Showing 162001 words to 165000 words out of 249044 words

Chapter 55 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14960

tausayinta, Ummi ta zubar da hawaye tana mamakim yadda wasu uwa ko yan'uwan suke juyawa abun da aka haifa baya har ya rasa gata, alhalin ba su san halin da yaran suke samun kansu ba. Sai da Emily ta samu natsuwa a kafadar Ummi sannan Ummi ta share mata hawayenta.

"Shiga ki huta, za a kawo miki abinci"

Ta daga kai ta fice daga Kitchen din ta haura sama, Ummi ta kalli Nafisa daya daga cikin yan matan da take riko ta ce.

"Ki zuba abinci ki kai mata, a fadawa Kulu ta shirya mata wani abu mai ruwa ruwa ko zata iya sha, wacan abincin kuma ki kaiwa Aliyu idan kin je ki fada masa sai Daddynsa ya iso za mu zo"

"Tohm Ummi"

Daga haka ta haura sama, Nafisa ta debi abincin ta kai dakin Emily sannan ta sauko ta fita harabar gidan neman Kulu, bayan ta sanar mata umarnin Ummi ta sake dawowa falon sai ta samu Ummi na jiranta.

"Ungo ga wannan tufafin shigar mata da shi, ki je ki kaiwa Aliyu abinci yanzu nan"

"Tohm"

Ta karbi tufafin ta shigar da shi dakin Emily sannan ta fito ta saka mayafinta ta dauki abinci ta fice, Direban da ya kawo Ummi ne ya dauke ta zuwa asibitin bayan sun isa ya rika mata kayan har gurin dakin da Aliyu yake ba abar shi ya shiga ba dan haka yace ta fadawa Aliyu yana gaishe shi, ta amsa da Toh ta shiga ciki.
Ta shiga ciki sai ta same shi zaune akan kujera yana tasbihi da alama sallah ya gama.

"Sannu Yaya Aliyu ya jikin?"

Ya daga mata kai sai da ya shafa addu'a sannan ya amsa.

"Alhamdulillah"

"Ga abincin ka, Ummi tace na kawo"

"Ni zan iya cin abinci yanzu na sha tea ma babu jimawa, maybe zuwa anjima zan iya ci"

"Tace a fada maka sai Daddy ya iso za su tare"

"Okay, Ina Emily?"

"Tana can gida tare da ita aka maka girkin ai"

Aliyu ya kalli cooler abinci mai kyau da tsada da Ummi ta siya gurin Khadeeja Candy.

"Zuba min abinci"

Nafisa ta bude Warmers din ta fara zuba masa soyayyar shimkafa da kaza sai kamshi take.

"Yauwa Khaleefa yace yana maka sannu da jiki"

"Wane Khaleefa?"

"Direba?"

"Da shi aka zo daga Abuja?"

"Eh shi ya kawo ni yanzu"

Ya karbi abincin ya fara ci yana taunawa a hankali.

"Idan kin tafi ki fadawa Khaleefa nace ya je kauyensu ya huta na kwana biyu har sai an neme shi, ita kuma Ummi ki fada mata na bawa Khaleefa hutu"

"Ka kore shi kenan?"

"Aa ai ba zan hana shi hanyar cin abincinsa ba, but for now bana son Emily ta ganshi ranta ya bace, yaje ya huta za a rika biyansa har sai idan Ummi ta bukaci a daina tun da Direban ta ne ba nawa ba"

"Okay"

"Idan kin koma ki shiga gurin Emily make sure ta ci abinci please, kuma ku rika janta da hira kar a wareta, ko nuna mata banbanci ku rika janta a jiki Please"

"Okay"

Ya kalli wayarsa dake kan gado tana ringing, Nafisa ta dauko ta miko masa ganin sunan Mama Baraka ya saka shi kallon Nafisa ya ce.

"Zaki iya tafiya, Muktar yana nan zai min komai idan ina bukata"

"Okay Allah ya baka lafiya"

"Ameen"

Ya amsa ya aje wayar kan cinyarsa ya cigaba da cin abincin a hankali.





TURHAN POV

Yana harabar gidan yana video call Fatima a hannunsa sai waving take yi ta gaban wayar, ganin direban Ammy ya saka shi sauke wayar ya nufeta Fatima na hannunsa. Ammy ta fito motar cikin wani yanayi da ke bayyana damuwarta amman hakan be hana da ta kalli Fatima ta yi murmushi ba, ta kai hannu ta karbeta daga Turhan kamar wata yar jaririya, Turhan ya karbi jakar Ammy ya bi bayanta suka shiga falon.
Sai da ta fara zama sannan ya zauna Ammy ta sumbanci goshin Fatima ta sumbanci hannunta ta shafa kanta tana murmushi.

"Tafi can dakina dake sama ko kuma gurin wayar da Aliyu ya baki zan yi magana da Dadynki"

Fatima ta juya ta kalli Turhan dake murmushi ita ma ta yi murmushin jindadi ambatar daddynta da Ammy ta yi ta sauka kan cinyar Ammy ta nufi upstairs, daga Ammy har Turhan binta suka yi da kallo sai da ta haura, sannan Ammy ta kalli Turhan.

"Kana kama da mahaifinka sosai, ko kadan ba ka yi kamada ni ba, a kamanni da hali duk baka rago shi ba"

Turhan ya fadada murmushinsa yana zaton Ammy zata yabi mahaifinsa ne.

"Shi ma ya mu'amalance ni kamar yadda ka yi ma Aisha"

A take murmushin dake fuskar Turhan ya gushe.

"Ta inda ya dara ka, shi be gabatar da ni a matsayin baiwa ba a gidansa, na shiga a matsayin mata, amman boye ni yake bana fita idan yayi baki saboda kar a gan ni, matansa duka biyu basa bukatar ganina dan haka ban isa na chudanya da su ba, shi kansa auren ya zamo masa dole ne kawai a haka yake zaune da ni, da aka samu cikinka sai ya ji tsoro kar na fara yin zuri'a da shi alhalin baya bukatar wani jinsa a cikin familynsa sai nasa, be yarda na shayar da kaiwa, ina haihuwarka aka karbe aka bawa wata balaraba ita take shayar da kai take maka hidima, da ya ga baka yi kama da ni ba har dadi ya ji, shiyasa bayan na haife ka sai aka hada kai da hadimata aka ba ni maganin hana haihuwa na sha ba tare da na sani ba, da maganin ya zauna a cikina sai ya haifar min da rashin lafiya, a dole yake bani kulawa saboda kar na fadawa mahaifin ya wufintar da kyautar da yayi masa, sai da ya ji ya gani da wahala da ni sai wata rana ya saka na shirya masa abinci, ban san ya aka yi ba amman dai bayan ya ci abinci ya kamu da ciwon ciki aka je asibiti suka tabbatar guba ce, abun da har na kasa ganewa shi ne shi ya saka gubar da kansa ko kuma hada baki yayi da likitan saboda ya fadi hakan? Daga gidan sarauta aka wuce da ni gidan yari wai ina son kashe sarki, mahaifina ya shiga ya fita ya samu daker aka fitar da ni, a wacan lokacin sun yi nufin kashe ni saboda su share labarina. Da aka dawo da ni kasar nan sai ya aiko da min da takardar da saki, wannan maganin da aka ba ni ya zama sanadin da ban samu lafiya ba sai da aka yi min aiki aka cire min mahaifa gaba daya"

Ammy tana labarin tana zubar da hawaye, ta kalli Turhan.

"Kasan me yasa na fada maka duk wannan?"

Ya girgiza kai alamar a a jiki a mace ido na zubda hawaye.

"Saboda na fahimci na yi kuskure na hada aurenka da Aisha, balaraben asali be son bakar fata, balaraben mutum yana da dagawa, ina tuna yadda na yi ta yaki na yi ta fadi ta shi na ganin hankalin mahaifinka ya dawo gareni amman hakan be samu ba, indai akan auratayya ne balarabe be taba karbar bakar fata. Gaba daya sun ture karantarwa da koyarwa Ma'aiki da yace wani be fi wani ba sai wanda ya fi jin tsoron Allah"

Ya share hawayensa.

"Ammy me ya kawo wannan maganar?"

"A yanzu da na fada maka ka ji dadin abun da mahaifinka yayi min?"

Ya girgiza kai.

"Taya kake tunanin Fatima zata ji? Ya zaka ji idan wani yayi ma yarka haka? Da ace ba mahaifinka ne ya aikata min haka ba me zaka yi?"

"Ba zan bar shi da rai ba?"

Ammy ta daka masa tsawa hawaye na sauko mata.

"To kai ba zuciya ce a kirjinka ba? Me yasa baka ji haka lokacin da kake cutatawa amanar da na baka ba? Aisha nan uwar wasu ce ai gashi nan ta haifa maka ฦดa, yar wasu ce ita ma yar adam ce idan aka munana mata tana jin zafi kamar yadda zaka ji"

"Ban san... San... Iya abun da ta fada miki ba, amman Wallahi ban taba dukanta ba, kuma ba a taba dukanta na kyale ba, ban tana hana mata abinci ba, a lokacin da kika aura min ita na yi kuskuren na kin karbarta ne saboda ina tsoron yadda zan gabatar da ita a matsayin mata a masarautar Mahaifina ba lallai ya karbeta ba, matata ma haka kuma wacan lokacin ina jin kamar darajarta bata kai ba, amman yanzu duk na gane kuskuren hakan"

"Ta fada min irin zaman da kuka yi, kuma ta fada min a yanzu saki take so"

Turhan ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ransa ya bace sosai.

"Idan tana son saki zata iya fadar tana son saki ba sai ta saka kin tuna da abun da be kamata ki tuna da shi ba"

"Ni na hada auren yanzu kuma zan raba, ka rubuta takardarta ka ba ni zan kai mata"

"Zan sake ta, amman ba zan bata Fatima ba"

"Tsakanin kai da yarka babu ruwana a ciki, amman tsakanin kai da ita ni na hada yanzu kuma zan raba"

Ya hade rai sosai ya tashi ya haura sama gurin da yarsa take. Ammy ta dade zaune a gurin zuciyarta na mata turkuki sannan ta tashi ta shiga dakin, a daren kwana ta yi da bakinciki tuna baya da kuma bakinciki abubuwan da suke faruwa a yanzu. Turhan kuma ya kwana tare da yarsa da tunanin abubuwan da yayi Emily, motsi kadan idan Fatima ta yi sai ya farka domin a kirjinsa ta kwana har safe.
Washe gari suka hadu gurin karyawa, Ammy ta juye halshe ta gudun kar Fatima ta fahimci me suke magana akai, da yaren Larabcin Sudan ta ce.

"Idan ka rubuta takadar ka ba ni da kaina zan tafi na kai mata"

Ya tsayar da cin abinci da yake ya kalli Ammy da babu fuskar wasa a maganarta ya ce.

"Da gaske kike yi Ammy? Wai da gaske kike na saki AISHA?"

"Na taba maka wasa a irin wannan gabar? Alkawari ma daukar mata kuma zan cika"

Ya kasa hade abincin dake bakinsa sai dawowa yayi da shi ya zuba a plate din.

"So nasty"

Fatima ta fada tana daukar plate dinta ta bar dinning din sai yamutsa fuska take saboda ta yi arba da kazanta. Be kula ta ba sai kallon Ammy yake.

"Idan har zan sake ta to miye amfanin nemanta da aka yi ta yi? Kin ce na gyara abun da na bata idan na rabu da ita ta ina zan gyara abun da na bata? And Fatima za a raba mata hankali, bana son ta yi irin rayuwar da na yi"

"Daman ai ba sonta kake ba ka fada min, nemanta kuma ya maka rana tun da ka samu Fatima, daman ni burina a nemi yafiyarta kuma asan halin da take ciki, ita ma kuma ba sonka take ba"

"Na ji ita tana da hujjar da zata ki ni, ban damu ba idan tana sona ko akasin haka, amman ni nace bana sonta wannan a baya ne, kuma na fada ne kawai saboda ta ji haushi ke ma kuma ki kyale ni, amman yanzu ne lokacin da zan gyara komai, taya kuma zaki ce na sake ta? A yanzu babu wanda nake son farantawa rai kamar ita, Fatima da ke"

"Idan kana son faranta mata to ka sake ta mana, bata bukatarka a rayuwarta"

"Ni ina bukatarta, idan na sake ta ai ban gyara lafina ba, na kara batawa kenan, kawai ranki ne a bace Ammy amman ni ba zan saki Aisha ba noooooo"

"Ka sake ta idan kana sonta kuma ka yi nufin gyara laifinka zaka gyara ko baka tare da ita, ka sake ta sai ka sake bibiyarta idan zuciyarta ta natsu ta yafe maka zata iya amincewa ta sake aurenka"

"La la la lala lalala idan na saki Aisha ba zata zabe ni, ta sake aurena ba ko da kuwa maza sun kare a duniyar nan, a yanzu ni nake bukatarka ba ita take bukatata ba, la la la Ammy laa ba zan saki Emily ba, ki can ba ni umarni na bi amman ban da wannan la Ammy laaa"

Ya mike tsaye.

"Kina cikin fushi zan tafi sai kin huce"

Ya nufi yarsa dake zaune kasa tana cin abinci tana game sumbance ta ya hada goshinsa da nata ya lumshe ido yana jin wani irin sanyi da be tana ji ba a duniyar, sanyi rahama na arzikin samun haihuwar da yake nema ido rufe. Sai da ya sake sunbantarta sannan ya mike tsaye ya juya ya kalli Ammy.

"Zan yi magana da Aisha, zan dawo da ita kusa da ni, a masarautarmu za mu yi rayuwa mai kyau, idan na sake ai wani banza ne zai aureta, idan mahaifina ya jure ni ba zan jure kallonta a gidan wani ba, zamanta da Aliyu ne su suka kitsa mata komai ni kuwa sai na nuna masa ni namiji ne"

"Babu wani hucewa da zan yi, wajibi ne ka sake ta wannan dole ne"

Ammy ta fada tana dukan dinning din da karfi. Turhan be sake cewa komai ba ya haura sama ya dauki keys dinsa ya sauko ya fice daga gidan gaba daya.
[7/16, 10:07โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy



๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’*


*ยฉ Khadeeja Candy*



Page 5๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ


Nafisa ta shiga ta sanar da Ummi hukuncin da Aliyu ya yanke akan Khaleefa, Ummi ta dan yi jimmin sannan ta ce.

"Shikenan zan yi magana da shi"

Ummi ta tashi da kanta ta dauko kudi mai kauri ta sauko kasa sai kyalli take tana zuba kamshi saboda kwalliyar da ta yi ma mijinta kai kace ba ita ya haifi Aliyu da Yayansa Yusuf ba saboda yadda take kula da jiki, kuma bata taba yarda cewar ta tsufa da yi ma mijinta kwalliya ba.
Kamin ta karasa fita falon aka turo kofar falon aka shigo daman ta ji tsayarwa mota. Yusuf ne tare da matarsa suka shigo, Ummi ta saki baki

"Ah ah ikon Allah yanke tafiyar kuka yi kuka dawo??"

Ummi ta rumgume surukarta tana murmushi, Khadija ta yi dariya

"Shi yace kar a fada miki, wai zaki ce ba sai mum dawo ba"

Ummi ta dago tana kallonsa da harara.

"Daman baka yi nufin hutun ba ko?"

Yayi dariya.

"Ummi ke da kike mahaifiyarsa kika gagara jurewa ki zauna Abuja sai da kika zo nan balle ni da nake yayansa na san zafinsa fa, ita kuma wannan kin santa da lakuwa duk inda ta ji dake a guri sai ta zo"

Ya karasa yana nuna matarsa.

"Eh mana ai ita ce yata, kai miye hadina da kai"

Yayi murmushi ya daga kafadunsa ya nufi cikin falon.

"Toh ga ka ga guri nan, barka da zuwa"

Ummi ta fada tana murmushi ta kalli Yusuf kadan ta dauke kai domin bata wasa da shi sosai, ba kamar Aliyu ba da ta dauka tamkar kanenta, Yusuf ta aje shi a muhallin ษ—an fari ne. Shi ma kuma ya dauke ta uwa ya dauki mahaifinsa aboki shi kansa ya fi sakewa da mahaifinsa kusan duk wani abu da ya shafi kasuwancin mahaifinsa shi yake tafiyar da shi, sukan tattauna abubuwa da dama ba tare da Aliyu ko ita kanta Ummi ta sani ba.

"Zauna Khadija bari na sallami wani na dawo"

Ummi ta nufi kofa ta fita, sai da ta fita harabar gidan daya daga cikin yaran gidan ya zo da sauri yana tambayar wani abun za'ayi mata.

"a Khaleepa nake nema direban da muka zo da shi ina yake?"

"Oh Khaleefa"

Yaron ya kwala masa kira, sai ga Khaleefa ya fito daga BQ da saurinsa ya karaso gurin Ummi ya gaisheta. Ta amsa sannan ta ce.

"Ai kauyenku a Kaduna nan ne kace ko?"

"Eh Hajiya"

Ta mika masa kudin hannunta.

"Ga wannan, ka yi na mota ka tafi gida ka duba su kuma ka tsaya a can ka kwana biyu, har sai ka ji daga gareni"

Gabansa ya fadi ya kalli kudin jiki a sanyaye.

"Hajiya wani laifin na yi?"

"Aa ba laifi kai yi ba, ba korarka aka yi ba, za'aci gaba da biyanka albashi nan da kwana biyu kuma zaka dawo aiki"

"Hajiya saboda na yi magana da Emily ne? Wallahi baki san abun da yake tsakanina da ita ba wata kila da ba ki fusata har haka ba"

"Ba saboda ka yi magana da ita ba ne"

"Ku kuke da komai na ku, duk hukuncin da kuka yanke yayi daidai, amman ina rokon alfarma daya dan Allah a ba ni damar magana da Emily akwai abubuwan da nake son na tambaye da yawa, kuma akwai wadanda nake son fada mata"

"Ita ce bata bukatar ganinka shiyasa aka bata hutu"

Khaleefa ya zube kasa ya hada hannu biyu.

"Hajiya ki dubi girman Allah ki taimaka ki roki Emily ta saurareni, kusan rabin rayuwar nan na karar da ita gurin neman Emily ne, dan Allah Hajiya ki taimaka min na yi magana da ita, akwai zuri'a a tsakaninmu ina son na tambaye ta, kuma Wallahi a musulma na santa ya aka yi ta zama haka? Dan Allah Hajiya ki ba ni dama"

"Damar ba daga ni ba ne, daga ita ne bata bukatar magana da kai a yanxu, ka tafi gida idan ta bukaci hakan zan maka waya, yanzu dai ka tafi dan Allah kar na fito na same ka a nan"

Ummi ta duka ta aje masa kudin ta juya yana ta mata magiya kamar zai zauce har da kwalla a ido. Ko da Ummi ta shiga falon ta samu Yusuf ya haura stairs, sai Khadija a falon da Nafisa suna hira.

"Ke baki kawo mata komai ba? Ke kuma kamar bakuwa ba zaki shiga ki dauko ruwa ki zuba abincin ba"

"Ni na ci abinci, Abban Maama ne dai be ci komai ba"

Ummi ta zauna tana tambayar jikokinta.

"Ni na manta ina kuka bar yaran?"

"Suna can gida, tare da nanny"

"Wai ku wannan rayuwa da kuka daukarwa kanku anya zata yi? Ku gaba daya rayuwar turawa? Komai dai nanny? Haihuwar ma tun da aka haifi biyun nan shiru ba kari? Kuma kuna kallon yadda muke a gidan nan daga Aliyu sai mijinki sai Ramla da bata yi aure ba, Aliyu kuma shi Allah be ba shi haihuwar ba, ku kuma daga yin yan biyu sai ku tsaya haka? Muna son zuri'a gaskiya"

Khadija ta yi murmushi.

"Allah ne be kawo ba Ummi"

"Ku yaran zamani masu dabi'ar turawa ta ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login