Showing 42001 words to 45000 words out of 249044 words

Chapter 15 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14989

da farincikin dole sannan ta tura kofar da shiga.

“Hello Big Guy”

"Dariya yake amman yana ganinta sai ya hade rai ya juya baya daga kan gadon da yake zaune”

“Har yanzu fushi kake da ni London?”

“Sannu da zuwa”

Chidimma ta fada, ta mike tsaye London ya rike hannunta alamar baya son ta tashi. A haka dai Emily ta danne zuciyarta ta karasa kusa da shi ta gefen da fuskarta take ta leke shi da murmushi a fuskarta.

“My Handsome Guy...”

Aiko yace me zai mata ba ihu ba, yana ihu yana matsawa nesa da ita kai kace be santa ba ne, ko ayi zaton sace shi zata yi. A gurin ta watsar da kayan dake hannunta cikin tsawa da fara magana.

“Kullum damuwata akan yarana ne, tun ina karami ban san wani wanda ya damu da matsalata ba, ban san wani wanda ya damu da farincikina ba, kowa da na gama masa amfabi jefar da ni yake, guduna yake yanzu kuma ta kai har ga Yayana? To ka zauna da wanda kake so”

Ta fice daga dakin a fusace. Chidimma taja shi jikinta ta rumgume jikinsa sai rawa yake domin ba kasafai take masa fada ko tsawa ba.

“Momy bata son London, Momy ta yi fushi ta tafi ta gurin Fatima, Fatima kawai Momy take so, bata son London, ta gaji da London ta tsane shi”

Tana masa maganar tana shafa bayansa.

“Bata son yayi wasa da kowa, amman Chidimma tana son London tana barinsa yayi wasa da ruwa tana fita da shi yawa”

London ya bata rai sosai ya labe a jikinta kamar zai yi kuka, sauka ta yi daga kan gadon ta duka kasa.

“Hau bayana zamu yi doki”

Da sauri ya hau yana dariya domin yana son kalar wasar da take masa.



TURHAN POV.

Sai da Faruk ya gama yi mata bayanin dalilinsu na zuwa gidan da turanci, domin Turhan baya jin turanci sai larabcin Sudan sai kuma hausar da ta kasance yaren mahaifiyarsa.
Matar ta yi murmushi ya gyara zaman kujerar da ta yi mata kadan kasancewar kujerar one seater, ita kuma mace ce mai jiki sosai ba kadan ba.

“Bani da wata alaka da Emily a yanzu, tana raye ko a mace ba matsala ta bace, ban kuma damu na san kowane irin hali take ciki ba, mu dai mun daukota daga gidan marayu ne da nufin bata kyakkyawar rayuwa da gata, sai gashi ta watsa mana kasa a ido ta gudu ta bi saurayinta, idan ma wani laifin ta yi muku ko to ku tafi can wani gurin ku nemata, bana da alaka da ita a yanzu”

“Amman baki san wata hanyar da zamu iya ganinta ba? Ko jin labarinta? A lokacin da ta bar nan kina da labarin inda ta koma da zama”

“Ban sani ba”

Ta mike tsaye ta fice ta bar musu falon, Faruk ya fadawa Turhan abun da ta fada, sai ya tabe baki yana magana da kakkausar murya.

“Butulu ce ma shiyasa ba zata ga daidai ba a rayuwarta, gashi nan ta zo ta shiga tsakanina da mahaifiyata, an kai karshen ba zan sake nemanta a ko'ina ba yanzu”

A tare suka fito da Faruk suka shiga mota, kamin su isa masaukinsu Turhan ya kira mahaifiyarsa a waya, sai da yayi mata kira biyu sannan ta daga wayar.

“Hello Ammy”

“Kuna lafiya?”

“Lafiya kalau, Ammy na yi iya yadda zan iya, na yi neman yarinyar nan har na gaji ban samu inda take ba, macen da ta rike ta ma tace bata da labarin inda take a yanzu, ban san ya zan yi ba Ammy”

“Ban cilasta maka nemanta ba Turhan kai ka cilastawa kanka”

“Amman Ammy fushi kike yi da ni fa, idan ban samu yarinyar nan ba ba zan samu yadda nake so a gurinki ba”

“Na dade da yafe maka, kuma bana fushi da kai, iyakar abun da na sani shi ne, Aisha ta tafi da farinciki, ta tafi ta bar min wani tabo da na kasa kankare shi a zuciyata, a duk lokacin da na kalleka sai na ga wannan abun a tare da kai, a dawo lafiya Allah ya tsare hanya”

Ta aje wayar. Turhan ya ji kamar ya buga kansa da motar.

“Allah ya kara tsine miki albarka Emily mushirikar banza, yadda kika jefa rayuwata a matsala kika raba ni da mahaifiyata Allah ya hana farinciki kusantarki”

Ya dafe kansa ya rufe ido, a yanzu kam ba shi wata babbar makiyiya irin Emily. Macijiyace yarinyar nan kawai rabar mutane take tana cutarsu haka zuciyarsa take raya masa. The fallowing day yayi sallama da Faruk yayi masa alheri sannan ya kamo hanyar dawowa Kaduna.
Yana sauka Airport ya sanarwa mahaifiyarsa babu bata lokaci da aika masa da direba ya dauko shi zuwa gida.
Ko da ya iso ya samu an shirya masa abinci mai kyau a dinning, amman be kula komai ba saboda hankalinsa yana gurin mahaifiyarsa, dakinta ya shiga sai ya zame ta zaune tare da Jawahir suna dariya da alama hira suke, sai dai shigowarsa ya saka Ammy sauya dariyarta zuwa murmushin da ba kasafai take masa ba.

“Sannu da zuwa”

Jawahir ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin. Cikin wata irin tafiya ta kaisaita daya saba yi ya karasa gaban mahaifiyarsa ya zube kasa ya zauna.

“Barka da yamma Ammy”

“Barka Labarabe”

Ya dan dago Kadan ya kalleta ya maida kansa kasa.

“Ammy ki yi hakuri da abubuwa da suka faru, na yi ina yina a yanzu amman ban samu ganin Aysha ba”

“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”

“Ameen”

Ammy ta mike tsaye da nufin bar masa dakin sai ya sha gabanta da fadin.

“Na yi zaton komai zai wuce idan na dawo, Allah dai ya gani na iya yadda zan iya akan yarinyar nan abu ya gagara, Ammy ki daina bari ana zuga ki kina juya min baya”

Jin haka ya saka Ammy ta dawo ta zauna.

“Su waye suke zuga ni?”

“Jawahir mana Ammy, ita take tare da ke kullum wasu abubuwan ita zata saka ki yi min, saboda bata san zafinki ba, ba ke kika haifeta ba”

“Kai da kasan zafina ai gashi nan na aura maka yar mutane ka watsa min kasa a ido”

“Dan kuskure kadan ne na aikata Ammy, dan haka”

Ya nuna kan akaifarsa.

“Amman gaba daya kin canja min, kuma iyakar biyayya ni na san na miki, bana son yarinyar nan kika ce na aureta na daure a haka na aureta, addininmu ba daya ba, na san a lokacin da na aureta ta musulunta amman yawanci ai musuluntar karya suke yi saboda su yi makirci, kaskanci ne a gurin namiji irina, jinin sarauta kuma jinin larabawa ya auri mace irin Emily, sam bata cikin irin matan da nake so, ya kamata ki duba min Ammy”

Fuskar tausayi ta bayyana a fuskar Ammy.

“Baka fada min baka sonta ba a lokacin da na hada aurenku ba ba zan cilasta maka ba, Allah kadai ya san kalar azabar data sha a hannunka da masarautarku, baiwar Allah”

Ya dago yana kallon Ammy cike da mamaki, shi a tunaninsa idan na fada mata duk wannan zata tausaya masa ne, madadin haka sai ta kara jin tausayin Emily din ma.

“Haka ne, kaskanci ne auren wanda ba bata tashi a addinin musulunci ba, kuma wanda ba yarenka ba, ba yar sarauta ba ina mai baka hakuri akan hakan Dan sarauta”

Ta mike tsaye ta fice daga dakin.

“Da ace zan samu damar yin ido biyu da Emily a yanzu, tabbas zan bata hakurin saboda Ammy, amman bayan kwana biyu sai na hada ita da bokanta na kashesu, yarinya kamar mayya gaba daya ta tafi da zuciyar Ammy, ita wacan katuwar kafirar maganin be kamata ba sai Ammy, ni kadai ta haifa a duniya amman yanzu ta tsane ni saboda wata shegiyar yarinya.. عار عليك يا إميلي,
”عار عليك

Yama fadar yana wargar da hannu, be san kaskanci da wulakanci ba sai da Emily ta duro gidansu, tashi yayi ya fice daga dakin ya shiga dayan dakin yayi waya da matarsa da mahaifinsa sannan yayi wanka ya fito falon.

“Tun kamin na yi aure, ina addu'ar idan na yi aure Allah ya bani ya mace, sai gashi kuma da na yi auren na haifi namiji, sai ya zama ba zan sake haihuwa ba, a lokacin da Aysha ta zo gidan nan sai na ji kamar addu'ar da nake yi ce a can baya Allah ya karba min ya ba ni ya mace ta wani bangaren da ban yi zato ba, yarinyar nan ta tsaya min a rai”

Labarin da ya sauko ya samu Ammy na bawa Jawahir kenan, Jawahir din kawai ya kalla yana ayyana munafurcinta a zuciyarsa ya fice ba tare da ya taba abincin da aka jera masa a dinning ba. Bayan fitarsa Jawahir ta kalle Ammy.

“Dan Allah Ammy ki yi hakuri ki cire Aysha a zuciyarki, ki kaddara ta mutu, ki shirya da Ya Turhan ku dawo kamar yadda kuka a da, Wallahi tausayi yake ba ni”

Ammy ta kalleta tana murmushi.

“Baki san waye mahaifin Turhan ba shiyasa yake baki tausayi, larabawa suna da zuciya mai tauri, shi kuma ai jinin mahaifinsa, nonon ma na larabawa ya sha ba nawa ba, kar yi mamaki idan aka ce miki ya sake aikata kuskure bayan wannan”

Jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai cike da tausayi.


ALIYU POV.

“Tun jiya da aka kawo ki asibitin nan kike fushi da ni, ko dan rantsuwa da alkawarin da na daukar miki ai ya kamata ace kin yarda da ni”

“Cikin alkawarin da rantsuwar ai na ga chat dinku”

“Ke yanzu ko a mafarki aka ce miki ina son Emily zaki yarda”

Ta dube shi kamar zata yi kuka.

“Har ka rike sunanta ma”

“Turhan fa ya auri yarinyar nan kuma har sun haihu da ita, Turhan kuma abokina ne mahaifiyarsa kamar uwa take a gareni, taya zan iya soyayya da ita ma balle har nace zan aureta? Kuma addininmu ba daya ba, ba abun da kike tunani ba ne”

“Yanzu dai gashi nan ai ka janyo min nakuda Edd na be cika ba amman gashi nan nakuda ta same ni, kuma gashi sun ce idan ban haihu da kaina ba za su min CS”

Ya rumgumeta.

“Zaki haihu da kanki lafiya In Shaa Allahu”

“Me yasa ba zaka fadawa Turhan gaskiya ba, bayan kasan nemanta yake idan har baka da wata manufa akanta? Ka san yadda Turhan yake son haihuwa amman baka fada masa yana da ya ba, idan baka da wata mummunar manufa akansa miyasa ka yi haka?”

Tana maganar tana cige baki tana numfashi da karfi.

“Idan Allah yasa kin haihu lafiya wan warware miki komai”

“Allah dai yasa na haihu lafiya, Allah yasa na tashi Wallahi babu wanda zata aurar min miji Wallahi Allah kuwa na rantse”

Shi dai kallonta kawai yake be yi zaton tsananin kishinta ya kai haka ba sai yau.

“Ummi bata iso ba har yanzu?”

“Ta iso kin san ai ta fi kusa, ta sauka gida ne sai ta yi wanka zata zo, su Hajiya ma suna hanya”

“Ka min addu'a Aliyu”

“Ina ta yi”

Ya shafa kanta yana ta karanta mata addu'o'i.
Misalin karfe goma sha daya na safe iyayen Kameela suka iso asibitin, a lokacin nakudar ta taso mata gadangadan ya fito waje sai addu'a yake yana kai da kawo. Da waya ya kwatanta musu gurin da yake har suka iso, kana kallon mahaifiyarta zaka fahimci tana cikin tashin hankali haka ma yayarta. Cikin ladani ya gaishe su kamar yadda ya saba mahaifiyar ta amsa rai a hade domin Kameela ta labarta mata komai ta waya.

“Hajiya ai da kun wuce can gidan kun dan huta tun da ni ina nan”

“Aa kara dai zamana kusa da yata, tsayuwarka a nan wani amfani yayi mata, ba kai ne sanadin duk wannan ba”

A take Anty Shafa wacce ta kasance yayar Kameela ta karbe zancen Hajiya ta dora da nata.

“Gaskiya Aliyu baka kyauta ba, kasan matarka tana da ciki be kamata kana yin wasu abubuwan ba”

Aliyu ya kalli Anty Shafa da duba na tsanaki.

“Me tace na yi.?”

Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dauke kai da tayi. Ya ciro wayarsa yana amsa kiran mahaifiyarsa.

“Okay Ummi bari na zo na dauke ki”

Ya sauke wayar, ya kalli sarakuwarsa.

“Zan je na dauko Ummi daga gida yanzu”

“Toh”

Ta amsa masa a takaice cikin bacin rai. Aliyu ya saka kai ya fice cikin rashin jindadi, daman ya san za a rina domin Kameela bata da sirri ko kadan mu'amalar auratayya ma sai ta fadawa kawaye ta, be yi mamakin dan ta fadawa iyayenta sanadin nakudarta ba, wannan halin nata na rashin sirri yana bata masa rai sosai.
Ko da ya isa ya samu Ummi a harabar tana jiran isowarsa.

“Ummi madadin ki zauna a ciki kika fito waje”

“Idan ka iso ai zaka iya dadewa shiyasa na tsaya jiranka a nan, mu tafi”

Kamin ta shiga motar ya fito da sauri ya zagayo ya rumgume ta.

“I miss you Ummiiiiii”

“Kai wai baka san ka girma ba, baka jin kunyata”

“You're my best friend my first love”

Ya je zai sumbance ya ta tureshi ta bude motar ta shiga, dariya yayi ya koma motar yaja suka fice daga gidan, suna tafi suna hira har suka isa asibitin ya zagaya ya bude mata ta fito ya suka jera zuwa gurin da ya bar su Hajiya dazun.
Ummi na hango Hajiya da Anty Shafa ta kalli Aliyu.

"Kasan ka fadawa iyayenta sun zo to ni miye na fada min na zo?”

“Ke ma ai mahaifiyarta ce”

“Idan ba mahaifiyarta a kusa ba”

Ummi ta dan sham kamshi domin ko kadan bata son raini. Anty Shafa ce ta fara gaishe da Ummi sannan Hajiya ma ta miko mata gaisuwa.

“Lafiya kalau”

Daga Hajiya har Ummi babu wanda yacewa wani an iso lafiya.

"Allah dai yasa ta haihu da kanta, idan ba ita ba haushe zaka dauki halin da namiji ka saka a zuciya”

Cewar Anty Shafa. Ummi ta yi kasa da ido tana saurarenta, kamin ta dago ta kalleta tana murmushi.

“Shafa ya yaran? Ya Step Mom dinku? Har yanzu dai shiru kin ki kawo mana kati?”

“Ina nan ina lalabe Ummi kin san mazan sai a hankali, yara suna lafiya”

Ta amsa cike da gatse.

“Haka ne Allah ya kawo na gari”

“Ameen”

Ta amsa. Aliyu ya ciro wayarsa dake ringing ya fice daga gurin, Ummi kuma ta nemi guri ta zauna Hajiya nata safa da marwa tana daga hannu tare da rokon Allah ya saukar da Kameela lafiya.

“Ameen ya rabbi, idan ba sakarci irin na Kameela ba, yaushe namiji zai maka alkawarin ba zai kara aure ba ka yarda, gashi nan ta jawa kanta nakudar dole”

Hajiya ta juyo ta kalleta.

“To miye laifinta? Allah dai ya bude mana idonta lafiya?”

“Ameen”

Ummi dai bata ce komai ba sai saurarensu take, ta san kuma saboda ita ake yi dan ta ji. After like one hour Kameela ta sauka lafiya sai dai abun da ta haifa be zo da rai ba. Hakan kuma be hana iyayenta mijinta da surukar murna ba domin ita dai ta haihu lafiya bayan ta sha wahalar nakuda.
Sai da Aliyu ya rada ma yaron suna sannan aka yi masa sallah aka binne shi a makabarta musulmi dake garin Part-harcour.
Ko kadan Aliyu be jidadin yadda yaron ya zo babu rai ba, sai dai babu yadda xa'ayi da hukuncin Allah sai hakuri, ganin yanayinsa ya saka Ummi ta hade maganganunbda take da su a zuciyarta ta daga masa kafa.
[4/22, 9:24 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL


🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️


Page 1️⃣5️⃣

Ta hado tea ya kawo ma Ummi.

“Ni ba irinka bace, me zan yi da tea yanzu da yamma"

Murmushi yayi ya zauna yana updating status dinsa domin sanar da duniya matarsa ta haihu amman dan be zo da rai ba. Bayan ya gama ya aje wayar ya kai hannu zai dauki tea kiran Kameela ya shigo wayarsa, fasa shan tea yayi ya dauki wayar.

“Hello...”

"Kana ina“

“Ina gida“

“Tare da wa?"

Ya kalli Ummi sannan ya amsa mata

"Tare da Ummi"

"Na ji Hajiya tana maganar wai zata tafi da ni gida gobe idan an sallame ni”

“Kamar al'ada ce ko mace ta koma gida idan ta yi haihuwar fari”

"Bana son na barka, ni bana son tafiya, za a iya min komai a nan mana"

"Haka ne amman idan ta nuna tana son tafiya dake ba zamu iya hanawa ba”

“Ina son idan ta maka maganar tafiyata kace mata aa kana son na zauna a nan din"

Yayi shiru be ce mata komai ba jin hakan ya saka ta kashe wayarta, domin ita ma ta san mijinta ba kasafai take saka shi abun da be yi niya ba.

"Kameela ce?“

“Bata son tafiya gida, ni kuma ba zan iya jayayya da iyayenta ba, bana son abun da zai kawo mana rashin jituwa musamman da Hajiya“

"Rashin jituwa na nawa kuma? Bayan wanda aka sha kamin auren?”

“wacan ai ya wuce Ummi, kuma tun daga lokacin sun san ni ba kanwar lasa ba ne, Aliyu kike ji fa Ummi”

Ya fada yana murmushi, Ummi ta tabe baki.

“Aliyu soyayya? Romeo baban kauna, sharukan din masoya? Mai alkawarin da ba zai iya cikawa ba”

Ya kalleta da dan mamaki still yana murmushi.

“Ummi ina kika samo duk wannan kuma?”

“Baka yi alkawarin cewar ba zaka kara ma Kameela abokiyar zama ba?”

Ya rausayar da kai.

“Ta fada miki ne?"

“Aa ai kasan iyayenta ba yan dattako ba ne, sun fada dan na ji kuma na ji"

Ya shafa kansa.

"Idan baka yi hankali ba, kishin Kameela sai ya halakata ya jefaka a matsala, domin zafin kishin yayi yawa, madadin kai kuma ka nuna mata abun da take yi kuskure ne sai kawai ka shimfida mata tabarma ta hau, akan wane dalili zaka mata alkawarin ka haramtawa kanka abun da Allah da kansa ya hallata maka? Kai da malami ne Aliyu, ban yi tsammanin wannan daga gareka ba”

“Ummi baki fahimta ba ne”

Ummi ta hade rai.

“Toh fahimtar da ni“

Ya gyara zamansa ya aje wayarsa gafe.

“Ummi ke kika haife ni, kin san halina ciki da waje, tun kamin na yi aure ke kin sani, bana da ra'ayin auren mace sama da daya, Allah ya hallata mana auren mace mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login