Showing 222001 words to 225000 words out of 249044 words
shigo da kanta ta kama Emily ta fita da ita bayan Daddy ya fada mata abun da ya faru.
Daddy ya sanar duk wanda ya kamata ya sani cikin kankanen lokaci, Dr A-B ya tafi kai tsaye yayi magana da Madam Baraka ya fada mata abun da ya faru, sai ta daga waya ta kira Emily ta sake tambayarta da gaske Aliyu take so Emily ta amsa mata da eh.
Kamin a daura auren sai da Daddy ya jira Aliyu ya tambaye shi ko yana son Emily.
"Eh ina sonta Daddy?"
Ya amsa kai tsaye babu boye boye babu kwankwanto, gabansa sai faduwa yake ba kamar ya san wainar da ake toyawa.
"Tohm za a a daura aurenku, daga baya abubuwa za su biyo baya"
"Na gode Daddy Allah ya ba ni ikon sauke nauyin da za a dora min"
Daddy ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba. Sannan ya sanar da Ummi yadda suka yi, Ummi ta shigo ta ta sanar da Emily halin da ake ciki yan'uwan Daddy da nata duk sun hallara gidan.
"Anjima idan an fito sallah La'asar za a daura aurenku da wanda kike so Aisha"
Emily ta kalli Ummi tana kuka.
"Allah kasa ya rike ni amana..."
Ummi ta kama hannayen Emily tana hawaye.
"Wallahi ko ba ni da rai Aliyu ya ci amanarki, ban yafe masa ba..."
Emily ta kwantar da kanta jikin Ummi, Ummi ta rungumeta tana amsa sallamar Mama Baraka.
[8/21, 10:14 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 7️⃣0️⃣
🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟
🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘
Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji!
Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida.
✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji?
• ✅ An yi ta da tsafta da inganci
• ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau
• ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa
• ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida
• ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman
📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka!
🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed).
💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau!
📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku.
👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa!
_________
Karfe 4:30pm aka daura auren Aliyu da Aisha, bayan sauke sallah farilla ta La'asar. Daddy da yan'uwansa suna gurin, yan'uwan Ummi ma wasu daga ciki suna gurin.
Dr A-B ne ya bada auren Daddy da kansa ya karbawa dansa auren Emily, masu shaidu suka shaida aka yi addu'a sannan masu tafiya suka tafi, Daddy da Dr A-B suka nufo cikin gidan da ragowar goro da dabino. Daddy ya nufi bangarensa Dr A-B kuma ya shiga falon Ummi ya tambaya ina Aliyu yake.
"Baya gidan, amman yanzu zan kira shi ya zo"
"Emily fa?"
"Tana sama, Nafeesa tashi ki kai shi"
Ummi ta umarce ta, Nafeesa ta mike tsaye ta wuce gaba Dr A-B na bayanta har suka shiga cikin dakin da Emily take zaune tare da Mama Baraka. Nafeesa ta juya ta fice, Dr A-B ya zauna kusa da Emily sai ta dube shi idonta a kumbure ta yi kuka sosai har ta gode Allah.
"An daura aurenki da wanda kike so yau, ina miki addu'ar Allah ya ba ku zaman lafiya, kuma ya saka mutuwa ce za ta raba"
Ta kara matsawa kusa da shi ta rumgume shi tana jin sanyi.
"Na gode, wannan karo na farko da jinina ya bada aurena..."
Ta furta murya na rawa tana kuka, ita kadai ta san me take ji, tana son Aliyu kuma tana tsaron abun da gaba zata haifar, gashi ta watsa kasa a idon manyan mutane babu wanda ya fahimce ta, shi kansa Dr A-B ganin take yayi mata abun da take so ne kawai ba dan ya gamsu da zabinta ba. Ta dago kanta amman ta kasa kallon kowa.
"Allah ya ba ku zama lafiya"
Cewar Mama Baraka tana share hawayenta. Sun kusa rabin awa a dakin har aka fara kiran Dr A-B saboda Alhaji Bulama zai bar gari kuma tare za su tafi. Ya mike tsaye kenan sai ga Aliyu ya turo kofar dakin ya shigo da sallama duk suka amsa masa ban da Emily da kanta yake kasa, tana ta lissafin rayuwa. Idan Aliyu ya juya mata baya shi kan ita kam ta gama rayuwa kuma makiya za su mata dariya. Dr A-B ya kama hannun Emily ya mikar da ita tsaye ya kama hannunta ya kama hannun Aliyu ya saka hannunta cikin na Aliyu.
"Ga amana an baka, ta wahala ka sani, muna fatan daga kanka ta dace, a gaban iyayenmu ta zabe ka ta bar wanda shi ya so ya aureta a yau, dan Allah karka bata kunya. Sannan zan tunatar maka a yanzu Emily tana da uwa, dan'uwa da kuma uban da zata sani nan gaba kadan, karka kuskura ka ce zaka taba ta. Ta fada kai take so kuma na tsaya har yanzu ne saboda na tabbatar da cikar burinta, na sauke nawa nauyin, ni zan tafi ina muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya na bar ku lafiya"
Ya dauke hannunsa daga kan na su ya nufi kofa ya fice daga dakin, Mama Baraka ta mike tsaye ta bi bayansa. Aliyu ya kama hannaye Emily duka biyu ya rike yana kallon yadda take hawaye.
"Na san nisar tafiyar da kika yi, a hanya kin taka kaya, kin tsallake rame, kin yi dingishi kin karaya, na san zafin wutar data kona ki, na san buri da mafarkinki, ka karanci zuciyarki na san kudurinki, kin yi rayuwar kadaici. A yau ni da ke mun zama iyali, zan zame miki mijin da baki taba tsammanin samu ba, zan cika duniyarki da farinciki har sai kin manta da damuwarki, kuka ya kare hawaye, ba zaki sake zubar da hawaye akan ɗa namiji ba, fargaba ba zata sake kusantarki ba, kin zama jinina, farincikina, kaunarki ce rayuwarta, ina mai tabbatar miki baki yi kuskuren zabe ba"
Ya sake hannunta ya matsa baya kadan ya zube kasan guiwoyinsa ya hade hayyansa.
"Na gode da kika yarda da cewar zan iya! Na gode da kika ba ni wannan damar, na gode da kika yarda a dora min wannan nauyin na gode da kika yarda na zama silar warakar duk wani ciwo naki, na gode da kika so ni, na gode da kika aminta da ni, na gode da kika aure ni, na gode Saruniyar mata, mace mai hakuri da kyakkyawar zuciya, na gode Ayusher na gode... Na gode... Na gode na gode..."
Ta kasa komai wasu hawaye na dabam suna sauko mata, sai ta lumshe ido tana maida numfashi. Aliyu ya mike tsaye ya matsa daf da ita har yana jin fitar numfashinta.
"Bude idonki ki kalli mijinki, mijin da be san komai sai ƙaunarki, mijin da samunki ya zama babbar kyauta da rahama a gareshi"
Ta bude idon ta kalleshi ido cikin ido daf da daf gab da gab das da das...
"Ayusher ina ƙaunarki, ke tawa ce ni ne ABOKIN RAYUWARKI"
Ya rada mata cikin wata murya da be san yana da ita ba, furucin yana fitowa ne har can kasan kasan kogon zuciyarsa. Ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta. Sannan ya ware hannayenta.
"Ina tsarin Allah daga shedan la'ananen, duk wani abun kin, ko na cutarwa da zai shiga tsakanina dake, ina neman tsari Allah daga duk wani abun da zai saka na bata miki rai, kuma ina rokon duk wani alheri da zai kara mana zaman lafiya da kaunarnan junanmu, ina neman rahamar Allah a duk inda za mu saka gaba, ina neman rahama daga Ubangijin da shi ya hada mu, ya kawo mu a nan kuma ya nuna mana wannan ranar mai muhimmanci a rayuwarmu, Allah na gode da wannan kyauta da ka yi mini, da sunan Allah mai rahama mai jinkai"
Ya rumgumeta halal hug ya saka a kirjinsa, wani irin rumguma yayi mata sosai kamar za a kwace masa ita, ya yi squeezing dinta har sai da abayar dake jikinta ta dage, yayi sama da ita kafafuwanta suka dage. Emily ta yi shiru..... Hawayen suka yanke mata, numfashinta na fita a hankali yana shiga da kamshin turaren jikin mijinta, ba a taba rumgumarta ta ji damuwarta da fargaba sun gushe mata ba sai a yau.
Babu wanda ya taba rumgumarta ta ji hankalinta ya kwanta ya samu sukuni ba irin Aliyu.
Yanzu ta san me ta rasa, sai a yanzu ta san what truly halal hug means, ka so a so ka so na hakika dabam yake, auren wanda yake kaunarka kaunar ta gaskiya ta hakika a dabam take, son wanda yake sonka so na hakika dabam yake, lallai akwai wata irin rahama da farinciki, jindadi da cikar buri a auren soyayya. Ranar yau kadai ya nuna mata tana da muhimmanci, wunin yau kadai ya shafe duk wani fargaba da take, ta share duk wata damuwa da ta fuskanta.
Lallai macen da miji yake so Sarauniya ce, a yau Aliyu ya furta mata kalaman da babu wanda ya taba yi mata su a ranar aurenta, shi da kanshi yake gode mata, a yau ta shaida soyayyar gaskiya marar algussu. Aliyu be kalleta a matsayin mace da ta taba aure biyu ba, be kalleta a matsayin ta haihuwa biyu ba, ya kalleta a matsayin macen da yake so, lallai mai son be ganin ramarka, a yau ta dandanin miye auren so da masoyin gaskiya.
"Meyasa ban hadu da kai ba tuntuni?"
Ta tambaya tana murza kanta a kirjinsa kamar zata tsaga kirjinsa ta shige cikin zuciyarsa. Sai ya bata amsa cikin rada shi ma idonsa a lumshe cike da kwalla, auren soyayya suka yi da Kameela amman ko ita bata nuna masa kaunar haka a ranar aurensu ba kamar Emily.
"Ita ce tambayar da na dade ina yi ma kaddara, miyasa bata hada ni da ke, tun farkon da ta bude miki shafi"
"Aliyu ina ƙaunarka"
Ya bude ido ya sauketa ya rika fuskarta yana kallon cikin kwayar idonta.
"Duk wata kauna ta furuci ko ta aiki, ko wanda take zaune a zukanta masoya, Ayusher na fi kauna, kaunarki, na fi numfashinki son kasancewa da ke, ni da ke ABOKAN RAYUWA ne, sai da mutuwa"
Ta yi sauke wani sanyayen numfashi ya lumshe ido tana murmushi.
“Madalla da kasancewarka cikin rayuwata, ka zamo min tauraro mai haske. Madallah da ABOKIN RAYUWA irinka"
Ya kai goshinsa ya hade da nata, hancinsa a saman nata, ya saka yatsunsa na dama cikin nata, na hagu ma haka suka tsarkafe yan yatsunsu cikin juna.
"Abokiyar tafiyata, har tsawon rayuwa, Madalla da ABOKIYAR RAYUWA irinki"
Sun dade a haka sannan ya sake ta ya matsa baya. Ta kalleshi tana murmushi a yau ta san yadda rumgumar masoyi take mantar da damuwa, ya sameta tana kuka ya maye mata gurbin hakan da murmushi.
"Idan akwai abun da kike son aikatawa, ni halalinki ne just do it"
Ta taka one step forward kamar ya san manufarta sai ya maida hannayensa baya ya duko da fuskansa ta sumbanci gefen fuskansa da sauri, ta juya baya tana jin kunya. Murmushin dake fuskarsa ya fadada har ya bayyana hakoransa. Ya nufi kofar fita har ya kusa isa sai kuma ya yanke tafiyar ya juyo ya dawo gurin masoyiyyarsa ya rumgumeta ta baya, sai kuma ya juyo da ita, da sauri ta saka hannayensa ta rufe fuskarta. Hannayen dake fuskarta ya sumbanta ya goga fuskarsa yana dariya sannan ya saketa ya fice dakin ya rufe mata kofa yana jin kamar kar ya tafi ya barta.
TURHAN POV.
A lokacin da ya fito daga falon na Daddy waje ya tsaya jikin motar da suka zo, ya ji duniyar kamar tana juya masa, ko da wasa be yi tsammanin Emily zata juya masa baya har haba ba, kuma a gaban iyayensa. Dadin dadawa kuma ta furta sunan wanda take kaunar a gabansa cikin kunnensa.
Miya yayi ma Aliyu? Ita ce tambayar data fara zuwa masa a rai. Miyasa ya dauki bata masa ta wannan hanyar? Wace irin kiyayya Emily take masa har haka? Be samu amsoshin tambayayinsa ba Sarkin ya fito, kamin ya shiga motarsa Alhaji Bulama ya fito tare da Mahaifin Kameela, shi dai ya san ya shiga mota, yadda aka yi suka kama hanya har suka isa gidansu Ammy shi ne abun da be san yadda aka yi ba.
Ya zauna cikin falon yana sauraren yadda Alhaji Bulama yake labarta mata abubuwan da suka faru, yana jin mahaifinsa yana magana da ita amman be fahimce me suke magana kai ba, a yau ne karo na farko da yaren larabci ya subuce masa a kai.
"Aliyu... Aliyu... Aliyu..."
Furucin Emily nata dawo masa, be san yaushe aka mahaifinsa ya fita ya dai ji Alhaji Bulama ya dafa shi yana fadar maganar da be gane ba, yana zaune a falon kowa ya fice be san an yi ba sai da Ammy ta girgiza shi.
"Turhan nan?"
"Ammy me na yi ma Aliyu? Ina ta kokarin tariyo rayuwarmu ta baya zaman da muka yi, me na masa? Ashe ko ba ni da rai bancanci yayi min hallaci ba?"
Ammy dake tsaye ta zauna idonta cike da kwalla.
"Ka yi hakuri Turhan, ba a taba cin amana aka yi nasara ba, muna nan da kai hakki zai bayyana"
"Miyasa ita ma ba zata fahimce ni ba? Ko. Kalaman ne nawa ba su kai ba? Wallahi ina sonta ina kaunarta Ammy, kuma ba zan sake cutar da ita ba, Wallahi na yi alkawari ba zata sake zubar da hawaye akaina ba"
Hawaye ya sauko ma Ammy, ko wace uwa bata son ganin danta cikin damuwa balle kuma Ammy da Turhan kadai take da shi, bata tana ganin tsananin damuwa a tsare da shi data gusar masa da hankali ba irin yau.
"Tashi ka tafi ka yi sallah"
Be haura sama ba sai ya fice falon a masallacin yayi alwala yayi sallah, suna fitowa masallacin mahaifinsa ya kira shi akan ya shirya, jirginsu zai tashi karfe 5pm, daga shi sai DR A-B ake jira saboda Dr A-B yace ba zai bar garin ba sai an daura auren Emily da Aliyu kuma karfe 4:30pm za a daura. A nan ya ji wani labari da yafi furta sunan Aliyu azaba a zuciyarsa. Daker ya iya kawo kansa falon Ammy. Yana shigowa ya nufi agogon dakin ya tsaya yana kallo yadda dakika take juyawa ta zama minti. Jikinsa yayi ma kafafuwansa nauyi yana ta lilo jiri na dibansa kamar zai fadi.
Yana ta kallon agogon da second din ke dis da bugawar zuciyarsa yana jin wani dubu na haye masa kai. Har agogon ya nuna karfe 4:30pm. Turhan ya rufe ido, Ammy dake tsaye bayansa tana kallonsa ta karaso ta rike ɗanta tana jansa baya a hankali har ya zauna kan kujerar dinning.
"Ammy a yau na san rashi, na san miye kiyayya, na kuma san miye soyayya, da na sani ƙeya, tsanar da Aisha take min ta kai har ta auri abokina ta bar ni? Shin ita bata tafiya ne? Ammy ina son yarinyar nan miyasa kika cilasta na sake ta? Ammy ma rasa Aisha, uwar ƴata na rasa ta, cikon farincikina na rasa shi a yau....!"
Hawaye ne masu zafi suke sauko masa, ko Ammy sai da tsoro da tausayin ɗanta suka kamata, domin bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na gasawa da rudani irin wannan ba.
" Dady?"
Ya ji muryar yarsa da sai a yanzu ta filo daga dakinta ta sauko kasa duk abun da ake bata sani ba. Turhan ya saka hannayensa biyu ya dafe kansa baya son yarsa ta ga hawayensa. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi.
"I miss you... Dady ka dawo? Ina Momy kace tare za ku zo ba?"
"Momy ki ta zabi Aliyu Fatima, ta barki ke da Dady, Momy ki ta auri Aliyu bata auri Dady ki ba, tace Aliyu take so ba Dady ki ba"
Ammy ta fada mata tana hawayen tausayin danta gaba daya ta rikice. Cikin tsoro Fatima ta bude hannayen Turhan babu hawaye a fuskarsa amman suna kwance a cikin idonsa, sai kawai ta fashe da kuka sosai ta rumgume. Ya dauke ta ta dora saman jikinsa ya hade duk wani abu da yake ji ya fara rarrashinta. Wayarsa ta yi kara alamar shigowa sako, ya ciro wayar ya duba Dr A-B ne ya aiko masa da sako cewar za su tafi shi ya tsaya sai next week, ya aje wayar ya kalli mahaifiyarsa sai ya sakar mata murmushin karfin hali.
[8/25, 8:41 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 7️⃣1️⃣
KAMEELA POV.
Sosai ta natsu tana sauraren labarin da Hajiya take bata kamar yadda Alhajin ya fada mata yadda abubuwan suka faru.
"Wai kawai sai ta bude baki tace Aliyu... Na ce daman dai hadin baki aka yi da uwarko?"
Kameela ta kai tsaye.
"Hajiya dan Allah karku bari a yi auren nan, Wallahi ina son mijina, kuma na san yana so na, kawai makircin yarinyar nan da uwarta"
"Zancen banza, aure ai tuni aka daura, babanku yace mai gidansa da dansa ba su bar garin nan ba sai da aka daura auren, wai da la'asar sai kace auren kauye"
Anty Shafa ta karba mata.
"Auren kauye ai yafi na wannan arniyar daraja, kuma shegiya ce shiyasa suka daura auren kar ya subuce, dadin dadawa kuma Mama Baraka ai zata iya yin komai saboda ace yarta ta auri Aliyu kin ga ai ta yi gasa da ke"
Kameela ta dora hannu a kai.
"Na shiga uku, Innalillahi... Hajiya ina son mijina ina son Aliyu"
Hajiya ta daka mata tsawa.
"Ke dalla gafara can mahaukaciya, Aliyu autan maza ne halam? Tun da kika aure shi wani farinciki kika samu? Kuma ke da kike ikirarin ba zaki