Showing 111001 words to 114000 words out of 249044 words

Chapter 38 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14996

dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari.

A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace.
Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba.

Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin.

"Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji"

"Bana tunanin komai"

"Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai"

Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye.

"Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba"

Sai ta yi murmushi.

"Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja.
Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai"

Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina.

"Ni"

"Eh, ɗana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu, shiyasa nake ta boyonki ina fargabar kar wani yace yana sonki ki karba, kin ga idan ya aure shi zai aje ki a nan dole zai rika zuwa akai akai, kuma ni na zan samu nawa jikokin ta bangarena, idan ba haka ba ina tunani gaban kadan dauke shi zasu yi ba za su bari na zauna da shi ba"

Na sauke ajiyar zuciya ina tambayar kaina to idan kuma ya zo ya ga ban masa ba fa. Kamar tasan abun da nake sakawa sai tace.

"Karki damu da wai ba zai so ki ba, sai so ki ina mai tabbatar miki zai kaunace ki Aisha kamar zai yi hauka, ke kanki zaki yi mamaki yadda zai kula da ke, saboda ni na zaba masa ke da kaina kuma kin sha wahalar rayuwa Allah zai saka miki ta hanyarsa In Shaa Allahu, abun da na cutar da ni a zaman da muka yi da mahaifinsa shi ne shi baya so na, da ace yana so na da ba zan wahala a yadda na wahala ba, amman ke na san Turhan ba zai bari ko yatsa a nuna miki ba, dana yana da kirki sosai yana da tarbiyar kuma yana da addini daidai gwargwado na miki alkawarin Turhan ba zai taba cutar dake ba ba zai taba cin amanarki ba"

Ta yi min campaign ta gyara danta sosai da halin da ta san ba nasa ba ne, ta fada min abun da ba haka yake ba, ta lullube danta da kyawawan halayya alhalin akasin hakan ne a tare da shi. Ni dai ban iya cewa mata komai ba, domin kyautatawa tana biyo kyautatawa ne, ta ina zan iya cewa danta bana kaunarsa macen da bata san ni ba ta rike ni ta kyautata min ni da ɗana, gashi ta yi kuskure bata tambayi ra'ayi akan kudirinta ba, idonta ya rufe akan muradinta da kuma burin da take da shi. Dafa ni ta yi

"Aisha karki damu, na lura da kyakyawan halayen dana, kuma ba zan ce ni din mace ce mai nagarta 100 bisa dari ba amman dai na san na kam kamanta na kan kyautata iya yadda zan iya, ba zan yarda a cutar da wani ina gani ba sai inda karfina ya kare, Wallahi ba zan bari Turhan ya cutar da ke ba na miki alkawari, ke din abar tausayi ce Aisha baki da kowa kuma gani ba ki jidadin aure ba, duk wanda ya ji labarin ki dole ya tausaya miki, wata kila ta dalilinki zan samu aljannata gashi ina jinki kamar yata, ba zan taba bari Turhan ya cutar da ke ba"

Ba zan iya amsa mata da aa ba amman a lokacin na ji a jikina ban shirya sake wani auren ba, idan kuma nace ba zan auri danta ba a ina zan zauna? Zai kula da ni wa zai rike ni ni da ɗana? Ina cikin wannan tunanin muka ji kyallowar Ibraheem ni da ita muka tashi da sauri muka shiga cikin falon na haura sama na dauko shi ihu kawai yake na yi rarrashi na na ba shi madara be saurara, sai ya yanke shawarar na tafi da shi asibiti haka na saka hijab cikin tashin hankali muka tafi asibitin, su yi iya bincikensu sun ba mu test da hotuna kala kala amman ba a gano asalin damuwarsa ba sai da ya shekara biyu cif, suka ce min ɗana Autism ne, ga shi yana fama da sickle, daga lokacin hallayarsa ta sake yau ciwo gobe lafiya baya yarda da kowa sai ni sai kuma Ammy mai aikin Ammy ma daker yake yarda da ita, ko sallama aka yi da karfi sai ya fasa ihu jiki yayi ta rawa ya cige, tun ina jin tsoro har na saba, ɗana ya sha wahala gashi kuma yanzu be rayu ba, kuma be ji sauki ba har ya bar duniya, kuma be ga ubansa ba"

Ya rufe baki tana kuka.

Aliyu ya mike tsaye ya nufi windows office din ya tsaya tana kallon harabar ma'aikatar, sai a yanzu na fahimci dalilin Ammy na juyawa Turhan baya, ta ki ta fahimce shi ta saurare shi.
Ya sake juyowa ya kalli Emily dake ta kuka, dawowa yayi gurin teburin ya zari tissue ya mika mata ta karba tana shaye hawayenta.

"Ba zan ce na fi sauran ba, amman dai na miki alkawari daga yanzu wani ba zai sake cutar da ke ba, sannan ina son na ja kunnenki akan Tasmia karki sake yarda da ita, abu na karshe da zan fada miki shi na har yanzu Ammy tana sonki, mace ce mai kirki kawai danta ne ya tsaba alkawari, saboda wannan ta juyawa Turhan baya, wannan dalilin ya saka yake nemanki, yanzu haka ya fada min bata da lafiya kuma yana tunanin kamar har da tunaninki ya saka ta ciwo"

Ta kalle shi tana hawaye.

"Asha ma ba nadama yayi ba, ashe ma..."

Ta kasa karasa.

"Dan Allah Aliyu ka yi min alkawari ba zaka taba fada masa inda nake ba"

Ya kalleta sai yayi shiru na dakiku kamin ya amsa mata.

"Na yi, ba zan taba bari Turhan ya san inda kike ba ta dalilina sai idan ke kika yi ra'ayi, you have my words"

Ta daga masa kai alamar gamsuwa.

"Mu je na kai ki gida"

"Zan iya tuki na zo da mota"

"No i want to take you home safely"

"Amman za a iya cewa ranar mun shiga mota daya, kuma yanzu a sake ganin mun shiga"

Ya rumgume hannayensa.

"A duk lokacin da zan aikata wani abu uku nake dubawa kuma nake jin nauyi, Ubangijina, mahaifaina, matata, Ubangijina ya san ba ni da wata mummunar manufa akanki, sai kyakkyawa, Matata ta san da ke, iyayena ne suka rage su kuma na san ba su da matsala, the rest can go to hell, let's go"

Ya fara takawa ya isa kofar ya bude ya juyo ya kalleta sai ya samu shi take kallo.

"Aliyu yana da banbanci da sauran ki saka wannan a zuciyarki, you can trust me"

Ta mike tsaye ta isa kofar ta fito sai ya janyo kofar a daidai lokacin da Amal ta fito office dinta, dan tsaye ta yi da farko irin na mutum da mamakin ganin sabon abu ya rufe shi, Aliyu yayi kamar be ganta ya jera da Emily suka wuce, a tare suka sauka kasa suka isa har gurin motarsa ta bude ta shiga, shi ma ya shiga.

"Amman lokacin tashi aikin be yi ba"

Yana yi ma motar key ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba.

"You need to rest, labarin zaki karasa min wani lokacin, don't stress yourself"

Ya tashi motar suka kama hanya, sai ta maida dubanta gurin agogon da ya bata tana ta murza agogo a hankali. Kallo mace ya wuce sau biyu zuwa uku haramun ne a gurinsa amman Emily ya kasa dauke idonsa a kanta, musamman a yau da tausayinta ya zame masa nauyi, tukin kawai yake amman idonsa da hankali yana gurinta har ya isa gidanta, ya faka a wajen gate din gidan yana kallonta.

"Aliyu..."

Ta kirashi da muryarta kasa kasa. Ya amsa mata yana kallonta zuciyarsa cike da tausayinta.

"Ka taba marmarin abun da baka taba samu ba?"

Ta tambaya har lokacin bata kalleshi ba.

"A'a"

Ya amsa mata bayan few seconds.

"Me kike marmari?"

Ta kalleshi tana kuka.

"Iyayena, ni uwa amman ni ma ina neman tawa uwar ina jin kewarta duk da ban taba kasancewa da ita ba, me yasa suka jefar da ni, me na yi musu? Miyasa gashin kaina yake yake da idanuwa na, ni yar asalin wace kabila ce, wa na biyo mahaifina na ko mahaifiya? Minene asalin sunana? Su waye yan'uwana? Duk ba ni da amsar ko daya"

Ya busar da iskar bakinsa.

"Emily kuka kike son na miki ne?"

Ta girgiza kai.

"Toh dan Allah ki yi daina kukan nan haka, kin cika zuciyata fal da tausayinki, a yanzu kuma bana son ganin damuwarki, ban wanzu a wacan duniyar da kika sha wahalar rayuwa ba, amman ina ta dorawa kaina laifi miyasa ban san ki tun a farko ba? Wata kila duk wannan wahalar da baki shata ba, iyayenki kuma wata kila ma sace ki aka yi aka kai a gurin ba tare da sanin iyayenki ba, domin alama suna nuna ke ruwa biyu ce, amman ki daina kukan kin ji?"

Yana mata maganar cikin sanyin murya da rarrashi. Ta share hawaye.

"Good Girl"

Ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito.

"Na san Fatima bata nan yanzu, amman anjima idan ta dawo school ta huta ni ma na tashi aiki zan zo na dauke ta mu je yawo"

Ta bata fuska kamar zata fashe masa da kuka.

"Aliyu dan Allah...."

Be bari ta karasa ba ya tare numfashi ta.

"No no no noooooo Emily ba abun da kike tunani ba ne, ina son na dandana mata dadin uba ne, tun da kin nuna mata na uwa, kuma kin wahala da yawa ya kamata ki huta, wani ya dauki responsibility, you're not alone we're Family"

Kallonsa kawai take.

"Kin min izini?"

Ta daga mishi kai.

"Thank You, ki yi hakuri da fadan da muka yi dazu ki yafe min"

Ta yi murmushi, shi ma murmushin yayi tana tsaye yana kallonta har ta shige ciki, sannan ya koma motar ya koma gurin aikinsa.
Yana shiga office abu na farko da ya fara yi shi ne kiran Ammy ya gaishe ta kuma yayi mata ya jiki domin tabbatarwa idan da gaske bata da lafiyar ko kuma fadar Turhan ne kawai.

"Alhamdulillah"

"Ammy me ke damunki?"

"Sun ce hawan jini ne da ciwon suga, amman dai Alhamdulillah sauki yana samuwa"

"Kina gida ne ko asibiti"

"Ina asibiti"

"Allah ya kara sauki, In Shaa Allahu zan shigo na dubaki"

"Aa karka damu, ba sai ka wahalar da kanka ba ina tunanin da na kara samu sauki kadan za su sallame ni"

"Allah ya kara sauki, amman dai zan shigo In Shaa Allahu"

Daga haka yayi mata sallama, after like one hour, kira ya shigo wayarsa da bakuwar number sai da ya kai karshen typing din da yake sannan ya amsa wayar.

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikumussalam, Aliyu kana lafiya?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah"

"Baka gane mai magana ba ko? Mama Baraka ce"

Ya dan yi shiru kamin ya amsa.

"Maa Shaa Allahu Mama ya gida fatan kowa lafiya"

"Alhamdulillah, Aliyu idan ka samu lokaci ina son mu yi magana ka kira ni, nasan yanzu kana kan aiki ne ko?"

"Eh gaskiya ina gurin aiki"

"Toh idan ka koma gida ko zuwa dare ne sai mu yi magana"

"Lafiya dai ko?"

"Lafiya amman ba kalau ba, akan matarka ne bata fada mana abun da ya hada ku ba, kai kuma baka biyo sawunta ba, ta zo mana nan duk ta rikice ta zama abar tausayi, sai dai ka samu lokaci za mu yi magana"

"Okay Mama"

Ya sauke wayar ya cigaba da aikinsa. Sai 4pm ya tashi aikin a hanya yayi sallah la'asar ya isa gida ya dafa ma kansa indomie ya ci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani voile lace na maza black color mai kyau, ya saka bakar hulla ya sha turare da bakaken talkama kamar wanda za shi zance, ya cika aljihunsw da sabbin kudi sannan ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanya sai gidan Emily, da ya isa unguwar be karasa gidan kai tsaye ba gudun kar ya janyo mata matsala, sai ya faka gida uku kamin nata, sannan ya kirata a waya.

"Hello"

"Assalamu Alaikum"

Ta amsa, sai kuma ta yi shiru.

"Gimbiyar tawa ta shirya ne?"

"Oh oh oh Fatima?"

"Yeah"

"Eh ta shirya"

"Toh a fito min da ita, ina waje nesa da ku sai kin saka ido sosai zaki iya ganina gida na uku kamin na ku, bana son na zo kusa ne ban san ko Vito yana ciki ba kar yace zai miki fada ko ya dake ki, kin san ni kuwa a yanzu ba zan saka ido ko yatsa wani ya nuna miki ba"

Ta yi murmushi mai sauki tana jindadi tare da sauke numfashin da ya ji shi har cikin zuciyarsa. Ya zauna a motar na tsawon mintuna goma sannan ya hango ta ta fito sanye da bakar abaya ta rolling dankwalin abayar ta rufe kanta kai kace musulma ce, ta yi kwalliya sosai har da jan baki, tun daga nesa Aliyu yake kallon fuskarta tafiyarta da yadda bakar abayar ta yi mata shegen kyau ko kyaltawa baya yi gaba daya ta dauke hankalinsa ko Fatima da ya zo domin ita be gani ba sai Emily, da ta iso gurin motar sai ya sauke gilashin ya jingina da kujerar motar yana kallonta kamar wanda ya zauce.

"Sannu"

Ta fada ta muryar mai dadi idonta suna jan hankalinsa ga wani tsadadden murmushi a fuskarta. Yayi murmushi ya sauke kansa kasa.

"Emily ashe kina da kyau, na gode da kika karramani, wannan shigar ta dace da kyau, kin yi ma abayar kyau sosai"

Ta yi murmushi ita kanta ta san ta yi kyau.

"Wata kila da zaki rika suturta jikinki haka da manyan kaya masu sauko miki su rufe tsiraicinki da zan yi ta kula ina fahimtar kyaunki ne, kuma zan fi sake jiki na jidadi, kin san ban taba kula da kina da kyau ba sai yanzu?"

"Saboda na saka abaya?"

Ya girgiza yana kallonta da murmushi.

"Aa saboda kin rufe jiki, kin dace da sunan Aisha, daga yau ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login