Showing 186001 words to 189000 words out of 249044 words

Chapter 63 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14940

da rashin son tafiyar Ummi ta ce

"Tohm Allah ya tsare, ya kaika lafiya amman da jami'an tsoro zaka je?"

"Aa zan tafi da addu'a dai"

Ummi bata sake cewa komai ba ta mike tsaye ta.

"Aliyu kana son yarinyar nan ne?"

Ya daga kai ya kalli Ummi sai kuma ya kalli wani gefen alamar nazari.

"Aa iyakar abin da na sani shi ne, ina matukar tausayinta, ta shiga mawuyacin hali tun daga haihuwa uzuwa yanzu, kuma ina ganin a yanzu babu wanda ya kamata ya kyautata rayuwarta irin musulmi, ya kamata ta san muma akwai na gari cikinmu, ban ce zan iya ba amman ina son na ga na maye mata gurbin wasu abubuwan da ta rasa ne"

Ummi ta sauke numfashi a hankali ya fara takawa cike da girma ta fice daga garden din. Ta yi mamakin ganin bakuwar mota a gidan, duk kuwa da ta san gidansu gidane dake yawan samun baki koda yaushe amman wannan motar ta musamman ce domin sunan mahaifin Kameela ne a jikin number motar, hakan yana nufin motar gidansu ce daman su plate din motarsu ma da sunan familysu ake yi.
Ta hau entrance din ta tura kofar falon da ba a gama rufewa ba ta shiga, ta gangan ta yi kamar bata san da kowa a falon ba har sai da Kameela ta mika mata gaisuwa.

"Ummi ina wuni?"

Ummi ta kalli gefen da Kameela take zaune.

"Kameela? Ina ce dai lafiya?"

Cikin yanayin damuwa Kameela ta amsa.

"Lafiya kalau Ummi, na je asibiti ne gurin Aliyu aka ce an sallamo shi, shiyasa na zo gida"

"Okay, akwai wani hakki naki da yake kansa da be sauke ba ne?"

Ta girgiza kai kwalla na taruwa a idonta.

"Aa na zo na duba lafiyarsa"

"Baki bukatar duba lafiyarsa Kameela domin a yanzu babu wani abu a tsakaninku, amman duk da haka mun gode da ziyara zaki iya tafiya"

"Sau ba goma ina zuwa ganinsa asibiti ba su bar ni na shiga ba, yanzu kuma na zo gida ba zaki bar ni na ganshi ba Ummi? Wata uku har da sati a sama ban saka Aliyu a ido ba wannan ma azabtarwa ce, saki daya yayi min Ummi ba uku ba akwai sauran gyara"

Ta fada cikin kuka. Ummi ta taka zuwa inda take tana kallonta.

"Haka ne, akwai sauran gyara a halayyarki Kameela, tun da har son zuciya zai iya daukarki ki yi kokarin kashe mijinki, kuma zuciyarki ta raya miki mahaifiyar mijinki zata yarda ki sake zama da danta saboda hauka ce ta haife ni, kuma zuciyarki ta raya miki wai akwai sauran gyara tsakaninki da mutumen da kika so ki shafe rayuwarsa daga doron kasa, har kika ikirarin an azabtar da ke da rashin ganinsa, ada can kina tunanin idan kika kashe shi gawarsa za a aje miki kina kallo?"

Kameela ta kara fashewa da kuka.

"Wallahi Ummi ina son Aliyu... Kishi ne Wallahi, kowa zai iya kuskure ki dauke ni kamar..."

Ummi ta nuna ta da yatsa da taka mata tsawa

"Ke yarinya kama hanya ki fice, idan kishi ne miyasa ita mahaifiyarka bata kashe mahaifinki ko kishiyarta ba? Abunda nake gani a labarai kika so ko wace jarida ta yi ado da fuskar dana a jiki? Lallai har yanzu baki da hankali"

Ummi ta nuna mata kofa da yatsa. Kameela ta nufi kofar tana kuka ta fice, Ummi ta tsaya jiki windows har sai da ta ga ficewarta a gidan sannan ta juyo ta nufi stairs.

TURHAN POV.

Wani irin kuka sosai Fatima take da daukar numfashi tana kiran sunan Momy.

"Momy... Momy..."

Ammy ta kalli Fatima dake kwance kan godonta tana bachi a motse saboda tunani da rashin cin abinci. Sai kuma ta kalli danta da ya fi Fatima rama da shiga tashin hankali saboda damuwarsa da Fatima take da tambayar ina Momynta, ga kuma rashin sanin halin da Aisha take ciki domin tun da ta tafi har yanzu ba a samu wanda ya ji duriyarta ba, kuma bata dawo gurin yarta ba.

"Da ace na san haka rayuwa zata zame maka ta zame mata daban hada auren nan ba"

Ammy ta fada cikin tsananin damuwa, abu ne da yake bayyane a gurin kowa babu wanda zai ce ya taba ganin Turhan a cikin wata matsala da ta haifar masa da rashin cin abinci na kwana daya, sai ga shi a yanzu baya iya cin abin kirki bachi ma wani lokacin sai yayi da gaske yake yi, saboda tunanin tambayar da Fatima take masa, da kuma tunanin a wane hali Aisha take ciki, a dayan bangaren kuma yana auna tsakanin tsanar da ta yi masa, saboda kawai yarta ta zaba shi sai ta tafi ta bar shi da ita har na tsawon lokaci babu sako ba aike babu wata hanya da za a iya samunta.

"Haba Ammy be kamata wannan kalamin ya fito bakinki ba, ai ke alheri kika yi nufin aikatawa kuma shi kika aikata kuma alheri ya samu tun da gashi ina da Fatima, ni ne na kawo duk wata matsala da muke ciki yanzu, tunani ne sai na rasa wane zan yi, kullum da fargaba nake farkawa a guntun bachin da yake daukata a karshen dare, fargabar tambayar Fatima, ga shi ta dauki damuwa ta saka a ranta yanzu ta daina sakewa da kowa ta daina walwala, kuma ita kanta Aisha yanzu ba mu san wane hali take ciki ba, kuma ina fargabar kar ace ta fada wani hali saboda rashin Fatima idan har haka ya faru laifin a kaina zai sake komawa"

Ta kalleshi cike da tausayi.

"Ka yi iya kokarinka kuma na baya ba, ka nemeta a lokacin da baka san tana tare da yarka ba, a yanzu kuma da ban saka ka ba, ka saka kanka ka je har garin da ta zauna baka sameta ba, a garin nan bana tunanin akwai inda kafarka be taka ba gurin nemanta, nan ma baka dace ba, tun da ka baro Sudan baka koma ba saboda Aisha, a haka ma ka biya Turhan kuma ina alfahari da kai, jikina yana raya min kamar tana wani guri kusa ta boya ne kawai saboda ta fitine mu, tun da gashi yanzu Fatima kullum sai ta daga mana hankali saboda neman mahaifiyarta"

"Amman me yasa bata dawo ba?"

"Saboda ta azabtar mu mana, saboda idan ta waige mu sai mu mika mata Fatima jiki na rawa"

"Da ma dai ban sake ta ba, zata iya zuwa fa ta dawo da auren wani akanta"

"Zuciyar yarinyar nan bata da kyau, duk wata uwar kirki ba zata iya tafiya mai tsayi haka ta bar yarta ba, saboda kawai ubanta yayi mata ba daida ba, ni miyasa ban kyale ka ba? Bayan duk abun da ubanka yayi min? Wani lokacin idan na tsaya ina tunani sai na rika ganin kamar ba Aisha bace ban yi zaton zata iya aikata haka ba"

"Na fi tunanin kamar bata lafiya, ko kuma wani abun ya same ta, wata kila da yanzu ta dawo, domin yadda nake jin Fatima ni kam ba zan ma iya sati ban saka ta a ido ba"

"To ya sani tun da ta zabarwa kanta guduwa? Wani abun ba kaddara ba ce har da hali"

"Kuma ni sai nake ganin kamar Aliyu ya san inda take, kawai dai yana wasa da hankalina ne ko kuma yana jiran na nemi taimakonsa ne wanda abun ne da ba zai taba faruwa ba har abada, gashi ba wani tufafin kirki take sakawa ba yanzu"

Yana maganar cike da zafin kishi marar misaltuwa.

"Idan har abun da kake zargi ya tabbata to ni ina baka shawarar ka hakura da yarinyar Turhan, shi kuma sai mu ga idan dan halak ne"

"Ai be san kunya ba Ammy ina cire kafa tasa zai saka ya taka, da ace ya san kunya ba zai aikata abun da ya aikata min ba, domin no matter what ya fi kusanci da ni fiye da Aisha, amman ya zabi ya ci amanata, na san ban kyautata ba amman dai ai ni abokinsa ne Aisha kuma be da alakar komai da ita"

"A wani mutum makiyinka ne Turhan a cikin yan'uwa ma akwai su kuma munafikin mutum yana da wahalar zama da ganewa, amman ba zaka taba sanin sai wani abun ya faru, wani zaka samu yana maka hassada ne domin idan babu wannan ban da dalilin da zai saka mutum ya zabi bare sama da wanda ya sani ba, kuma har ya nuna maka kirkiri ai kiyayya ta kai kiyayya, sai dai ka yi taka tsantsan"

Turhan yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin gaba daya kansa ya kulle ta ina zai samu Aisha? Ina ta shiga? Tana raye ko kuma tana cikin wani hali? Miyasa zata masa irin wannan horon mai azabtarwa haka? Tsanar da take masa ta kai har can? Amman ta saba guduwa halinta ne. Wani bangare na zuciyarsa ya raya masa, sai dai be gamsu da hakan ba domin yana ganin ga rayuwarta a nan wato Fatima.
Ya jingina jikin mota yana kallon tausarin da suka yi sararin samaniya ido, ya tsada idonsa gurin wata tauraruwa wacce ta fi sauran haske a dare.

"Na zabtu Aisha, na azabtu fiye da yadda kike tunani, na shiga damuwa na rashin sanin halin da kike ciki, fargabar irin tarbar da zan samu a gareki ya hana ni walwala, ban taba sanin muhimmancin wani abu na kimanta shi ba kamar yadda nake jinki a yanzu, na yi iya yadda zan iya na san wane hali kike ciki amman hakan ya gagara, yaushe zaki dawo gareni? Idan kin dawo zaki saurere ni kuma dai yafiyar ba yanzu ba ce? Kin ce baki taba so na ba, kin yi komai saboda mahaifiyata, yanzu miyasa ba zaki yi saboda yarki ba? Ina son ki Aisha ina son kasancewa da ke"

A hankali yake lumshe ido yana budewa zuciyarsa cike da kuna, ya hade yawu.

"Ni mai tarin laifuna a gurinki na sani, amman ki ba ni damar da zan gyara mana, kina ina Aisha? Na ji fiye da yadda kika ji a lokacin da na barki, saboda ni a yanzu kin tafi ki bar ni da azababben Ciwon Sonki da tsananin kishinki, kin bar ni da tunaninki, ga fargabar abun da zai same ki da yadda zaki karbe ni, a yanzu ke baki jin komai saboda bana kusa da ke, amman ni ina jin duk wata azaba ta duniya saboda rashinki"

Ya juya baya.

"Ban san dacin rashi ba da kewa ba sai da na rasa ki, amman zan nemo ki, zan jure duk wata tsana ko tsangwama daga gareki har sai kin yarda ni ABOKIN RAYUWARKI ne, a inda na wulakanta zan daukaka darajarki wannan alkawarina ne, ki yafe min Aisha, dan Allah karki bar ni, ina da bukatarki a kusa da ni, ko da ke baki ra'ayi na na san ba zaki so ni ba, amman ni ina Sonki haka ma ya wadatar, abun nan ba shi da sauki ko kadan, ya wuce duk yadda kike tunani"

Ta lumshe ido ya cije lebensa na kasa cike da kukan zuci wanda ya fi na hawaye daci. Sai a yanzu yake ta kara dorawa kansa laifin abubuwan da suka faru, yake nadamar abun da yayi mata kuma yake ganin rashin dacewa a hakan, babu komai a tare da shi a yanzu sai tsantsanar kaunar Aisha da kewarta da kuma nadamar da bata da amfani.



EMILY POV.

Ya aje mata tsarabar da yayi mata a gafen gado sannan ya kai hannunsa ya taba jikinta sai ya jishi da zafi kamar kullum. Taba ta da yayi ya saka ta bude ido daman idonta biyu ba bacchi take ba, ta kalleshi da idanuwanta da bata iya budewa sosai.

"Babu ranar da zaki ji sauki idan ba zaki daina tunani ni ba, tunanin nan shi yake haifar miki da damuwa, ita kuma damuwa bata barin kwakwalwa ta huta, kwakwalwa kuma bata mikawa kowa matsalarta sai zuciya da jiki"

"Am so fighting for peace, ina ta yin kokarin abun da zan iya, da kowane numfashi ina tunanin yata da rayuwata, na yi marmarin kurciyarta a lokacin da ban san tashin hankali ko bacin rai ba, ban san muhimmanci iyaye ko yan'uwa ba"

Ya zauna gefen gadon sai ta tashi zaune ya kalleta gaba daya ta bi ta fita hayyacinta saboda tunani da damuwa, kusan tun da ta zo gidan ta gagara sakewa da kowa abinci sai dai a kawo mata a daki, sai idan yana gidan yake cilasta mata fitowa dinning ta ci abinci tare da kowa, ga ciwo kullum lafiya ta ki sama mata salama. Dr A-B yayi iya kokarinsa gurin dauke mata hankali da wasu abubuwa amman hakan be samu ba, ko Tv aka kukuna mata madadin damuwa ta ragu sai ta karu, idan ta ga yara, idan kuma wani bangare ne da ake kuka haka zata yi ta kuka kamar gaske. Idan ta auna yadda take ji a yanzu da ta san Fatima tana hannu da guri mai kyau, sai ta yi mamakin yadda mahaifiyarta ta iya jefar da ita kuma ta jure rashinta, a nan ta fahimci wasu mutanen an yi su ne kawai saboda su kaunaci mutane ba dan su samu kaunar daga gurin kowa ba.

"Da nace zan saka a dauko Fatima ko? Kika ce aa kuma saboda ita kullum kike damuwa?"

"Bana son kowa ya san inda nake, ina jin aminci da natsuwa a nan, kawai dai na gafara sabo wa da kowa ne, kuma ina ta guje ni bayan tsawon shekarun da muka dauka a tare, idan har zan kusance ta sai ta bukace ni, ina son na saba da rashin komai kamar yadda kaddara take koya min"

Ya kai hannu ya shafa kanta cike da tausayin hawayen da take zubarwa.

"Kina horar da kanki ne kawai, Fatima karamar yarinya ce bata iya gane daidai ko kuskure yara suna bin son zuciyarsu ne kawai"

"Haka ne, ni ma son zuciyar na bi ya kai ni ya baro"

"Wannan tunanin yake haifar miki da damuwa, Momy ta fada min tun da na tafi baki fito ba, da zarar tafiya ta kama ni zuwa wani guri baki sake fitowa, kuma zuwa yanzu ya kamata ace kin sake jiki da kowa Emily"

"Ka yi hakuri zan saba, amman ba lokaci daya ba, abun ba shi da sauki ko kadan"

"Na sani, yanzu taso muje mu ci abinci a upstairs"

Ya share mata hawayenta, ta san duk yadda zata musa masa ba zai taba barinta ta zauna a dakin ta ci abincin ba, dan haka ta sauko da kafafuwanta sai ya yaye mata bargon dake jikinta ya rika hannunta ya nufi kofa ya bude ya rike mata ta fito ta yi rama sosai kurmin idonta har ya fada, kana ganinta ka ga mace mai damuwa. A falon Momynsa yake cin abinci dan haka ya nufi upstairs watching her steps har suka haura ya shiga falon yana rike da hannunta.

Tun da suka shigo akan hannunta da Dr A-B ya rike Aliyu ya sauke idonsa, kamin ya isa gurin fuskarta, for the first time ya ji kamar yaje ya da gudu ya rumgumeta ya fada mata komai zai wuce, saboda yadda yayi marmarinta da kuma damuwar da ya gani a tare da ita ga wata rama da ta yi abun tausayi. Tsayawa ta yi cak, Dr A-B ya kalli kafarta kamin ya kalli fuskarta zuwa abun da take kallo, sai ya ga mutanen da ba bakin fuska ba ne a gurinsa musamman Mama Barakat. Ya kalli mahaifiyarsa dake zaune zai yi magana ta riga shi.

"Ka same ni ɗaki zamu yi magana"

Ya saki hannunta.

"Je dakinki"

Ta juya tana jin abun some how, taya suka san tana nan? Ko dai shi ya fada musu? Ta sauka kasa tana tafiya hawaye na sauko mata har ta isa kofar dakin ta murda ta shiga ba tare da ta juyo ba balle ta rufe.

"Har yaushe zaki yi ta gudu ne ke kam Emily?"

Ta juyo ta kalleshi har ga Allah bayan yarta shi ne mutum na biyu da ta yi marmarin gani.

"Taya ka gano ni?"

Ta taka ya shiga cikin dakin.

"Ta yadda mutuwa take neman rai, duk inda kika shiga zan nemo ki Emily, duk inda kika tafi zan biyo sawunki"

Hawaye ya sauko mata

"I don't need to do this, ban cancanci wannan sadaukarwa ba"

"You just don't know what you mean to me, tabbas ban cancanci sadaukarwa daga gareki ba, alfarma nake nema, Emily ina son na maida ke gida"

Ta yi baya baya ta zauna tana rumgume da hannayenta tana wasu hawaye masu zafi. Ya karasa cikin dakin yana kallonta cike da tausayi. Ya zauna nesa da ita tana kallonta shiru yatsasu na tsawon lokaci, kamin ya yanke shirun da fada mata abun da ta fi bukatar ji a yanzu.

"Fatima tana lafiya, amman ta yi marmarinki sosai"

Ta lumshe ido, bata da tabbaci abun da Aliyu ya fada amman dai ta ji sanyi a zuciyarta.

"Why are you here?"

Ta tambaya ido a lumshe, muryar a dakishe, Aliyu ya amsa mata kamar mai rada.

"To take you home"

Ta girgiza kai tana maida numfashi sai dai bata ce komai ba, ita a tunaninta rayuwarta ta zo karshe mutuwa kawai ya rage mata. Aliyu ya cigaba da kallonta cike da tsantsar tausayinta dake ta dawainiya da shi.

"Duk lokacin da kika ji ba zaki iya ba, ina nan kusa da ke, hankalina zai fi kwanciya ace duk lokacin da kika farka, zan kasance kusa, na ga nauyin da kike ɗauka ke kaɗai
yaƙin da kike yi, tabon da kika nuna"

Ya hade bacin ran daya tsaya masa a wuya.

"Ba sai kin ɓoye shi ba yanzu
zan zama ƙarfinki, kuma na yaki baƙin cikinki, idan dare ya yi miki sanyi kuma duniya ta zama maras tausayi a gareki, ki bar ni in zama lafiya da kike nema"

Yayi shiru na dan lokaci.

"Zan ɗaga darajarki, zan share hawayenki
zan tsaya tare da ke cikin kowane hali, farinciki bakinciki ko kuma duka, idan kina buƙatar hannun da zai rika ki ya tsamo ki daga rijiyar da kika fada, zan miƙa nawa, idan kina buƙatar yin ihu, ki yi zan ji kukanki na saurareki Emily"

Yayi shiru yana kallom hawayenta, hawaye take sosai har wani kololon kuka ke mata yawo a zuciya.

"Duk abin da zan ɗauka don ki samu nutsuwa dauka, zan tsaya tare da ke, hakan zai samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login