Showing 27001 words to 30000 words out of 249044 words
tare da tace komai ba.
“How are you?”
Kamar jira take sai kawai ta fasa masa da kuka, kuka sosai mai dauke da ihu kai kace yayi mata bushara da mutuwa ne, har sai da mai gadin da mai sharan harabar gidan suka mike tsaye suna kallonta. Be sake furta komai ba ya kashe wayar, ita kuma ta cigaba da kuka da karfi har numfashinta na rawa tana shafa sarkar Cross din dake wuyanta. Da sauri Mai gadin ya karaso kusa da ita yana tambayar lafiya, bata amsa masa ba ta mike tsaye ta shige falonta a kan kujerar falon ta jefar da wayarta da jakar ta haura sama ta shiga dakinta ta kwanta saman gado tare da jan filo ta rumgume tana cigaba da kuka sai dai wannan karon babu kururuwa...
VITO POV.
Ya aje bottle din Hennessy XO dake hannunsa that's Worth 430k, ya gayen dake kusa da shi.
“A siya min ticket din tafiya ina Port Harcourt yanzu nan”
“Okay Sir”
Ya jingina da kujerar da yake zaune gaba daya ransa ya bace jin kukan Emily da yayi, after like 10m gayen ya dawo ya sanar masa babu flight din da zai tashi daga Lagos to Port Harcourt yanzu sai gobe. Ya dago ya kalleshi.
“Ka fadawa manager Happy Home Hotel ya siya min ticket din tafiya Port Harcourt, a siye tickets din duka ina son tafiya yanzu nan”
“Okay Sir”
Ya sake komawa ya kwanta jikin kujerar da tunani biyu, mutumen da ya gani dazun da kuma kukan da Emily take, kokarin hada biyun yake yaga yadda za su zame masa daya ko zai samu amsar kukanta, sai dai zuciyarsa bata natsu da hakan ba. Yadda ya bukata haka maganer hotel din ya aiwatar aka daukar masa shatar jirgi private jet shi kadai daga Lagos to Port harcourt, tun kamin ya bar Lagos ya turawa direbansa dake port Harcourt sakon lokacin da zai sauka, so that ya zama cikin shiri. In less then awa biyu ya sauka Lagos daman daga Lagos to Port Harcourt 1hr 10m ne to nonstop flight. Yana sauka direbansa ya dauke shi a cikin 2022 -BMW X3 baka mai bakin gilashi.
Be sauka ko'ina ba sai gidan Emily, yana fitowa motar be tsaya rufewa ba ya nufi kofar shiga falonta da saurinsa irin saurin dake ake hadawa da guda, a falo ya fara cin karo da Fatima tana zaune a dinning tana shan cornflakes, kallonta kawai yayi ya dauke kai ya kalli wayar Emily dake aje kan kujera da jakarta, be taba komai ba ya haura sama ya tura kofar dakinta a hankali ya shiga. Talkaminsa ya fara cirewa sannan ya taka ya karasa bakin gadon yana kallon fuskarta a take zuciyarsa ta fara rawa ganin yadda fuskarta ta yi ja ta kumbura saboda kukan da ta yi, idanuwanta a lumshe tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take irin na yaran da suka gaji da kuka suka yi bachi.
Zaunawa ya fara yi a hankali sannan ya kai hannunsa ya dagota ya kwanto da ita a jikinsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, jira kawai yake ta farka ta fada masa wanda ya saka kyakkyawar sarauniyarsa kuka. Jin ana shafa fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali ta sauke su akan fuskar mutunen da murmushi ba shi da muhalli a gurin. Ta tashi zaune tana kallonsa sai na juya ta kalli gadon ta kalli agogo ta ga karfe biyar na yamma ta sake kallonsa.
“Yaushe ka zo?”
Ya ki ya amsa sai kallonta yake.
“Kace min zaka tafi Lagos? I thought kana can”
Nan ma be ce mata komai ba sai kallonta yake.
“Why are you here?”
Ya saka yatsansa ya shafe mata gefen bakinta.
“Waya taba ki?”
Kallon fuskarsa take zuwa kirjinsa da boturan rigar suke bude, sannan ta sake kallon fuskarsa sai ta fashe da wani sabon kuka.
“Kowa baya so na, babu mai bukatata a kusa da shi, Fatima tana bata min rai yau sauran kadan mota ta bugeta saboda ta bata min rai, na tafi asibiti London yace baya so na ya tsane ni”
Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta tare da dora chin dinsa saman kanta.
“Sai kuma wa?”
So yake ta ambata masa sunan wani dabam ba yayanta ba tace su suka bata mata rai, domin ya san ba zai iya taba yayanta ba, amman zai iya taba kowa bayan jininta. Ita kuma bata yarda sunan kowa ya fito daga bakinta domin ta san waye Vito ta san abun da zai iya, kuma ta san yadda yake sonta. Ya dago ta daga jikinsa ya rike fuskarta da hannunsa biyu yana kallon kyakkyawan idanuwanta.
“Akwai wanda ya taba ki bayan Fatima da London? Akwai wanda ya fada miki wata magana?”
Ta girgiza kai alamar aa, ya mutsa bakinsa kamar zai yi magana sai kuma ya saketa ya mike tsaye, kasa ya sauka ya shiga kitchen ya dauko mata ruwa ya fito har ya nufi stairs ya fara takawa sai kuma ya juyo ya dawo gurin da fatima take zaune a dinning ya kalleta.
“Idan kika sake batawa mahaifiyarki rai har ta yi kuka idonta ya kumbura kamar yau, sai na miki danyen hukunci”
Ya fada fuskarsa babu alamar wasa sai ma kara hade mata rai da yayi.
“I hate you, kuma Momy ba zata aureka ba”
Ta fada masa cikin tsiwa tana murguda baki. Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya dauke kai ya haura sama. Tana ganin haka ta mike tsaye ta nufi wayar mahaifiyarta ta dauka ta haura sama da gudu ta shiga dakinta, jakar makarantarta ta bude ta dauko kati da Aliyu ya bata ta zauna bakin gado tana cire password din wayar.
ALIYU POV.
Misalin karfe 3pm ya faka motarsa harabar gidan ya bude ya fito yana kallon bakuwar motar dake fake kusa da balcony. Bayan ya rufe motarsa ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Matarsa ya tarar a tsaye tare da wata bakuwar fuska dake rataye rike da karamin mayafi a hannu dayan hannunta kuma rike da jaka.
Aisha na ganin shigowarsa sai hankalinta ya tashi, ta juya ta gefen da bakuwar take tana tarewa dan kar Aliyu ya kalleta da kyau, domin atamfar dake jikinta da matse ta sai dai ba sosai ba, amman ta karbe ta yi mata kyau. Ta inda ta yi sa'a mijinta baya daga cikin irin mazan nan da suke son kallon mata balle kuma ya san halin matarsa da kishi ko a tv ya kurawa mace ido sai ta yi masifa balle kuma a zahiri, tun kallon farko da yayi ma bakuwar a farkon shigowarsa be sake kallonta ba.
“Sannu da zuwa”
“Sannu Babyna ya gidan?”
“Lafiya Kalau”
Yayi kamar be san da bakuwar ba ya shafa fuskar matarsa zai wuce sai ta gabatar masa da kawarta tana dan kareta.
“Tasmia ce ta zo mana”
“Maa Shaa Allah, ina mata barka da zuwa”
Ganin alamar be gane ta ba ya saka ta ce.
“Tare muka yi Secondary School”
“Nice”
Ya fada ba tare da ya kalleta sannan ya wuce zuwa dakinsa, tun da ya bada baya Aisha take kallon Tasmia ta ga ko ta kalli mijinta and yes ta kalleshi da kyau har ya shige ciki, Aisha ta dan canja mata fuska tare da jefa mata zagi cikin wasa sai dai har a zuciyarta ta ji zafin kallon da ta yi ma Aliyu.
“Yar iska me kike kallo? Da wani billenki a nan”
Tasmia ta kalleta ta yi murmushi.
“Masu ciki fa zuciyarsu a kusa take, daman gaki ba tsaye kin san ance short people suna da saurin fushi, wai su da fushi 5&6, ni kin ga tafiyata”
Ta nufi kofa, Aisha ta tsaya a gurin bakinciki ya hanata raka kawar da suka shafe shekaru ba su ga juna ba, sai ma binta da ta yi da harara. Aliyu na shiga dakinsa wayarsa ya fara cirowa ya aikawa Turhan da sako bayan ya gama karanta wanda ya turo masa.
“Yau gidan marayu hudu muka je ba mu dace ba, ko'ina cewa suke ba su santa ba”
“Baka amsa ni ba, Turhan me ya rabaka da yarinyar nan? Me yasa ka sake ta?”
Ya aika masa sannan ya aje wayar ya fara cire tufafinsa.
[4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣0️⃣
EMILY POV.
Tana shan ruwan tana shan ruwan tana ajiyar zuciya kai kace yar yarinya ce aka saka kuka, hannu ya kai yana shafa saman kanta har ta shanye ruwan, sai ya karbi kofin ya aje.
“Ba Fatima ce kawai ta saka ki a cikin damuwa ba, waya taba ki?”
“Ita ce kawai”
Ya kalleta ba dan ya gamsu ba, ba zai cilasta mata ta fada masa abun da ya haifar mata da damuwa a yanzu ba, amman da sannu zai sani domin ya san yadda take sauyawa idan ta shiga damuwa. Mikewa yayi tsaye rike da cup sai ta rike hannunsa na hagu ta dago tana kallonsa da idanuwanta dake bayyana damuwa sosai. Komawa yayi ya zauna sai ta dora kanta a cinyarsa ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali, ta sani bata da sauran kima a idon kowa sai Vito a yanzu, ita din ba abar tausayin kowa bace sai mutumen da ya ganta a rana ya saka a inuwa kuma ya lullube ta da kulawa da kauna, yake gudun bacin ranta yake kaunarta fiye da kansa, tana jin kamar shi kadai ya rage mata a yanzu.
“Mommy ta fada min zata zo satin nan, idan ta sauka a nan na san zata rage miki kewa, ko ba komai zaki samu uwa zata kula dake kamin ta tafi, amman idan baki ra'ayi zata sauka gidana sai idan kin bukaci ganinta”
Ya fada yana shafa fuskarta a hankali kaunarta na kara zafafa a zuciyarsa. Bude idon ta yi ta tashi zaune tana kallon wani gafen, ta yi marmarin kasantuwa kusa da wasu iyalin, sai dai kudurin da take da shi ba zai barta ta sake kusantar iyalin Vito ba a yanzu. Ta mike tsaye ta cire ribbons din dake kanta jan gashinta ya sauko har bayanta, sai ta tsaya gaban madubi tana cire dankunenta, shi ma tsayen yayi ya matsa kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubi, baya bukatar ta bashi amsar tambayarsa, ya zauna da ita na tsawon shekara bakwai ya san me take so da wanda bata so, yana iya karantar yanayinta tun kamin ya san dalilin farinciki ko bakincikinta. Ya dafa kafadarta har lokacin kallon fuskarta yake ta madubin dake tsaye gabansu, ta dago ta kalleshi da blue eyes dinta.
“Zata zauna a gurina har sai kin bukaci ganinta”
“Ba wai bana son zuwanta a nan ba ne kawai...”
Bata karasa ba ya juyo da ita ta fuskance sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskarta yana kallon zanen halintarta hancinta.
“Ina sonki Emily, ina sonki, so mai tsanani irin son da alkalin ba zai iya rubuta bawa, irin son da zan karar da kalamai gurin furtawa, ina sonki, irin son da zan iya kashe kowa a duniyar nan na rayu daga ni sai ke, zan iya rabuwa da kowa na rayu da ke, rashin zaman mahaifiyata a kusa da ke ba zai haifar da komai ba sai karin kaunarki, kar hakan ya dame ki, zata a gidana har sai idan ke da kanki kin bukaci ganinta”
Ya karasa yana kallon kanta, yana sonta wannan rubuce yake a cikin kaddararsa, shiyasa baya haufin nuna kaunarta a ko'ina haka kuma baya babu wanin abun da zata aikata a duniyar nan da zai saka ya nisance ta. Ya runtse ido yaja dogon numfashi ya sauke ya bude idon ya sauke su a kanta.
“Har yanzu baki san miye so ba, har yanzu baki fahimce waye ni ba, har yanzu baki san irin son da nake miki ba, amman ina fatan wata rana zaki san haka”
Hawaye ya sauko a idonta sai ya share mata da yatsanta.
“Zan tafi gurin London komai zai wuce”
Ya saketa ya matsa baya, kallonsa kawai take har ya fice sannan ta lumshe ido hawayen na cigaba da sauko mata, tana tsananin tausayin Vito fiye da yadda take tausayin kanta, ya mata fahimtar baibaine amman ta san son domin ta so mutumen da be dan darajar ta ba, son ne ya janta ga halaka har ta rasa makomarta ta butulcewar mutanen da suke rike a matsayin ďiya. Tana jin tsoron irin son da Vito yake mata, tana tsoron abun da zai haifar tana tsoron yadda makomarsa zata zama idan babu ita a kusa da shi.
Tufafin jikinta ta cire ta daura tawul ta shiga bandaki ta kunna shower da nufin wanka sai kuma ta samu kanta da zama a cikin tube din tana nadamar shiga rayuwar Vito da ta yi...
Ta dade a haka sannan ta yi wanka ta fito bata shafa komai ba ta saka short gown ta kwanta kwanta saman gadonta, korar da aka yi mata a yau ta dawo mata a rai, a take hawaye ya cika idonta, meyasa bata da sa'a a rayuwa? Meyasa farinciki yake mata nisa? A duk lokacin da ta daura damarar gina ramen farinciki sai bakinciki yayi mata kawanya, idan bata samu damar tsayawa da kafarta a yanzu ba sai yaushe zata yi? Ita kenan ba zata iya bawa kanta farinciki ba sai idan wani ne ya bata, wanin ma Vito mutunen da ya gama mata komai kuma bata da wata sakayya da zata masa, yanzu ko nan gaba.
Motsin turo kofar dakin da Fatima ta yi da gudu ta shigo ya saka ta yanke tunanin da take ta tashi zaune, kamin ta yi wani yunkurin goge hawayen da suka bata mata fuska Fatima tace.
“Momy ki duba wannan number ki goge ta, amman karki kar duba abun da na tura gashi nan yana kira na san zai ce na goge ne kuma ban iya ba ban gane gurin ba, yace koya min amman na manta ban san ya ake gogewa ba...”
Kamar wanda aka ce amsa kiran mana, haka ta taba green botton din sai ga fuskar Aliyu ta bayyana.
ALIYU POV.
Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya gama sannan ya zauna gefen gado ya dauki wayarsa yana duba whatsapp dinsa, domin a yanzu ba shi da wani abu mai muhimmancin kamar jiran amsar Turhan, gashi kuma har yanzu Turhan be amsa masa ba bayan kuma ya karanta sakon nasa. Yaje wayar yayi ya mike tsaye ya fara shafa mai ya shirya tsab cikin shigar kanana kaya black T-shirt and White jean, yana tsaka da fesa turare Aisha ta shigo dakin, fuska ba yabo ba fallasa tana kallon bayansa har ta karasa kusa da shi.
“Ga abincinka can a falo fa, kai nake jira ka sauko mu ci”
“Na ci abincin a waje”
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, sakin baki ta yi tana mamakin furuncin, tasan waye mijinta cin abinci a waje ba dabi'arsa ba ce.
“Wai duk fushin ne haka? Fisabilillahi ganin chat kawai ya kai ace ka dauki fushi da ni har haka?”
Ya juyo ya kalleta.
“A gurinki abun da kika aikata ba laifi ba ne?”
“Idan ma laifi ne ai ya kamata kayi min uzuri ko? Har sai idan na sake aikatawa”
“Rashin daukarsa laifi shi yake kara bakanta min rai, taya zaki zauna da kawarki ki labarta mata yadda muke rayuwa a shimfidar da ko dan'uwanki ba a yarda ya sani ba, taya zaki ji idan kika kama ni ina fadawa abokina yadda nake da ke a gado?”
“Dadi zan ji mana, ai kana fada masa yadda na iya gyara shimfida ne, Aliyu wannan abun fa is normal, yanzu rayuwa ta canja ba yadda muke a baya ba ne, wacan rayuwar da kake tunani ko iyayenmu ba su yi ta balle kuma mu, amman dai shikenan tun da baka so zan daina”
“Ina fatan haka”
Ya furta yana kokarin danne fushinsa domin kara bata masa rai take da kalamansa na yanzu. Murmushi ya sakar mata ya matsa kusa da ita.
“Muje mu ci abincin”
“Ba kace ka ci abinci a waje ba?”
Ta fada tana masa kallon da yafi kama da harara, ya fadada murmushinsa tare da shafa cikinta.
“Wasa nake kawai ina fushi ne amman yanzu na sauko”
Ya rike hannunta suka fice daga dakin, falo suka sauka ya ci tuwon shimkafa da favorite miyarsa miyar kuka, sai da ya ci yayi nas sannan ya soma bata labari, da hira ta yi dadi sai ya dauko mata zancen sabuwar ma'aikaciyarsu da kuma fadan da ta yi da Amal a yau. Har a ranta ta ji dadin korar da aka yi mata domin bata son kowace mace a kusa da mijinta, Amal din ma dan ta zama dole ne.
“Kasan wasu matan ba ba su da kai, musamman kabilun nan kara ana musu haka, ta nan za su fahimci matsayinsu, kuma wasu ma fa kawai neman maza ke kawo su”
Tana maganar tana yatsina fuska. Kallonta yayi yana girgiza kai.
“Madam ba fa ni kadai ba ne namiji a kamfanin nan, kawai ke da kin ji maganar mata sai kishi ya tashi”
“Matan ne fa yanzu kamar za su auri namiji da karfi, idan mutum be yi taka tsantsan ba sai a aure masa miji”
“Ke da kika san waye mijinki ai be kamata ki daga hankalinki akan ko'ina zan shiga ba, kuma karki manta ke kadai zaki rayu a gidan Aliyu daga ke sai yayanki, ko kin manta alkawarin da na yi miki? Ba ke ba kishiya”
“Ban manta ba amman ku maza ai wani lokacin zaku iya ganin mace ku bi ku rude kanta duk wani alkawari da kuka yi ku watsar da shi, musamman idan ka ga wata fara kyakkyawa yar doguwa”
Yayi murmushi.
“Allah ya saukaka miki wannan kishin, ni bana da ra'ayin karin aure”
Dadi ya lullubeta ta kwanta jikinta.
“To yanzu zaka je ce ta dawo aikin ne ko kyaleta zata ka yi?”
“Aa ai ta riga ta rasa kenan, ni ban san a ina take ba balle nace ta dawo, kuma an riga an yi replacing dinta da wata ai”
Sanin halin matarsa ya saka shi bata wannan amsar.
“Haka ma yafi, waya sani ma ko tana da kyau”
Wannan karon dariya yayi, domin ta