuma wakilan sarakunan Potiskum da fika,
yaran dake sanye da farar riga da dark blue wando dogo sai farar hula sunyi kyau matuk'a ciki harda *Umar Farouq Umar Shuwa* Makarantar zata koyar da yara duka ɓangare biyu wato boko da arabic a farashi mai sauk'i a duk k'arshen zango na karatu,
Anyi taro an watse lafiya da fatan Allah ya yiwa makarantar albarka.

Haka rayu take tafiya Usman na kulawa da Matar shi da d'anshi dakuma cikin Ummul daya girma,
Shiko Faruq yazama mai gida Uku gidan Abba ga gidan Daddy dakuma gidan Abeenshi Usman.

Yau lahadi wanda ya kasance ana cikin bikin auren Rukayyat da Nuru abokin Usman kuma yaune aka gama shagalin bikin bayan abokai sun reko aggo Nuru sun gama komai sannan Usman ya d'auki Ummul enshi suka nufi gidan su,
Suna isa Ummul ta wuce dakinta Wonka tayi cikin jin gajiya ta zauna gaban dressing mirror tana murje jikin ta da turaruka masu k'amshi tana kallon cikin ta da ya fara motsi a y'an k'wanakin nan ajiyan zuciya tayi tare da yin murmushi tana,
"barka na yau da Farouq yana guna da bazai barni na hutaba da surutun shi".
tana d'aure igiyar rigar baccin ta taji woyarta na suwa,
saida ta gama kimtsawa sannan ta dauki woyar ganin ya Usman ta dan karya wuya ta amsa kiran,
"Ummuna ina kikene kin barni ni d'aya".
a hankali tace,
"Gani nan zuwa Hamma Usman na".
tana fad'in haka ta katse kiran sannan ta fita ta nufi parlour shi,
zaune ta sameshi kan kujera yana ganin ta ya nuna mata cinyarshi alamar tazo ta zauna
ba musu ta matso gareshi ta zauna kan cinyarshi suna fuskantar juna,
hannun shi yasa yana zare igiyar rigar baccin nata,
kamo hannun tayi sannan ta tallabo kanshi bakinta ta manna kan nashi tamai wani irin zazzafan kiss sannan tasa hannun ta wore rigar tata cikin lumshe ido ta jawo kanshi ta cusa a tsakiyar k'irjin ta yayinda tasa yatsunta kuma cikin sumar kanshi tana mai wani salon romancing mai rud'a tunani,
gaba d'aya ta gigitashi sai juya kanshi yake a k'irjinta duk ta inda yaga dama hannun shi kuwa na shafa cikin ta da ker ya budi baki a hankali yace,
"Um....! Umm...! Ummu na Allah ya miki albarka kin gama min komai a rayuwa ta tunda kike samamin farin ciki".
Kai ta d'an d'ago ido cike da k'ollah tace,
"Hamma Usman dole na gyara yanzu na tunda na b'ata bayana nayi kuskure a baya bana fatan kuma maimaita kuren da nayi danko gashi har gobe ina dana sani,
ya Usman da nayi biyeyye yadda *'YAR FULANI* tayiwa bappan ta biyeyyah da na tabbata bazanyi dana saniba amman da nak'i yiwa iyayenmu biyeyya yanzu *MI WASMITI*
*NAYI NADAMA*
mai tarin yawa naga illar bijirewa zabin iyaye
tabbas na yarda *NAMIJI BAYA KAD'AN* dan naga jarumta da girman shawarar da Aliyu k'anin bayana yayi ta bani a lokacin baya tabbas da nabi shawarar Aliyu da a zaman aurena da Hamma Umar da
*A TAUSAYWA JUNA* yayi tasiri a kanmu amman taurin kai da zugar shaid'an sun hanani tausayawa *BANDIRAWO* na k'iyeyya tasa na manta cewa Hamma Umar fa *BANDIRAWO* nane na kasa yarda k'addarata ashe a hankali
*RUBUTACCEN AL,AMARI* na bibiyar rayuwata,
Hamma Usman kalli yadda *rubutaccen al, amari*
da k'addara yadda suka had'amu aure Hamma Usman ina son Hamma Umar ina mai addu'a aduk wani motsina da numfashina *Hamma Usman ina sonka*".
Murmushi yayi cikin jin dadi da tarin k'auna ya rugumota yana murza k'irjin ta murya can k'asa yace,
*"ALLAH YA D'AIYIBA*

*Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah*
Na godewa Mahaliccina daya bani rai da lafiya da damar rubuta wannan littafin daga forko har zuwa k'arshe inda na tubk'e bakin zaren labarin Alhamdulillah

Abinda nayi dai-dai Allah ya taramu a kan ladan abinda nayi kuskure bisa ajizanci na d'an Adam Allah ya gafarta min.

Masoya na ina alfahari daku zanyi kewarku zakuyi kewata dan ina son hutawa sosai kafin na faro sabon novel na watakil mai suna *FULB'E Nigeria* ba mamaki kuma na canza sunan,

Godiya mai tarin yawa agareku masoyan Hamma Umar tabbas kunsa zuriyar Shuwa farin ciki da addu'oin da kukayiwa dansu Usman yace a mik'a godiyarsa gareku

*Afwan Afwan Afwan ina mai neman gafararku mace ko namiji Babba ko yaro na kusa dana nesa wanda nasani da wanda ban saniba wanda muka tab'a magana da wanda bamu tab'a magana ba wala Allah ko akwai wani abu da ya bata muku rai a cikin labarin ga dan haka ina mai neman yafiyar duk wanda na sosawa rai a zahiri banyi komai da nufin batawa kowaba Ina fatan samun yafiya daga ko wanne sashi ku yafe min tun ina raye inko na nabar duniya masoyana Addu'arku nake buk'ata ni na yafewa kowa*

Moh Allah wuji furd'ata
Fullo be fulaku Moh Allah saini sunata
Moh Allah hokki b'uri moh baba hokki

*By*
*GARKUWAR FULANI🐄🐪🐫 Fauziyya Fiji ga salon mu🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😆😂😘😘😍🤝😂😆😆*

*Bissalam*


Copied By

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.

















Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login