Showing 90001 words to 93000 words out of 249044 words
taba min gorin komai ba, be taba nuna min gajiya akan kula da ni ba"
Tasmia ta dafa kafadarta.
"Irin wannan ne kike neman rabuwa da shi? Ai shi ya fi kowa cancantarki Emily, babu wani sakamako da zaki masa sai na aurensa, akasin hakan kamar kin butulce masa ne, kuma ina tabbacin amana ba zata barki ba, ki yi tunani akai"
Emily ta daga mata kai tana hade abun da ya tsaya mata a makoshi.
"Amman dawowa zai yi ne da ya ce ta zo ta girka masa abinci?"
"Yana nan daman, na boye miki ne saboda ki zo"
Tasmia ta ji yan hanjinta sun kaɗa ta mike tsaye da sauri gumi na karto mata, bata ko tsaya yi ma Emily sallama ba ta rumgumi jakarta ta nufi kofar falon ta bude Emily na mata magana bata kulata ba, da sassarfa ta isa gate tana samun ficewa sai ta ranta a na kare ta aina da gudu tana yi tana waiwaye har sai da ta yi nisa da gidan sannan hankalinta ya kwanta.
Emily ta dauki shawarar Tasmia na cewar kar ra koma aiki, duk kuwa da irin kyautatawa Aliyu zato da take, amman zai iya amfani da damar ya dawo da Turhan a rayuwarta ita kuwa a yanzu bata bukatar kowa, sai dai ta dayan bangaren ta san taba bukatar aikin haka ta kwana da tunanin yi ko bari har garin Allah ya waye bata samu matsaya ba.
Bayan Fatima ta wuce school, Emily ta shirya ta sauko rike da jakarta da wayarta, kallo daya ta yi ma Vito dake zaune yana karyawa ta dauke ido ta nufi kofa.
"Zaki je neman aiki ne? Har shaguna nawa zaki rika bi kina neman su dauke ki aikin da ke kanki zaki iya daukarsu? Idan har baki son kudi da nake aje miki ne toh a shagon siyar da talkami da kika nemi aiki ne, shi ma nawa ne, kudin dai still daga karkashina za su fito"
Ta juyo ta kalleshi ta dauke ido ta yi ficewarta. Da gaske gurin nasa ne ko kuma dai ya san mai gurin wata kila kuma yana mata barazana ne kawai saboda ya daureta a guri daya, har ta isa gurin aikin na su Aliyu bata daina tunanin maganar Vito da kuma Tasmia ba, ta duk inda zata auna Vito ya cancanci zama da ita, kuma sakamakon da zata masa na mallaka masa zuciyarta ne da yake bukata kamar yadda Tasmia ta fada, wata kila zata iya shawo kan Fatima ta amince da shi. Ta shiga gurin da ake aje motocin kamfanin tana duba motarta domin ta manta gurin da ta faka ta a wacan karon.
Sai da ta yi rabin gurin sannan ta ga motarta ta matsa key din hannunta ta bude motar a gurin da zata zauna ta yi arba da wata farar takardar dauke ta rubutu, hannu ta kai ta dauki takardar sannan ta shiga ta zauna.
"Idan kin riske sakon nan, ki shiga office dinki ki yi signing cewar kin bar aikin a hukumance kamar yadda kika karba a hukunce"
Ta daga kai ta kalli harabar sannan ta aje takardar ta fito motar ta rufe ta nufi cikin ma'aikatar, bata sha wahala gurin haura sama ba domin ba wannan ne zuwanta na farko ba, ta shiga Elevator har hawa na 4 ta fita ta doshi hanyar da office dinta yake, kallo daya ta yi ma kofar office din Amal ta dauke kai ta murda office din da yake zaman nata a da ta shiga.
Ga mamakinta sai ta sami Aliyu tsaye a gaban teburinta yana saka two cube of sugar a tea dake kan teburinta.
"Babu gaisuwa?"
Ya fada ba tare da ya kalleta ba.
"Ina kwana"
"Lafiya kalau"
Ya saka Tea spoon ya motsa tea.
"Zauna"
Babu musu ta nufi kujera dake facing din gefen teburin ta zauna, ya dauki tea din ya aje a gabanta.
"Na san baki karya ba, dauki ki sha"
Nan ma kasa musa masa ta yi, sai ta saka hannu biyu ta dauki cup din ta kai baki ta fara sha.
"Sai kawai kika ji kira daga sama ko? Ana zaginki?"
Ta sauke tea din ta rike a hannunta.
"Ki yi hakuri laifina ne, ya kamata na fada miki waye ni tun farko, ko da yake baki bukaci jin haka ba"
Ta dora idonta akan ragowar tea din dake hannunta.
"Amman kamin wannan fada min miye aikin Vito?"
Ta kalleshi da kyawawan idanuwanta ta sauke kai kasa, ba tare da ta amsa masa ba, domin ba zata iya tonawa Vito asiri agurin kowa ba.
"Dialer ne na Drugs?"
Ta sake dubansa.
"Ba fashi yake ba, da boyo zai rika yi ke ma ya boye ki, ba zai iya shiga ciki mutane kamar yadda yake yi a yanzu ba, kuma ba matsafi ba ne da yanzu ya bada ke ko kuma ya mallake ki sai yadda yayi da ke, idan kuwa baya duka biyun nan to yana siyar da kwaya, shiyasa yake samun mahaukanta kudi ko? Kuma shiyasa ya mallaki bindiga ta hanyar da be dace ba, saboda shirin ko ta kwana, domin ya san a tsakaninsu ma suna iya samun matsala da junansu, kin san sana'ar da yake ba sana'a ce mai kyau ba, shiyasa kike kokarin gina kanki kina son ki bar karkashinsa? Siyar da kwana ya kara masa karfi sosai da mutane ko? Da kuma jami'an tsaro shiyasa yake yadda ya ga gama? Kuma yana sha shiyasa bakinsa yake baki idonsa yake da ja kuma yake saurin fusata idan kika masa laifi sai kwakwalwarsa ta nuna masa dukanki ne kawai mafita"
Kallonsa kawai Emily take tana mamakin yadda yake cankar abubuwa line by line a daidai.
"Na zo nan ne saboda mu yi maganar Vito?"
"Aa kin zo nan ne saboda mu yi maganar ki da kuma tawa"
Ya zauna.
"Mutane za su yi mamaki idan suka tarar da ni a office dinki, na sakan shiga office kowa na so karbar abu ko hannatawa da kaina idan bana bukatar wani ya shiga tsakani, amman ban taba zama office din kowa ba sai Emily"
Ya duba agogo hannunsa.
"Da farko zan fara da baki hakurin abubuwan da suka faru, matata bata fahimce ki kuma tana da zafin kishi"
Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya cigaba.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[5/22, 7:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣9️⃣
"Sunana Aliyu Aliyu AA Bappa Mudallab, sunan mahaifina Aliyu Mudallab amman ana kiransa da Bappa Mudallab kasancewarsa da na farko a gurin mahaifinsa, mahaifina dan siyasa amman a baya yayi aikin gobnati kamin ya sinci kansa a siyasa, ya fara da commissioner kamin yayi dan majalisar hijar kaduna har sau uku daga baya ya tsallaka zuwa tarayya neman sanata, mahaifina manomi ne sosai, kusan siyasar ta karbe shi ne kawai har yayi suna a ciki, amman abun da ya dogara da shi muma muka jingina, ni kaina na kam taba noman a lokacin damina, mahaifina kuma yana nema a rana da damina da baraza, yana da gonaki da gidajen shanu da ake saffara Madara da Fresh kirdirmo, da manshanu, haka kuma mahaifina yana kiwon fili da kaji.
Mahaifiyata kuma mace ce da bata komai sai rainon yayanta uku da Allah ya bata, Ummi bata sana'ar fari balle na baki, mu uku kawai ta haifa Yayana Yusuf, sai kuma ni Aliyu sai kanwarmu da ta zo bayan an fidda rai da samuwarta wato Ramla. Ummi ita kadai ce a gurin Mahaifinmu bayan ita be sake auren wata matarba, kuma har yanzu ba mu taba jin wani abu tsakaninsu ba, ko da yake ita da shi yayan wa da yayan kanwa ne, wato su kansu abokan wasan junansu ne. Yayana samanin tattalin arziki ne, gwararre ne sosai a bangaren Economics shiyasa mahaifinmu ya dauke shi ya damka masa rabin ragamar kasuwanci a yanzu shi yake tafiyar da komai, Mahaifina kuma ya maida hankali gurin Siyasa, ni kuma na karanta Engineering ne wannan ya saka ake yawo da ni gari gari gurin aiki, na zauna a sokoto na yi zama a Kano na zauna a Lagos daga baya aka dawo da ni part hart-cour, tarbiyar gidanmi Alhamdulillah Ummi ta yi kokari da jajircewar Daddynmu, ta bangaren karatun addini duk gidanmu babu rago, ba dan karki ce na yi son kai ba da sai na je na fi kowa kokari ta bangaren Karatu, domin na yi karantar wa a islamiya har uku ba dan a biya ni ba, sai dan na samu ladar kawai, hasali ma ni nake musu ihisani a duk wata, da dare kuma sai na je wata islamiyar maza da ta zama majalisi na karo karatu, a islamiyar ne ma na hadu da matata wadda nake aure a yanzu, Kameela. Dalibata ce mai kokari sosai tana da kaifin basira tana yawan zuwa makaranta even though dai takan taba rashin jin magana sosai a makaranta domin ana yawan kawo min kararta, amman ni ban duba wannan ba, na duba karatunta ne domin ni ina son mace mai addini saboda yayana su samu uwa ta gari, sai dai kamin mu auri junanmu mun sha gwagwarmaya saboda iyayenta bata so na, ni ma kuma Ummi na ba wani gamsuwa ta yi da auren ba kawai dai ta mara min baya ne saboda tana son abun da yayanta suke so, banbanci jam'iya da kuma yin nasara da faduwa ya yi tasiri sosai a gurin iyayenta har ta kai suna kallonmu a matsayin makiyansu, ada abun ya fi haka tsami ma, amman dai auren mu ya saka an yafe wasu abubuwa wasu abubuwan kuma an ba shi baya, a lokacin akwai masu son Kameela ita kuma ni take so, iyayenta kuma Governor da yake Mulkin garin Kaduna a yanzu His Excellency Rilwan Mu'azu Mai Nasara shi suka so ta aura, domin abokin mahaifina ne kuma gashi yana Governor, da ta aure shi ita ce zata zama first Lady domin matarsa bata yi karatu mai surfi da zata iya tsayawa a gaban mutane ta yi turanci ba, amman kishi be bar Kameela ta amince da zabin iyayenta ba, kuma kishi be bari kudi ya rufe mata ido ba. Kameela mace ce mai kishi sosai gaskiya, daga lokacin da na fara soyayya da ita na gano haka, bata bari kowace daliba ta kalle a inda nake karantarwa, tun ina boye alakarmu ina jin kunya sai ga shi ta bayyanawa duniya, yadda take yawan fada da dalibai a makarantar a kaina sai ki dauka ni kadai ne namiji, kuma wasu da yawa ba so na suke ba kawai gaisuwar mutunci ce da girmamawa a matsayina na Malaminsu amman duk bata duba wannan ba, an kai ruwa rana tsakanina da iyayenta da kuma iyayena har ta kai na ce ni na janye daga auren saboda ba zan dauki wulakanci ko raini ba, sai dai damuwar da Kameela ta shiga a lokaci saboda tana tsananin so na ya saka na dawo na yarda zan aureta, amman duk wani hidima da ake ta biki like event ban yi ba sai ta Walima ita ta maza kawai ban da mata, ita ma ta yi nata dabam, amman wani shagalin biki da zai janyo shidai a lamarinmu ban aikata ba, kasancewar ni ba mutum ne mai son bidi'a ba, shekara daya da aurenmu Allah ya ba mu karuwa, amman abun be zo da rai ba, yanzu haka Kameela tana gida gurin wankan amman ta gama tana shirye shiryen dawowa ne, lokacin da kika kira ni naje ganinta ne wayar tana hannunta, kin san mace mai kishi bata iya rike kanta idan ta ji muryar wata macen a wayar mijinta, amman dai na ja mata kunne, wannan shi ne takaitaccen labarina, ina fatar a yanzu hankalinki zai kwanta da Aliyu"
Ta yi murmushi sosai ta ji dadin yadda yake tsara mata labarinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali muryar ma kasa kasa kamar mai magana da karamar yarinya.
"Ba ki tambayi ya aka yi na san Turhan ba, ko ya aka yi ni da shi muka zama abokan juna"
A take murmushin dake fuskarta ya gushe, Aliyu ya saci kallonta kadan.
"Kamar na taba fada miki mahaifina yayi rashin nasara har sau uku ko? Sai a na hudu ya samu nasara? Toh a rashin nasararsa ta farko gurin takarar sanata bayan ya fadi zabe sai Shugaban kasa na wacan lokacin ya nada shi ambassador Nigeria to Sudan, a lokacin ne ya tafi har da ni domin Ummi bata yarda yaranta su yi nesa da ita, kusan da mu take shawarar komai da mu take hira kuma Allah ya dora mata son yaya kamar dai yadda kike ji Fatima a yanzu, da muka koma can sai kyakkyawar alaka ta shiga tsakanin Sarkin Sudan na yanzu da kuma mahaifina"
Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude.
"Na manta ban fada miki ba, ni mutum ne mai son wasan tseren doki, wani da wata wasa sai ita a koda yaushe idan na samu free time haka zan hau doki na yi ta zaga gari, idan kuma akwai gurin wasan zan tafi na yi, a Khartoum muke zaune babban birnin kasar sunan a birnin akwai wani babban filin wasa na wasa da dawaki, na kam tafi yin wasa duk Weekend, duk yadda nake da son wasan dokin nan Turhan ya fi ni, kuma ya fini gwanewa domin shi dan sarauta ne ni kuma haye na yi, a duk lokacin da muke je wasa akan shirya tsare tsakanin yayan manya ko yan sarauta, wata rana sai aka hada mu na nuna gwanewa shi kuma ya nuna min ya fi kwarewa akai, da haka dai muka sabu ya zama mun san junanmu idan an shigo za a gaisa, har kai idan na shigo be shigo ba wasan baya dadi ni ma bana shi dadi haka shi ma ta bangarensa. Muka fara following juna da a social media, har ta kai muna gaisawa a waya ko chat, har mukan hadu mu yi hira ko mu tafi wani gurin shakatawa da dawaki. A lokacin Turhan ba shi da ikon shiga Nigeria ba Nigeria kadai ba mahaifinsa be yarda ya bar kasar ba, har ya kan bukaci na ba shi tarihin Nigeria da yadda kasar take, da ya ji cewar daga kaduna na fito sai yake ba ni labarin mahaifiyarsa yar kaduna ce amman baya zuwa gurinta mahaifinsa ya hana shi fita Kasar saboda kar ya tsallaka ya tafi gurinta, amman ita an mata lamuni tana zuwa ganinsa, kuma suna magana da waya, wata rana tsaman sai gashi ta shigo da kokon bararta gurin Mahaifina ta hanyar Ummi, tana son Daddy yayi mata tsaye a bawa Turhan damar ziyararta a duk lokacin da ta so, mahaifina ya sha wahala sai da ya jajirce sannan sarkin ya yarda domin ganin yake kamar Ammy zata karbe masa Turhan ne, kuma su a gurinsu bakar fata ba shi da wata kima, like kamar mahaifin Turhan be so mahaifiyar Turhan ta zama bahaushiya har Nigeria ba, mu kan mu saboda muna yayan manya ne a lokacin ya saka ake daga mana kafa a dole, mahaifina yayi nasarar karya dokar sarkin aka bawa Turhan damar ziyararta kasar a duk lokacin da ya so, saman kuma bayan ni yana da wani amini Munir dan Nigeria ne sosai shi kuma a can yayi karatu a can yayi rayuwa daga baya ya dawo gida, Ummi ta san Turhan, Ammy ma ta san ni ta dalilin abota da kuma abubuwan da suka faru, sai ya zama abotarmu ta kara kwari sosai, kusan rabin hausar da ya iya gurina da Ummi da yaran da Ummi take riko a lokacin ya koya, daman kuma na tarar da shi mahaifiyarsa ta shimfida masa kaunarta da yarenta da rabin al'adarta a zuciyarsa da kansa, amman ma kaunarta Turhan yana son Ammy sosai, daga haka abotarmu ta daure har yau"
Ya sauke numfashi a hankali.
"Na yi mamaki da na ji kin tsani Turhan har kina gudun ganinsa, domin ban san wani hali mummuna na Turhan ba, shiyasa na kagu na ji wane irin zama kuka yi da shi, taya rayuwarsa ta sauya har ya munana miki haka?"
Emily ta kalli hannun Aliyu dake sanye da agogon data dawo masa da shi.
"Baka yi tunani ba? Da ace ni yar sarki ce ko kuma balaraba kamar shi ba zai wulakanta ni ba? Farkon abun da Turhan ya fara kushewa a tattare da ni shi ne halittata, kamin ya muzanta tubana, sannan ya kaskanta asalina"
Ta yi shiru idonta na cika da hawaye. Ya dauki takardar a gabanta ta ciro pen a aljihunsa ya dora