Showing 15001 words to 18000 words out of 134562 words

Chapter 6 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa

sha sannan suka fita a tare Usman ya nufi wurin aikin shi shima Hamma Umar ya nufi cikin damaturu,
kasan cewar ya jumma'ace aikin ba yawa sosai.

11:00 Am kiran Adam ya shiga woyar Hamma Umar d'in,
yana d'agowa yace.
"Adam ya akayi ne?."

"Yauwa Hamma Umar dama Abba ne ya aikoni da masu gyaran labulaye yace a canza labulayen toh munzo kuma baka gida gashi gidan a rufe."

"OK gani nan zuwa yanzu ku jirani kad'an bari in k'arisa aikin dan tare zamu koma cikin potiskum d'in."

"Toh" yace sannan suka koma cikin mota suka zauna.

Jimawa k'adan Hamma Umar d'in ya iso ya bud'e musu gidan nashi suka shiga ,
a take su Abdul suka canza labulayen gidan kab sannan suka kimatsa komai suka shimfid'e carpet masu lau shi da taushi gaba d'aya gidan ya d'auki k'amshin da shek'i ga k'amshin sabon penti ga k'amshin sabbin kayan d'akin ga k'amshin kasan cewar Hamma Umar ma abocin tsabta da k'amshin ne komai yayi ras sai shek'i da k'amshin yake zubawa,
shi kam Hamma Umar yana tunanin me Abba yake shirin yi tunda yasan har yau Ummul bata san da zancen ba haka dai ya bar abin a ranshi tunda shi bashi da yawan magana,
su Abdul na gamawa suka d'auki hanya tare da Hmma Umar..


Suna zuwa gida sallan jumma'a suka tafi,
Bayan an taso masallacin ne Dr Umar ya wuce chemist d'in shi,
Abba kuwa da sauran gida suka dawo,
Itako Ummul zuwa yanzu ciwon cikin ta ya fara tsananta,
tana zaune a parlour Nenne tana d'an juya kai Aliyu ya shigo parlour kallon ta yayi cikin kula yace.
"Sannu Anty Ummul ko inje in kira Hamma Umar ne?."
a d'an wahalce ta harareshi tace.
"Barni in mutun."
Dariyan tsokana yayi sannan yace.
"Kije Abba na kiran ki."

Da sauri ta d'an zaro ido gami da dafe k'irji cikin tsoro tace.
"Ni? da gaske Abba na kirana?."

"Ehh wallahi da gaske ne,
toh menene dan Abba ya kiraki ji yadda kike zaro ido."

"A a wallahi Aliyu Abba baya kirana ko batun makaran ta ne Nenne yake gayawa ta gaya min,
ni dai naji tsoron kiran nan nashi."

"Toh koma dai menene kije maji daga baya."
cewar Aliyu kenan.

A bak'in kofar parlour Abban ta tsaya tare da yin sallama ,
Daddy ne ya amsa tare da cewa .
"Ummul na shigo."

Kai ta sunkuyar cikin jin tsoro ta shiga a hankali can gefen Daddy ta zauna yayin da zuciyarta ke luguje,
a hankali ta gaida su,
sannan tace.
"Abba Aliyu yace kana kirana."

Kallon ta yayi cikin k'aunar y'ar tashi a hankali yace.
'"Ehh ina kiran ki."

Sai kuma duk sukayi shiru,
can dai Abba yayi gyaran murya tare da cewa.
"Ummul ni wayene a gareki?."
Kai ta d'ago cikin k'arin firgici a hankali tace.
"Mahaifina."
Kallon ta ya kumayi sannan yace.
"A duniya bayan mahaifi yarki akwai wanda ya fini sonki?."

Baki na rawa tace.
"A,a babu."

"Na tabbatar kina da sanin cewa shariya ta bani damar zab'a mik'a majin aure ko."

"Ehh."
ta bashi amsa hawaye na bin fuskarta.

Shi kuwa gyaran murya yayi sannan yace .
"Abin da ban saniba ko zaki iya min biyeyya kan zab'in da nayi miki."

Zuwa yanzu kam ta k'asa magana sai kai take gyad'a wa tana wasa da yatsun ta.

Cikin bada umurni Abba yace.
" toh nayi miki miji,
kiyi biyeyya a kanshi ko bana raye shine mijin ki, mahaifiyata da d'an uwana sune shaida,
na bada auren ki ga d'an uwanki Umar Faruoq."

Kalaman Abba sun maida Ummul kurma sun sata wani irin razani da firgici gaba d'aya jikin ta rawa yakeyi bugun zuciyar ta kuma kamar zai b'allo ya fito woje kunya yayi mata wani irin nauyi cikin rawan baki tace.
"Hamma Umar Faruoq?."

Kai Abba ya gyad'a mata tare da cewa.
"Ehh shi d'in dai."

Hannu tasa cikin tsoro ta kama kanta ta bud'e baki zatayi magana Abba ya dakatar da ita cikin tsuke fuska yace.
"Tashi ki tafi bana buk'atar jin komai daga gareni ba shawara bace umurni nane wannan."

Tanaji Abba na cewa tashi Amman ta k'asa ko d'aga yatsarta,
sai da taji ya zuba mata tsawa,
cikin firgici ta mik'e ta fita ,
tana fita kai tsaye part d'in Nenne ta ta nufa ,
tana zuwa a parlour ta samu su Ya Usman su ya Adam ya Sadik da Aliyu kai tsaye cikin bedroom ta shige,
Usman na binta da kallon ganin yadda take a firgice.

Tana zuwa ta zauna gefen Nenne dake kan sallaya cikin wani irin yanayin ta kifa kanta kan k'afafun Nenne cikin cushewar sauti ta saki wani irin galabaicen kuka mai cike da tausayi kuka takeyi mai tsuma zuciyar mai sauraro kukan take da sauti,
Nenne kam tana ganin haka tasan me yasa ta kukan gaba d'aya sai zuciyarta ta cika da tausayawa y'ar tata,
su Ya Usman kuma suna jin kukan da takeyi cikin sauri suka shigo d'akin ,
cikin tarin tausayawa Usman ya zauna gefen ta baki na rawa yace.
"Ummul meke faruwa? meya sameki? meke miki ciwon?."

Ba amsa sai kukan da takeyi,
Nenne kuwa tsuke fuska tayi cikin fad'a tace.
"Ke ni tashi a kaina tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina kukan banza bazan kiyi magana ba."

Cikin kuka mai cushe zuciya ta d'ago kanta baki na rawa tace.
"Wayyo Allah wayyo Nenne kiji abin da Abba yace min Nenne wallahi ina son Mustapha ina sonshi yana sona dan Allah Nenne ki bawa Abba hak'uri wallahi ina son Mustapha."

Wani irin dogon tsaki ya Adam yaja cikin buga mata tsawa yace.
"Ai Mustapha yafi miki kowa a duniya tunda har kike kuka da umurnin Abban mu,
ni wallahi kin saman na k'ara tsanar sa."

Juyowa tayi cikin kuka tace.
"Ya Adam kasan da waye Abba zai had'a ni?".
A hatsala yace.
" Na sani mana kuma yafi Mustapha da komai."

Cikin kad'uwa da bugawar zuciya Ya Usman ya kalleta tare da cewa.
"Waye za'a had'a ki dashi?."

Kuka ta saki tare da cewa.
"Ya Usman waifa Abba da Hamma Umar zai had'a ni aure."

Ido Usman ya zaro cikin wani irin yanayin yayi wani irin.....


By
*GARKUWAR FULANI*

πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

page 1⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡






*Zan abbato mutanen sokkoto su y'an kwaraine basu da tsoggoma idan kaje ka sanya fad'a musu zasu rik'eka da kyau harda lallamah k'warai-k'warai na gane duniya mai sonka shike yi maka hiddima masoya na na sokkoto kun gaman gata gaisheku πŸ€πŸ˜πŸ˜˜πŸ‘πŸ»πŸ€nakeyi domin kuke raba gardamaπŸ‘πŸ»πŸ€ sokkotawa ina al'fahari daku domin baku da hassada a zuk'atan ku shiyasa na sadaukar da wannan shafi gareku sokkotawaπŸ€πŸ˜˜πŸ‘πŸ»*











*Ha*nnushi ya tura kasan pillow dake gefen ta da niyar zai jawo laptop d'in shi daya bari a wurin,
lalubawa yakeyi aman baiji inda laptop d'in yakeba dan d'akin yana da duhu gashi kan gadone mai rumfa duk yasha gyara da shimfid'a da labulaye sai ya k'ara duhun,
Ita kuwa Ummul tana ganin shi dan ita ta dad'e a d'akin so duhun yabi idonta shi kuma yanzu ya shigo d'akin shiyasa yake ganin duhun sosai,
tab'e fuska tayi cikin ko in kula tasa hannu ta turo laptop d'in nashi k'asa dai-dai sautin kan yatsunshi ta turo shi,
shi ko da sauri ya sunkuya da nufin yasa hannu ya taro laptop d'in kar ya kai k'asa gudun karta lalace,
amman ina cikin rashin sa'a ta fad'o kan yatsunshi tsinin aggil d'in jikin marfinta ya caki kan farcen babbar yatsarsa,
cakar da a take farcen ya tsage lokaci d'aya jini ya fara zuba a take k'afar ta fara wani irin b'ari dan azabar daya ratsashi gaba d'aya yatsar kuma sai motsi take kamar zata fice a jikin shi,
cikin wani irin azaba dayaji ya ziyarci k'ahon zuciyarshi ya dafe kanshi da k'arfi hannun shi sai rawa suke gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka taso ida nunshi sukayi jazir ya kasa magana sai harshen shi ya d'an zaro ya rink'a d'an kad'awa yana furza numfashi tuni zufa ta keto mai ta sashoshin jikin sa,
harshen yake d'an kad'awa yana fidda sautin.
"Shihhhhhhhh ahhhhshhhhhh."
Sai kuma k'afar tashi daya d'an d'ago yana yarfawa,
Ita kuwa Ummul sai murmushi mugunta ta rink'a yi tanaji dariya nason kufce mata murmushin takeyi tuk'uru cikin jin dad'in azabtar dashi da tayi sai wani kad'a kai takeyi tana magana a ranta.
"Kad'an ma kaji Hamma Umar wannan shine makullin wahalar da zakasha a hannun na,
kaida azabtuwa kun kullah,
Sai kayi kuka cur-cur da hawaye ka sai ka gommace kid'i da karatu sai ka sakeni saki mafi muni wanda zan haramta maka har sai inna nasake wani auren an sakeni."

Kai ta jinjina taci gaba da maganar zuciyar da bata saniba na yanzun ya fito fili cewa take.
"Tabbacin da nake dashi ko ince yak'ini na sani Mustapha bazai sakeni ba har Abadan zamu rayu tare."

Da sauri Hamma Umar d'in ya bud'e idanun shi daya rumtse jin sautin Ummul d'in kan gadon ya tsurawa ido cikin wore idanun shi ,
fuskar ta ya tsare da ido cikin zafin nama ya mik'a hannushi kan gadon,
ita kuwa ganin haka tayi wani irin dira daga kan gadon a guje tayi woje a parlour ta samu ya Usman da su Hajjajo da Inna tare da Anty Halima da Anty Shuwa k'anwar Nenne,
cikin rawan jiki ta koma gefen ya Usman ta zauna cikin tura baki da tsuke fuska,
Anty Halima ce ta kalleta cikin tuhuma tace.
"Me kika aikata? kika fito a guje haka?."
fuska ta k'ara tsukewa sannan ta kalli Anty Shuwa dake ta danna mata harara cikin son yin kuka tace.
"Nayi ai ban sani bane."
Hajjajo ta bud'e baki zatayi magana kenan sai kuma tayi shiru ganin Hamma Umar d'in d'aya fito cikin d'akin nata ,
tafiya yake yana d'ingisa k'afar tashi duk inda ya taka sai jini dake zuba gaba d'aya jijiyoyin kanshi sun taso kanshi a k'asa yake tafiya hannushi rik'e da laptop d'in nashi yayinda d'aya hannun kuma yake rik'e da iPhone d'in shi,
Ya Usman ne da Anty Halima sukayi kanshi da sauri cikin rawan baki Ya Usman yace.
"Hamma Umar me ya fasama yatsa yaushe ya fashe kalli yadda jiki ke zubafa."
Anty Halima kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin duk jini ya wonke mai k'afarsa cikin sanyi murya na rawa tace
"Hamma Umar a tsaida jinin nan mana ya dena zuba."

kai ya gyad'a musu cikin jarumta da dauriya ya nufi hanyar fita yana ce musu .
"Ba komai fa."
har yake bak'in k'ofar fita,
Hajjajo da Inna sukayi kanshi da sauri cikin kula da tsananin k'aunar jikan nasu suka kalleshi,
kusan a tare suke magana.
"Kai Farouq me ya fasama k'afar?
kayi magana kayi shiru ?."
kai ya jinjina a hankali yace.
"Tuntub'e nayi."
fad'in haka da yayi ne yasa suka rink'a jeromai "sannu-sannu Amman kaji azaba kam ai abinda ya fasa farce ba k'ara min abu bane."

Su tsoppin sun yarda Amman Anty Halima da Anty Shuwa kam sun gane sarai Ummul ce taji mai ciwon dan ganin yadda take zare ido da alamun rashin gaskiya Ita,
kuwa Ummul har cikin ranta take jin dad'in ciwon da taji mishi,
a wani sashin zuciyar ta kuwa tana mamakin yadda Hamma Umar d'in ya rufa mata asiri yak'i cewa Ita ta fasa mishi k'afar,
dan ta tabbaya d'aya fad'a Ita kuwa da ta shiga 9 nema ba 3 ba.

shi kuwa Hamma Umar ko inda take bai kallah ba ya fice yana d'ingisa k'afar,
ya Usman kuwa karb'a laptop d'in Hamman nashi yayi ya rik'e cikin raunin fuskar sa kamar zaiyi kuka dan tausayawa d'an uwan nashi,
har zasu fita ya juyo ya kalli Ummul d'in cikin raunin da yanayin tuhuma dan ya gane itace silar ciwon Hamman nashi,
itama kallon shi takeyi cikin sanyi ta rumtse idonta,
shi kuwa juyawa sukayi suka tafi.

Suna zuwa part d'in su Hamm Umar d'in yayiwa yatsar tashi dressing sannan yawa kanshi allurar ya kuma sha magani.

Ita kuwa Ummul suna fita Anty Shuwa da Anty Halima suka jata d'akin dake gefen na Hajjajo suka rink'a yi mata gyare-gyare tare da tsumata da irin tsumukansu na shuwa'arab ,
Anty Shuwa ce ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Ummul d'in cikin tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."

Kai Ummul d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah a barni hakanan."

A fad'ace Anty Shuwa tace .
"Sai kinsha muguwar banza yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Halima ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Hamma Umar d'in."

Haka suka rink'a yi mata fad'a da nasiha sunayi suna tsumata tare da dilketa da murjeta.

Haka nan kullum Sai sun murjeta sun tsumata,
ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta kuma tamkar auduga komai nata yasha gyara sai wani k'amshin mai sanyi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman k'afafun ta da hannayen ta kuwa an musu zanen Lalle na mu samman komai na Ummul ya fito rasa ta fito a shuwa'arab d'in sak.


A gefen ago Hamma Umar kuwa ,
komai Ya Usman ne yake gudanarwa gaba d'aya ya gayyato abokon Hamma Umar d'in nashi ...

Yau ta kama Jumma haji babbar rana Wanda ya kasance gobe asabar ne za'ayi d'aurin aure Ummul da Hamma Umar .

Toh a rayuwar shuwa'arab akwai wata al'adar da sukeyi a duk lokacin da zasuyi bikin su ,
suna yin wannan al'adar tasune kamar gone za'a d'aura aure ,
kuma wannan al'adar tasu tana kunshe da wata al'adar kuwa Wanda a halin gaskiya a yanzu haka gaba d'aya shuwa'arab sunbar yin wannan al'adar ta biyun na farin dai sunyi Amman na biyun kam ,
a shuwa'arab d'in ma na zamanin yanzu da yawa basuma san al'adar ba dan tuni anbar yin al'adar duk da dai a zamanin da d'in ma a cikin aggwaye 100 da wuya a samu aggwaye 5 masu yin wannan al'adar domain al'adace mai nuni da d'auka alk'awari da kuma rik'o da amana suna kiran al'adar da sunan *Nad'in uwar gida*

So shiyasa aggwayen yanzu basa wannan al'adar ta biyun kenan fa,
Amman na farin kam har yanzu shuwa'arab sunyi kuma in an gama na farinne akeyin na biyun,
so Yau jumma'a tun safe aketa shirin wannan al'adar tasu na. farin wanda dama asan dashi shi kuwa na biyu ba wanda yake da tabbacin za'ayishi a cikin shuwanma wasu basu san da wannan ba,
tun safe aka k'afa tantuna a harabar gidan nasu aka shimfid'a kilisai na al'farma aka ajiye kujera na gani na fad'a kujera masu taushi gaba d'aya an zagaye wurin da kolliyoyin zamani tare dana al'adun shuwa'arab d'in,
cikin kujerun kuwa a tsakiyar kujerun akwai na aggo da amarya wanda sunayen su ke rubuce a Kansu sai na k'awayen Amarya da abokin aggo suma duk sunayen su na rubuce akan kujerun nasu.

Yadda ake al'adar tasu kuwa bayan an gama kimtsa wurin aggo zai fara zuwaya zauna da zugar abokan shi sai bayan ya zauna da mintuna kad'an sai a fito da amarya,
fito da amaryarna kuma 'Yar uwar amaryar ce ta jini zata fito da amariyar rik'e da hannun ta ,
sai ta mik'a hannun amariyar ga hannun y'ar uwar aggo ko d'an uwan aggon,
daga nan sai shiko d'an uwanshi ago yaja hannun Amarya ya kaita kusa da aggon ya ajiyeta,
so y'an uwa da abokin arzik'i zasu tashi sunyi ta yiwa Amarya lik'in kud'i da gudumowowinsu,
bayan duk an gama lik'inne sai shi kuwa aggo ya tashi yayi nashi lik'in,
shike nan itace al'adar su ta farin .


So haka aka tsaba wannan al'adar bayan an sauk'o sallan jumma'a Hamma Umar da abokanshi duk suka dawo gidan suka d'an huta sannan matayen su kuwa suna cikin gida ,
bayan anyi sallan la'asarne sannan aka fara shirin fita wurin taron,
abokon Hamma Umar manyane masu cikar kamala abokai ne daku masu karatu kun sansu haka kuwa matayen su,
haka sukayi shiga ta al'farma shiga irin ta shuwa'arab d'in sukayi baki d'ayan su suka fito rasa tamkar larabawa,
Suma matayen su da k'awayen Amarya Ummul shiga sukayi ta shuwa'arab d'in gaba d'ayan su laffaya suka yane jikin su dashi suma dama gasu kyawawa. Haka yasa wurin taron ya zama tamkar a k'asar larabane ,
wani abin burgewa kuwa duk woni sak'o da luggu har cikin fulawowi na gidan an ajiye kaskon turaren wuta sai wani irin k'amshin ke tashi hakan yasa nishad'i a zuk'atan duk wani bani adam dake zaune a wurin.


5:00 pm zugar ago da abokanshi suka ido farfajiyar gidan Ya Usman ne a gaba yayinda sauran abokon ke binshi a baya ,
Hamma Umar kuwa yana tsakiyar su yasha sutura ta al'farma ya fito cikin haiba da cikar zati sajenshi sai wani irin shek'i yakeyi farar fatarshi ta fito ras tamkar balarabe sumar kanshi kuwa. yayi luf gwanin sha'awa ya murza hula a kan nashi yayinda gashin nashi yabi k'eyarshi da zagayen fuskar shi,
idanun shi kuwa wani d'an siririn glass ne mai haske irin na Doctors ke manner a fuskar sa.

dai-dai lokacin da suka fito a dai-dai lokacin kuma matayen abokan aggon suna suka fito ,
gaba d'aya wani taku suke a jere kamar yadda kujerun ke Jere kowa da matarsa a gefen Hamma Umar ne ya fara zama sai babban abokin shi ,
Hamma Yusuf da Ayshar sa sai Hamma Hassan da Fateemar shi sai kuma. Hamma Bashir da Ruk'ayyar shi
Sai Hamma Mahmoud da Khadija shi sai kuma Hamma Aliyu Haydar tare da Minalin shi,
A d'aya gefen kuwa
wasu manyan abokan Hamma Umar d'in na gani da matayen su, Amadi da Nadiyar shi,
sai Abuturrab da Batul d'in shi sai kuma Salim da Tawa
Sai Abdullahi tare da Maryam d'in shi,
daga gefen su kuwa Fauziyya ce da Al'ameen sai Aisar tare da
Bintun shi
sai kuma Abbah da Ruky pinkyn shi,
ga kuma Ridwan da Zakiyya
can kuma kusa dasu Ahmad Ana Muslim ne tare da khadijan shi
sai kuma Assadiq da Safiyyar shi tare Hibbah da Faheem.

Gaba d'aya sun zauna cikin nitsuwa da al'farma suna zaune cikin cikar haiba sun fito tamkar taurari sai shek'i sukeyi da wani irin k'amshin da suke zubawa zamane sukayi na masoyan gaske.

Bayan sun zauna da kamar minti 5 Dangi da k'awayen Amarya da sauran mutane sukazo suka zauna,
cikin nitsuwa da lumana,
Jim kad'an,
suka fara jiyo wani irin k'amshin na k'ara ratsa hancin su gaba d'aya sai wani irin shauk'i ya ziyar cesu ido suka lumshe tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login