Showing 231001 words to 234000 words out of 249044 words

Chapter 78 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14993

iyaye sun fita aka barta da kanenta da wasu daga familyn Mama Baraka da suka zama kawayenta na short period of time. Abokan Aliyu suka rako shi ya shigo falon da manyan tufafi babbar riga har da hula. Kowane yana rike da babbar leda suka cikin big center table din da kayan taba ka lashe da suka shigo da su. A nan ta san wani abu siyen bakin amarya, abokan Aliyu suka siye bakinta da kudi mai kauri da siyayya da, sun yi farinciki sosai domin ba su bar gurin ba sai da kowa ya ji saukar alert.

Sai da kowa ya watse Aliyu ya rufe kofar sannan ya yarda ya bude fuskar matarsa, sannan a hankali ya yaye duk wani abu dake jikinta ya rage daga dankwalinta sai lace ne kadai, har sarkar cire mata yayi saboda yana ganin kamar sun mata nauyi, ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta sannan ya cire abun hannun ya aje, ya sauko kasa ta zauna ya daga kafarta abun adon dake kafarta ya cire bayan ya sumbanci kafar sannan ya aje ta a hankali, ya dago dayar ya cire ya sumbance ta ya aje kasa. Ita kanta ta ji a jikinta jumma'ar da zata yi kyau, tun daga laraba ake ganewa, Aliyu ne kadai Jarumin dake tsoron tana jikinta saboda gujewa tsallake iyakokin da musulunci ya gindaya musu.

Har bayan aurensu, be taba kokarin taba jikinta ko wuce gona da iri saboda ta zama mallakinsa ba, kamin ranar yau idan ya rumgume ta ko ya sumbance to ya fahimci tana cikin damuwa ne sai yayi mata haka saboda ya kwantar mata da hankali, shi ma yana kokarin ganin be tsallake iyakoki ba duk kuwa da ya san halalinsa ce tun da an daura musu aure.

"Abar kauna? Komai na ki yayi kyau"

Ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta, kunyarsa da take ji a yanzu ta fi wanda ta ji a washe garin ranar da aka daura musu aure. Kafarta daya ya daga a hankali yayi mata chakulkuli, ta motsa kafarta murmushi ya cika fuskarta kunya ta saka ta rufe idonta. Yatsansa ya saka yana bin layin lallen da aka zana mata a kafa a hankali kamar mai zanen yana kallon kai kace be taba gani lalle a kafar mace ba.
Har sai da ta kasa jurewa ta hanye kafarta. Sai yayi murmushi ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje ya zauna kusa da ita, ya juyo da fuskarta ta fuskance shi.

"Qalbi, bude idonki ki kalli mijinki, masoyinki, mallakinki abokin rayuwarki na har abada, mijin da yake jin ya fi kowa sa'a da rabo saboda ya same ki"

Ya kara matsawa kusa da ita sosai har jikinta yana taba na shi.

"Kin san me, uwar ƴaƴa? Tun daga ranar da kika shigo rayuwata, komai ya canja. Na rasa yadda zan bayyana, amma ke ce farin cikin zuciyata. A duk Lokacin da na gaji, sai murmushinki ya bani ƙarfi. A duk lokacin da na shiga damuwa, sai kalamanki su zama shauki da nutsuwa a raina."

Ya ɗan janyo hannunta ya riƙe, yana tana saman yatsunya, ya ci gaba da cewa

"Kin fi zinari daraja a wurina, kin fi dukiya ƙima. Wallahi idan na dubi idanuwanki, ina jin kamar na mallaki duniya baki ɗaya. Ke ce zuciyata, ke ce abokiyar tafiyata har ƙarshen rayuwata."

Emily ta bude ido tana jin daɗin maganganun a zuciya, kowane harafi yana tsarata ya isar mata da sako. Ya saka karamin yatsansa cikin nata irin yadda yara suke yi.

"Na yi alkawari ba zan taɓa barin ki, ki ji kaɗaici ba. Zan kasance tare da ke cikin farin ciki da bakin ciki. Domin soyayyarki ita ce hasken zuciyata, kuma ke ce sarauniyar gidana"

Hawaye ya sauko mata ya saka yatsansa ya share mata, ya sakar mata murmushi mai taushi ya girgiza mata kai alamar no more tears, ya kwamto da ita kirjinsa yana shinshinar gashin kanta dake kamshi. Slowly and slowly ya dago kanta ta kalli saitin idonsa ya sauko da fuskarsa sai ta lumshe ido tana jin sanyin lips dinsa a saman nata lips din, kamin ya raba lips din gida biyu ya saka nasa a tsakiya.
Wani sako mai nauyi da mai wuyar dauka ya aika mata mata ta tsakanin bakinsa da nata, a lokacin da ya cire bakinsa cikin nasa sai ta kalleshi a rikice tana maida numfashi, sai kuma ta lumshe ido ta yi murmushi ta maida kanta kirjinsa tana mai jin kunya.

Sun samu lokaci a haka sannan ya tashi dauro alwala ita ma ta yi suka yi sallah, yayi musu addu'a, ya dauko abun tabawa ya ciyar da matarsa, sannan sauya tufafin jikinsa zuwa ma bachi, ita ma ta sauya nata bayan ya bata guri ya fita falo har sai da ta gama sannan ya dawo. Abubuwa da Emily bata saka ran Aliyu ya sani ba, ko ya iya ta gansu, bata yi zaton zai zo mata a haka ba, saboda yadda take ganinsa da kokarin kawarda kai.
Kusan duk wani abu mai sunan damuwa sai da Aliyu ya matar da ita a daren, har take jin kamar ita ce ta kwashe kason jarumin namiji, ta rika jin kamar bayan Aliyu babu wani namiji mai halayya da dabi'un da ya rage irin nasa.

A kirjinsa ta kwana har safe, ba kuma a daren kadai ba, a kowane dare bayan daren tarewarta tana kwana a kirjinsa ne, idan yana gidan da rana kuma tana sarkafe cikin hannayensa, duk wani abun da zai bada space a tsakaninsu be yarda da shi ba. A nan ta gane kalmar soyayya ba a cikin kalami kadai take ba har a cikin aiki da zamantakewa. Matukar hali da hallayar da Aliyu ya sauke ta da su a gidansa zai daure, to bata jin akwai wata macen da zata fita dace ko jindadin aure a halin yanzu. Idan ya fita har kewa take, shi kan shi kamin ya dawo gareta ya yi missing dinta kamar ba a gida daya suke rayuwa ba. Awa ashirin da hudu yana jin kamar a kara musu wasu awanin domin sun masa kadan.

Kusan duk wanda ya shiga gidan sai ya yaba da yadda aka gyara ko'ina kuma aka zuba kaya, sosai Mama Baraka ta yi kokari wajen ganin ta fitar da yarta kunya, kuma ta faranta mata rai, kuma kwaliyya ta biya kudin sabulu domin ta siya komai a gurin Khadeeja Candy ne.
[8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*



Page 7️⃣3️⃣

🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟

🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘

Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji!
Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida.

✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji?
• ✅ An yi ta da tsafta da inganci
• ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau
• ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa
• ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida
• ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman

📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka!
🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).

💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau!

📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku.
👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa!


Jin alamar mutum a bayanta ya saka ta juyo, sai suka hada ido, yana sayen da wando bachi sai farar vest dake jikinsa. Ya daga mata gira like how far, ta aika masa murmushi.

"Ina kwana"

Ya daga kafadunsa.

"Ni ma ban san inda yake ba"

"Okay good morning"

"it's morning but not Good Morning?"

Ta kalleshi with confuse.

"Why?"

Ya jingina da kofar kitchen din yana bata amsa tare da saka hannayensa aljihu.

"Cox i didn't get a kiss from my wife"

Ta juya ta aje wukar hannunta tana murmushi, kana ta sake juyawa ta nufi inda yake ta yi dage zata sumbance shi ya yi dage shi ma yana kauce fuskatsa.

"Bana so, sai da na yi magana rike abun ki bana so"

Ta zagaye hannayenta a wuyansa.

"I'm sorry haba autan maza, na tuba handsome na maka kiss ma kamin na fito kitchen fa"

"Aa ni ban ji ba, kuma waya ce ki bar ni ki zo kitchen? Ke dai kin dange sai kin wahalar da kanki ko?"

"Babu wahalarwa a cikin hidimar miji ko wace kala ce"

Ta sake kai bakinta da sauri zata masa kiss ya kauce yana dariya.

"Na ce bana so"

"Toh ba ni wanda na baka dazun, da kana bachi dawo min da abuna"

"Kiss din?"

"Eh"

Yayi dariya mai sauti.

"A ina kika ba ni?"

"A nan"

Ta tura masa bakinta.

"Ni na san ba ta nan aka ba ni ba, amman tun da wayo za'ayi min a yaudarini ba matsala"

Yayi mata kiss din. Ta sake shi tana ja baya cikin zolaya da muryar yaudara ta ce.

"Ba a nan na yi maka ba, a nan na yi maka"

Ta nuna kumatunta. Ya fusgota ya dawo da ita jikinsa.

"To dawo min da abuna, na baki na ki"

Ta noke kasa tana dariya. Binta yayi kasa yana mata kyaculculi sannan ya sake ta ya nufi plantain din da take yankawa tana soyawa at the same, ya dauki wukar yana yankawa ta karaso ya kwashe sannan ta dauki daya ta hura ta nufin ba shi.

"Ki daina hura abun da abun da zaki ci, Annabi ya hana, hura abinci"

"Na karu da wannan, amman akwai zafi fa"

Ya aje wukar ya dauki daya ya bude yana riritawa a hannunsa har ta sha iska.

"Bude bakin"

Ta bude ya saka mata.

"Kai zan bawa fa"

"Kuma kuka ci?"

"Kai ka ba ni ai"

Ya kai hannunsa ya rikota suka fara kokawa ala dole sai ya cire wanda ya saka mata a baki, ita kuma ta yi hanzarin taunewa ta hade har tana kwarewa sai dariya take. Sai da ya ji tana dari sannan ya sake ta.

"Wai Qalbin miyasa baki jin magana?"

Ya nufi gurin da ruwa suke ya dauko mata ta bude bottle din ya daga kanta ya saka mata a baki, ta sha kadan tarin ya kwanta.

"Kai ka koya min ai"

Ya kai ruwan bakinsa ya sha kadan.

"Ni din?"

"Ko da aka kawo ni gidan nan har kunyarka nake ji, amman ta bi ka bala ni"

Tana maganar tana dariya. Sai ya kai bakinsa yana hura amsan kanta.

"Haka ake yi ma yarinya idan su ta kware"

"Yarinya matar...."

Ya zaro ido.

"Ni din? Ni za ki duba ki cewa yaro? Gaskiya ne da sauranki"

Ya aje ruwan hannunsa kamin ya juyo ta gudu daga Kitchen din, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ya nufi kofar kitchen din ya rufe ta ciki, be bude ba sai da ya karasa aikin da take ya hada komai a ya zuba a mazubinsa sannan ya bude kitchen din ya kawo musu komai a inda suka saba karyawa.
Al'ada ce ta ya sabawar kansa tun a lokacin da ya auri Kameela, idan ya rigata tashi shi yake hada musu komai na karyawa, idan kuma ita ta riga sai ta hada, sai dai ya fita kokarin hadawa domin tana yawan bachin safe shi kuma ya kan fita aiki dan haka baya jiranta yake hadawa musamman lokacin da take da ciki, har na rana ma wani lokacin girka musu yake ko yayi musu takeaway.

A yanzu kuma ya dora daga inda ya tsaya da Emily, banbancin Emily da Kameela shi ne, Emily tana son girkawa Aliyu abinci saboda tana son yi masa hidima tana son ta yi masa abu na faranta rai, abun da zai yaba mata. Tana gwada new recipe wani yayi dadi Wani kuma yayi ba lada ba la'ada, shi kuma da yake gwanin zama da mace ne, be taba kin yaba mata ba. Ko be yi dadi ba yabawa yake ya gode mata, sai dai ya fara mata inda za ta gyara ko su sake yi tare.

Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa. Ita vata yarda ta yi nisa da shi, shi ma kuma be koya mata ba. Idan ya fita har kewar dawowarsa take, takan tanadi labarai kala kala da take ba shi, kama daga na littafi zuwa na mutane da take ganina kafafin sada zumunta, wani lokacin har kudi yake sakawa idan labarinta yafi na shi armashi zai biya, idan kuma nata ya fi armashi zata biya, ita ta kan biya ta wata sigar ne, shi kuma ya biya da kudi. Zamantakewa suke kamar daman can ita ce matarsa ta farko, ita ma shi ne mijinta na farko, ko da yake masu iya magana sun ce macen da miji ke so kullum yar gata ce.

Tun bikin su da sati biyu Ummi ta bar su a garin Kaduna ta koma Abuja gurin mijinta daman can take zama dawowarsa, abubuwan da suka faru ne suka saka ta dawo Kaduna da zama, a yanzu kuma tun da sun kamalla komai cikin aminci da farinciki sai ta koma gurin tata ibadar ta aure. Kamin ta tafi sai da ta yi musu huduba sosai, musamman Aliyu, saboda tana ganin Emily kamar bata da matsala. Ta gargadi Aliyu ta yi mata uzuri da kuma taka tsantsan akan zamantakewarsu, ya rufe ido kuma ya toshe kunnuwansa daga masu suka ko gulma, ita kuma ta yi biyayya ga mijinta ta gujewa bacin ransa, sannan ta toshe kunnu daga wasu kannan maganganu.

Ummi ta roki Emily karta zafafa akan zaman Fatima a hannunta, domin abu ne da dukansu suka sani Turhan ba zai yarda Fatima ta zauna tare da su ba, ko da kuwa tana son haka.

"Ki daurewa zuciyarki ko babu dadi ki masa uzuri, saboda ya so ki be samu ba yanzu kuma yana da yarki, to ki masa hakuri ya ji sanyi ko ta nan, kuma karki bude hanyar da zata kawo baraka da mijinki akan yarki, sannan karki yarda mijinki ya raina yarki ko ya kaskantar da ita, kuma ko da tana can ki rika kula da ita akai kai, dan Allah ku bawa marada kunya, kar a ji kanku, idan sulhu ya gafara da mijinki, akwai mahaifiyarki idan abun ya ci tura, ina nan kuma mahaifinsa na nan, ba fata muke ba, amman dai kar aji a waje"

Nasihar Ummi ta saka Emily ta dauke kai daga damuwa da rashin Fatima a kusa da ita, domin washe garin ranar da aka daura musu aure Ammy ta aiko aka dauki Fatima, har yau Fatima bata san ya dakin Emily yake ba, saboda ta ki kawota ita kuma bata son ta matsa abun ya zame musu matsala. Dan haka ta saka musu ido, Fatima na garin nan bata nan bata da labarinta almost 3 months da bikin babu amo babu labari.




KAMEELA POV.

"Ko da mafarki ban dauka Aliyu zai iya juya min baya har haka ba, kusan duka kawayena na bata da kowa saboda da shi, gaba daya rayuwata ta ta'allaka ne akansa"

Kanwarta Farida ta dafata.

"Kameela ke kika dauki Aliyu wani shege fa, tun farko be dace da ke ba"

Kameela ta dube ta.

"Zaki iya fada min illar Aliyu daya?"

"Zan fada miki da yawa ma, kin ga dai akwai masu sonki masu kudi amman kin nace sai shi, kuma ɗan makiyinmu ne"

Ta yi murmushi.

"Ba zaki gane ba, wannan ba illa ba ce, kuma na gujewa duk sauran ne saboda suna da aure, Aliyu kuma saurayi ne, Aliyu ba shi da wata illa da za a dube shi da ita a hana shi aure, amman ya ci amanata"

"Ko yanzu fa kin ki bawa sauran dama ne, mutane na nuna suna sonki"

"Farida ba zan iya zama da mai mata ba"

"Ko da Aliyun ne ya dawo?"

Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar a yanzu.

"Dan Allah karki bari son Aliyu ko abun da yayi miki ya hanaki kula wasu mazan, ki duba fa da zai yi aure ma be zauna a gidan da kuka zauna ba sai ya zabi zama a wani gidan kuma ya kwaso kayanki ya aiko miki, da kin mana yadda muke so ai da yanzu kin riga shi aure"

"Ba auren ba ai mazan ne, yanzu duk namijin da zaka ce ya saki matarsa ya aureka ba zai yarda ba, ni kawai sai idan na samu saurayi zan yi aure"

Farida ta gwalo ido.

"Eyyy sai kice ya saki matarsa ya aure ki? Tsakani da Allah Kameela ki aje wannan tunanin a gafe, yanzu fa gasar kudi ake ba ta kishi ba, kishi da hauka na talaka ne, indai mutum yana da yan kudadensa iya ruwansa da wani kishi, kuma duk manyan mutanan da ke sonki kowa da matarsa da yara ta ina zai saki matarsa ya aureki? Wani ma mata biyu"

"Ki daina zancen manyan mutane, na auri wanda ya kusa haihuwa da majina zan ji ko da kishi ko yayansa? Ko kuma so kike na sake auren na fito?"

"Aa amman mai kudi wake zancen majinarsa? Murar ma ai sai talaka, da kudinsu wa zai kula wannan kuma mataki suke dauka, ni Wallahi kawai ki yarda hannu ya koma miya bawan Allah nan yana aurenki first lady zai maidaki, daman yana neman yar boko kuma wayayen kyakkyawa ta nuna mai dan jiki fit haka dai kamar ke"

Kameela ta ja tsaki ta tashi ta fice ta bar mata dakin. Ta yi ma kanta alkawarin ba zata sake waiwayar Aliyu, ta riga da ta aje shi a gafe yanzu saboda ya yi aure.
Abu kamar wasa kamar gaske, Kameela ta kasa kula kowa, idan ta ji labarin kana da aure da iyali sai ta aje ka a lissafi. Mahaifiyarta da iyayenta suna kokari sosai gurin lurar da ita abubuwan da ya kama ta dauka da muhimmanci a aure amman ta kasa domin ba wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login