Showing 21001 words to 24000 words out of 249044 words
taba fada dalilin da ya saka bayan Turhan ban sake haibuwar kowa ba?”
“Aa be taba fada mana ba, Abba baya zama yayi hira da mu yadda kike yi Ammy”
Ammy ta yi shiru tare da dora hannunta daya akan daya.
“Dauke breakfast din nan”
“Baki ci komai ba Ammy”
Ammy ta daga mata kai, Jawahir ya tashi tsaye da dauke breakfast din ya fice, Ammy ta mike tsaye ta nufi karfen dake balcony din ta tsaya yana kallon harabar gidan. Ammy na jin lokacin da Jawahir ta bude kofar falon ta fito balcony din da Ammy ta fi yawan zama musamman da safe idan zata karya ko kuma da yamma.
“Mahaifinku ya taba fada muku cewar na zauna a gidan kaso?”
Mamaki ya cika fuskar Jawahir.
“Gidan kaso kuma? Yari fa kenan Ammy”
Ammy ta daga mata kai ba tare da ta juyo ba.
“A zamanin da na yi yan matancin, a cikin yayan sarakuna musamman na yankin arewa bana jin anyi wata yar sarki mai farinjini irina, ba nufin sarautar gidanmu ko kudin mahaifina ba, ina maganin farin jini ne wata baiwa da Allah ke hallita bawa da ita”
Ammy ta juyo tana murmushi ta kalli Jawahir dake tsaye.
“Ba ni da kyau sosai, haka kuma ni dan ba za a kalleni ace min mummuna ba, kamar yadda ni ba fara ba amman ba fi fararen matan kyau da shiga zuciyar maza, bana zama a guri na tashi wani be so ni ba, na yi farinjini sosai, yayan manyan mutane da manyan mutane sa kansu sun nuna sha'awar kulla danganta da mahaifina ta hanyar aurena, a lokacin da ace za a titsi ni na fitar da wanda nake so ba zan iya ba, domin hankalina ba a kan soyayya yake ba, kuma dukan masu neman aurena suna kyautata min yadda ya kamata na so su, mahaifina kuma yana alfahari hakan”
Ta nufi kujerar data tashi ta zauna Jawahir ma ta zauna a kujerarta tana kallon Ammy fuskarta fal da mamaki.
“Wata rana mahaifina ya karbi babban abokinsa kuma babban sarki garin Khartoum, masarautarmu ta san da zuwan sarkin kusan kasar ma ta san da haka, domin ya gana da shugaban kasar wacan lokaci kamin ya iso masarautarmu, bayan tafiyarsa mahaifina ya shigo cikin masarauta ya saka aka kira ni, na zauna a gabansa kaina na kasa ya sanarmin cewar ya kyautar da ni aure a gurin dan Sarkin Khartoum, a wacan zamanin idan iyaye suka yanke shawara ba a musawa ko da a gurin bayi ne balle kuma yayan sarakuna, wacan lokacin yayan sarakuna basa aure sai yayan sarakuna yan'uwansu, na amsa masa babu musu, a lokacin ba zan iya amsa cewar ina son kyautar da mahaifina yayi min ko akasin haka ba, iyakar abun da zan iya shaida an aurar da ni ga mutanen da ba su san darajar dan'adan ba, mahaifina ya kulla alakar ne saboda ya karfafa zumuncinsu, kuma yayi bugun kirji cewar Balarabe ya auri yarsa Maryam ta yi farinjini, sai dai mahaifina ya manta cewar balaraben Asali baya son kowa sai balarabe dan'uwa, kadan ne suke son wani yaren, sai dai ko kadan basan son bakar fata, kuma basa son girmama ra'ayinsa, basa kallonsa da kima, balaraben mutum baya son bakar fata ko kadan, da fari sun nuna kamar za su janye, domin mijin da aka ba shi kyautata be shirya karin wani auren ba bayan wanda yake da shi da farko, ban san miya ja ra'ayinsa ba, sai kuma ya amince”
Ammy ta share hawayen da ya sauko mata.
“Daga lokacin da aka daura min aure, aka dauke ni akai kai a masarautar, sai na fara fuskantar kalubale, tun da na shiga masarautar ban saka mijina a idona ba sai da aka yi sati biyu, idan na fito cikin masarautar sai na fuskanci wulakanci, ba irin wulakanci na bawa da sarki ne, wulakanci irin na banbancin launin fata, wulakanci irin na wanda aka kyauta a gurin da ba a da bukatarsa, na fuskanci tsangwaba domin yarenmu da na su ba daya ba, kusan babu wanda ya san an auro a wajen masarautar domin ba a fita da ni, ba a nuna ni a matsayin surukar gidan, sai matar da na tarar wato uwargidana Maimunatu, surukarna suna wulakanta ni mijina da abokiyar zamana ma haka, ko da rana daya ban taba fadawa mahaifinta halin da nake ciki ba saboda bana son ya ji cewar ya zaba min abun da be dace ba”
Ta rufe ido hawaye na sauko mata.
“Shiyasa nake matukar tausayin Aysha, ni kadai na san irin tsangwamar da ta fuskanta a masarautar, domin na san yadda abun yake, gashi kuma Turhan ya watsa min kasa a ido ya tsaba alkawarin da ya daukar min”
Ta bude ido har lokacin hawaye ke saukowa daga idonta, ta mike tsaye ta nufi kofar falon ta bude ta shiga, kai tsaye ta nufi stairs ta shiga dakinta.
EMILY POV.
Ta kara minti talatin akan lokacin da Amal ta fada mata na shigowa office, domin ta shigo kamfanin karfe bakwai saura mintuna na safe, a tare suka nufi elevator ita da mutumen da suka shiga wacan karon, wannan karon ma a tare suka shiga, ta rasa dalilin kaddara na hadata da wannan mutumen, ko da yake a kamfanin yake aiki kamar ita, dole za su rika haduwa ko da bata so, kamar yadda za ta yi ta haduwa da mabanbanta mutane a gurin. A yau din bata cikin walwala da zumudi kamar jiya, saboda danta dake can kwance a asibiti, gashi kuma yarta Fatima na fushi da ita, thirdly kuma bata samu wadataccen bachi ba, ga gajiyar aikin jiya tattara a jikinkinta, sai ya zama mood dinta ya canja gaba daya, ta sama silent ba kuzari.
“Good Morning”
Ta gaishe shi saboda tana son ta yi masa tambayar da ba lallai ne idan ta yi ma Boss dinta Amal ta amsa mata ba. Aliyu ya kalleta kawai ya dauke ido ba tare da ya amsa mata ba, hakan kuma ya harzukata.
“Daman fa tambaya ce kawai zan yi, karka yi zaton ko ina son kullum alaka da kai ne ko wani abu makamanci haka, haduwar da mu ke kaddara ce ke hada mu, ba wai dan ina son haka ba, ni maza ba burge ni suke ba, so ka sauke girman kan please”
Ya juyo ya kalleta a nan din ma ba zai iya karyata kyaunta ba, amman ba zallar kyaun yake kallo ba yadda take bulbule shi da masifa a duk lokacin da kaddara ta hada su ne yake mamaki.
“Daman zan tambaye ka ne, ko bakon zuwa ma'ana new comer zai iya daukar hutu saboda wani uzuri na rashin lafiya”
Nan din ma be jin zai iya amsa mata, sai kallonta da yake kamin ya dauke kansa. Da yaren turanci take masa magana, sai dai ganin be amsa ta ba ya saka ta wani furuncin da Hausa.
“Wato dai ma'aikatar nan kowa dan iskan kansa ne, kowa jin kansa yake, na tambaya wata kila shi ma sabon dauka ne kamar ni, sai kallona yake babu amsa kamar kurma, idan na sake magana kace min aku”
Wannan karon be kalleta ba, be kuma bar murmushin zuciyarsa ya fito a fuskarsa ba har suka tsaya a 4 -floor. Ta saka kafa zata fice
“Tambaya kawai mutum yayi maka shiru kamar kurma”
Ta fada da Hausa.
“Aku”
Ya furta a daidai lokacin da Elevator ya zo rufewa, ya furta mata hakan ne saboda ta san yana jin yaren da ta yi magana da shi. Sai ta juyo da sauri ta kalli elevator da already ya rufe, zuciyarta na bugawa da karfi, sai a lokacin tunani ya zo mata, what if shi babban ta ne a gurin aikin? Wata kila yana a hawa na 5 ne ma ko kuma sako yake kaina, amman be yi kama da karamin mutum ba. Bata dauka yana jin hausa ba, a tunaninta Igbo ne ko yorba, shiyasa bata yi magana da duka yarukan ba sai hausa, bata yi tsammanin a kusa zata samu mai jin hausa ba kamar ita ba, ko da yake ita ma zama a arewa ne ya saka ta kware a hausar ba mamaki shi ma ya zauna a can din ne.
Idan ba haka ba Parthcourt da Zamfara ai akwai nisa sosai, a take ta tunatarta kanta abun da ta manta, kamfani ya kan hada mutane kala kala wasu ma daga wata kasar wasu kuma daga wasu yarukan.
Fargabar rasa aikinta ko janyowa kanta wata sabuwar matsalar ya hanata ta sukuni har ta gyara office din Boss dinta ta gama, duk kuwa da wani bangare na zuciyarta yana raya ba wani babba ne a kamfanin ba, domin bata taba ganin wani ya rako shi ba, haka kuma zuwan da yayi da safen nan ya fahimtar da ita haka, domin da babba ne a kamfanin ba zai shigo a irin wannan lokacin ba sai 10 ko 9am kamar yadda Amal take shigowa, wannan tunanin ya yaudari zuciyarta har ta samu sukuni.
ALIYU POV.
Kusan duk wanda ya san shi fari sani a kamfani ya ga shigowarsa a irin wannan lokacin zai yi mamakin haka domin be saba shigowa a irin wannan lokacin ba. Ya wuni da tunanin matar nan da sake gani a yau, yadda halshenta yake iya furta hausa da kyau haka ya nuna alamar ta taba zama arewa ko kuma daga arewar take ma, sai dai abun da ya daure masa kai siffarta gashin kanta ba sun sanar da duk wani mai kallonta cewar ita din baturiyace, haskenta yayi yawa blue eyes dinta da jan gashinta ya fahimtar da shi haka.
Sai dai ya kasa tantancewa shin ita din ce matar da abokinsa yake nema ko mai kama da ita? Idan har kama ce ta ina taya sunan zai zama daya Aisha? Ta ya idon da gashin zai zama hali da jikin ne kawai zai banbanta? Sau hudu yana daga waya zai kira Turhan sai kuma ya fasa domin ba shi da wata kwakkwaran hujjar da zai rike cewar matar da yake gani a kamfaninsu ita din ce matar da Turhan yake nema, idan tsabanin haka ne zai wahalar da abokinsa ne, saboda haka yana bukatar hujja, domin Turhan ya fada masa cewar ita wacan tana da jiki kuma bata da masifa gashi bata yi boko ba, ba kamar wannan ba. Ko dai yan biyu ne, ya tambayi kansa sai kuma ya rasa wa zai bashi amsar.
Misalin karfe daya ya shiga bandakin office din yayi alwala ya fito ya kashe Bluetooth din dake kunne yana fitar da kirar'ar Qu'ane ya shimfida carpet yayi Sallah, sannan ya mike tsaye ya fito daga office dinsa.
“Nick, if there are any newly recruited employees named Aysha, please bring their files to my office”
“Okay Sir”
Ya bada umarnin sannan ya fice ya sauka kasa gaba daya, Elevator na budewa yayi arba da mutane biyar masu jiran budewarta ciki har da kyakkyawar karamar yarinya mai goye da jakar makaranta, tana sanye da uniform pink short skirt and White shirt, an yi mata parking din bakin gashinta a baya, tana ta kallonsa da blue eyes dinta kamar yadda yake kallonta babu kyabta ido. Zanen halittar fuskar yarinyar ya saka shi manta mutanen dake mika masa gaisuwa kuma suke jiran fitowarsa domin su shiga Elevator.
[4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 8️⃣
“Hi”
Ya furtawa yarinyar yana faɗaɗa fuskarsa da murmushi, matsawa ta yi baya ta ta kauce daga mutanen da duke tsaye jiran fitowarsa, hakan ya bashi damar fitowa har ya amsa gaisuwar da ake mika masa, sannan ya kalli yarinyar data matse jikin ginin dake bayanta kamar zata shige ciki, gashi ta hade rai irin na yaron da yayi arba da bakuwar fuskar da be sani ba. Tsayawa yayi a gurin har sai da kowa ya shige cikin Elevator sannan matsa kusa da ita yana murmushi ya mika mata hannunsa.
“Hi”
Ta hade hannayenta ta kawar da fuska.
“Momy na tace na daina magana da wanda ban sani ba, za a iya sace ni”
Murmushin fuskarsa ne ya fadada ya gingina kai.
“Gaskiya ne, ni ma ta fada min haka ta fada miki shiyasa ba zaki amsa ni ba idan na miki magana, amman na san ki mahaifiyarki ta nuna min hotonki a wayarta tun da dadewa shiyasa yanzu ma ina ganinki na gane ki”
Ta juyo ta kalleshi.
“Da gaske”
Ya daga mata kai.
“Uhm-”
“To waye kai?”
“Ni...”
Ya nuna kansa yana tunanin me zai fada mata, sai ta ce.
“Are you her new boyfriend?”
Ya wara ido.
“Boyfriend? No... Karki ji haushi ki yi kishin Babanki”
“Ni ba ni da Baba ai, Momy na tace bata haife ni da Baba ba, tsaya ma ka ji sunana Fatima Aysha Emily, amman yayana yana da Baba shi sunanshi Londom Hamza, amman shi babansa ya mutu kamar yadda Momy ta fada, amman ni ba ni da Baba, amman ka ga kowa yana sa baba ko a makarantarmu kowa yana da baba ban da ni, shiyasa na matsu Momy na ta yi new boyfriend so that na samu Baba, saboda na tsani Vito bana son shi shi kuma wai yana son Momy ne, amman ni bana son shi....”
Sai da ta kai ayar zancen sannan ta numfasa, mamaki da burgewa ya saka Aliyu jan numfashi.
“Hmmmmm wannan yarinyar ya a je da ke Hi-five”
Ya mika mata hannu ta mika masa nata suka taba, shi kam abun nema ya samu daman bincikarta yake son yin, sai kuma yayi sa'ar ita din ku ace gurin magana, ya kama hannunta yana murmushi tunawa da yayi da matar dazun wanda tace idan ta sake masa magana ya kirata da aku and he did.
“Ciki zaki shiga?”
“Eh Momy na tace na zo na same ta a nan saboda yau nannynmu tana gurin London ba shi da lafiya yana asibiti shi sickle ne kuma Autisms, baya yarda da mutane sosai daga Vito sai Nanny Chidimma sai Momy sai ni”
Ya nufi elevator ya danna ta bude. Sai da suka shiga sannan ya sake tambayarta.
“Shi Victor shi ne Babanki? Ko saurayin Momy kika ce ko?”
Ta tofar da yawu.
“Allah ya kiyaye bana son shi, sunan shi Vito not Victor Vito sunan yan Italian ne da aka samo daga latin word “Vita” Vito yana nufin rayuwa, sunansa ke nan?”
“Amman miyasa kika tsane shi? Ba shi da kyau ne”
“Yana da kyau, amman baya yin dariya, and wata rana idan Momy ta bata masa rai sosai yana dukanta, i just hate him, kawai ina zama da shi ne dan dole, amman Momy tace da sabon aikin da ta samu yanzu zata siya gida zamu koma can Vito ba zai sake zuwa gurinta ba”
Aliyu ya daga girarsa sama ya sauke yana tan tabe baki kadan.
“Wow, okay”
“Ina son haka, and na san idan Momy ta bar gidan Vito zata samu Boyfriend sai ya zama Daddyna, ni ina son Daddy”
Aliyu ya rage tsayinsa ya kama fuskarta ya rike cike da tausayi, ko bata fada masa uwarta ba ya fahimci akan waye take magana, secondly fuskar abokinsa dake shimfide a yarinyar yake kallo.
“Amman kai kana da girlfriend?”
Yayi murmushi kawai ya mike tsaye ba tare da ya amsa mata ba. Ita ma bata sake cewa komai ba har suka sauka a 5floor.
“Momy na tace a 4 Floor zan sauka office na biyu hannu dama shi ne nata”
“Na sani, ina son na kai ki office dina ne mu gaisa”
Ya shiga office din yana rike da hannunta, ta bude ido tana ta kallon office din.
“Amman kai ya sunanka?”
“Aliyu”
“Okay Mr Aliyu are you Muslim or Christen?”
“Muslim amman Momy na Christen ce, but her name is the Aysha”
Ya bude fridge dinsa ya dauko mata lemu ya bata.
“Taya kika zama musulma mamarki ba musulma ba?”
Ta nufi kujera ta zauna ba tare da ta jira ya mata izini ba.
“Okay, Momy na tace babana musulmi ne shiyasa ta saka min suna Fatima kuma na tashi ta ga ina son musulunci shi ne take barina ina yi, ta koya min sallah, ta fada min ita ma ta taba yin musulunci, amman yanzu ta daina”
Ya zauna a kujerar dake facing din wanda take zaune.
“Kin fada min baki da baba? Taya kuma zaki ce babanki musulmi ne?”
“Ni ma haka Momy na ta fada min, shiyasa nake son ta samu new boyfriend ya zama daddy na, amman kai kana da mata?”
“huh-?”
Ya bude baki not knowing what to say. Ta yatsina fuska.
“Kana da ita?”
“Uhhhh No”
Ya amsa mata saboda ta saki jiki da shi ya samu abun da yake so.
“Okay Good”
Ta masa thumb up ta fara shan lemun da ya karba ya bude mata ya bata, ya ciro wayarsa ya dauketa hoto.
“Hoto kake daukata?”
Ya juyar da wayarsa ya kalli wayar ya manta flashlight din wayarsa a kunne yake.
“Kin min kyau ne shiyasa nake daukarki hoto, kina da kyau, zan so haihuwar kyakkyawar yarinya irinki, so ina son na dauko hotonki ne na aje ina kallo a wayana, saboda mamanki tana min rowarki ba zata tura min hotonki ba”
Ya fada mata haka ne saboda ya wanke kansa.
“Why? Ko zaka sace ni ne?”
“Nooooo ta fada min akwai hotunanki masu yawa a wayarta, nace ta tura min tace aa ba zata tura ba”
“Idan kana so zan tura maka”
“Taya?”
“Zan karbo wayar Momy na tura maka”
“Aa ai ba zata yarda ba, amman ina son ki yi a boye, zan rubuta miki number na sai ki saka a wayar Momynki ki duba whatsapp dinta ki tura min hotunan ta can idan kika tura sai ki goge karki bari ta sani, kin iya turawa ai ko?”
Ta daga mishi kai.
“Na iya, amman ban iya gogewa ba”
Ya bude whatsapp din wayarsa ya nuna mata yadda zata goge.
“Kin gane?”
“Yes”
Ya tashi ya bude karamar durowa ya dauko katinsa ya bata.
“Idan kika gama sai ki jefar da katin a inda ba za a gani ba”
“Okay”
Samun hotonta da hoton mahaifiyarta zai taimaka masa sosai gurin samawa abokinsa mafita cikin sauki.
Ya matsa kusa da ita ya rumgume ya sumbanci kanta, sai ta lafe a jikinsa ta yi shiruuuuu kamin ta dago ta kalleshi ta yi murmushi.
“Muje gurin Momy ki kar ta nemi ki bata ganki ba, amman wannan