Showing 78001 words to 81000 words out of 249044 words

Chapter 27 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14975

a duniyar sai naki, bana jin akwai wanda ya zame min wajibi na kula da shi sai ke, ina son ki Emily ko a ina nake tunaninki nake, duk wani abu da nake kauna a duniya bayanki yake"

Ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali.

"Baki tunanin lokaci yayi da ya kamata mu bawa junanmu farin ciki? Ya kamata ki bude zuciyarki ki manta da baya da rayuwar baya, a ganina lokaci yayi da ya kamata ace jira ya kare tsakanina da ke"

Ta dago daga jikinsa ta kalleshi.

"Emily lokaci yayi da ya kamata mu yi aure"

Ta ji gabanta ya fadi ba tare da dalili ba.

"Kin san ni kin san waye ni, na san ki kuma na so ki, kuma kin san cewa har kasa ta nade wani be isa ya so ki ba sai ni, toh bata lokaci na miye? Har zuwa yaushe zan yi ta jiranki?"

Ya kama hannunta.

"Na lura baki son na taba ki a yanzu, shiyasa nake daga miki kafa, a yadda nake sonki na fi son mu yi komai cikin farin ciki, kuma auren ki kadai ne zai tabbatar da hakan"

Ta zare hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tsaya ba tare da ta ce komai ba.

"Kina jiran mutanen da suka wulakantaki ne su dawo miki? Ko kuma wani kike dako a gaba? Mutanen da suka rasa ki sun rasa ki kenan har abada, wanda kuma yake zuwa nemanki idan wani abu ne a zuciyar sa toh yana wahalar da kansa ne kawai domin ke mallakina ce kamar dai haka"

Ya cire zobe hannunsa ya nuna mata sannan ya maida zoben a dan yatsansa. Ya mike tsaye ya fice daga dakin ya barta tsaya tana mamaki da tambayar kanta wa ke zuwa nemanta? Wata kila Tasmia ce, amman namiji yace, bayan Aliyu bata san wani namiji da zai zo nemanta ba, ko kuma Turhan ne? Ta tambayi kanta, for the first time bayan dawowarta gidan ta ji tana bukatar wayarta, wayar da tun a ranar da London ya mutu bata sake bi ta kan wayar ba, a zamanta nan kuma tunaninta ya tafi a gurin danta da ta rasa bata damu ta nemi wayar ba.

Tun da ya dawo da ita gidansa bata fita ko'ina daga cikin gidan sai harabar gida, ya dauko Chidimma da Fatima ya dawo da su gidan a tare da ita ga kuma mahaifiyarsa.
Sai dai ko kadan Fatima bata son zaman gidan saboda mahaifiyar Vito da take ganin ta takura mata, kuma ga shi bata so bata masa biyayya Vito. Emily ta nufi kofar dakin ta fito ta sauko hawa na biyu a zatonta Vito yana gurin domin ya fi yawan zaman a falon dake hawa na biyu, a gurin ta zauna tana tunanin ko dai Aliyu ya bawa Turhan addireshinta ne ya zo nemanta? Ko kuma Aliyun ne da kansan yake nemanta.? Kamar an tsikare ta mike tsaye ta sauka falon na farko bata karasa sauka ba ta ji muryar Fatima tana ihu da fadin

"I hate you... I hate you"

Ta sauka da sauri ta nufi gurin da Fatima take tsaye Chidimma na gefenta tana rike da cups din da aka fasa, Vito na zaune kan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon Fatima fuska babu annuri.

"Me ya faru?"

"Me yake sabu a ciki? Rashin kunyar da yarki take yi ko kuma fadar bata son Vito a gaban kowa? Gaba daya yarinyarki bata da tarbiya, taya zata kalli idon mutumen da akarkashinsa kuke tana zaginsa?"

"Ki yi hakuri Momy ina iyakar kokari gurin ganin na gyara halayyar Fatima na san abun da take ba shi da kyau amman ita yarinya ce"

"Ina kokarin da kike yi nuna min na gani. yara nawa ne sa'ainta basa abun da take? Yarinya karama amman ta iya shiga idon manya? Idan ba Vito ba wa zai iya zama dake ko yarki?"

Sai a lokacin Vito ya mike tsaye domin ya ji mahaifiyarsa ta fara saka Emily.

"Okay that's enough"

Yaja Emily ya maida ita bayansa.

"Ba laifinta ba ne, wannan yarinyar da kika gani ga dukan alamu bakin halin mahaifinta ta dauko shiyasa bata kama da Emily ko kadan, saboda babu halin ta ko daya a tare da ita"

Fatima ta sake kallonsa

"I hate you i hatee youuuuuuuuu"

Ta kalli mahaifiyarta.

"Momi na ce miki bana son nan gida nake son tafiya bana son nan"

"Okay zamu je"

Emily ta amsa da sauri kana ta kalli Vito.

"Ina son zan koma gida"

Momin ta Vito ta yi dariya.

"Baki da ra'ayin kanki kenan sai na yarki? Karamar yarinya zata juyaki tana fada miki yadda zaki yi? Shiyasa kike kyale ta tana abun da ta ga dama?"

Emily ta daka mata tsawa.

"Yata ita kadai ta rage min a yanzu ba ni da wata bayan ita, abun da take so shi nake so, ki cire idonki akan yarinyata, tun da muka zo gidan nan kullum sai kin ce ga laifinta"

Momynta ta mike tsaye tana kallon Vito.

"Kajinta ko?"

Vito ya kalli Emily calmly yace

"Je ki jirani gurin mota, Chidimma zata hado kayanku yanzu zan kaiki gida"

Emily ta kama hannun Fatima suka fice daga falon, Chidimma ta sauke numfashi ta nufi Kitchen ta zuba cups din hannunta a shara sannan ta fito ta haura sama inda dakin Fatima da Emily yake.

"Kana ji tana fadar abun da yarta take so shi take so? Daman ina tunanin bata lokacinka kake yi a kan yarinyar nan baka yarda ba"

"Bana bukatar Emily ta so ni, tun da ni ina sonta hakan ya wadatar, na sani tuntuni ban gama shiga zuciyarta ba, amman da sannu zata gane kuma zata gode min ta kaunace ni, zuwa lokacin da ta rasa Lisa (Fatima) za ta gane bata da kowa sai ni"

"Idan kuma hakan bata faru ba fa?"

"Abun da yake nawa nawa ne har abada ke kin sani, dole zan yi ma Emily uzuri saboda ta sha wahalar rayuwa, kuma ta tashi bata da kowa bata yan 'uwan bata san kowa a jininta ba sai yaran da ta haifa, daya ya mutu sauran daya to me zai saka ba zata ki abun da yarta take ki ba?"

"Wai miye a wannan yarinyar da lekewa haka ne? Kana da kudi zaka iya samun kowace mace kake so a duniyar nan, idan ma fari ne akwai fararen mata, idan kana ganin kamar ita baturiya ce zaka iya tsallakawa ka auro wanda kake so wanda ta fita kyau da komai, ita wannan fa har ta haihu kana ta wahala da yaran da ba naka ba"

Ta nufi windows din falon ya daga curtains din yana kallon Emily dake tsaye jikin motarsa tana cizon hannunta.

"Abun ba daga kyau ba ne kawai, wani abu ne ya hada zuciyata da kaunarta ya daure, kamin ita ai na ga mata da yawa ban so kowa ba sai ita, bayan ita ban ga wata wanda zan iya so ba, yarinyar da dukiyata bata dame ta, sanin tana da damar da zata iya sakawa na wulakanta kowa akanta be taba burgeta ba, ita kadai ce macen da ta saka na ji ina sha'awar tara iyali, mutuwar danta nan tana da damar ta tuhume ni saboda ni na barshi na fita alhalin ba a barinsa shi kadai, amman bata tana ce min komai akan haka ba bata taba nuna min bacin ranta ba, a yanzu zuciyarta a bushe take, nakasassun mazan da suka rayu da ita basu gwada mata komai ba sai azaba shiyasa har yanzu bata san yadda zata so kowa ba"

Ya juyo ya kalli Mahaifiyarta.

"Akwai mata da yawa, amman masu irin halinta kadan ne, a idona kuma ita kadai ce, kuma baki fahimce ta, karki sake fadin wata magana marar dadi akan Emily indai kina so, ki so Emily...!"

Yana kawai nan ya nufi kofar falon ya bude ya fita, Emily na hango shi yana saukowa ta nufo shi da sauri tana hawaye.

"Vito I'm sorry kasan be kamata na yi magana da mahaifiyarka haka ba, raina ne ya bace kuma..."

Be bari ta karasa ba ya rumgume.

"Na fahimta"

"Zaka iya bata hakuri?"

"Eh, shiga mota muje"

Ya sake ta sai ta zagaya ta shiga motar Fatima daman ta dade a ciki zaune sai cika take tana batsewa kamar wata babba. Be jira Chidimma ta zo ba yayi ma motar key.

"Chidimma bata zo ba"

Be ce mata komai ba yaja motar suka fita daga gidan. Har suka isa gidan da ya tanadar ma be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba, amman hannunsa na rike da nata yana tuki da dayan hannun. Be gama farkin ba Fatima ta bude motar ta fita ta bar masa gambun a bude, fita yayi ya zagaya ya rufe motar ya budewa Emily ta fito tana kallonsa, ta kai hannu ta taba fuskarsa sai ya matsa baya ya bata hanya ta ratsa shi ta nufi cikin gidan shi kuma ya koma motar yaja ya fice gidan.
Ta samu gidan yayi kura yayi gummm irin na gidan da aka dade ba a shiga ba, guri ta samu kusa da Fatima ta zauna tana jin kewar danta London yana dawo mata.

"Kin ce zaki nemi kudi zaki yi gida mu bar karkashin Vito amman har yanzu ba ki yi ba"

Emily ta dube ta.

"Zan yi Fatima zan nema har ma dace zan zama miki irin rayuwar da kike so, ba ni da wani nauyi da ya rataya a wuyana yanzu sai na ki, amman ki daina abun da kike yi, ba haka yara suke ba, meyasa ke kika fita dabam?"

Ta yi shiru tana turo baki, Emily ta ja jikinta ta rumgume tana jin rashindadin fadan da ta yi mata a yanzu.

"Momy, yanzu tun da London ya mutu zan iya amfani da sunan mahaifinta a makaranta? So that yan ajinmu su daina min dariya?"

Ta tambaya murya kasa kasa, Emily ta hade wani abu daya tsaya mata a makoshi ta lumshe ido.

"I miss him"

Cewar Fatima cikin sautin kuka. Emily ma kukan take.

"I miss him too"

Ta kara kankame yarta hawaye masu zafi na sauko mata. A haka Chidimma ta zo ta same su bayan direban dake gidan Vito ya kawo ta.

"Zan yi kokari na baki rayuwa mai kyau Fatima, ni kam ba zan miki abun da iyayena suka min ba, ba zan taba bari ki ji cewar baki da kowa ba, ba zan taba wulakanta ki kamar yadda mahaifin London da naki suka yi ba, ina son jini ko yaya yake"

"Momy waye babana? Baki san bani da baba ba? To waye kuma baba na?"

Fatima ta tambaya tana lafe a jikinta. Emily ta share hawayenta da sauri.

"Idan kina son uba to ki rike Vito a matsayin Ubanki"

"Bana son shi"

Emily ta dago ta.

"Baki da hujjar tsanarsa, kalli gidan da kike zaune, makaranta mai kyau ya saka ki, ya dauki mai girka muku abinci, tufafi sai wanda kika zaba kike sakawa, a ciki wadanda na aura akwai wanda ya bani rabin rayuwar da kike ciki yanzu?"

Ta dauke da mari tana daka mata tsawa.

"Karki sake min maganar abun da ya shafi ubanki"

Fatima ta saka wani irin ihu ta dafe kunci, Emily ta tashi ta bar mata falon. Sai dai bata iya fushi ba dan haka ta dawo ta rarrashi yarta saboda tana jin babu mai rarrashinta sai ita ta rumgumeta, a tare suka kwana kamar yadda ta saba mata a yanzu tun bayan mutuwar London kullum a gado daya take kwana da Fatima.
Washe garin ranar bayan Fatima ta tafi makaranta Chidimma tana ta aikin gyara gida Emily ta shirya ta fita saboda tana jin gidan ya mata babu dadi. Taxi ta shiga ta tafi gurin sabuwar kawarta Tasmia daman bayan can ai bata da wani gurin zuwa. Bata same a apartment din nata ba dan haka ta zauna a gurin har sai da Tasmia ta dawo. Da gangan ta yi kamar bata gane Emily ba.

"Malama lafiya?"

"Lafiya kalau"

"Toh na ga kin zauna a nan ne"

"Ina jiranki ne"

"Kina jirana? Kin san ni ne? Wani abun zan miki ne?"

"Haba Tasmia"

"Malama ni fa ban san ki ba ban taba ganinki ba"

Emily ta mike tsaye.

"Karki fara wannan wasa"

"Fine na gane ki, amman fa gaskiya ba zaki zo ki janyo min matsala ba"

"Bana fatan janyowa kowa matsala, kin tsorata ne?"

"Yanzu dai ba wannan ba me kika zo yi nan"

Ta yi shiru na mintuna.

"Bana da gurin zuwa ne kawai na zabi na zo nan, kuma na ji anje nemana gida na yi zaton ko kece ko Aliyu"

"Ba ni ba ce, ni ba zan tafi gidanki ba yanzu kam, Aliyu ma ba shi ba ne domin be taba zuwa nemanki ba"

"Okay zan tafi, duk lokacin da kika ji zuciyarki ta natsu da ni, kin san gidana kuma kina da number da wayata, sai anjima"

Emily ta tafi ta barta tsaye a gurinta tana binta da kallo. A taxi ta dawo kamar yadda ta tafi a taxi ta shigo gidanta tana share hawaye. A falo ta samu Vito zaune Chidimma na zuba masa ruwa a cups.

"Do you take my phone?"

Ta tambayi abun da yafi zame mata wajibi a yanzu, domin jiya ta duba ko'ina bata ga wayarta ba. Vito ya kalli Chidimma yayi mata alama da kai sai ta tafi dakinta ta dauko wayar ta mikawa Vito da hannu biyu be karba ya aje cups din dake da sauran ruwa ya kalli Emily, sai ta juya da wayar bangaren Emily da hannu daya ta mika mata.

"Akwai wata number data turo miki sako har sau hudu wai ki kirashi ya damu da ke"

Emily ta karbi wayar da hannu daya sannan ta ware dayan hannunta ta wanke fuskar Chidimma da mari.

"How dare you take my phone? Har ki karanta min sako?"

"Ta saman screen na karanta sakon ni ban san password din ba ma, shi ma na kunna wayar ne kawai saboda na tabbatar tana yi saboda faduwar da ta yi a hannuna, bayan haka kuma na kashe ta kamar yadda take"

Cewar Chidimma cikin kuka.

"Waya aikeki daukar min waya? Tsawon kwanakin nan da na yi ban damu da wayata ba ashe tana gurinki?"

"Ba ita ta dauki wayar ba, ni na bata ta aje, amman me zai saka wani ya turo miki sako? Miyasa zai damu da ke?"

Vito ya bata amsa sannan ya dora mata da tambaya, Chidimma kuma ta fashe da kuka har da zubewa kasa.

"Burinka kai ka raba ni da kowa, so kake ka ga ina rayuwa cikin kunci, matar da na samu mai kyakkyawar zuciya ta rike ni a matsayin kawa yau naje ta nuna bata san ni ba, saboda ka lalata tsakaninmu ka firgitata"

Ta dauki ragowar ruwan da ya sha ta watsa masa a fuska.

"Ni na saka ya damu, zo ka kashe ni ka huta"

Ta wuce fuuuu ta haura sama, binta yayi da kallo sai kuma yayi murmushi ya kalli Chidimma dake ba shi hakurin ruwan da Emily ta watsa masa, ya rikota ya mikar da ita tsaye.

"Karki damu"

Ya fice ya bar falon. Emily ta shiga dakinta ta zauna tana ta haki kamar wanda ta yi yaƙi, ta kunna wayar ta cire Password ta shiga messages box dinta na sms sakon Aliyu ne kadai sakon da ya banbanta da sauran sakwanin dake wayarta na Mtn. Ta karanta duka sakwanin sannan ta gwada kiran numbersa.






ALIYU POV.


"Wato baki ma wani damu da ni ba kalli yadda kika yi kiba kika yi fari"

Yana maganar yana kai mata abincin da ta shirya masa a karamin falon mahaifinsu. Ita kuma tana rike da wayarsa tana abun da ta saba yi masa a waya, wato bincike amman har ta yi ta gama bata ga wani abun da zata zarge shi da shi ba.

"In ji wa? Wannan kibar fa ta haihuwa ce kowace mace tana yi da muke Video call baka gani ba"

"Aa waya ai rage miki kyau take rabin raina"

Ya sake kai mata wani spoon din.

"Kina nan kina cinyewa Alhaji abinci ko?"

Ta yi dariya tana kallon wayar da kira ke shigowa da number da babu suna a jiki, a take ta amsa kiran ta kara a kunne.

"Hello... Aliyu..."

Ta ji muryar mace tana ambaton sunan mijinta.

"Wacece wannan?"

"Emily ce"

Mai kiran ta amsa mata kai tsaye.

"Emily....?"

Ta furta da mamaki, Aliyu ya aje Spoon din hannunsa ya mika mata hannu.

"Ba ni wayar"

Ta mika masa kamar ba ita ba.

Aliyu ya dora wayar a kunnensa.

"Emily kina lafiya?"

"Ina lafiya"

"Babu abun da ya same ki?"

Kameela ta zaro ido tana sakin baki.

"Aa na kira ne saboda na riski sakonka a wayata"

"Okay, ina tare da Matata yanzu"

Gudun kar zuciyar Kameela ta sosu ko ta yi zargin wani abu ya saka be ce mata zai kirata ba sai kawai ya kashe wayar. Tsabar mamaki Kameela bata san lokacin da ta mike tsaye tana kallon Aliyu ba.


_______________________

Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[5/18, 7:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login