Showing 48001 words to 51000 words out of 134562 words

Chapter 17 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

tab'ani."
Jin haka ta fizgota leimar ta cillata gefe haka ko iska ya debeta yayi woje da ita,
shi kuwa da sauri ya d'ago hular rigar shi da take konce a kafad'an shi ya rufe tsakiyar kanshi dan in ruwan sama ya bugi kanshi yana sashi zazzab'i da ciwon kai mai tsananin,
hannun shi kuwa ya hard'e a k'irjin shi tuni ya jik'e cikin rawan sanyi da karkarwa ya jawota jikin shi a hankali yace.
"Toh aikin rama mu tafi cikin gida kiyi hak'uri k'anwata."
cikin kuka tace.
"Ban rama ba kam,
kuma bazan shiga gidan kaba sai in zan rama marin da kayi min."
murya na rawan sanyi yace.
"Na yarda mu shiga saiki rama."
baki ta tura sannan tace "toh."
hannun ta yaja suka shiga cikin gidan ,
suna shiga d'akin ta ya nufa da ita,
a gaban mirror ya tsaya da ita,
cikin rawan sanyi ya cire mata mayafin nata sannan ya zuge zip d'in rigar ta yasa hannu zai cire mata rigar tayi maza a juya tana hararan shi tana cewa.
"Ka barni in cire abina da kaina ."
"Na barki nima bari inje in cire nawa."
sai kuma ya bud'e durowa ya zaro mata riga da wondo wondon iya guiwa sai rigar mai d'an fad'in wuya ta yadda kafad'an ta yake fita inya ta saka kayane mai tashi da sulbi,
kan gado ya ajiye mata sannan ya fita ya koma bedroom d'in shi,
yana shiga ya canza kayan shi sannan ya fito ya nufi kitchen tea ya dafa musu mai zafi wai maganin sanyin,
d'akin shi ya koma da niyar d'auko woyarshi yana rik'e da cups d'in yana juyowa da nufin zai fita kenan ya ganta tsaye a bak'in k'ofar shigowan fuska a had'e tace.
"Zan rama fa ehe."
Ido ya tsura mata cikin mamaki ajiye cups d'in yayi kan mirror sannan ya juyo a hankali yace.
"Toh zoki rama."
shigo wa tayi ta tsaya a gaban shi ta d'an d'ago kanta tana kallon fuskar shi,
shi kuwa kollon d'an tsawonta yake tunda ko fuskarsa in zata kalla sai ta daga wuya da kai,
kuma wai shine tana ikirarin tazo ta rama marin daya mata,
cikin ranshi kuwa jira yake yaga iya rashin kunyarta zata mareshin neko k'ak'a,
ganin tana ta d'ago wuya da k'afafun ta dan ta isoshi tsawo ta kasa,
sai ya d'an rok'ofo kanshi ya sunkuyar dai-dai tsawonta cikin rumtse ido yace.
"Rama."
fuskar shi ta tsurawa ido ta d'ago hannun zata yarfa mai marin sai kuma tayi maza tayi k'asa da hannun sai hawaye car-car a idanun ta,
shi kuwa jin shirun ne sai ya bud'e idanun shi ganin tana kallon fuskar shi tana kuka yasa ya d'an yi murmushi cikin kula ya jawota jikin shi ya ruggume ta kanshi ya sunkuyar dai-dai kan hab'arta daya maran a hankali ya rink'a fese mata iskan bak'in shi mai sanyi sannan yasa tafin hannun shi yana share mata k'ollah,
ita kuwa cikin kuka tace.
"Ni dai sai na rama amman ba, a fuskar kaba."
murmushi yayi a ranshi yace.
"Gaskiyar bahaushe wata fuskar tafi k'arfin mari."
fahimtar da yayi bazata iya ramawan bane,
sai ya mik'o mata cup d'in tea shima ya d'auki d'ayan ya fara sha yana lumshe ido cikin lallashi yace.
"Kisha tea sai na goyeki a madadin marin."
ajiye cup d'in tayi tace ita bazata shaba kuma shima ya ajiye sai ya goye tan,
murmushi yayi ya ajiye cup d'in yana jin sanyi na ratsashi,
tsakiyar d'akin ya dawo kan carpet ya durk'usa ya mik'e tsawonshi kamar mai konciya sai kuma ya d'an taso ya k'afa hannun shi a k'asa sannan ya mik'e tsawonshi ,
cikin sanyi yace.
"Toh zoki hau."
murmushi mugunta tayi dan tanaga bazai iya d'aukar nauyin taba,
da sauri ta matso ta zauna a tsakiyar bayan shi sannan ta tonk'oshe k'afafun ta ta d'an ware hannun ta sannan ta had'a yatsun ta haka👌🏻 tana ta murmushi mugunta ,
dai-dai lokacin woyarshi ta rink'a suwa ita kuwa sai gyad'a kai take tana lumshe ido,
yana kallon ta duk abin da takeyi,
a haka har
zuwa wani d'an lokaci sannan ya manna jikin shi kan carpet d'in ya kwanta yana maida numfashi,
itako murmushi tayi sannan ta mik'e zata tafi,
sai ya rik'o hannun ta ya fizgota jikin shi ya matseta gam cikin maida numfashi yace.
"An gaya miki ni dokine da zan goyeki a banza,
nima saina samu maganin sanyin da kika samin."
Baki ta tura tace.
"Toh ai ba ladan mari bane,
kuma ni bani da
maganin sanyi."

"Kina dashi mana."

"Toh ina yake?."
hanun shi ya cusa cikin jikin ta tare da lumshe ido yace.
"D'umin jikin kine kawai zai cire min wannan sanyin inba hakaba zai sani zazzab'i."
tureshi tayi ta mik'e sai kuma ta d'an yi k'ara jin yadda yake murza hannun shi a kan k'irjin ta,
murmushi yayi ya mik'a hannun kan gado ya jawo blanket sannan ya jawota jikin shi kan carpet d'in ya kuma rufesu da blanket d'in,
hannun shi yasa yana shafa cikin ta a hankali yace.
"Ina son Baby daga gareni Khairi kiyi Addu'a Allah yasa yau nayi ajiya a nan."
tureshi takeyi shiko sai murzata yakeyi a hankali yace.
"Kiyi hak'uri in kasance dake."
Cikin fad'a tace.
"Bana so."
da sauri yace.
"Karya ne kina so kam."
hawaye ta fara zubdawa tana jin yadda yake murzata da juyata,
ita kuwa,
tureshi take d'an yi duk da yau yana binta a hankali ba zafi sosai,
amman sai kuka takeyi cikin raki tana cewa.
"Bana sonka na tsaneka."
duk da yana cikin duniyar nitsuwa Amman yaji zafin kalamta gare shi,
a ranshi yake fad'in.
"Ko cikin yanayin da ma'aurata suke ruggume juna dayin musayan kalaman soyayya shi a cikin yanayin ma Ummul tureshi take a madadin ta mak'ale shi sannan kalaman k'iyeyya take fad'a mishi a madadin na soyayya kuma kuka take na jin tsanarshi a madadin tayi kukan gamsuwa,
haka ya zame jikin shi ya konta gefe sannan ya jawota ya ruggume ta da k'arfi yana fidda nannauyan numfashin a hankali yace.
" wata rana zaki soni Khairi ,
fatana Allah yasa jinin na ya gauraye da naki,
ki haifarmin d'ana nasan shi kam zai soni."
manne wa tayi a jikin shi dan ya gajiyar da ita ga kasala daya k'ara rufeta numfashi ta rink'a maidawa a hankali,
cikin ranta kuwa fad'i take.
"Tabbas in nayi garaje Hamma Umar zai d'irka min ciki ya barni da matsala."
a haka da wannan tunanin tayi bacci a jikin shi,
shi kuwa ruggume ta yayi har saida yaji baccin ta yayi nisa sannan ya mai data kan gado shi kuma ya gyara wurin yaje yayi wonka yayi al'wala yazo yayi ta nafilfilin daya saba da karatu qura'an,
sai k'arfe 2:30 ya konta ruggume da ita.

Washe gari da safe bayan ya gaba komai ya shirya ya fita,
yana fita itama ta fita kai tsaye kemis na bayan layinsu taje k'wayoyin family planning ta seyo tazo ta boye wanda kullum sai tasha,
acewarta bazata haihu dashiba in yana son haihuwa ya saketa ya auro wata.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum sai tasha maganin a boye duk da ba wani bashi kanta takeyi ba,
bayan ta fara shan maganin da kwana goma kawai ranan ya shiga ya samu tasha maganin kenan tana rik'e da sachet d'in,
sosai Ummul taji tsoro da mamakin yadda Hamma Umar d'in ya birkice mata tamkar zaiyi hauka bata tab'a ganin baccin ranshi kamar na wannan ranar ba,
ya rink'a surface mata fad'a daga karshe ya kwashesu yace zai kai ya nunawa Abba ,
ganin haka tayi ta kuka tana bashi hak'uri tare da cewa bazata sake shaba,
ganin yadda ta nuna bazata kuma ba yaji dad'i ya yarda ya barta bayan yayi ta mata nasiha.

Toh fa bayan sunyi haka da kwana biyu ta lallab'a taje wani prvt hospital ta shirga k'ariyar ta kan cewa da yardar mijin ta suko tunda aikin kud'i ne ba wani dogon bincike suka sa mata y'ar robarnan da ake tsawa a hannu suka d'inke mata,
suka amshi kud'insu ko a jikin su,
koda ta dawo haka tayi ta wasan b'uya da Hamma Umar d'in har saida wurin d'inkin ya worke ras ta yadda bazai ganeba,
shi kuwa kullum addu'ar shi Allah ya bawa Ummul d'in ciki yanaga duk abin nata zai ragu inta fara haihuwa dashi.


Yau Saturday tun safe Hamma Umar baije ko inaba yana gida ko parlour bai fitoba yana d'akin shi ,
dan ya fara gajiya da azabtar dashi da Ummul keyi,
ita kuwa Ummul tun safe ta shirya a nufinta in taga ya fito zai tafi potaskum zatace zata bishi,
ganin shiru-shiru bai fito bane har bayan sallan la'asar saita fito a hankali ta nufi d'akin nashi,
a hankali tayi sallama tare da tura k'ofar ta shiga,
kan gadon ta hoggoshi yana kwance yayi rigingine ida nunshi a lumshe ba komai a jikin shi sai towel dake d'aure a k'ugunshi alamun daga wonka ya fito,
shiru bai amsa sallamar taba,
shigowa tayi cikin d'aga k'afafun ta a hankali bak'in gadon taje ta tsaya tana son ta tasheshi ta rasa ya zatayi ta tasheshin gashi gaba d'aya ganin surar jikin shi na bata tsoro,
a hankali ta durk'usa a bakin gadon cikin kauda fuska ta fara magana.
"Hamma! Hamma! Hamma ka tashi mana."
yana jinta yayi shiru kamar maiyin bacci a ranshi kuwa farin ciki yake da shigowar ta d'akin nashi,
ita kuwa tashi tayi ta zauna gefen shi a bakin gadon a hankali tace.
"Hamma yau bazaki je gida bane? Hama weekand d'in ma baza'a fitaba ni ina son zuwa inga Nenne na."
murmushi ya d'an yi gano yawo take son fita shiyasa take wani yin ladabin kura ga mai akuya,
mik'a yayi a hankali sannan yasa hannu ya jawota kan k'irjin shi hannun shi yasa ya rink'a shafa bayan ta a hankali yace.
"Zamuje mana in kina so."
Mutsumutsu ta rink'a yi cikin had'e fuska tace.
"Ehh ina so mana ka tashi mu tafi."
towel d'in nashi ya rink'a murzawa tare da jawo blanket ya rufe su sannan ya k'ara jawota jikin shi a hankali yace.
"Bazan iya tuk'in ba sai an bani maganin."
hannu tasa tana ture hannu shi da yaketa b'alle boturan gaban rigar ta mai dogon hannu wai duk dan ta boye tabon abin family planning d'in ne,
shi kuwa ido a rufe ya zare rigar tata,
sannan ya kuma rink'a shafa wutanta ido a lumshe a hankali har ya isa kan damtsen hannun ta da akasawa robar,
ido ya bud'e jin kamar d'an k'urji a cikin hannun nata gashi da alamun kamar tabo,
da sauri ya tashi zaune cikin hamzari ya d'ago ta ya manna ta a k'irjin shi sannan yasa hannu ya kamo hannun nata ya d'an daga,
da sauri ya tureta cikin wani irin yanayi ya kafa mata.






By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 2⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇






*I*do ya tsura mata yana k'ok'arin k'ara jawo hannun nata,
ita kuwa da sauri ta janye hannun gaba d'aya har jikin ta na rawa sai ta konta a kife ta cusa hannayen nata k'asan k'irjinta ta konta kan hannayen tayi luf tana d'an mai da numfashi,
shi kuwa k'ara matsota yayi cikin yanayin tabbaya yace,
"Khairi me a hannun ki?"
bata kula shiba sai d'an mirgino wa tayi jikin shi cikin yanayin yaudara ta d'an konta kan k'irjin shi hannun tasa ta cusa a bayan shi,
Ido ta lumshe tare dasa hannun tana shafa sajen shi har zuwa kan k'irjin shi tanayi tana lumshe ido,
shi kuwa gaba d'aya ta zuba mishi kasala duk jijiyoyin jikin shi sun mace,
ganin haka sai ta sake konta wa ta juya mishi baya ta kifu,
shi kuwa sunkuyowa yayi ya rink'a kissing na tsakiyar bayan ta yanayi yana murzata gaba d'aya ya gigice ya gigitata a haka ya samu abinda yafi kwana 12 bai samuba,
ita kuwa abinda ta saba fad'a mai shi take furta mai,
"Bana sonka ni na tsaneka".
hakan ya tunzura shi ya murzata har saida yaji ya huce ya kuma gamsu,
sannan ya juya mata baya cikin maida numfashi yace,
" Sai ki nemo wanda kike son yazo ya kaiki gidan ko".
rai a b'ace ta jawo blanket d'in ta hard'eshi a jikin ta ta mik'e tana jan shi tana,
"Sai Allah ya saka min tunda saida kayi tayin pakala iya son ranka sannan yanzu kace bazaka kaini ba".
tana fad'in haka tana k'ok'arin fita d'akin,
shi kuwa har cikin ranshi yake jin dad'i dan ya samu gamsuwa da ita kuma ta d'an sake mishi,
abinda bai saniba boye laifinta take sonyi,
itako har taje bakin k'ofar fita tace,
" Ni kuwa bazan sake zuwa d'akin nan ba kuma mutun ko yazo min d'aki rufewa zanyi".
Murmushi kawai yayi ya bita da ido,
dan sakarcin Ummul yarin tane a ciki,
ba gashi yanzu buk'atar tace ta kawota ba har ya samu shima tasa buk'atar ta biya so yasan gaban ma hakane.


Haka rayuwa tayi ta tafiya,
Usman kuwa a gefen shi ciwo ba sauk'i kullum sai gaba gaba yakeyi.

Yau Saturday tun safe Usman bai lek'a ko k'ofar parlour suba,
Nenne kuwa gaba d'aya hankalin ta na kanshi ganin har bayan la'asar bai shigo ba yasa ta mik'e ta nufi part d'in nasu,
a hankali tayi sallama,
shiru bai amsa ba dan yana zaune a k'asa a bak'in gado ya kifa kanshi a jikin gadon yana kuka mai cushe numfashi,
a hankali Nenne ta rink'a jin sautin kukan nashi,
tare da tari mai yanayin ciwon zuciya,
a hankali ta shiga cikin d'akin kai tsaye bakin gadon taje ta zauna cikin sanyi tasa hannun ta tadafa kanshi,
da sauri ya d'ago kanshi yana goge k'ollah dake bin fuskar shi,
cikin k'arfin hali yayi murmushi ,
ido ta zuba mai cikin tuhuma tace,
"Usman a zaton ka bansan meke damun ka bako?"
kai ya jinjina tare da yin murmushi yace,
"Nenne bani da matsalar komai".
ido ta sake tsura mishi sannan tace,
" Ummul ce matsalar ai".
cikin sauri ya rink'a juya kai yana jin kunya na ratsashi ya za'ayi ya k'asa control d'in k'aunar Ummul a ranshi har mutane su gane yana son matar d'an uwanshi,
ita kuwa Nenne kafad'an shi ta dafa a hankali tace,
"Ban tab'a zaton shak'uwar ka da Ummul ya zama so a tsaka nin kuba har aka d'aura auren Ummul da Farouq duk a zaton shak'uwace kawai a tsaka ninku,
Usman na fara Azargin kana son Ummul ne bayan Umar ya tafi da ita gidan shi,
tun lokacin da ka fad'i ka suma na gane akwai abinda kake b'oyewa a ranka,
ban gaskanta hakan ba sai randa kukaje gidan Ummul kuka dawo nanma kai ta aman jini sai kuma randa su Umar d'in suka zo manna ka birkice,
sannan tunda suka tafi baka samu sukuni da kowa ba kuma doctor ya shaida mana akwai abin da kakeso kuma kana b'oyewa,
Usman ni yanzu nasan Ummul kake so".
tunda Nenne ta fara magana yayi shiru yana kallon ta,
saida ta furta "Ummul kake so".
sai ya kife kanshi kan cinyarta ya saki wani irin kuka murya a hargitse ya rik'o hannun ta ya rink'a juya mata kai a birkice yace,
" Asiri na ya tonu naji kunya har gaban Ubangiji na tunda matar aure zuciya ta ke so ina zankai wannan zunubin? naji kunya a idanun duniya na rasa wacce zanso sai matar d'an uwana shak'ik'ina wanda bayi da b'uri a duniya daya wuce farin ciki na".
sai kuma ya kuma kife kai yayi ta kuka mai tarin firgici cikin rawan murya ya durk'usa gaban Nenne a hankali yace,
"Nenne ki rufa min asiri ki tayani b'oye wannan sirrin nawa kodako zai zama ajalina dan Allah karki gayawa ko daga ni sai ke ".
itama Nenne kuka takeyi sosai dan Usman ya zama abin tausayi,
a hankali tace,
" kana ganin a haka zakaci gaba da boye abin a ranka ne?"
Kai ya jinjina a hankali yace,
"Nenne taima kona zakiyi kisa baki Abba da Hamma Umar su barni intafi India inbar k'asar gaba d'aya na tabbatar zan samu sauk'in abin a raina in nayi nesa da Ummul".
kallon shi tayi a hankali tace,
in dai haka zai sama maka sauk'i toh ba matsala".

Haka kuwa akayi Nenne ta ajiye Hamma Umar da Abba tayi ta rokawa Usman d'in a barshi ya tafi ai yace ya samu lafiya kuma daga can zai k'ara ganin doctor,
shi kam Hamma Umar har cikin ransa baya son tafiyar da d'an uwanshi zaiyi amman Abba da Daddy sun yarda dole shima ya yarda,
shi kuwa Usman ya fara shirin tafiya cikin happy da kewar d'an uwanshi da Ammin su abar k'aunar su ji yake kamar ya fasa tafiyar dan gani yake kamar shike nan ya rabu dasu kenan har abadan,
haka dai ya d'aure ya tafi.


Gidan Alhaji Bello kuwa mahaifin Mustapha gaba d'aya rayuwar Mustapha ta juya ta canza Mustapha ya zama abin tausayi dan tabbas har cikin ransa yake son Ummul mahaifin shi kuwa ganin ya rasa Ummul d'in ne yasa yace zai had'a shi da y'ar k'anwar shi,
yau tun safe aketa fama da Mustapha iyayen shi sun sashi a gaba kan batun auren amman sai ya d'ago ya kallesu fuska cike da k'ollah yace,
" Daddy ni ba zanyi aure ba Daddy dan Allah kuyi hak'uri ni bana son auren ,bazan iya auren bafa".
Ido Daddyn ya zuba mishi cikin sanyi yace,
"Mustapha shin kana fushi da hukuncin Ubangiji ne? ya za'ayi kace bazaki yi aure ba bayan kuma kana da damar yin auren ashe dan ka rasa Ummul bazaka so y'ar uwarka Amina ba shin ko zakaci gaba da son matar aure?"
kai ya rink'a juyawa yana zubda k'ollah yace,
"Daddy bana son Amina kona aureta bazata ji dad'in zama da niba Daddy bana son cutar da ita".
Mahaifiyar shi ce ta kalleshi cikin tausayawa tace,
" Mustapha wata rana zaka so Amina na kuma tabbata zatayi ma biyayya tunda dama ita tana sonka kuma indai mun isa da kai toh ka aminci da auren nan".
a hankali ya mik'e cikin rawan murya yace,
"Shike nan Daddy na aminci indai hakan zai saku farin ciki".
murmushi Daddy yayi cikin jin dad'i sannan suka bishi da Addu'a,
shi kuwa yana fita d'akin shi ya nufa a parlour ya konta a k'asa yayi shiru yana tuno irin shirin da yakeyi na auren Ummul kawai sai ya rink'a kuka yana istgifari dan tuno cewa Ummul fa yanzu matar aure ce,
haka akayi ta shirin auren Mustapha da Amina..



Gidan Hamma Umar kuwa tun randa Ummul taje d'akin Hamma Umar d'in ya kusance ta daga Wannan ranan ,
rayuwar Ummul ta fara canzawa wani irin abin al'ajabi da tsoro ya rink'a bibiyar Ummul,
tun daga yamma cin wannan ranar Ummul ta farajin hannun ta da akasawa robar family planning d'in yana mata wani irin nauyi sannan sai taji hannun kamar ba a jikinta yaje ba gaba d'aya sai zuciyar ta ta rink'a tsinke wa wata iriyar kasala ta rink'a rufeta,
a haka a daddafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login