Showing 18001 words to 21000 words out of 249044 words
yana duba shi akai akai, kin ga kamar irin yanzu, da ace akwai likitan dake duba shi ba sai kin yi wahalar zuwa ba, sai idan abun ya gagara, yana da ki samu likitan da zai duba shi koda yaushe, yadda kike daga hankalinki wata rana ba zaki iya kawoshi asibiti ba”
Ta daga masa kai, sai ya daga kafadarta alamar karfafa guiwa ya wuce, ita kanta zata so ace akwai likitan dake duba danta duk lokaci, sai dai tasan Vito ba zai yarda ba, domin baya yarda da kowa ya shiga gidanta balle kuma rayuwarta ko ta yaranta, ta yi ta kokarin yin haka yin haka ba sau daya ba amman be amince mata ba. Ta shiga dakin ta rufe kofar a hankali ta karasa kusa da shi tana kallon fuskarsa.
Rayuwarta take tunawa a wani dare makamancin wannan da rashin lafiya ta kamata, ita kan ta fishi wahala kwananta uku tana ciwon ciki kamin akaita asibitin, sai kuma aka rasa mai jinyarta domin bata da kowa sai gamon tsintsiya da ragga wato mutanen da aka raine ta a tare da su a gidan marayu.
Ta zauna a kujerar dake kusa da gadonta ta kama hannunsa ta rike, jininta ne wannan shi ne kadai zata iya shaidawa duniya cewar ita din daga gareta yake, kuma shi din nata ne, bayan wannan da kanwarsa bata da wani abun tunkaho, da ace ta rasa shi a yau da daren yau ya fi kowane dare muni a gareta. Hannu ta saka ta share hawayen idonta tana tunanin Fatima ta san zata ji tsoron zama ita kadai a gidan gashi bata fito da waya ba balle ta kira Chidimma tace ta shiga ta kwana tare da ita, haka kuma ba zata iya barin ďanta shi kadai a irin wannan lokacin da bata san karfe nawa ba ta tafi gida.
Bachi rabi da rabi ta yi saboda tunanin Fatima, da kuma danta dake tsare da shi, sanyin asuba na fara saukowa ta mike tsaye daga kan kujerar yana mika, kamin ta sirina ta sumbanci danta dake bachi ta shafa kansa zuwa fuskarsa, tana matukar tausayin rayuwarsa saboda yadda tasa kaddarar ta zo, shi din ba kamar sauran yara ba ne, gashi kuma ciwon sickle be barshi yayi walwala ba. Ta dago ta nufi kofar ta bude a hankali ta fice ta rufe, haka ta taka har gurin motarta babu talkamin domin bata zo da su ba, sai da ta yi ta dubawa sannan ta gane gurin da aka aje mata motar.
Ta tuka motar cikin natsuwa ta isa gida, sai dai ta yi horn ya kai goma kamin mai gadin ya taso ya bude mata, ta faka a gurin da ta dauki motar ta bude ta fito tana amsa tambayar jikin London da mai gadin yake domin ya ga yadda aka fita da shi.
“Ya ji sauki”
Ta amsa a gajiye sannan ta nufi cikin gidan ta bude ta shiga, sama ta haura da sauri ta shiga dakin Fatima, ba karamin dadi ta ji ba ganin Chidimma na rumgume da ita suna bachi, ta yi murmushi kadan sannan ta juya ta fice daga dakin ta shiga nata dakin, tufafin jikinta ta cire ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito daure da bathrobe ta daure kanta da tawul.
Kitchen ta nufa tana hamma ta kunna gas ta shirya abun karyawa, sannan ta fito a daidai lokacin da Chidimma ta sauko kasa.
“Good Morning Maa”
“Morning Chi”
“I'm sorry na kwana a nan ne saboda Fatima ta same ni tana ta kuka wai ba zata iya kwana ita kadai ba”
“Kin kyauta na jidadin haka, ga abun karyawa nan na shirya ki shirya yanzu ki tafi asibiti gurin London, saboda zan tafi gurin aiki yanzu, ki fadawa direban Fatima idan ya daukota daga school ya kirani zan fada masa inda nake aiki sai ya kaita saboda kar dawainiyar ta miki yawa, idan na tashi zan biyo asibitin idan sun ba mu sallama sai mu dawo tare”
“Okay Maa”
Emily ta ratsa gafenta ta haura sama, cikin kankanen lokaci ta shirya ta fito dakinta ta leka dakin Fatima sai ta same ta a bandaki tana wanke bakinta
“Good Morning My Love”
Fatima ta juyar da fuska, cikin rashin jindadin abun da ta yi Emily tace
“Idan kin tashi daga School ki fadawa direbanki ya kira ni, zai kawo ki gurin da nake aiki idan ban tashi ba a lokacin, saboda Chidimma zata tafi asibiti gurin London, ni kuma zan tafi aiki”
Tana fadar hakan ta ja mata kofar bandakin ta rufe ta fito daga dakin ta sauko kasa tana jin zuciyarta na mata babu dadi, ta karasa dinning wayarta na ringing a karo na uku, tea ta zuba ta daga cup din ta sha rabi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta fice.
A road din unguwarsu ta amsa kiran Vito dake ta shigowa wayarta, ta sani ba dan baya garin ba da yanzu ya karaso gidanta, domin a ka'ida idan yayi mata kira uku bata daga ba to ba zai yi na hudu ba, zata ganshi gidan ne.
“Hello”
“Are you okay? Lafiya kike?”
Ta ji kamar ta ce masa aa ina cikin damuwa kuma ta fada masa London yana asibiti amman bata son daga masa hankali, haka kuma bata son yana shiga al'amurranta kokarin jenye shi take daga jikinta.
“Yeah I'm fine”
Dakikun da ta dauka bata ba shi amsa ba ya saka shi fahimtar tana cikin damuwa, daman kuma ya karanci muryarta.
“Don't lie to me, me ya faru bayan bana nan?”
“Fatima ce kawai bata jin magana”
Yayi shiru ba tare da ya ce komai ba, sannan ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya ta tari okada ta hau ta, be sauketa ko'ina ba sai gurin aikinta.
ALIYU POV.
8:36pm...
Gaba daya yanayinsa ya canja zuciyarta ta sosu kuma ransa ya bace sosai saboda abun da yayi arba da shi a wayar matarsa. Sai dai a cikin sharudansa akwai kokarin kwantar da hankali da kuma yin uzuri a duk lokacin da wani abun bacin rai ko tashin hankali ya same shi, ya sani ya dara matarsa Aisha Ilmi da goge, kamar yadda ya fita shekaru haka ya fita hankali da zurfin tunani domin hankalin namiji ba daya yake da na mace ba. Ba da'asar bace bincikar wayar matarsa domin ya yarda da ita 100% ko da yake ita bata yi masa irin wannan yarda ba saboda kishi, a duk lokacin da ta samu dama sai ta bincike wayarsa, sai dai tana daga masa kafa domin bata taba daukar wayarsa ta bincika ta same shi yana chatting da mata ba, ko wani abu makamancin wannan, abu ne da ya daukarwa kanta nisanta wayarsa da duk wani abu da zai dauki hankalinsa daga matarsa a lokacin da tafi bukatarsa a kusa da ita. Ya haddace password din wayarta, ita ma ta haddace masa saboda yarda da suka yi da junansu.
Ya aje wayar yana kokarin saita kansa, domin be kamata ya nuna mata bacin ransa a yanzu ba, ko ba komai tana dauke da juna biyu zata iya damuwa, haka kuma ba zama lallai abun da yayi arba da shi a wayarta ya zama wata illa ko laifi a idonta ba. Ta kalleshi bayan ta sallame sallar Isha'i tana murmushi.
“Ki yi min addu'a”
“Ai kullum ina maka addu'a amman cewa nake Allah yasa daga ni babu kari”
Ya daga kafadunsa yana murmushi mai sauti.
“Daman ai daga ke babu kari, wai baki yarda da alkawarin da na yi miki ba?”
“Na yarda mana, amman matan yanzu fa shaidanu ne, kai dai Allah dai ya tsare kawai kuma ya kawar da idonka”
“Ameen”
Ya girgiza kai ya kai hannu ya dauki dabinon ajwa ya kai bakinsa, sai da ta kammala addu'ar sannan ta dawo kusa da shi ta zauna ta cire hijab din. Janta yayi a hankali ya kwantar jikinsa.
“My one and only ina bukatar tuna miki wani abu, kuma ina son ki dauke shi serious”
Ta dago kadan ta kalleshi.
“Minene?”
“Sirrinmu sirrinmu ne, be kamata wani ya ji ba, musamman na auratayya, yadda muke mu'amala da duk wani abu da ya shafi gonarmu be kamata wani ya sani ba”
Gabanta ya fadi, domin ta fahimci kalamansa sai dai kunya irin na wanda aka tsinkawa zane a kasuwa ba zai barta ta nuna masa ta fahimci nufinsa ba.
“Ni bana gane yarenka ka fito fili ka fada min abun da kake nufi”
Ya tashi zaune da kyau ya fuskanceta.
“I'm sorry na shi whatsapp dinki na san be kamata na shiga ba wata kila akwai sirrinki da yan'uwanki da be kamata na ji ba ko na sani, akan hakan ina baki hakuri, wani sako ya shigo ta sama kuma na bude na gani, wata kila saboda na samu damar tunatarki me Allah ya nuna min sakon”
“Kana ta jan sakon da tsaye please minene?”
Ya aje numfashi a hankali.
“Na ga wani chat da kike da kawarki Huda, ban san iya aminci ko yardar dake tsakaninku ba, amman Aisha ban jidadin yadda kike fada mata sirrin shimfidarmu ba, ko a musulunci babu kyau, kuma maganganun ne da basu dace ba”
Ta dan wara ido tana murmushin da ya kusa zame mata dariya.
“Haba dai, wannan fa duk zancenmu ne na mata, kuma ita da ba ganinka take ba ma”
“Ko dai minene tun da kika ga musulunci ya hana be kamata ki aikata ba, akwai illa ciki? Fadin amfanin me zai mata? Shikenan kin bude mata cikinki ta san sirrinki ta san sirrin mijinki, yadda muke mu'alama da komai ta sani, ban jidadi ba kuma in miki daukar mace mai hankali ne mai sani ya kamata, ban yi tsammanin zan ga haka ba, kuma ban jidadi ba”
Ya karasa da dan fada domin ya fahimci kamar bata dauki abun a wani abun ba, ganin haka ya saka jikinta yayi sanyi, shi kuma be sake ce mata komai ba ya tashi ya fice daga dakin. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dauki wayar felling guilty ta bude chat din tana dubawa tare da mayar da amsar tambayar da Huda take mata, kamin da kara da.
“Ke yau ya duba wayata ya ga chat dinmu”
Sannan ta kashe data ta gyara kwanciyarta da kyau, domin abu ne da ta sani idan suka samu tsabani shi yake bata hakuri, shi yake nemanta. Ba dabi'arsa bace bawa miji hakuri idan ta yi laifi, haka kuma ba mace ce mai saurin karbar laifinta ba, idan ma har ta aminta tana da laifin kenan.
And to her hira da kawa ko a group chat da mata yan'uwa Normal ne domun suna suna fadar yadda suke tasu mu'alamar kuma dukansu mata ne babu maza, bugu da kari tana ganin aminci da jindadi ke saka irin wannan chat din.
Bayan duk wannan ma why zai dauki wayarta ya shiga chat dinta da kawarta ko kawayenta har ya ga abun da suke tattaunawa, a ganinta a nan kam shi yake da laifi, kuma dai chat irin wannan tsakanin mata ai ba wani abu ba ne, dan haka bata shirya ba shi hakuri a yanzu ba. Yadda ta ayyana haka ne ya faru domin bayan ta yi bachi ya dawo dakin ta kwanta a kusa da ita, daman can no matter how suka samu tsabani baya taba raba gado da matarsa balle kuma har ta kai ga ya raba daki.
Yayi bachi not like usual yadda ya saba, domin yana son ya nuna mata illar abun da ta yi, dan haka be shirya abun karyawa ko ya jira ta shirya masa ba yayi wanka ya yi shirin office ya fice daga gidan at early morning.
[4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 7️⃣
TURHAN POV.
“Shikenan zan jiraka a waje”
Ya aje wayar ya nufi gurin da suitcase dinsa yake ya bude ya ciro wani karamin roll on ya murza a wuyan hannunsa sannan ya aje a mirror dake dakin ya sake nufar wayarsa ya dauka ya saka aljihu ya dauki key din dakin ya fice ya rufe dakin.
Stairs ya bi har ya sauko daga hawa na uku zuwa na daya, kamin ya karaso kasa ransa ya gama baci domin Turhan ba mutum ne mai son motsa jiki ba sai dole, ko kadan baya son aikin wahala balle kuma wahalar ita kanta da baya hada hanya da ita.
Harabar hotel din ya fito yana kallon yadda tsari da kawar babbar hotel din take daga kasa, domin sun sauka sa dare ne a jiya, gajiya bata bashi dama kamar yadda hutu ya bashi a yau da safe ya kalli ko'ina ba. Kusa da wata flower ya tsaya yana kallon ko'ina da kyau, kyam idonsa suka sauka akan wata hallita mai ban tsoro, mutum ne irinsa namiji mai kirar mazaje da jarumtaka, Turhan ya dauke idonsa daga kallon mutumen da shi ma kallonsa yake babu kyabta ido. Ganin sarkar Cross a wuyan mutumen da murdaddiya fuska irin na wanda baya sha'awar dariya, ya saka shi fahimtar addininshi da nasa akwai banbanci, tattoo jikinsa ma ya sanar da hakan.
Feeling awkward ya saka shi ciro wayar dake aljihunsa ya fara dannawa, ya dauki lokaci a haka kamin ya sake dagowa ya kalli harabar, a karo na biyu ya sake kallon gurin da mutumen dazun yake tsaye yana kallonsa and wannan karon ma yana tsaye and still kallonsa yake har yanzu, irin kallon nan mai daure kai ga wanda ake yi ma shi, da mace ce take kallonsa sai yace ko tana sonsa ne, amman namiji kamar wannan da zai yi wahala su hada hanya da imani abun tambaya ne a kallon da yake masa, zuciyarsa ta raya masa wata kila yayi masa kama da wani ne da ya sani ne, idan ba haka ba kallon da yake masa yayi yawa, and babu wani dalili da zai saka yayi ta kallonsa haka.
Kallo ne mai rikitarwa da mamaki ga wanda ake yi ma shi, hakan ya saka Turhan jin babu dadi kuma ya dan tsorata, ganin ba garinsu ba ne, haka kuma ba gurin da ya saba mutanen ba ne, ko be taba zuwa ba, ya kan ji ana fadar bad side na Lagos, dan haka dole ne yayi taka tsantsan. Takawa ya fara yi cike da izza da takamar da suke zame masa jini ya isa gate din hotel din hannayensa rumgume a bayansa sai kamshi yake zubawa tafiyarma ita kanta ta karbe shi kana ganinsa kasan babban mutum ne kuma dan babban gida.
Sai da ya fice daga katon gate din dake bude sannan ya juyo kadan ya kalli mutumen dazun domin jikinsa ya ba shi har lokacin yana kallonsa, ga mamakinsa sai ya ga mutunen yana kallonsa har yanxu, kusan kallon yanxu yafi muni fiye da na dazun, domin a yanzu yana iya hango tsana da harzuka a idanuwan mutumen da be san waye ba, be kuma san dalilin haka ba.
Wannan karon Turhan be tsaya shawarta zuciyarsa ya daga wayarsa ya kira Faruk.
“Wai baka karaso ba har yanzu? I'm not safe here fa, ina jin tsoron irin mutanen da suke a nan gaskiya”
“Gani isowa ranka ya dade, na kusa karasowa, ka kwanta da hankalinka babu komai In Shaa Allahu, Hotel din da ka sauka hotel ce mai tsaro sosai, ba wani matsala In Shaa Allahu, da akwai matsala ai oga Aliyu ba zai bari na sauke ka a wannan hotel din ba”
“Ina fatan haka”
Ya fada sannan ya sauke wayar tare da jan dogon numfashi, wannan karon be yarda ya sake juyawa ya kalli bayansa ba, balle ya san da wanzuwar mutunen dazun ko akasin haka, sai ya cigaba da tafiyarsa. Kamin ya sake daga wayar ya kira farar uwar data kawo shi duniya. Ringing daya biyu ta daga, daman bata ignoring call dinsa idan tana kusa da waya, tun a lokacin da suke shiri da juna da kuma yanzu da ta sauya mu'amala da shi, banbancin wacan kiran da kuma yanzu, idan ya kira bata kusa bata mayar masa da kiran, kamar yadda ba zata amsa kira da saukin kiransa ba, ba kamar can farko ba da take daukin kiransa da far'a da na jindadi kuma yake kiransa idan ta samu miss calls dinsa, a yanzu sai dai ta amsa masa duk abun da zai fada ne ba a cikin dadin rai ba.
“Ammy ina kwana?”
“Lafiya Kalau”
“Ammy na sauka Lagos jiya da dare sosai, na yi tsammanin ganin kiranki ki tambaya ko na iso lafiya”
“Gashi ai mun yi magana yanzu, kuma da ba lafiya kake ba dole za a kira a sanar min”
Wani abu na rashin jindadi ya ji ya ratsa zuciyarsa, jiki a sanyaye ya furta.
“Haka ne, Ammy na zo nan ne neman Aisha kuma duk saboda ke ne, ba dan ke ba ba zan yi haka ba, ina fatan dacewa ki taya ni da”
Kalmar duk saboda ke ne, ya tsayawa Ammy a rai lallai ne ta sani danta yana son farincikinta da albarkarta haka kuma yana nuna cewar har a yanzu bana son zabin nata kawai dai zai nemi Aisha ne saboda gyara laifina ba dan tsantsar nadama da kaunarta ba.
“Fatan nasara Turhan Mohamed Abdo”
Tana fadar hakan ya aje wayar. Ta lumshe ido ta hade bakinta guri daya ta gumɗe tana maida numfashi a hankali. Jawahir ta rufe magazine din dake hannunta tana kallon Ammy cikin yanayi na damuwa.
“Ammy kina daukar abun nan da zafi ne sosai, ni da Maama dukanmu yayane a gurinki, be kamata ki yanke shawara ko ki yi wani hukunci mu saka baki ba, amman bahaushe yace mai shawara aikinsa baya baci, sai dai ba shi da sirri, kuma mai shawara ba ya nadama, amman na san ranki ya bace sosai akan Yaya Turhan amman ya kamata ki yi hakuri...”
Bata karasa ba Ammy ta bude idonta ta kalleta, tsoron furuci ko fadan da zai fito a bakin Ammy ya saka ta yanke maganar da bata karasa ba. Ammy ya gyara zamanta da kyau tana kallon Jawahir.
“Jawahir mahaifinki ya taba baki labarin cewar bayan haihuwar Turhan ban sake haihuwar kowa ba?”
It take her 5 seconds to answer.
“Ammy abu ne da kowa ya sani a familynmu bayan Turhan baki sake haihuwa ba”
“Amman ya