Showing 129001 words to 132000 words out of 134562 words
Chapter 44 - Rubutaccen Alamari... By Aisha Garkuwa
Adam sannan yasa hannu ya janye airpiest ɗin dake kunnen Adam ɗin dan kar yaji abinda zaifaɗa yayi k'asa da murya yace,
"Uwan Farouq Abba Daddy cuwa".
Hakan na nufin da Abba da Daddy sukaje unguwa haka Usman yayita mai tambayoyi yana amsamai suna dariya sannan yace, "Abeey Ummiena". tashi yayi daga kan sallayar yaje ya nunamai fuskar ta yace, "tayi bacci,
inta tashi da safe zata kiraka ku gaisa ko Bobona,
yanzu kabawa bah Adam saika kwanta kai bacci, i love u".
Shima a gwarance yace , "i wov u Abeey".
ya fad'a yana ɗaga hannu ya cire abin daga kunnen shi ya mik'awa Adam ya juya yayi kwanciyar shi shiko Adam saida ya gyara mai lulluɓa sannan yaɗau wayar yafita palour.
Saida ya zauna a kujera sannam yace,
"Meya faru? naganku a asibiti haryanzu bata daina kukanba ko?". Cikin damuwa yake maganar,
"Ba kuka tayiba Adam nadawo na sameta kwance da zazzaɓi sai kuma tacemin kirjinta nima naɗauka ciwon zuciyar ne amma da mukazo sai akace ba shi bane".
Ajiyar zuciya Adam yayi sannan yace,
"meke damunta to?". yana sosa kai da wata y'ar dariya yace,
"Abee zaka zama kaima".
"yes that's my bro, dan Allah karka faɗawa kowa nizan faɗa". Murmushi yayi a zuciyar shi yace,
"Kai kaɗai zan iya faɗawa wannan ".
Da haka sukayi sallama ya mata fatan samun sauk'i sannan ya katse wayar.
Sai da safe aka sallamesu dan jikin yayi kwari sosai sai shogoɓa da raki,
haka suka koma gida tanata narke mashi shikuma yasamu aikin yi sai lallaɓata yake yana rarrashi a cikin ranshi kuwa yana tuna randa yaganta da cikin farouq da yanda yake lura da Hamman shi da duk motsin da zatayi akan idonshi sai sannu yake mata, yakanyi k'ollah yana gogewa a ɓoye dan karta gani,
Itama kuma hakan ne a ɓangarenta da Usman da yaɗan kauce zata goge k'ollah tana tuna burin zuciyar Hamma Umar d'inta.
Yau da Asuban fari Usman ya kira Adam wanda shima dai-dai shigowarshi daga masallaci sallah asuba kenan yace,
"Adam ka haɗamu video call dasu Abba kuma inaso ka tabbatar kowa yana gurin har Daddy".
Bai tsaya jin abinda Adam zaice ba ya ajiye wayar yakoma bedroom ya ɗauko dogowar rigar Ummul da ɗan k'aramin mayafin rigar yafito palour itako Ummul tana kwance kan 3seater ya ɗagota ya jinginata jikin kujera ya saka mata doguwar rigar daya ɗauko ya lulluɓa mata ɗankwalin daman y'ar shimi ce a jikinta da wando 3quater itako kallon shi kawai take,
Adam ko yasami su Abba da Daddy a palour Hajjajo ya sanar dasu sakon Usman nason magana da kowa a guri guda kiran kowa na gidan akai Ammi kuwa kawai a zaune take amma jikinta sai rawa yake kirjinta na bugawa da k'arfi. bugu ɗaya Adam yayi Usman ya ɗauka ya jingina wayar da kujerar dake kallon su shima Adam jingina tashi wayar k'irar samsung tab E yayi yanda kowa zai gani sannan ya koma ya zauna.
Shiko Usman komawa yayi ya zauna gaban Ummul a k'asa ya tonk'oshe k'afafun shi ganin haka jikin Ummul da Abba dake kallon su yafara rawa Nanne ma k'irjinta na bugawa tai k'arfin hali tace,
"Usman meza kai haka kul karkayi wannan alk'?". Ammi ce ta ɗagawa Nanne hannu alamar ta kyale shi kanshi a k'asa yakamo k'afafun Ummul wacce tuni tasa mai kuka tana girgiza mai kai tana k'ok'arin janye k'afarta,
da k'arfi ya rik'e k'afar ya ɗora kan cinyar shi batare daya ɗago kaiba cikin sanyi da k'auna da begen tuno Hamman shi yace,
"Ni Usman Ibrahim Umar Shuwa nayi alk'awarin kulawa da matata da k'arfina da dukiyata da lafiyata da zuciyata da kuma raina".
wani irin razana Ummul tayi zuciyarta tayi wata irin bugawa shiko dasauri yatashi ya katse kiran yadawo ya rungumeta dukkan su suna wani irin kuka mai cin rai saida suka ɗau lokaci a haka sannan tazame jikinta bakinta na rawa a hankali tace,
"Ya Usman kaima haka zakayi min? bazan jumreba bazan iyaba dan Allah ka janye wannan alk'awarin wallahi ina sonka inason ka ina son Hammana kar kuyimin haka please banaso in rasaka ina sonka ya Usman".
Hannu yasa ya kwantar da kanta a k'irjin shi cikin rauni yafara cewa, "bazaki rasani ba Ummul ni nakine kamar yadda Hammana yake naki,
Insha Allah babu abinda zai faru sai al'khairi kidena tunanin abinda yafaru da Hammana zaifaru akaina kowa yanada sanadin shi insha Allah nizan k'arasa abinda Hammana ya fara na kyautata rayuwarki da saki farin ciki,
zan rayu dake Ummuna zan baki duk irin kulawar da Hamma na yaso baki".
haka yayi ta rarrashinta suna manne da juna.
Sukuwa a gida kowa kuka yake sabida tunawa da Hamma Umar da kuma tausayawa Usman da Ummul,
Ammi ce cikin k'arfin hali irin nata tace addu'a ce tsakaninmu da waɗannan yara domin jininsu ɗaya kuma haka Allah ya tsara musu rayuwarsu tabbas wannan shine Rubutaccen al'amari daga Allah,
Daddy ne yace,
"Wai ni kam meya kawo wannan abun kuma a yau?".
Adam da shikadai ne keda amsar tambayar yace,
"Daddy jiya a asibiti suka kwana Ummul ba lafiya amma likitan yace ba ciwon zuciyar bane wai tanada cikine, inaganin shiyasa Usman yin hakan".
Hamdala kawai sukeyi dukkansu Ammi da Nanne kuwa suka tashi suka fita kowa da abu biyu a lokaci guda a ranshi murnar samun k'aruwa da kuma tunawa da kamilin ɗansu Dr UMAR IBRAHIM UMAR SHUWA....
*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
page 4⃣0⃣
*Na*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*
*Nandis ngd matuka Allah bar zumunci da k'auna dear Allah k'ara basira naga novel mai suna sai NAGA AYSHA GARKUWA karki damu zakiga garkuwa amman bakisa number kiba kuma inada mgn dake so ina son number ki, kuma kar kici gaba da typing sai munyi mgn ngd bandirawo🤝😍😘*
*Wannan shafi nawa gaba d'ayanshi tukuicine ga masu suna AYSHA ina k'aunar wannan suna mai daraja ina son duk mai wannan suna ina al'fahari da sunan ina k'ara yiwa iyayena addu'a da sunka samin wannan suna mai daraja sukamin zab'i mai kyau a lokacin da bansan kainaba ya Allah ka sakawa iyayenmu da ma fificiyar sakaiya Allah ya basu jannatul firdausi Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati*
*B*ayan duk sun tashi a taron nasu Adam ma ya mik'e ya koma part enshi bayan an idar da sallan azahar,
misalin k'arfe 2:00 Adam ya shigo ɓangaren Nenne yadda suka saba samun Nanne da Ammin a wannan lokacin hannun shi rik'e dana Farouq suna shiga ya sami kan 3seater ya kwanta yaɗan matsa shima Farouq ya hau ya kwanta a gabanshi ya lumshe ido sannan yace,
"Ammi wai kina nemana inji Aliyu?".
fuska a sake tace,
"eh sonake ka kiramin Usman".
Mik'ewa yayi ya ɗaga Farouq yace,
"my boy jeka ɗauko mana waya a ɗaki".
Da gudu ya fita bai jimaba sai gashi da wayar Nanne ce tayi ɗan murmushi tace, "masha ruwa magirmi, su Adam anyi ɗan aike har wani dadi kukeji ku aiki Farouq gashi baida k'iuya".
Shiko Farouq kai tsaye ya mik'awa Adam wayar ya koma gefen shi yayi kwanciyar shi,
Ringing tayi kamar zata katse sannan Usman ya ɗauki wayar murya can k'asa yace,
"Ya akai gwauro?". dariya Adam yayi sannan yace,
"Ammi ce keson magana da kai". Tashi yayi ya zauna ya ɗago Ummul dake kwance jikin shi ya mannata da k'irjin shi sannan ya jingina da jikin gadon ya ajiye wayar yasa handsfree ya ajiye sannan yace,
"Ammi ina wuni?".
Cikin murmushi tace,
"lafiya lau ya Ummu na?".
"Alhamdulillah tana lafiya Ammina".
"Masha Allah".
Tace sai kuma ta d'anyi shiru zuwa d'an wani lokaci sannan tayi ajiyan zuciya tare da yin magana a hankali tace,
"Usman am sai yaushe zaku dawo?
wallahi hankalina zaifi kwanciya in tana kusa dani ga Farouq ma yana kewarku,
ka dawomin da yarinyata kusa damu zan kula da ita".
Da sauri ya jawo woyar ya kashe handsfree ɗin yaɗauka yasa a kunne dan gudun kar maganar Ammi ta ankaro da Ummu ta fara regima akan a koma cikin sanyi da rauni kamar zaiyi kuka yace,
"Ayyahh Ammi wallahi ba komai fa zan kula da ita sosai dan Allah kiyi hak'uri ban gama aikin da nazo yiba kuma bazan iya zama ni kadai ba". Ajiyar zuciya tayi sannan cikin jin tausayi d'an nata tace,
"To naji, amma dan Allah ka lura min da ita ni gaba ɗaya gani nake bazaka iya kula da itaba dan kaima da kanka Usman yaushe ka koyi kula da kanka". murmushi yayi dan sanin gaskiya ta fad'a dan Hamman shine ke kula dashi ajiyan zuciya yayi yanaso ya kauda zancen dan ganin yanda Ummul ta k'ureshi da ido yasan zata iya yimai rigima yace,
"Gata nan ma Ammi". Saka mata wayar yayi a kunnen ta aiko shagwaɓewa tayi tace,
"Ammina ina wuni?". saida ta gyara zama sannan tace,
"lafiya lau Mamana ya jikin? kina cin abinci ko? kin bar kuka ko? kinga kiyi hakuri ki rink'a cin abinci kinji kuma ki rink'a shan magani saboda ki rink'a samun k'arfi ko Ummu na?". Sake narkewa tayi tasa hannu ta ture hannun Usman da yaketa faman shafa cikin ta yana lumshe ido sannan tace,
"To ". hira suka d'anyi sannan sukayi sallama ya katse wayar dama ya k'osa,
Janyota ya sakeyi ya manneta da jikinshi ɗan ture shi tayi tace, "kai ya Usman kai baka gajiya ne? tun ɗazu ka hanani bacci sai tumurmushe min jiki kake yi".
Baice komaiba sai sake tura kan shi da yayi a tsakanin k'irjinta yana goga fuskar shi. Hannu yasa ya cigaba da shafa cikinta dake lafe a jikinta kamar bataci komai ba, ture hannun shi tayi cikin shogoɓa tace,
"Wallahi shima ɗan nan da zai iya daya gudu saboda wannan shafe-shafen naka".
Dariya maganar ta bashi saida yayi dariyar me isar shi sannan yace,
"Waya cemiki ɗane? to nidai y'a mace nake fatan na harba, sannan waya ce miki miji na gajiya da matarsa bari in gwada miki aikin rashin gajiya".
Janyota yasakeyi ya matseta yafara lasar lips enta da harshen shi yana matsa ta,
ganin da gaske yake ta narke fuska ta marai raice tace,
"Kayi hak'uri saina huta".
Rik'e hannu yayi sannan ya janyota kan kirjin shi ya kwantar da ita shima ya lumshe ido a hankali kamar me raɗa yace,
"Inaso in faɗa miki wata magana amma saikin min al'kawarin bazakiyi kukaba".
D'ago kanta tayi ta kalli idon shi sannan ta maida kanta ta kwantar tace,
"bazan yiba tunda bakaso, daman nima bana sanin inayin kukan".
Rungumota ya kumayi yace,
"Yauwa kinsan Garba ɗan gidan Bah yahaya na kusa da gidan