Showing 81001 words to 84000 words out of 249044 words
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣6️⃣
Ya daga kansa kadan ya kalleta irin duban na lafiya?
"a gaban idona Aliyu?"
"Zauna"
Ya mata umarni.
"Wacece wannan miye tsakaninka da ita?"
"Zauna"
Ya sake fada peaceful.
"Na ban zauna ba, wacece wannan matar?"
"Emily ce, tsohuwar matar Turhan ina tunanin min mun taba magana da ke akanta"
"Toh ya aka yi kake Communicating da ita? Taya number wayarka ta shiga hannunta? Har ta kiraka har ka damu da lafiyarta? Na shiga uku kirjina"
Ta dafe kirjin tana numfashi da karfi daman tuni ta fara daga masa murya irin dagawar da kowa zai iya ji.
Kansa ya sauke kasa be sake ce mata komai ba, domin ya san halin matarsa da kishi karamin abu ne ya fita hayyacinta a yanzu nan ta fara masa hauka.
"Ni ban ma yarda ba, mu ga wayar mu gani waya sani ko soyayya kuke ka boye wani guri da ba zan gani ba"
Ya mika mata wayar ta karba ta sake shiga chat dinsa ta duba ta fito ta sake duba inbox dinsa, kamin ta shiga longcalls dinsa ta yi forwarding number Emily zuwa number ta.
"Wai ke da na yi ma alkawarin ba zan miki kishiya ba, miye abun tashin hankali idan kin ga ina magana da wata? Har yanzu hankalinki be kwanta da ni ba? Kuma ko aure zan yi ta ina zan aure matar da abokina ya aura?"
"Aliyu ka ci amanata Wallahi da kake waya da matar nan, ashe ina nan ina wankan jego kana can kana soyayya da wata, jira kawai kake na daga kafa"
Ta fada cikin kuka da hargowa, sai ya mike tsaye ya karbi wayarsa.
"Idan kin huce kin sauko zan dawo mu yi magana"
Ya juya ya fice ya barta a gurin tana gurnanin kuka, wani irin ihu ta saka tana shure shure duk ta watse abincin da suka ci da wanda ya rage a warmers ta watse kayan gaba daya a kasa kamar mai aljannu, da sauri Anty Shafa da Farida suka shigo suna tambayar lafiya sai kuma ta kasa fadar komai saboda bata son su ji abun da Aliyu ya aikata kar su mata dariya ko su ce Allah ya kara.
"Ba komai"
Ta tashi tana cigaba da kukan ta fice daga falon suka bita da kallo.
"Ba komai take wannan kukan"
Farida ta fada sai Anty Shafa ta kyalkyale da dariya.
"Ya gumama ai kadan kika gani daga halin maza, yarinyar da kin yi auren kudi ma da kin more, amman yanzu ai sai bakincikin ya miki yawa ko rabuwa kuka yi ga kiyayyar aure ga ta siyasa"
"Ai dai tun da ta nace sai shi sai ta ga babu dadi kuwa"
Cewar Farida Anty Shafa ta fice domin labartawa Hajiya Asma'u wato Mahaifiyarsu abun da ke faruwa, Farida kuma ta fita kiran mai aikinsu domin gyara gurin da Kameela ta bata.
Kameela na shiga dakinta ta fada kan gado ta fashe da wani sabon kuka tana jin kamar ta shake wuyan Emilyn da bata taba gani ido da ido ba. Ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta duba number Emily din ta kira number, sai kuma ta kashe gudun ajin abun da take fada ko halin da take ciki ya saka ta fito dakin ta sauka kasa ta fice daga bangarensu zuwa bangaren Mama Barakat, ta bangaren ma ba shiga ta yi ba waje ta samu inda babu wanda zai jita ta sake kiran number Emily ringing biyu Emily ta amsa kiran da tsoro domin bata tsammani shigowar kira daga bakuwar number.
"Hello"
"Sannu karuwa, yar iska marar aji mai bibiyar mazan mutane, me kokarin raba aure fasika yar titi, kafirar banza yar wuta, saboda ke baki tsaya kin yi zaman aure ba shiyasa kika kokarin ruguza nawa auren ko? Toh Allah ya fiki, Wallahi ki fita sabgar mijina ko na kashe ki, Aliyu ya fi karfinki ba zai taba sonki ba ba zai taba auren mace irinki ba, karki sake kiran mijina a waya karki sake magana da shi idan ba haka ba Wallahi sai na lahira ya fiki jindadi, akan mijina zan iya komai, shegiya marar tarbiya haihuwar hasara, ke je gurin mijinki mana, wato so kika ki kashe min aure kamar yadda ke naki yake kashe ko? Me yasa dole sai Aliyu? To mijina musulmi mai addini babu abun da zai yi da fasika irinki, wato so kike ki lalata masa tarbiyar ko? Ki shige jikinsa da sunan matar abokina ki gwada masa duniya"
Uffan Emily bata ce mata ba har ta yi maganganun da zata yi ta gama.
"kina jina dam ubanki ko na sake maimaitawa? Ko da yake ke ai baki da uba ma, baki san zafin hakan ba ko da an zage ki, shiyasa yanzu kike son ki rusa gida ko? Toh ki shiga hayyacinki ni bakar macijiya ce"
Ta kashe wayar tana huci, kamin kuma ta saka ihu ta fashe da kuka, ta dawo main door ta shiga bangare Mama Barakat ta zauna a falonta tana ta rusar kuka, Mama Barakat ta fito Kitchen da saurinta tana tambayar lafiya. Da yake Kameela ba mace ce mai rufin asiri da iya rike cikinta ba sai ta fara fadin.
"Aliyu ya cuce ni, ya ci amanata mutuwa zan yi zuciyata"
Mama Barakat ta yi mata tambayar duniya bayan wannan Kameela bata sake cewa komai ba, ganin haka ya saka Mama Barakat barin bangarenta ta tafi bangaren uwargidanta tana tambayar me ya samu Kameela take kuka da kiran Aliyu ya cuceta. Hajiya Asma'u dake zaune gefen gado tana kwance sarkar zinari ta girgiza kai cikin saurin maganarta ta ce.
"Mu ba mu san me ke faruwa ba, bata ma fada min ba, amman yara sun shigo suna fadin sun ganta tana kuka ta watse kaya, yanzu kuma kuka yake can?"
"Wai ko dai ce mata yayi zai yi aure? Kin san fa yayi mata alkawarin ba zai mata kishiya ba, kuma yadda Anty Kameela take da shegen kishin nan zancen kishiya ne kawai zai daga mata hankali haka"
Farida dake kwance gefen da Hajiya Asma'u take zaune ta fada.
"Aiko da na ci mutuncinsa Wallahi, dan ubanshi har cikin gidan Ubanta zai tarar da ita kuma ya fada mata zai mata kishiya? Kuma fa karamin aikin uwarshi ne ta saka shi kara aure a yanzu, ko dan abun da aka yi a gurin haihuwar nan"
Cewar Hajiya Asma'u, Mama Barakat tace.
"Wata kila dai wani abun ne, amman ga alamu Aliyu yana da hankali ba zai fada mata zai kara aure a gidansu ba, ya kamata dai a bincika"
"Baki gama sanin duniya ba Baraka karki ce zaki fada min mutanen cikinta, ke lokacin da aka rufe idon Alhaji aka aura masa ke ba ido da ido ya kalleni yace zai aure ki ba?"
Ta karasa da hararar Mama Barakat, Mama Barakat ta yi murmushi kawai ta juya ta fice. Hajiya Asma'u ta kalli Farida.
"Miko min wayata na kira shi, ya zo na ji abun da yake faruwa, idan ma wai auren ne burinsa to ko sai dai ya rabu da Kameela dan yadda take da kishi ba zan bari ya halaka min zuciyar yarinya ba shi ya je ya more rayuwa ya bar ni da jinya, ko kuma ya fasa auren domin babu wanda ya masa cilas din yi mata alkwarin ba zai kara aure ba, kuma dan ya kai dan iska ya zo har cikin gidan nan ya fada mata zai kara aure? Aiko yau sai na ci mutuncinsa, yaushe ma aka yi auren da za'ace ya kara aure, duk makircin uwarsa ce na sani saboda ba son Kameela take ba"
Farida ta mika mata wayar, Hajiya Asma'u ta kamo number Aliyu ta aika masa kira.
ALIYU POV
A gidansa dake Kaduna ya koma daman a can yake sauka a duk lokacin da ya zo ko suka zo tare da Kameela, a gidan aka fara kaita lokacin da take Amarya anan aka mata jere da komai, akwai mai gadin gidan da mai share harabar sai kuma mace daya dake zuwa every Friday ta yi mopping din gidan ta saka turare ta gyara ko'ina. Bayan ya faka motarsa ya bude ya fito ya shiga cikin gidan kana ganinsa kasan baya cikin jidadin, ba komai ya janyo masa haka ba sai rashin uzuri da kuma fahimtarsa da matarsa bata yi, yadda take da zafin kishi kuma hankalinta yake gushewa yana damunsa, ga kuma rashin rufin asiri idan ba haka ba miye na daga murya tana ihu da kuka akan abun da be taka kara ba balle ya karya.
Shi dai kam ya so ya samu mata mai fahimta da uzuri, ba laillai sai aure ko soyayya kadai ke shiga tsakanin namiji da mace ba, akwai wanin abun da zai iya hadawa aiki ko taimako ko kasuwanci ko kuma wani abun na dabam kamar dai shi da ya shiga tsakanin Emily da Turhan. Wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya gwada kiran Kameela domin ya ji babu dadi a halin da ya barta, sai ya ji line busy ya kashe kiran ya sauke numfashi a hankali ya tashi ya shiga Bedroom dinsa ya zauna sannan ya kira Emily. Kiran farko bata daga ba na biyu ma haka, a ka'idarsa baya yi ma mutum kira fiye da biyu amman saboda yana son magana da ita ta son sanin halin da take ciki sai ya sake kiranta a karo na uku. Ta daga amman ta yi shiru bata ce komai ba.
"Emily?"
Bata amsa ba, shi kuma be damu da hakan ba ya cigaba.
"Daman na aika miki sako ne saboda na damu na san halin da kika ciki, ban sani ba ko Vito yayi miki duka saboda abun da na aikata ko kuma ya kore ko wani abun, shiyasa na aika miki da sakon kuma ina yawan kiran wayarki a kashe, na je gurin Tasmia nemanki ita ma bata samu labari daga gareki ba, amman dai kina lafiya ko? Ba wata matsala?"
Ta yi shiru tana hawaye, kukanta ba shi da sauti amman jikinsa ya raya masa kuka take.
"Emily akwai wata matsala ne?"
"Aa zan yi farinciki idan ka aiko min da motata ba tare da na zo dauka ba ko kuma kai ka zo gidana ba, kuma zan fi kowa farinciki idan baka sake kirana ba, ko neman ji daga gareni, na gode da duk wani taimako da ka yi min tun daga ceto rayuwata da ka yi har zuwa taimaka min gurin rufe London na gode, alakarmu ta tsaya nan"
Ta kashe wayar, mamaki fal a fuskarsa gaba daya ma ta taushe kusurwar tunaninsa, me ya faru? Vito ne na cilasta mata yanke alaka da shi tun a yanzu ko kuma tana cikin wata matsala ne da bata son ya sani? Ko kuma barazana yayi mata da rayuwarsa ko ta yarinyarta? Sai ya ji ya gagara natsuwa da hakan a take ya sake kiransa sai ta ki ta daga.
"Ba kince kina neman hanyar da zaki saka min da abun da na yi miki ba? To yanzu ina son ki saka min ta hanyar fada min me yasa kika yanke alakata da ke? Kina cikin wata matsala ne?"
Ya aika mata da sako, sms din ya fita wayarsa kiran surukarsa Hajiya Asma'u na shigowa wayarsa. Sai ya daga da sallama
"Assalamu Alaikum"
"Aliyu ka zo yanzun nan ina nemanka"
"Hajiya Lafiya?"
"Idan ka zo zaka ji"
Ta kashe wayar, a yanayin yadda ta ji muryarta ta gautsi ya san ba lafiya ba. Ya mike tsaye kenan sakon Emily ya shigo wayarsa.
"Matarka ta yi min iyaka da kai a yanzu, ta kira ki kafira yar wuta, da fasika karuwa, na ji ni ba musulma bace amman ni ban taba yin fasikanci ba, tace ban san zafin uba ba, ban zauna gidan aure ba shiyasa nake son ruguza nata ka yi hakuri ba hakan nake nufi ba, bana nufin lalata rayuwar kowa, bata fahimta ba tace ina son na lalata rayuwar aurenta, to me zai saka na yi hakan? Miye ribata idan na yi hakan? Bana bukatar wani tashin hankali a yanzu, ban san kana da mata ba, amman zuciyata ta raya min at age dinka daman ba zai yiyu ace baka da aure ba, ka yi hakuri dan Allah kuma ka bata hakuri"
Yana gama karanta sakon ya koma ya zauna yana cire hullar kansa, domin yau shigar manyan kaya yayi. Abun da ya fara zuwa zuciyarsa shi ne a ina Kameela ta samu number Emily ma? Ya fito daga sakon Emily sai ya ci karo da na Kameela dake kasan na Emily a nan ya duba akwai sakwanin da suke turawa juna amman last sakon da ya tura daga wayarsa zuwa nata layi number Emily ce aka yi forwarding, sai ya fahimci dalilin karbar wayarsa da ta yi dazun da sunan bata yarda ba bari ta duba a nan ta tura number Emily.
Sosai ya kai makura gurin bacin rai, kuma ya fahimci idan be yi ma tunkar hanci ba abun zai iya fin haka, domin Kameela bata tsaya ta yi tunanin abun da ya dace da kuma wanda be dace ba, karamin aikinta ne ace ta sanar da iyayenta abun nan da ta faru wata kila ma shiyasa mahaifiyarta take nemansa.
Ya dauki hularsa ya saka ya fito harabar gidansa ya shiga motarsa cikin bacin rai ya dauki hanyar gidansu Kameela, yana isa ya faka a inda ya faka dazun ya fito ya nufi kofar falon, sai da ya boye bacin ran dake zuciyarsa sannan ya shiga falon gudun kar surukansa su zargi wani abu domin be san dalilin kiran da Hajiya Asma'u take masa.
Yan matan da suke falon suka amsa masa suka gaishe shi, sannan ya nemi guri ya zauna yana baza kamshi turare, daman Aliyu akwai kwarjini da cika ido sai idan ba a hadu da shi ba.
Hajiya Asma'u ta sauko fuska a daure tana sanye da Australian Lace mayafinta a kafada ta zauna a kujerar dake facing din ta Aliyu.
Anty Shafa ma ta sauko ta sai ta yi ma kanenta umarnin su fita falon, duk suka watse aka bar Hajiya Asma'u kawai sai Aliyu da Anty Shafa.
Aliyu ya gaishe ta cikin ladabi, sannan ya gaishe da Anty Shafa.
"Aliyu me ke faruwa tsakaninka da Kameela?"
Aliyu ya kalleta da mamaki.
"Ina Kameela take?"
"Tana bangaren Mama Barakat. Anty Shafa ta amsa masa.
"Me ya faru Hajiya?"
Ya tambaya.
"Shi nake son na sani, saboda ta shigo tana kuka yan'uwanta kuma sun ce ta fasa kayan abinci a falon babansu, kuma Baraka ta shiga tace Kameela sai kuka take tana fadin ka cuceta"
Aliyu yayi shiru yana danne abun da ke masa zillo a zuciya.
"Daman dai na kiraka ne na ji ko abun da zamu iya shiga ne a matsayinmu na iyayenta, kuma ba ina maganar saki ba ne, bana tunanin saki zai daga hankalinmu ko na Kameela, tsoron mu kar a karya alkawarin da aka yi mata ne, domin babu wanda ya san kun yi, dan haka be kamata a karya ba, kowace mace da yanayin yadda Allah yake halittarta yara ne ga su nan na haifa amman kowa da halinsa da kuma yanayinsa, ina tunanin ba cilas aka maka ka yi mata alkawarin ba zaka mata kishiya ba, kai ka sakata a daki ka yi mata alkawarin, mace mai irin zuciyar Kameela ni dai a matsayina na uwa da na san darajarta ba zan iya kallonta ta shiga wani hali ba ba zura ido"
Cikin natsuwa Aliyu ya kalli Hajiya Asma'u.
"Hajiya maganganun da kike min kamar kina nufin by fire by force ban isa na yi ma Kameela kishiya ba?"
"Ba zan ba ka isa ka yi mata kishiya ba, ko kuma na hana abun da ka yi nufi ko aka saka ka abun da ka yi niya ba, Ummi take da wannan ikon ba ni ba, amman dai ni a matsayina na mahaifiyar Kameela ina mai tabbatar maka Kameela ba zata zauna da kishiya ba, a yanayin zuciyar Kameela ba zan bari a kashe min ya ba"
Aliyu yayi murmushi a bayaninta na yanzu ya fahimci har yanzu bata dauke shi a matsayin danta ba, if not ba zata fada masa magana haka ba, calmly ya fara magana.
"Na gode da wannan bayanin da kika min a yanzu Hajiya, kuma na gode da kika fahimci Ummi ce kadai ta isa ta saka ni abun da ban yi niya ba, ko kuma ta hana ni abun da na yi kuduri, wannan sharadin kuma tun farko ya kamata a fada min kamin na auri Kameela ba yanzu ba, amman duk da haka na gode zan kiyaye a huta lafiya"
Ya mike tsaye ya ciro 500k aljihunsa ya dora akan center table din dake falon.
"Anty Shafa a siyawa yaran wani abu"
Daga Hajiya har Anty Shafa babu wanda ya sake cewa wani abu binsa suka yi da kallo har ya fice. Yana sauka entrance din Hajiya Asma'u ya nufi bangaren Mama Barakat sai da yayi knocking sannan ya tura ya shiga, ta amsa masa da far'a tana masa maraba har da dauko masa ruwa.
"Mama Kameela tana nan ko?"
"Eh tana dakina na ce ta shiga ta kwanta na ganta sai a hankali, Allah yasa dai lafiya"
"Lafiya kalau Mama"
"Maa Shaa Allah haka muke son ji, Dan Allah Aliyu ayi hakuri, shi zaman aure dole sai da hakuri, ba zaman aure kadai ba gaba daya rayuwar duniyar ma sai anyi hakuri, kuma kowa da inda Allah yake masa jarrabawa wani ta bangaren aure, wani ta iyaye, wani ta yaya, wani ta abokiyar zama, wani ta surukai, dan'adam baya taba zama hakan nan dole sai da jarrabawa, kaf duniya babu wanda zai zauna 💯 percent babu damuwa, dan haka ka yi hakuri kuma ka danne zuciya"
"In Shaa Allahu, Mama na gode sosai"
"Ba komai, kai ai ko da yaushe ɗana a gurinmu, dole idan muka ga za'a kuskure sai mu lurar, tun da ku yara ne mu kuma manya, bari na kira maka ita"
Ta mike tsaye ta nufi staircase, shi kuma ya sauke kansa kasa, be dago ba sai da Kameela ta sauko, sannan ya kalleta fuska a hade.
"Zauna"
"Ba zan zauna ba"
Ta daka masa tsawa tana hararasa idonta har sun kumbura tsabar fitinar kuka.
"Ba ni mamaki Aliyu ashe jira kawai kake na daga ka fara soyayya da