Showing 195001 words to 198000 words out of 249044 words

Chapter 66 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14980

min gori, abubuwa na suka banbanta da na sauran masu iyaye, ban san gata ba ban iya komai sai guduwa daga wannan gurin zuwa wani, fada da kika yi cewar da saninki kika jefar da ni kuma baki taba tunanin ki waiwaye ni ba ya tsaya min a rai, mu ma yaya muna da hakki akan iyaye, baki yi adalci tsakanina da sauran yayanki ba, su kika zabi haifarsu da aure kuma kika zauna tare da su, ni kuma kika watsar da ni, baki yi tunanin waca kalar rayuwa zan yi ba, wane kalubale zan fuskanta ba, kin yi komai saboda gujewa kunyar duniya, shin ba na ji ku musulmai kuna cewa lahira akwai hisabi ba? Saboda kin haife ni ba da aure ba ni miye laifina? Ba shawara aka yi da ni kamin a haife ni ba, ya kamata ki yi tunanin idan kika jefar da ni wace kalar rayuwa zan yi? Zan rayu ko kuma zan mutu ne? Baki tunanin ni ma ina da hakki akanki? Taya kika iya kwantawa ki yi bachi alhalin kin san kina da ya a wani gurin da baki san wane hali take ciki ba? Wace irin uwa ce ke? Taya zaka sha wahalar ciki wata tara da nakuda kuma ka jefar da yaron? Shi ma fa rai ne? Uwa tausayi aka sani da ita ke da iyayen da suke haka ba ku kyauta ba, miye laifin wanda aka haife? Wai illar kawai saboda ba shi da uba, kuma ba da aure aka haife shi ba, miyasa baki yi tunani ba kamin ki haife? Wallahi na Wahala na wahala na wahala, ni kadai na san yadda na yi na Wahala na wahala na wahala na wahala na wahala........... Ahk ahk ahk..."

Ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya da ƙoƙon rai. Mama Baraka ta bar inda take ta dawo kusa da Emily ta zauna ta rumgume ta tana kuka.

"Ki gafarce ni, ki yafe ni na yi kuskure na sani, ki yi hakuri Emily ki yafe min..."

Emily kuka Mama Baraka kuka babu mai iya rarrashin wani...




______________________

Ga iyayen da suke haifar yara ba da aure ba su jefar, shin kun san kuna daukarwa kanku hakki ne? Hakkin zina hakkin haihuwa ba da aure ba hakkin jefar da yaro, ba ku san wane hali zai fada ba wace rayuwa zai yi a wane hali zai girma ko ya samu kansa ya rayuwa zata kasance, wasu yaran ba za su taba haduwa da iyayensu ba sai Alkiyama.

Allah ya tsaremu, ka tsarkake zuciyarmu.🤲
[8/4, 9:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t



*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*



Page 6️⃣2️⃣


Na tashi a wani ƙaramin gida a Beere, cikin unguwar da ruwa ke ta faman gudu daga bututun da babu mai kulawa da shi, cikin amo da hayaniyar kasuwa, da ƙamshin ewedu da ata rodo na mahaifiyata.
Baraka suke kirana ɗiya ga wani tsohon malamin addinin.
A cikin al'adun Yarbawa, mata suna da 'yancin yin kasuwanci, sana'a ko aiki tun da dadewa. Wannan ya bambanta da wasu al'ummomi da ke takaita mata ga aikin gida kawai. A yawancin biranen Yarbawa, musamman kamar Legas, Ibadan, da Abeokuta, za ki ga mata masu kasuwanci ko aiki a hukumomi.
Iyayen Yarbawa suna koyar da 'ya'yansu mace da wuri cewa ta rike kanta

Yana daga dabi'unsu su karantar da 'ya mace ta nemi ilimi ko sana'a domin ta rike kanta, ba tare da dogaro da namiji ba. Wannan ya sa da yawa daga cikin matan su ke da ƙwarin gwiwa wajen kokarin ciyar da kansu ko tallafa wa iyalansu.
Na koyi juriya daga rayuwa, ba daga littafi ba. Na girma ina kallon mahaifiyata tana dafa abinci a kan itace, tana kula da gida kusan nauyin mu da na mahaifina a wuyanta yake, mahaifina ba shi da wani karfi kuma be damu da nema ba, ta kan ce min:

“Baraka, mace na da ƙafa biyu  ɗaya tana goyon gida, ɗaya tana neman arziki.”



Na shiga cikin harkar girki wato siyar da abinci, tun ina 15yrs mahaifiyata kuma tana fita shago siyar da kayan masarufi, a lokacin ban fara karatu a kolege ba, na iya hada tuwo da hannu, da kwasar romon miyar ogbono cikin harba guda. Na kammala karatu a wata college Ibadan, amma bayan na gama sai na gane cewa takarda ba ta nufin abinci a kwano.
Domin bayan gamawa, ba aikin da ya biyo ba. Na zama kamar mutumin da ya haɗiye ƙashi, ba zai hade wuce ba, kuma ba zai iya fitarwa ba. Na tattara kayan da ba su wuce buhu biyu ba, na tafi Lagos, wurin kanwar mamata, saboda gurin da nake siyar da abinci a da gonati ta kwace, mahaifiyata ta kuma shagonta yayi kasa, ga shi mu bakwai mahaifinmu ya haifa ba daya ko biyu ba, ni ce ta biyu idan ban tallafi mahaifiyar da ta tsaya akan ilimi da abincin na ba me zan yi?

Na fara komai daga tushe. Na rika siyar da abinci a Mile 12, da jarin da mahaifiyata ta hada min, wata rana a siyar wata rana ba za a siyar ba, wani sa'in sai na roki kanwar Mamana ta ara min kudi nake samu na kulla wani jarin, gashi mijin aure ya gagareni a lokacin ko da yake ni kaina ban shirya auren ba domin ban tanadi komai na aure ba, haka mahaifiyata ma bata da wani abun aurar da ni a lokacin.

Na ci gaba da girki har wani lokaci sai wani NGO  ya fitar da talla, na neman ma'aikata, cika da takarduna na karatuna, ban sani ba ashe aikin ne silar wargewar rayuwarki, bayan wani lokaci. suka sanar min sunana ya fito. Na tafi gurin horarwa suka min interview bayan na yi nasara suka sake sanar min an dauke ni, farincikin be bar ni na kwana ba a ranar.

Kusan zan iya cewa addu'ace ta ba ni nasara domin babban guri ne da shugaban gurin ya kasance bature jar fata mai tsakanin fari da jan gashi ga kuma blue eyes, kyakkyawa ne mai far'a da son bakar mace kamar ba jan kunne ba, na fara aikin a gurin a matsayin sakatariya ina kula da komai zuwa kan lokaci girmama kowa bawa komai hakkinsa.

Sannu a hankali aka na saba da kowa a gurin ba iya ma'aikan gurin ba har da masu zuwa su fita. Daga gaisuwa da mutunci muka fara sabo da Rowan Alaric MacLeod wato shugaban gurin, a lokacin akan masa lakani da bello, domin farar fata idan suka tsallako kasashenmu sukan nemi suna su sakawa kansu saboda ku saje da mu kuma mu saki jiki da su.

Bature ne da ya zo daga Scottish, zan sake maimaita miki wannan, Me kyau ne sosai kamar ke kyaunsa ne abun da ya rude ne, na kasa dauke ido daga gareshi shi kuma ya saka min fuska ya rika ba ni damar matsawa kusa da shi, ba kuma zan miki karya ba ta dayan gefen ina hange kudi da yake da su, kamar idan na same shi a matsayin saurayi na huta, domin ba addininmu daya ba, na san abu ne mai wahala mahaifina ya amince na aureshi, ban sani ba ashe yana da mata, nina fara nuna matsa kauna sai ya sanar min yana da mata yar da yara biyu a tsakaninsu, hakan sai ya saka na yi baya, shi kuma a lokacin ne ya kamu da kauna ta sosai, sai kusancinmu ya fara yawa, har ta kai ya kan bukaci na kawo masa abu a gidansa ko kuma ya saka matarsa da kanta ta kira ni ta sanar min idan wani abun ya taso na aikin ko kuma familynsu kamar taron biki ko birthday ko kuma danta idan ba shi da lafiya ko yarta, ban sani ba ashe ya fada mata cewar nice kadai babu ruwana a cikin matan da yake aiki da su, ni ce kadai ya yarda da ni saboda sauran wasu ba su da amana wasu kuma suna nemansa.

Ashe yayi hakan ne saboda matarsa ta aminta da ni da shi, ko da an kawo mata wani zance ko ganin mu wani guri ba za a zargi komai ba, da haka muka fara mu'amala yana sakar min kudi yana nuna min kauna, na sake jiki da shi kuma na zama mai fuska biyu domin matarsa da wacce ta fini komai na mata kuma ta kasance yar kabilar igbo ta aminta da ni, amince da har yau bata daina ba. Ban ankaro ba na samu ciki na tafi asibiti da taimakon likita aka zubar da cikin dan wata biyu, muka sake komawa ruwa.

Ina samu kudi na aikawa gidanmu a inda nake kuma ina watayawa yadda nake so, rayuwa ta ci gaba a haka wata rana bayan gama al'ada na tafi aka ba ni maganin hana daukar ciki, aka fada min dokokin yadda zan sha kuma na bi ka'ida da haka ba ni da haufi muka cigaba da shedanci, ban sani ba ashe tun kamin na sha maganin na dauki cikin ki amman babu wata alama a tare da ni dake muna akwai ciki, idan lokacin al'adata yayi zan yi idan na gama na yi tsarki.

Wata rana, na tashi daga aiki, ina isa gida ciwon mara mai tsanani ya rufe ni, na sha magani be daina ba kuma be saba min haka ba, kusan ma zan iya cewa ba watan al'adata ba ne, da abun yayi min tsanani kamar ana murza mini ciki da mashin din wuta, sai na yi mamaki

"yau kuma al'adar ta zo min a tsakiyar wata da fushi ne? Amma me ya sa take murda ni kamar na yi hauka?”

Na sha paracetamol. Na dinga juyawa a gado. Amma ciwon ya ƙi sakina. Na daina numfashi da kwanciyar hankali. Cikin rudani aka kaini asibiti, bayan an ba ni gado na samu kulawar likita sai, Likitan ya dube ni, ya ce cikin natsuwa:

“Matar nan, ko kin san kina da ciki ne?”

Na ce da shi cikin zafin rai

“Dokta kar ka yi wasa da ciwo, al’ada ce kake gani, ba ciki ba ne.”

Sai ya ce da ni:

“Toh ina jin heartbeat ɗin yaro ma'ana bugun zuciyar jariri yana da rai a cikinki.”

Na ce

“Jariri kuma? Ciki?? Ai ni bana da ciki! Ba ni da wata alama ta masu ciki ma, Ina nono ya kumbura? Ina tashin zuciya? Al’ada ma tana zuwa kamar yadda ta saba!”

Cikin natsuwa ya ce

“Wannan ba ciki irin na mutane bane. Wannan cryptic pregnancy ne, ciki mai ɓoye kai. Na ga mata irin ki da yawa da ba su san suna da shi ba sai sun zo asibiti. Cikin na girma ne a ciki, yana ɓoyewa a waje. Kuma Jikinki da kwakwalwarki sun hana ki gane cewa kina ɗauke da rai.”

Ya ɗan tsaya, ya ce:

“Wasu mata sukan ci gaba da yin jinin da suke ɗauka a matsayin al’ada. Wasu ba sa jin canjin jiki saboda hormones ɗinsu ba su nunawa. Sai dai kawai wata rana a ga ciki ba tare da an shirya ba.”

Be gama bayani ba ruwa ya fashe min, a nan na saki hawaye. Ina kallon likitan kamar ace zai iya yin wani abu. Ina tambayar kaina da gaske haihuwa zan yi?
Bayan sa’a biyu kacal, na haifi wata yarinya da ta fi hasken idanuwa kyau, fara kyakkyawa mai matukar daukar hankali, ga jan gashi da blue eyes, kikashigo duniya cikin sirri, amma da annuri da kuka kamar kowane jinjiri.

Baki rage komai daga kamanin mahaifinkin ba, kuma baki dauko komai daga gareni ba, sam ba za a taba yarda ni na haife ki, saboda gene din farar fata yana da karfi, a duk yadda aka haihuwa ko da yara ba su dauko gaba daya ba, su daukon wani kaso, masu gene mai karfi kuma basa raga komai haka kika zo min, kamar dai na rike ki, amman ina tsoron kallon da duniya zata min da kuma abun da iyayena za su ce, kanwar mamana ta siyo kayan jaririya na saka miki na lullube ki cikin zane, tun a asibitin tayi min fada bayan ni ma na yi ma kaina, ni da ita muka shirya ba za mu bar asibitin ba sai dare saboda mun shirya jefar da ke a inda muke ganin zaki samu masu rika ki.

Sai karfe 8pm muka fita asibitin muka tari abun hawa zuwa inda ta bincika tun da rana ta samu, nesa da gurin muka mukaci mai taxi ya aje mu, da kafa muka taka muka isa gurin babban gida ne zagaye kuma inguwa ce da babu mutane sosai, na bude jakar da na zo da ita asibiti kuma wanda nake zuwa da ita aiki na dauko pen da farar takardar na rubuta sunanki "Aisha" domin shi ne sunan da na fi so, na saka a saman jikin ki sannan muka zagaya ta bayan gidan muka aje ki. Ni da ita muka yi ta gudu muka barki kina kuka, ni ma ina kuka.

Tun daga ranar mafarkinki be bar ni ba, ban kuma sake zuwa aikin ba, an aiko har inda nake nemana na sanar musu ba ni da lafiya, da kansa ya zo dubani amman ban fada masa ba, matarsa ma ta zo duba ni ita ma bata sani ba. Tsoron yadda duniya zata kalle ya saka ban waiwayeki ba, wata kila sun ga kin yi kama da turawa ne suka saka miki Emily, ko kuma basa bukatar musulmai ne, domin bayan na aje ki na sake bi da gurin sai na ga gidan marayun na Christian ne karkashin kulawar wata coci.

Daga lokacin kuma zaman garin be sake min dadi ba, sai na tattara na koma garinmu da zama, dan abun da na tara na cigaba da kasuwancina da shi, ban yi wata uku na miji aure ya fito min daga dangin mahaifiyata na aure shi, ba mu dade ba ya rasu kuma ban haihuwa da shi ba, bayan rasuwarsa rayuwa ta cigaba na kama sana'a duk inda na ji ana neman aiki na kan kusa na nema ni ma, amman ban yi nasara ba sai a wani banki da ke kusa da mu.

Sanadin wannan aikin na hadu da mijin da nake aure yanzu, kasancewar dan kasuwa a wacan lokaci ya kan siya abubuwa daga arewa ya shigo da su gurinmu, na gurinmu kuma ya dauka ya shiga da su, wata rana ya samu matsala ya zo bank a nan muka hadu.

Har ta kai ya san gidanmu ya fada min labarinsa kuma ya nuna yana son ya aureni, da farko iyayena ba su amince ba, saboda suna ganin bahaushen mutum baya rike aure tun a wacan lokaci sai dai kudin da yake da su sun taka rawa gurin amincewar iyayena, ni kuma ina hangen yadda bahaushe yake wadata matarsa da komai ba sai taje nema ba, a wacan zamanin mazan hausawa suna daukar nauyin dawainiyar iyalansu ne.

Da haka aka amince muka yi aure ya dawo da ni gidansa a garinsu, a nan kuma wani tashin hankali ya same ni, domin matarsa fitinanniya ce yayansa kuma fitsararru ne, sai dai yarda da yake da ni da kuma yadda yake kaunata ya taimaka min wajen jure zama da su, sannu a hankali likkafa ta yi gaba arziki ya kara bunkasa har siyasa ta shigo ciki, zuri'a kuma ta samu, ta karkashin kasuwancin ya zama bashi da uban gida sai Alhaji Bello Bulama wani mutumen Maiduguri ne wanda ya shahara ciki da wajen kasar nan ta bangaren kasuwanci.

Ba zan yi karya ba, mijin da nake aure a yanzu yana sona sosai domin ba ni da hayani duk kuwa da kasancewa ta bayarabiya wasu sukan ce yarbawa suna da fada, amman ni na sha banban, kuma na rike matarsa da yayansa da amana, sannan ni ce yar boko kusan duk inda zai shiga da ni yake zuwa, idan wani abu ya taso ma kasuwanci na kan ba shi shawara kuma idan ya bi sai ayi nasara, wannan ya saka har maigidansa ya san da ni, da muka tafi gidan muka samu tarba daga matarsa wacce ta kasance mai son mutane kuma ita ma yar kasuwa, muna gaisawa ni da ita muka gane juna, ita ce matar da na yi aiki da mijinta kuma mijinta ya amintar da ita da ni.

A nan ta fada min sun rabu da mijinta saboda baya son haihuwa kuma yana da wata mata a can bata sani ba sai da lokacin da zai koma garinsu yayi ya koma da ita, daga baya ta gano yana da wasu iyalan kuma ita baya son ta haihu da shi, ashe a can idan ka saki mace sai ka bata rabin dukiyarka musamman idan akwai yara, ta shigar da kara kotu ta rabu da shi aka danka mata dukiya mai yawa sai ta siyar da komai ta bar kasa ta dawo garinta na Lagos ta fara kasuwanci ta fada min bayan dawowarta yarta ta rasu ya rage yaro ne kadai take da shi.

Ta sake wani aure sai ta auri musulmi wanda ya kasance Alhaji Bello Bulama, mai gidan maigidana a bangaren kasuwanci, da haka ni ma na shiga cikin mukarrabanta, ta ja ni a kusa tana saka ni cikin huldodinta. Idan mijinta yayi tafiya ya dawo ko'ina mai gidana yake zai aje abun da yake yaje ya yarboshi, ba shi kadai ba kusan duk yaran da suke karkashinsa haka suke, idan zai tafi daga Kaduna tare muke zuwa saboda yana ganin mun san juna ni da ita kuma muna da kyakkyawar fahimta.

A lokacin da suka dawo daga Sudan muka tarbe su har ta hado ni da ke, ina ganinki jikina ya ba ni, ba na gane ki ba, na sanin ni ma ina da ƴa mai kama da turawa a wani gurin da ban sani ba ko tana raye ko a mace, amman daga lokacin da muka shigo jirgi kika ba ni labarinki sai na kasa rike kaina a kamaninki suka bayyanar min fuskar mutumen da na bi son zuciya na biye masa na lalata rayuwata.

Na tsorata kuma na yi bakinciki da halin da na ganki kuma kika fada min domin ni ce silar komai na san dole ina da kaso mai tsoka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login