Showing 126001 words to 129000 words out of 249044 words

Chapter 43 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14994

daura aurena da Turhan, a take na ji gabana ya fadi wani abu mai kauri da zugi ya tunkari zuciyata ya tsaya, tun daga wannan ranar har yau wannan abun be sauka ba. Kusan zan iya cewa auren dole Ammy ta yi min da Turhan domin bana son shi tsarin rayuwarsa gaba daya be yi min ba.





_______________________

Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen... ✍️



FOLLOW ME ON 👇🏻

FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08



Page 4️⃣0️⃣


Aliyu ya dago yana sauke numfashi ya kalli Fatima dake rike dayar wayarsa tana kallo, ita yake kallo ammam Emily yake tunani wahalar data sha a gidan Khaleefa be gamsar da alkalamin kaddararta ba har sai da ta sake zana mata wani shafin mai daci a tsakaninta da abokinsa. A yanzu ya fahimci duk abun da Ammy ta yi ma Turhan na juya masa baya ta yi daidai, ga kuma rashin samun haihuwa da be yi ba a yanzu sai kuma Allah ya jarrabe shi da son yaran ashe shi ya fara butulcewa tun farko.
Ya kai hannunsa ya shafa Fatima sai ta kalleshi ta yi murmushi, shi ma yayi mata murmushi sannan ya maida hankali gurin wayar ya kunna dayan voice note din ya cigaba da saurare.


***. ***. ***

A ranar da aka daura mana auren, Turhan be dawo gidan ba sai dare, ina dakina a lokacin da ya shigo tare da Ammy tana ta murmushi sai addu'a take zuba mana, shi ma yana murmushi kamar gaske, ni kuma na kasa ko daya kallonsu ko yin murmushi, London yana hannuna Ammy ta karbe shi ta fice aka bar mana dakin daga ni sai shi, kaina a kasa shi kuma ya nemi guri ya zauna ya dora kafa daya kan daya, sai a lokacin na iya dagowa na kalleshi farar shadda ce a jikinsa sai kamshi yake kamar angon kirki.

Mun dauki minti talatin a haka babu wanda yace da wani uffan, sannan ya taso ya karaso kusani da ni.

"Wani mummunan abu be taba faruwa da ni ba kamar aurenki"

Furucinsa ya tsari kaina, na dago na kalleshi sai ya tofa min yawu da karfi a fuska ya daki kafata dake da lalle da karfi sannan ya sa kai ya fice. A daren ban yi bachi ba, kuma ban yi kuka ba tunani ma na rasa wane zan yi, ina ta sake sake idan na kulla wannan na kulla wacan ta ko'ina zaren warware min yake na rasa gane inda zan raba na fake.
A daren Ammy ta kawo min international passport din da ta saka aka yi min saboda barin kasar zamu yi. Washe gari Assabar Ammy ta fara shirya min kayan da zan tafi da su, ita ta hada min komai nawa ido ne kawai sai kuma ɗana sa nake ta rumguma ina jin kewar rabuwa da shi, a daren Ammy ta yi min nasiha sosai kuma ta kara tabbatar min ɗanta ba zai taba cin amanata ba, kana ta yi min godiya na yadda na amince da kudurinta har aka kulla auren, ta ce na toshe kunnuwana daga kananan maganganu ko kuma abun da zan gani da be kai ya dawo ba, na kwantarwa da mijina hankali, ba can zamu zauna ba zamu je ne kawai mu dawo.


Ranar Lahadi da safe aka fito mana da akwatinanmu ni ma na fito cikin shirina ina rumgume da ɗana, Turhan ma ya fito cikin nasa shirin yana ta far'a kamar gaske, Ammy ta so ta rakamu Airport amman ya hana wai idan ta bimu har can zan fi kowa kewarta. Kuka be zo min ba sai da Ammy ta kai hannu ta karbi London dake hannuna sai ya fashe da kuka ni ma na fashe da kuka na karbe shi na rumgume, abun mamaki sai ga Turhan ya zo ya karbi yaron ya dankashi hannun Ammy ni kuma ya ciro handkerchief ya share min hawayena.

"Ki kwantar da hankalinki mana, ba wani dadewa zamu yi ba, muna gamawa zan dawo tare da ke, kuma a can zamu zauna ba anan kusa da Ammy"

Ya kama hannuna ya saka ni mota da kansa Ammy na ta saka masa albarka har sau uku sannan ta yi mana addu'ar Allah ya tsare. Direba ya ja mota muka kama hanya, ba mu zame ko'ina ba sai Airport aka yi mana duk wani check in da ya kamata har muka kai gurin jirgin, sai da muka shiga na gane ba guri daya za mu zauna ba, shi yana Business class ni kuma a economy, na zauna shiru ga damuwa na barin ɗana, ga fargabar abun da zan je na tarar ga kuma tsoron jirgin domin shi ne karona na farko da na hau jirgi. A Lagos muka fara sauka da na fito sai na tsaya sai da ya fito sannan muka kama hanyar Hotel a taxi, a hotel din ma babban daki ya kama ni kuma ya fada min zan zauna a karamin daki daidai ne, haka na karasa dan wunin daya rage na kwana babu wanda ya kwankwaso min yace ga abinci, tun bayan dan abun da na ci a jirgi da be rike cikina ba.

Sai 11am ya buga mun dakin hotel din na bude yace na fito zamu kama hanya, na fito da akwatina muka sake shiga taxi ta kai mu air airport aka yi mana screening aka auna kayanmu da duk wani abun da ya kamata sannan muka hau jirgin da zai dauke mu zuwa Sudan, a nan ma business class ya shiga ya bar ni a Economy, dan abun mutsa baki da aka kawo min a jirgin da shi na samu na karya bayan tafiya ta yi nisa suka kawo mana shinkafa na cinye tas da ruwan shayin kai tsabar yunwa ko ruwan sha ban raga ba komai sai da na cinye har ina bukatar kari. Na yi bachi ban farka ba sai da muka jirgin ya fara jijjigar sauka.

Yanayin kasar da garin, mutanen da yarensu dabam ne da na kasar mu, tun a Airport din na kara tabbatar dan sarauta ne, saboda motoci da suka zo daukarsa da kuma yanayin mutanen da suke tuka motar. Mota daya muka shiga da shi a motar yayi min gargadin da ban zan taba mantawa ba.

"Karki sake ki yi magana, kin ga hausar mutanen nan da na can ba iri daya ba, kuma za ki je ne a matsayin baiwa, zan sanar da kowa cewar ke baiwa da mahaifin Ammy ya bani, kuma zan sanar musu ke kurma ce, dan haka duk tsanani kar ki kuskura ki yi magana, kuma bayan nan karki nuna kin san ni"

Bance komai ba, a lokacin ma kuka baya zuwa min wata kila saboda damuwar ta yi min yawa ne ko kuma dai kukan ya gaji da zirarta idanuwana ne. Masarauta ce babba ko da yake ban san komai akan sarauta da fada ba, amman tabbas mahaifin Turhan babban Sarki ne a garin, ayi masa tarba ta girma, ni kuma aka kaini wani daki na daban aka sauya min tufafi zuwa aka ba ni na wasu masu kamar lafaya, wadanda ma'aikatan gidan suka sakawa. Masarauta ce mai matukar fadi da girma, ba Turhan ne kadai dan da Sarkin ya haifa ba amman kowa da bangarensa da kuma nasa bayin.
Nidai tun daga ranar ban sake saka Turhan a ido ba sai da na yi sati biyu, a kullum zuciyata tana gurin ɗana, aiki kam babu hutu musamman da ya kasance ni a karkashin matarsa aka barni, domin bangaren mahaifinsa dabam tun da naje ban taba ganin Sarkin ba, bangaren da Turhan yake da matarsa dabam, idan har na huta to dare ne yayi ya shiga turakar mijinta mu kuma sai mu samu hutu, na ga wulakanci na ga kaskanci ga yunwa ba a wani ba mu san adataccen abinci, idan ma aka kawo abinci wadanda suka manya ne suka kwashewa mu kanana a bar mana kadan, gashi ya fadawa kowa ni kurma ce ba damar na yi magana ko na nuna na ji wani abu, haka na yi rayuwa cikin tsananin azaba da azzatarwa, idan aka yi baki ni nake gyara ko'ina na gidan kuma ban isa na ce na gaji ba, gimbiyarsa kuma bayi ba su isa su daga kai su kalleta ba sai hukunci.

Wata rana na makara ban tashi ba, domin tun da asuba muke tashi mu fara aiki ga gidan da girma, kananan bayin da muke yin aikin ba mu da yawa, su kuma manyan aikinsu bangaren kula da baki ne ko abinci, sai wata babbar hidima idan ta taso. Ko da na isa na samu wata ta maye gurbina tana aikin mopping din da aka ce na rika yi kullum. Da farko na jidadi na yi zaton ko an dauke min ne na huta na wunin ranar ashe sun shirya kai karata a gurin babbar hadimar matarsa ne. Sai da aka gama komai na fito ina gyara gefen dawaki hadimar ta iso, da wani yare take min magana wanda ban iya ba, ko da ace na iya ban isa na amsata ba, saboda Turhan yace kar na sake na nuna ni ba kurma bace, ina jin tana magana amman ban waigaba, sai da aka tabo ni sai ta yi min alama da bachi da lokaci tana tambayar meyasa, ba ni da amsar bata dan haka na yi shiru sai kallonta nake tun da ban iya maganar kuramen ba balle na fada mata da kurmancin cewar ban san lokaci yayi ba, ashe hakan yayi mata ciwo, a take ta koma ciki babu jimawa wasu mata suka zo suka rika ni suka tafi da ni wani daki, tun daga yanayin dakin na san azabtar da ni za'ayi domin akwai bulala a cikin ga kuma wani namiji tunbuke da da katon rawani yana jiran shigowata.

Ba su tirsasani ba gurin shiga da kafafuwa na shiga, mutumen ya fara duka tun ina hawaye kawai ina kukan dole irin na kurame har kai ga ihu ina neman taimako, sai ga mutane an cika gurin kowa yana kallo da mamakin maganar dake fita bakina, sai da na samu sa'ida sannan na fito daga dakin na koma bangarenmu na kwanta ina jin fatata tana min zugi. Can da dare aka aiko daya daga cikin bayin da muke kwana da su ta kama hannuna ta fita da ni ina tafiya daker, daman haka suke min idan ana kirana saboda basu iya kurmanci ba ni kuma ban isa na yi magana ba. Da muka isa bakin fadar gimbiyar Turhan sai babbar hadimarsa ta yi min alama da na wuce ciki na shiga daga baki baki na zube kasa, sai ta yi tafiyarta. Na kusan awa daya a gurin sannan Turhan ya fito cikin shigarsa ta jallabiya da alkibba mai kyau hannayensa a baya ya karasa kusa da ni cikin wata irin tafiya ta kasaita ta ban taba ganin yayi irinta a gidan Ammy ba, fuskarsa babu annuri.

"An fada min kin yi magana? Saboda me?"

Maganar ma a rarrabe yayi min ita saboda kasaita ta.

"Dukan ne yayi min yawa ban san lokacin da na yi ihu ba, ka yi hakuri"

Sai a lokacin ya kalleni yana jin kansa.

"Wa yasa aka doke ki? Me kika yi?"

A tunani da sanin matarsa aka min dukan dan haka da ya tambaye ni sai na ce.

"Matarka"

Na kama hafafuwansa na rike ina kuka.

"Turhan dan Allah ka maida ni gida"

Ya ja baya.

"Karki sake taba kafata, tashi ki fice, kuma na fada miki ke kurma ce karki sake ki sake yin magana"

Na tashi daker na koma bangarenmu, na samu tufafin wata na dora kaina akai domin ni Turhan be bani nawa tufafin da Ammy ta hado ni da su ba, kuma bata kira ta ce a bani ba, kowa yana ta tufafi daga kala biyar zuwa sama ni kuwa kala biyu ne daga tufafin da yake a matsayin uniform dinmu sai tufafin da na cire. Ina dakin aka sake zuwa aka dauke ni hadimar Gimbiyar tana ta masifa sai dai ban san me take fada ba. Wacan dakin aka sake maida ni aka sake zaneni sai dai wannan karon ban yarda na yi uhu ba saboda Turhan ya gargade ni.

Dukan ne ya zama silar rashin lafiyata a masarautar har na tsawon sati gashi babu kyakkyawar kulawa babu maganin kirki, rayuwar bauta rayuwa ce ta kaskanci da wulakanci Aliyu, wanda ba zan yi ma kowa fatanta.
Da na fara jin sauki sai na koma kan aikina tun daga lokacin bana bari ma asuba ta yi ina bachi, da zarar karfe uku ta yi na dare na farka ba zan sake komawa bachi ba. Zamani ya waye duniya ta canja ban taba tunanin har a lokacin akwai sarakunan da suke mulkin bayin ba sai da na ga masarautarsu Turhan. Gashi basa ganin kimar bakar fata, domin a duka bayin babu larabawa sai yan wasu yarukan ko kabila, ni kaina sai su yi ta kallona wasu har taba gashin kaina suke suna yaren da bana ji, wani lokacin kuma a daga fatar idona a kalli idon.

A ranar da Allah ya kaddara za a samu cikin Fatima, da safe ne sosai ina goge fadar Hadimar Gimbiyar ta zo ta kama hannuna ta shiga da ni can ciki sannan ta saki hannuna ta fice, ina tsaye a gurin Turhan ya fito sai na yi hanzarin zubewa kasa na maida idanuwa kasa.

"Biyo ni"

Ya fada sai na mike tsaye na bi bayansa, da halshen larabci ya sallami masu saka turaren dakin sai daya daya umarci ta ba ni turaren na karba na bi bayansa har muka shiga bangarensa. Muna shiga ya nuna min inda zan aje turaren ya ce.

"Shiga wacan dakin akwai bandaki a ciki ki yi wanka, ki cire tufafin ki daura tawul"

Yana min maganar yana kallo da kyama da kuma dan bacin rai kamar wanda baya cikin yanayi mai dadi.
Na aje turaren na nufi dakin da ya nuna min na shiga, na cire tufafin jikina kenan ban kai ga shiga bandakin na ji shigowarsa.

"Dole ce kawai saboda kin min karya kince matata ce ta saka aka duke ki alhalin ba ita ta saka ba, kin saka ta kaurace min na tsawon lokacin nan"

Wata kila yana cikin uzurin da ba zai iya jira na yi wankan ba, ko kuma yana tsoron ta shigo ta tarar da mu ne sai ya yi abun da zai yi cikin gaggawa, bayan ya gama yana ta tsaki da tofar da yawu.

"Wannan ce bakar rana ta biyu a gurina bayan ranar da na aureki, kuma karki sake na ji maganar nan kin shigo dakina a gurin kowa ko kuma wata alama"

"Dan Allah Turhan ka maida ni gida"

Na roka ina jin kaina a cikin wani irin kaskanci da ban taba samun kaina a ciki ba.

"Idan kika sake fadin sunana ko daga ido ki kalleni sai na saka an miki illar da zai lalata miki idon, ko baki in yaso sai ki zama kurma da gaske, tashi ki bace min da gani"

Ya daka min tsawa rai a bace, a cikin rakunan bakincikina, ranar da Khaleefa ya sake ni ba zan manta da ita ba, ba zan manta da furucin da Turhan yayi a gareni ba na kiran ranar aure da kuma ranar da ya tara da ni a matsayin bakar rana ba, haka ba zan manta da ranar da na rasa ɗana ba. Na kimtsa kaina na fito ina jin jikina yana min wani iri domin na dade irin wannan alakar bata hada ni da kowa ba bayan na fito daga gidan Khaleepa. Na cigaba da aikina ina hawaye har na gama, sai rayuwa ta ci gaba tun ina saka ran Ammy zata zo ko kuma ta kira amman babu ko daya, gashi ni kuma ban taba rike waya ba tun bayan dana zauna a gidanta ban san ma ta ina zan same ta ba.
A haka na sake shafe wata biyu a gidan, kuncin da na shiga sai yafi na baya saboda matarsa da hadimarsa sun tsane ni a yanzu ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login