Showing 117001 words to 120000 words out of 249044 words
yayi murmushi ya shafa kanta, sai ya ji duk ta burge shi.
"Mun zama mu uku ko?"
"Yes, zaka zama Babana? Ni kadai ce ba ni da Baba a duniyar nan kowa yana da Baba amman kace zaka maida sunana Fatima Aliyu amman baka yi ba, har yanxu ana kirana Fatima Aisha Emily...."
"Ke ma kina da mahaifi Fatima, kuma na san da zai ganki zai kaunace ki sosai zaki ji dadi, da ace mahaifiyarki zata aje abun da ke zuciyarta ta dubi maslaharki da kin yi farinciki sosai, kina da uba sunanshi Turhan"
Ta dafa shi, hakan ya farfado da shi daga guntun tunanin da yake.
"Ka ji"
Ya lumshe ya bude sannan ya daga taya matsa da ita saman jikinsa ya rumgume ta, ba dan ya ji abun da take tambayarsa ba sai dan tausayinta da ya kama shi. Kiran Emily be shigo wayarsa ba sai kusan Isha'i a lokacin da yayi alwala yana warwarar hannun rigarsa Fatima ta shigo masa da wayar da ya bari a falo, har dakin da yake ta mika masa.
Ya karba ya kara a kunne, for the first time sai ya ji nauyi fara yi mata sallama.
"Salam alaikum"
Ta masa sallamar sai yayi murmushi ba tare da ya amsa ba ya ce.
"Yau dai kina da nuna min hallayarki na kwarai ashe kin iya sallama"
"Na iya mana, ni da na zauna da musulmai kuma Hausawa"
"Kina lafiya Emily?"
Ya tambaya, sai ta lumshe ido hawaye na sauko mata, ta girgiza kai kamar yana gabanta tana jin kamar ta fada masa ba lafiya ba, amman tana gudun abun da zai je ya dawo.
"Anyways na kira wayarki a kashe, saboda hankali na be kwanta ba da yanayin da na barki, kuma da na ji wayar kashe na damu sai na saka Tasmia ta bincika min ke"
Da ya kai iya nan sai ya yanke maganar saboda yana son ya gano idan Tasmia gaskiya ta fada masa ko akasin haka. Emily ta hade kukanta ba tare data bude ido ba ta ce.
"Me tace maka?"
"Me kika ce tace min?"
"Ban fada mata komai ba, bata ma min maganarka ba"
"Okay, ta fada min ta same ki kin yi ado kina yi ma Vito girki, nace toh ina nan na damu ita kuma tana can tana girki ma wanda ba mijinta ba, Allah yasa dai kar na samu zunubi"
Ta cige baki hawaye na sauko mata kana ta bude ta sauke numfashi a hankali.
"Ado tun wanda ka tarar na yi ne, ban sake wani ado ba, ina Fatima tana tare da kai"
Ya kalli Fatima dake cin apple.
"Yeah, amman Aisha na tambaye ki mana"
"Uhmmm, ku haka addininku ya yardar ku zauna da mutane musamman namiji kuna tarayya ko daba muharraminku ba ne...? Mu a gurinmu hakan ba abu ne mai kyau ba"
"Ban taba tarayya da Vito ba, wani abu be taba shiga tsakaninmu ba, a tsawon zaman da muka yi, yana jiran sai na aminta da soyayyarsa ne, ni kuma zuciyarta ta kasa fahimtarsa, wannan abun yana wahalar da rayuwata yana jefani a matsala, ni ban taba mu'amala da kowa ba sai Khaleepa da Turhan, shi ma Turhan ya fada min kan kuskure ne, kuma bakar rana ta biyu a gurinsa bayan ranar da aka daura mana aure, yana daga cikin dalilin da ya saka nake son gina rayuwata ni kadai ina son na zama mai ikon kaina"
Jin cewar bata taba zina ba ya burge shi, haka kuma jin cewa Turhan ya kira ranar da ya aure da bakar rana a gurinsa ya saka shi kara dora ayar tambaya akan zamantakewar aurensu.
"Fahimta, I'm sorry for misunderstanding you"
"Dan Allah ka bar Fatima ta kwana a gurinka, gobe sai a kawota"
"Okay"
Ta bukataci hakan ne gudun kar ya zo kawo Fatima ya hadu da Vito ko kuma ya ga dukan da Vito yayi mata yace zai dauki mataki ya jefa kansa a matsala. Falo Fatima ta koma tana kallo, shi kuma ya tsaya a dakin yayi sallah, be dago daga sujudarsa ta karshe ba sai da yayi ma Emily addu'a, bayan ya gama ya sauko falon ya umarce tayi alwala ta yi sallah, ba musu ta tashi zuwa jnda ta yi alwalar magariba ta yi ta dawo falon ta dauki hijab din Kameela daya dauko mata a dazun ta saka ta fara sallah, shi kuma ya shiga Kitchen ya fara gyara tattasai da attarugu da albarba ya kunna gas ya dora nama akai, ya fara yanka vegetables, sai ga Fatima ta shigo Kitchen tana tambayar me yake yi.
"Jallof zan girka kina ci?"
"Ka iya girki?"
"Sosai ma"
Ita ta yi ta taya shi hira yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita.
"Kai kadai zaka ci?"
"Aa ni da ke"
"A plate daya"
"eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?"
Ta yi dariyar jindadi
"A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so"
Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta.
Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi.
"Meyasa kake watsa min yawu"
"Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?"
"Aa"
"Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?"
Ta taso daga kwance da take ta rumgume shi.
"Da nan nake zaune tare da momy da mun rika jindadi, kowa yana son ace yana da ba Baba, momy ta maka girma amman zamu iya zama yayanka mu duka biyu"
Yayi murmushi ya shafa bayanta a haka ta sake yin bachi sai ya kwantar da ita ya fito falon, ya dauki wayarsa ya kira Mama Baraka, sai dai bata daga kiran nasa ba har ya yanke, aje wayar yayi a tunaninsa ta yi bachi domin tara da rabi har ta gota, yana dauke hannunsa daga mazaunin wayar sai ga kiranta ya biyo baya, sai ya sake dauka ya amsa, tare da sallama ta amsa masa suka gaisa sannan ta tambaye shi.
"Aliyu me yake faruwa tsakaninka da matarka?"
"Mama Me ta fada muku"
"Bata fada mana komai ba, an yi anyi da ita ta ki ta yi magana ba, sai kuka da damuwa abinci ma bata iya ci, gaba daya ta fita hayyacinta"
Yayi shiru na dan lokaci tare da tunanin alfanu da kuma rashin sa da zai haifar idan har ya fadi dalilin da ya saka ya turata gida, ba dan Ummynsa ba da babu abun da zai hana ya fadawa kowa abun da ta yi masa ko dan ta shiga taitaiyinta ta hankalta.
"Babu komai Mama"
"Aa mu fa iyayene, babu komai zaka turo ta gida ko sakinta ka yi?"
"Aa"
"Toh me ke faruwa tsakaninku? Aliyu ita rayuwar aure sai da hakuri na san ka yi ne, amman ka kara, na san idan ba kai ba ne ba zaka iya zama da Kameela ba, sai dai bana son kana duba sherinta ka rika duba alherinta ko dan ku bawa marasa da kunya, kaga yanzu dawowar da ta yi nan iyayen sun nuna babu ruwansu da ita yan'uwa kuma sai dariya suke mata, dan Allah ina rokon alfarma Aliyu ba dan na isa ba, sai dan na san ka da biyayya da kawar da ido da kuma hakuri da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka zo ko kuma ka aiko daukar maka matarka ka bata hakuri ka bawa iyayenta, ku shirya tsakaninku"
Ya sauke ajiyar zuciya.
"Shikenan zan yi tunani Mama"
"Aa ba tunani nake son ka yi ba, idan ka tsaya tunani ai sai shedan ya samu damar baka wata gugurwar shawara, domin shi kullum burinsa ya lalata rayuwar aure, dan Allah ya shirya cikin weekend din nan ka zo ka dauki matarka, gobe friday zuwa assabar ko lahadi sai ka shigo ka koma, ka turo min number Mahaifiyarka na kira ita ma na bata hakuri"
"Aa ba sai kin kira ba, bata ma san abun da ya faru tsakaninmu ba"
"Tohm ai haka ake so, ana son ma'aurata su zama masu sirri, Allah ya hada kanku ya baka hakuri da wuyan dauka, kuma maganar nan ta tsaya daga ni sai kai dan Allah, domin Kameela da iyayenta ba su san na kira ba, ni ce kawai na damu da halin data shiga shiyasa na kiraka mu yi magana, number ka ma a boye nasa yara suka dauko min, ba tare da sanin Kameela ko iyayenta ba"
"Na gode Mama"
"Toh Allah ya maka albarka, kuma ka kara hakuri domin matarka tana kaunarka sosai"
"In Shaa Allahu"
"Na gode"
Ya sauke wayar, ya amsa mata ne kawai saboda yana jin nauyin ce mata aa ba zai iya ba, haka kuma yana tsoron matsalar da fadin gaskiyar abun da Kameela ta yi masa zai janyo, ita yake tausayi ba kansa ba, domin ya san tana son shi, kuma ya san irin gwagwarmayar da suka sha kamin aure, kana ya san idan har aka ji abun da ta yi abu ne mai wahala wani namiji ya sake aurenta, shi kansa ya san auren Kameela jarabawa ne a gurinsa ba dan baya kaunarta ba sai dan zafin kishinta da kuma halin da take kokarin jefashi kuma ta jefa kanta.
EMILY POV.
Bata farka ba sai karfe takwas na safe, saboda tunani da kuma dukan da Vito yayi mata be barta ta sami bachi da wuri ba, daker ta iya saukowa daga kan gado saboda tsamin da jikinta yayi ko'ina ciwo yake mata. Bathroom ta fara shiga ta wanke bakinta ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai saboda ta gasa jikin sannan ta fito daure da tawul, rass gabanta ya yanke ya fadi ganin Vito tsaye a dakin yana jiran fitowarta. Tsayawa ta yi cak a jikin kofar bata karasa fita ba kuma bata koma ciki ba sai kallonsa take.
"Good Morning"
Ya tako zuwa inda take sai ta yi baya baya zata koma ciki, ta bata fuska sosai alamar zata yi kuka.
"Tsorona kike ji? I'm so sorry i didn't mean to hurt you ke kika janyo, jiya ban yi bachi ba saboda tunanin abun da na yi miki"
Ya karasa ya rikota ya fito da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa.
"I'm sorry"
Sun dade a haka kamin ta dago daga jikinsa ta nufi kujera ta zauna.
"Jikinki da zafi zan kira Likita ya zo ya duba ki"
"Bana bukata"
"I'm sorry Emily am sorry"
Ya karasa kusa da ita sai ya zauna a kasa ya kama hannunta ya rike.
"I'm really sorry, zuciya ce ta rufe ni"
"Wannan ba shi ne karon farko ba"
"Na sani, kuma ba zai zama karon karshe ba matukar baki daina kula wasu mazan ba, kuma baki cire ranki akan addinin nan ba"
Ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata ta mika tsaye, short gown ta dauko ta saka ta daure kanta da ribbon tana kokarin juyowa ta ji shi bayanta tsaye.
"I'm sorry Emily I'm sorry, i didn't mean to hurt you"
Ya juyo da ita yana kallon fuskarta dake zubar da hawaye.
"But you already hurt me, baka da banbanci da Khaleefa shi ma dukana yake, Turhan ma ya dukene, kowanenku yana juyani ne son ransa, idan kuka gaji da ni sai ku watsar, ina ta fadawa hannun mutanenda babu komai a gabansu sai son zuciya, na tabbatar da ace ni kanwarka ce, ba zaka yarda wani yayi mata wannan dukan ba, jiya ban iya bachi da wuri ba saboda radadin dukan da ka yi min, takamarka kawai saboda ina karkashinka ne, saboda kana ganin ba ni da kowa, da ace ina da gata ba zaka min wannan dukan ba Vito"
Ta wuce shi ta fice daga dakin, zaunawa yayi a kujerar data tashi dazun ya dafe kansa, babu abun da ya tsana kamar ganin hawayen Emily, a yau da ace wani ne yayi mata abun da yayi ba zai kwana duniya ba, but still yana jin babu dadi meyasa ba shi da hakuri why yake da saurin hannu? Yana son Emily yana mutuwar sonta yana kishinta wannan ne abun ne ya ci shi da yaki ya gagara fin karfin zuciyarsa har gobe...
Tana fita dakin ta nufi downstairs, sai kuma ta fasa sauka ta dawo saman ta nufi dakin London ta shiga, saboda tana bukatar gurin da zata kebe ta tausayawa kanta.
Sai dai kuma shiga dakin ya dawo mata da tunanin danta da kewarsa, dakin yana nan yadda ya bar shi babu abun da aka cire ko aka sauya, sai datti da yayi domin Chidimma ta daina share dakin. Kwalliyar dakin ta fara kallo sannan ta sauke idonta gurin hotonsa ta karasa gurin gadon ta zauna a kasa ta dora kanta akan gadon tana hawaye.
Can kuma ta dago tana kallon study table dinsa dake gefe daya, ta tashi ta koma kan teburin ta zauna saman kujera tana duba takardun da yake zane da su da rubutu, wani gurin ya zana ta ya zana kansa da Vito da Fatima da Chidimma ya rubuta sunan kowa, ta kai hannu tana shafa zanen, ta bude wasu takardu ta dauko tana dubawa, wani gurin ya rubuta, na yi fushi wani gurin ya rubuta i hate Momy, wani gurin ya rubuta I'm sick har ta kai gurin da ya rubuta.
"Chidimma tace Momy bata so na, bata so na bata so na bata so na, tana son Fatima Fatima bata son London, Chidimma tace Momy bata son London, Momy bata son London Momy ta tsani London"
Tana karantawa hawaye na sauko mata kamar ruwa, ta girgiza kai da sauri.
"Ina son ka dana, ka fi soyuwa a raina fiye da Fatima, baka fahimce ni ba ne"
Ta kwala wani uban ihu cikin kuka, ta mike tsaye da fito dakin da gudu kamin ta sauka kasa Vito ya fito dakinta ya biyo bayanta Chidimma dake mopping ma ta tsaya tana kallon Emily dake saukowa tana kuka rike da takardun.
"Meyasa kika saka dana ya tsane ne? Me na miki? Me yasa kika tsane ni? Me na miki? Kin sa ɗana ya mutu da tunanin bana son shi, baki kalli lalurar da take tare da shi me yasa kika cusa wannan a kwakwalwarshi? Yanzu ta ina zan fada masa ina kaunarsa? Ta ina zan nuna masa kaunar da nake masa? Why Chidimma why? Shiyasa ya daina son na rabe shi na baya yarda da ni sai ke? Why Chidimma why?"
Kalaman Emily ba su daga mata hankali ba kamar kallon da Vito yake mata.
" Ki amsa me yasa kika yi?"
Ta girgiza kai jikinta na rawa numfashinta na gargada.
"Ba haka ba ne, wata kila be fahimta ba shiyasa yake rubuta wannan, amman ban fada masa cewar baki kaunarsa ba, ba gaskiya ba ne"
"Meyasa Matata tsone miki ido? Na sha fada miki ki daina fada min idan Emily ta yi wani abu, kamar jiya, ke kika fada min ta shirya ta shirya Fatima cikin abaya sun fita, kika sa na zo na mata duka da ya tsaya min a rai yanzu yana ci na, kuma na gargade ki ba tun yau ba akan ki cire idonki akan Emily, the more kika fada min laifinta the more zan tsane ki, me yasa kika shiga tsakaninta da London why? Answer me....!!!“
Da farko cikin natsuwa ya fara magana da mugun kallo, daga karshe kuma ya karasa da tsawar da ta saka Chidimma sakin fitsari...
Hmmmmmm, masu karatu wai ba ku ganin Aliyu yana wuce gona da iri ne?
Ina Team Vito? Ni fa iya wuya muna tare🥰🥺 wanda ya so ka taimaka a lokacin da baka da komai ai shi ne naka.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy