Showing 165001 words to 168000 words out of 249044 words
za a gane ko daga Allah ne ko kuma daga ku ne, mu dai na mu daga Allah ne ai"
Ummi ta mike tsaye tana murmushi domin ta ji tsayarwa motar mijinta, da ganganta ta fada ma Khadija haka domin tana son ta ga tarin jikoki saboda Allah be fata yara da yawa ba, ba kuma zata iya zauna da Yusuf ta yi wannan maganar ba amman zata iya da matarsa.
A ranar gidan ya cika da jama'a saboda dawowar Daddy masu zuwa gaishe shi da suka zaba suka zo, wasu ba su san ma abun da yake faruwa ba sai da suka zo wasu kuma yan'uwa ne da abokan arziki suka zo masa jaje, da yammancin ranar Yusuf ya tafi asibitin duba dan'uwansa tare da matarsa da wasu daga cikin yan'uwa, Daddy kam sai dare ya samu zuwa tare da Ummi saboda mutane ba su bar shi ba sai bayan sallah isha'i.
Aliyu ya gaisa da mutane ciki har da abokai wasu ma ba a bar su sun shigo ba, yayi farinciki sosai da ganin dan'uwansa, Khadija sai zolayarsa take tana tambayar ina Kameela domin bata san wainar da ake toyawa ba, Aliyu dai daya gaji da tambayarta a fada mata sun rabu.
Subhanallahi daga haka bata sake cewa komai ba, daga asibitin suka wuce gidansu dake Kaduna daman suna hutun Anniversary ne abun da ya faru da Aliyu ne ya saka suka yi dawowar gaggawa.
Da dare Ummi suka zo duba shi tare da Daddy Ummi ta zo masa da wani abincin da ta girka masa, sun sha hira da daddynsa sosai na abun da ya same shi da wanda yake zargi da kuma abun da yake hararowa nan gaba, har statement din da police suka dauka sai da ya fadawa Daddynsa kuma a kaurara lamarin saboda yana son a dauki babban mataki. Daddy ya shaida masa already hukuma sun fara aikinsu, a nan ya kara warwarewa Ummi zare da bawa a game da Emily sannan ya kara fayyace musu abun da ya faru tsakaninsa da Kameela.
Aliyu yana son ya tambaya ya Emily take yana gudun Ummi ta masa fahimta ba daidai ba, alhalin shi kuma ya damu ne kawai ya san halin da take ciki.
"Idan ba mataki aka dauka ba ita kanta ba zata samu salama ba"
"Ai dole ne wannan, indai har aka tabbatar shi ne to ya kai karshe, ni da har na fi zargin Kameela saboda yarinyar bata da hankali, indai har zata iya saka maka guba to zata iya komai"
"Abu ne mai wahala Kameela ta yi haka, kuma bana zargin Turhan even though yana cikin bacin rai, amman bana tunanin zai saka ayi min haka, domin na fito gidan kenan ma ba a jima ba, lokacin be isa ace ya je ya samu wasu su yi min wannan dukan ba, na fi zargin Vito ne yake bibita saboda na zo da yarta kuma gashi ta biyo bayana and ita kanta ya saba dukanta balle kuma wani"
"Bincike dai zai tabbatar da komai In Shaa Allahu"
Ummi ta fada sai Daddy ya ce.
"Yanzu ita yarinyar tana Lafiya?"
Aliyu ya kalli Ummi da sauri yana jin amsar da zata bada daman tun shigowarsu yake son ya tambaya sai kuma ya danne zuciyarsa saboda Ummi.
"Tana lafiya"
"Amman ta fito waje?"
Aliyu ya tambaya, sai Ummi ta yi kamar bata ji shi ba. Daddy ya ce.
"Amman Aliyu kana tunanin Turhan zai fahimce ka kuwa?"
"Abu ne mai wahala mahaifiyarsa ma dazun sai da ta fada min magana"
Ummi ta fada, Aliyu ya tambaya.
"Me ta fada miki?"
"Shirmen mata ne, kasan mu sa kananan maganganu"
Aliyu yayi shiru slowly slowly ransa ya fara baci amman be ce komai ba. Daddy kawai ya koma gida Ummi a asibitin da kwana tare da dan'uwansu Muktar duk kuwa da irin yadda Aliyu ya so ta tafi ta bar Muktar din ya kula da shi, Daddy har zolayarta yayi wai ta zabi ɗa ta bar miji, ta fada masa ana canja miji ba a canja ɗa ba.
EMILY POV.
Wannan ne dare na farko da bata ji dadinsa, saboda ta kwana da kewar Fatima sosai, gashi ta yi bakunta a gidan da mutumen data sani baya cikin gidan sai bakin fuska. Abincin ma bata wani ci abun kirki ba abun duniya ya taru yayi mata yawa. Tun gabanin Asuba bachi ya yanke a idonta sai hawaye ne suke ta aikinsu ta yi iya tunanin ta yi iya hangenta amman ta gagara samun mafitar da zata iya amfani da ita yarta ta dawo gareni. Wannan dalilin ya saka duk yadda ta hana zuciyarta daga ganin laifin Aliyu sai ta kasa domin shi ya janyo mata komai. Ba zata hana zuciyarta aminta da shi ba, amman bata da tabbacin abun da yake zuciyarsa da na mahaifiyarsa, domin Ammy da Khaleefa darasi a rayuwarta.
Bata sauko kan gadon ba har sai da Ummi ta dawo daga asibiti ta leko dakin daman tun fitar Nafisa a jiya babu wanda ya sake lekota duk wani kai da kawo da ake a gidan bata fito ba. Ummi ta kunna wutar dakin ta kalleta.
"Kin tashi lafiya Emily?"
Ta tashi zaune.
"Good Morning"
Ummi ta karasa kusa da ita ta zauna tana kallonta da murmushi.
"Kin tashi lafiya?"
Ta daga kai kawai tana boye idonta.
"Za a kawo miki abun karyawa, asibiti na kwana gurin Aliyu na manta ban fada miki ba, and Aliyu ya bawa Khaleefa hutu saboda ki samu sakewa, zaki iya fitowa harabar gidan ko falo ki shakata, kuma ki saka tufafin da ya miki ki sake jikinki babu wani damuwa"
Nan ma ta daga kai. Ummi ta mike tsaye ta fice daga dakin. Sauka ta yi kan gadon ta shiga bandaki ta yi fitsari ta wanke da ruwa domin ta kasa daina wannan dabi'ar ta musulmai wato tsarki da ruwa ko wanke bayan gida da ruwa, ta wanke bakinta ta fito ta tana jin sanyi na abun da Aliyu yayi mata, ya fahimci feeling dinta tun bata fada masa ba, domin babu fuskokin data tsana a duniyar a yanzu kamar ta Turhan da Khaleefa. Ta zauna saman gadon ta kai hannunta ta dauki katin DR A-B data tsinta a jacket dinsa, ta dadde rike da katin tana kallonsa kamin ta dauki wayarta ta saka number shi duka biyun, sannan ta shiga gallery ta kama hotunan Fatima tana kallo sai ga kiran Aliyu ya shigo wayarta. Ta amaa da sauri tana fatan dayan wayarsa ce dakw hannun Fatima aka kira da ita so that ta yi magana da yarta. Tana jin sallama da muryar Aliyu ta san ba yarta ba ce. Bata amsa sallamar ba bata ce masa komai ba kuma bata amsa Good morning da yace mata ba, hakan ya saka shi fahimtar kuka take ko kuma fushi take da shi.
"Idan akwai abun da kike son aikawa ki aikata, karki bar tunaninki ya hana zuciyarki abun da take so"
"Ina son yarinyarta a kusa da ni, i want my baby"
Ta fada tana fashewa da kuka. Aliyu be ce komai ba ya kashe wayar. Kiransa na sauka kiran Vito ya shigo wayarta cikin kuka ta amsa kiran shi ma bata ce masa komai ba sai saurarensa take.
"Kalle ki Emily, kin yi yaudara kina tunanin kin yi nasara ko? Saboda zuciyarki na raya miki ba zan iya miki komai ba? Mamana ta yi gaskiya kin din ba abar yarda ba ce, idan kina tunanin kin gudu kin tsira to kin yi kuskure, ba'acin amanata a zauna lafiya, sai na ga bayan wannan dan iskan yaron da kike so, kuma sai na maida rayuwarki labari Emily, ba zan raine ki wani ya ci moriyarki ba, no way! Daman kina nemam damar butulce min ne, shiyasa kika karbar soyayyata bayan duk abin da na yi miki? Ban ga laifin komai da yake faruwa da ke ba, saboda ke yar iska ce fuck you Emily"
Maganar yake cikin yanayi na maye. Ta hade kukanta tana jin tausayinsa domin abu ne data sani Vito yana sonta, kuma ya kula da ita irin kulawar da kowa be bata ba, ba al'adarshi ba ce shan kayan maye da safe sai idan yana cikin damuwa, and she knows ita ce silar damuwar tun da har ya kira yana karanta mata wannan bayanan.
"Zan dawo Vito, zan karbi yata zan dawo zamu yi aure zamu irin rayuwar da kake son mu yi, kai kadai ne nauyin da ya rage min na sauke, but don't hurt anyone mutumen da kake kokarin ganin bayansa taimako kawai yayi bashi da wata manufa akaina, ba abun da kake tunani ba ne"
"I don't need you now, i already have Chidimma na yi replace dinki da ita, daman daga ke sai ita nw kuka san sirrina, dan haka zata kasance da ni har abada ke kuma zan baki mamaki, daman haka kike ko? Su ma butulci kika musu shiyasa suka horar dake, to ni horon da zan miki ya fi na su, a hannuna kike ina kallon duk wani motsi naki"
Ya katse wayar sai ta lumshe ido ta cije baki tana jin ba zata iya yafewa kanta ba, domin ta san yadda cutarwa take da ciwo and kasa samun soyayyarta da Vito yayi bayan duk taimakon da yayi mata ya zama kamar cutarwa. Ta kai hannu ta taba zuciyarta tana jin kamar ace zata iya cusawa kanta kaunarsa kai tsaye, tun bayan da Khaleefa ya ci amanar ta bata sake jin tana son wani da namiji ba, Turhan ma ta aure shi ne kawai saboda mahaifiyarsa ba dan tana son shi ba. Sai da ta fara raya ma kanta cewar zata cusa zuciyarta ko bata so ta amince da soyayyar Vito, ko dan rama masa alherin da yayi mata, be zama lallai sai tana son shi ba, zata iya zama da shi su rayu yadda yake so, sai kuma maganar Ummi ta fado mata arai.
"Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki...karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba..."
Ta bude ido tana ba kanta amsa zuciyarta kuma na raya mata Idan bata amince da soyayyarta ba zai iya cutar da Aliyu.
"But i have to Vito ya cancanci komai daga gareni"
Ta share hawayenta sakamakon turo kofar dakin da aka yi za'a shigo. Mama Baraka ce da lullubinta dauke da katon kwandon abinci yaranta yan mata biyu ma suna dauke da abinci, ta shigo da far'arta ta aje abincin a kasa suma suka duka suka aje Emily sai kallonsu take su ma suna kallonta, Mama Barakat ta zauna a bakin gadon tana kallon Emily.
"Ina kwana, kin tashi lafiya"
Emily bata amsa ba, duk kuwa da tana tunanin ko Ummi ce ta ce ta shigo mata da abincin. Mama Barakat bata damu ba ta gabatar mata da yaranta biyu.
"Kin ga bakuwar fuska ko? Wannan sunanta Misira, wannan kuma Hakima zaki iya kiransu da kawayenki ko kanenki"
Emily ta watsa mata harara.
"Bana son ganinki ba na fada miki ba? Duk wani abu mai alaka da Kameela bana bukatarsa"
Mama Barakat ta girgiza kai da sauri.
"Aa Wallahi zuwana ba shi da alaka da Kameela ba wai ina kokarin gyara abun da Kameela ta bata ba ne, Kameela yar kishiya ta ce kawai bayan wannan babu wata alaka, dan Allah ki yarda da ni"
"Ku ba abun yarda ba ne, ku fita daki nan"
Mama Barakat ta fara hawaye tana bude abincin da suka zo da shi.
"Dan Allah karki tsaurara ganinki da nake ina jin sanyi, kin ga abubuwa na shirya miki na karyawa ban san wanene favorite dinki ba, amman abubuwa sun kai bakwai a nan ki ci duk wanda kike so, jiya kuma na yi waya da ita mahaifiyar yaron da suka rike miki Fatima, da na ce zan je na same ta sai kuma na ga ba zan iya yakin ni kadai ba, dole sai da taimakon mai gidan sai na yanke shawarar na fada masa, kuma na fada masa sai dai ban yi nasara na samun amincewarsa ba, be ma fahimce ni ba, amman... Amman... Dai na san zan samu kansa"
Mama Barakat tana maganar jikinta na rawa kamar wanda aka turke, iya kar kokarin na fahimtar da Emily ne bata nufin cutar da ita.
Cikin daga murya Emily ta dagawa Mama Barakat tsawa domin ta fahimci so take ta shiga jikinta ta cutar da ita, bata san me suke kullawa ita da Kameela ba.
"I don't need your help, bana bukatar abincikin Bana bukatar komai daga gareki, ki fita ki bar nan i don't need you"
Babbar yarta ce misira ta kasa jure yadda Emily take magana da mahaifiyarsu ne ta daka ma Emily tsawa.
"Ke dan Allah wace irin mace ce, baki san darajar iyaye ba ne da zaki rika cin mutuncin mahaifiyarmu a gaban idonmu? Haba Mama Wacece wannan kika ta rawar jiki da ita ne, duk girkin nan da kika tashi kina yi tun asuba duk saboda wannan banzar ne?"
Misira na rufe baki Mama Baraka ta dauke ta da mari ta nuna mata kofa.
"Fita fita ki ba ni guri"
Misira ta kalli Mama Barakat da mamaki dafe da kumatu.
[7/16, 10:07 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 5️⃣3️⃣
Emily ya hade wani kunci daya tokare zuciyarta.
"Kin yi gaskiya, ban san darajar iyaye ba"
Ta juya ta kalli Mama Barakat.
"Kin gani ko? Yarki tana ganin na zafafa, dan Allah bana son na sake fadar wata magana ina girmama mutuncinki ki fita dan Allah karki sake dawowa"
Jikin Mama Barakat ya kara yin sanyi.
"Me kika sani game da uwa?"
Ta juyar da idonta ta wani bangare na dakin tana sosa wani kurji da ya dade yana mata kaikayi.
"Ban san komai ba, saboda tarihin rayuwata be taba wanzuwa da uwa ko uba ba, na tashi ba tare da uwa, uba ko. Yan'uwa ba, dan haka ban san dadin uwa ba sai rashin dadinta, ban san komai game da uwa ba domin tawa uwar bata taba rumguma ta ba, taba nuna min tarbiya ko akasinta ba, bata banbance min yadda zan yi rayuwa da mutane ba, shiyasa ban iya rike halshe ba, ban san zafin da ake ji idan an ci ma uwa mutuncin ba, amman ni ina fatan yata zata sani, domin na tsaya kanta, na iya yadda zan iya na rayu saboda ita, na yi ma kaina alkawari ba zan taba bari ta ji abun da na ji ba, ba zan bari ta yi irin rayuwar da na yi ba, zan hade duk wani bakinciki saboda ta yi farinciki"
Ta juyo ta kalli Mama Barakat idonta na zubar da hawaye.
"Dan Allah ki tafi bana son na sake fadar wata magana marar dadi a gareki"
Mama Barakat ta nufi kofa ta bude ta fice tana zubar da hawayen da suka fi na Emily zafi da kuna a zuci, Hakima na binta a baya. Emily ta daga kanta sama ta shanye hawayenta sannan ta sauke ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito ta zauna gaban madubi ta shafa mai ta saka turare kasancewar babu wasu kayan kwaliya ya saka ta lakaci man shafi ta shafa a lebenta ta shace kanta. Wandon balazo da rigarsa da Ummi ta bata ta dauka ta saka blue ne mai wani zane zanen baki sai rigarsa ta yadi baki da karamin dankwali baki, da dankwalin da daure gashinta madadin ribbons sannan ta dauki wayarta ta tsaya gaban madubi ta kalli kanta with full confidence.
Ta yi kyau babu karya, tabon dukan da Vito yayi mata ya bace confidence din data sakawa kanta ya kara mata kyau da kwarjini, bakin data shafawa mai sai shinning yake, ta juya ta nufi inda talkaminta suke ta saka ta bude dakin ta fita, ta sauko falon a daidai lokacin da Ummi ta zauna a kujerar dake facing din ta Mama Barakat tana fadin.
"Ki yi hakuri fa na barki a nan, na tsaya sallamar mai gida da abun karyawa ne"
"Ba komai, wata magana nake son mu yi dake ta fahimta, na kira Aliyu jiya ba daga ba, wata kil yana tunanin ko saboda Kameela ne..."
Mama Barakat bata karasa ba saboda saukowa Emily, daga Ummi har ita kallon Emily suke.
"Na ce Nafisa ta kawo miki abun karyawa ta kawo?"
Kamin Emily ta amsa tambayar Ummi Mama Barakat ta ce.
"Na zo mata da abinci amman bata ci ba"
Ummi ta kalleta da mamaki.
"Abinci kuma? Abinci aka ce mun rasa a gidan ne da har sai an dauko daga gidanki an kawo?"
"Aa na yi nufin kyautatawa ne kawai"
"Gaskiya karki sake Hajiya Barakat kin ga dai daga bangaren Kameela kike, duk abun da ya faru ya faru saboda Emily kar a zo a cutartar da ita ba tare da mun sani ba"
Mama Barakat na yi shiru ta sauke kai kasa, Emily ta kalli Ummi ta ce.
"Ina son zan tafi gidansu Turhan ko zaki iya sakawa a kai ni?"
Ummi ta kalleta cike da mamaki.
"Gidansu Turhan?"
Emily ta daga kai, Mama Barakat ta kalleta, Ummi was speechless for a little bit kamin ta ce.
"Lafiya?"
"Ummi yata tana can, zan je na yi magana da su ne"
"Zazzzaki iya?"
Ta daga kai with full confidence.
"Amman ki bari ki yi breakfast tukuna"
"Hankali ba zai kwanta ba har sai na tafi, idan na dawo zan karya"
"Okay, bari na yi ma direba kwatacen gurin, ina zuwa"
Ummi ta tashi rike da wayarta ta fita.
"Zaki iya zuwa ke kadai ko na raka ki? Kuma tafiyarki ba zata zama da matsala ba?"
Emily ta kalli Mama Barakat ya wacce ta yi maganar ta gafen ido.
"Na saba rayuwa da yin abubuwa ni kadai wannan ma zan iya"
Ta nufi kofa ya bude ta fita, a Entrance din ta tsaya tana sauraren Ummi dake fadawa direban inda zai kai Emily.
"Number gidan dai na manta, bari na tambayi Aliyu"
Ta daga wayarta a gurin ta kira Aliyu ta tambaye shi house number nawa ne gidansu Turhan, sai da ya fada mata sannan ya bukacin jin dalilin tambayar.
"Za mu yi magana daga baya"
Ummi ta kashe wayar ta kalli direban.
"Number 7"
"Tohm Hajiya"
Ya juya ya sauka ya nufi wata farar mota sai da ya juyo da ita sannan ta sauka ta nufi motar ta bude gidan baya ta shiga ta zauna, direba ya dauki hanya.
TURHAN POV.
Be yi nisa da gida ba kiran mahaifinsa ya shigo