Showing 219001 words to 222000 words out of 249044 words
ba ba shi da haufi, baya ga haka kuma baya ra'ayin wani ya kasance da matarsa sai shi kadai.
Da mahaifinsa ya fahimci abun da zuciyarsa take muradi sai ya karbawa bukatarsa. Ya fahimcin hankalin dansa baya a tare da su a yanzu, domin an maido masa matarsa an shirya tsakaninsu ya fahimtar da ita kuma ta yi masa uzuri, amman tunaninsa fa hashensa kullum yana gurin wacan matar ne da be da tabbacin zata dawo gareshi.
Ya saka mahaifinsa a gaba ne, da neman yayi masa ruwa da tsaki saboda yana ganin idan mahaifinsa ya wuce masa gaba Emily zata samu, yadda yake gani za a bullo ma lamarin abu ne mai wahala Emily ta tsallake tarkonsa.
Kamin su bar kasar Sudan sai da mahaifinsa ya kira Alhaji Bello ya fada masa bukatarsa da kuma rakiyar da yake son yayi masa, Turhan ma da kansa ya sanar da Dr Adam yadda suka shirya komai, ya fada masa yayi hakan ne saboda neman yafiyar Emily wata kila idan yayi wannan zata yafe masa. Dr A-B ya ba shi goyon baya dari bisa dari kuma ya tabbatar masa da cewar tare da shi za'ayi tafiyar.
Sosai kaunar Emily ta kama Turhan kusan da ya ji labarin musuluntarta ta gurin Fatima yayi murna yayi farinciki sosai. Sati daya da yayi a garin sai yake jinsa kamar shekara, tunaninsa yana kan Emily ne, har ta kai idan ya kalli matarsa sai ayyana da ma ace Emily ce, ko kuma idan Emily ce ga yarsu ga ta farincikinsa ya cika. Idan kuwa zuciyar ta tuna masa Aliyu yana can yana kalla masa mata sai ya ji kamar ya hade zuciyar ya mutu saboda kishi da bakinciki. Babu daren da baya mafarkin kasancewa da Emily, idan ya zauna shi kadai shiru baya tunanin komai sai nata, idan ya fita aiki tana nan a ransa, wasan dokin da yake idan yana yi sai yayi ta ayyana yadda zai koya mata wasan idan ta kasance matarsa.
Be fadawa Mahaifinsa cewar ba da aure aka haifi Emily ba saboda baya son mahaifinsa ya yanke kudurinsa ko ya ki goya masa baya, ya fada masa mahaifinta Bature ne kuma ba a kasar yake ba, mahaifiyarta kuma tana auren wani yaron abokinsa wato Bulama Bello step father din Dr A-B, ya fada masa uba daya suke da Dr A-B, ya kuma fada masa a yanzu tana zaune idansu Aliyu ne, sun yi makirci sun zaunar da ita gidan saboda ya kar ta koma gurinsa.
"Za mu nema maka yafiyarta da kuma aurenta gurin Ahji Mudallab, ba zan yi zuwa biyu ba"
Da mahaifinsa ya fada masa haka ba karamin dadi ya ji ba, domin hakarsa ta cin ma ruwa daman abun da yake nema kenan
Shi ma mahaifinsa ya gama sallamawa da fahimtar irin son da dansa yake yi ma wata mace da ba jintsi da jinin larabawa ba.
Turhan kam yana ganin ta ko'ina an daure Aliyu da iyayensa kuma an saka Emily a tsakiya ba zata iya cewa a a ba. Ta waya yake labartawa Ammy komai idan kuma yana video call da yarsa sai ya fada mata yana dawowa zai je ya dauko Emily za su dawo su zauna guri daya.
Sarkin Sudan da kansa ya daga waya ya kira Mahaifin Aliyu ya sanar masa za su neman yafiyar Emily a gidansa, a ciki satin nan da zai shigo. Saboda ya kyautata musu ya aje uzurinsa ya sanar da Ummi cewar ta daga zancen komawarta Abuja a satin zuwa Next week saboda zai dawo Kaduna a satin, sai dai be yarda ya fada mata ko Aliyu cewar iyayen Turhan ne za su zo ba, yayi hakan ne saboda gujewa Ummi ko Aliyu su fadawa Emily ko su shirya wani abun da zai zama laifi a gurin Turhan. Dan haka ya zabi shiru da bakinsa ba tare da ya fada musu dalilin dawowarsa ba.
Mahaifin Aliyu ya sauka Kaduna on Saturday, Sarkin Sudan ya sauka Abuja on Saturday tare da Turhan da yan rakiyarsa masu fassara masa daga hausa ko turanci zuwa larabci, a gidan abokinsa Bulama, sun samu kyakkyawar tarba a daya daga cikin manyan masaukan baki da Bulama yake da su, abinci aka kawo musu kala kala tun daga kan na Nigeria har zuwa na kasar Sudan. The following day suka suka shiga private jet na Alhaji Bulama zuwa garin kaduna, Dr A-B be fadawa Emily za su zo ba, duk kuwa da kasancewar tana kiransa akai kai da sabon layinta da Mama Baraka ta bata. Sai yayi tunanin ko Mahaifin Aliyu ya sanar musu da zuwan, sai dai duk da haka be yi mata maganar ba saboda yana son ta ganshi as surprise kamar wacan karon.
Even Mama Baraka bata san wainar da ake toyawa ba. Domin mijinta baya magana da ita, balle ya labarta mata cewar mai gidansa Alhaji Bulama zai sauka garin a ranar ta Lahadi ba, shi ne mutum na farko da ya fara isa filin jirgin ya tarbe bakin da aka sanar masa da zuwansu amman ba a fada masa dalili ba. Alhaji Bulama ya sanar masa ne saboda shi ne babban yaronsa kuma indai har za su sauka a garin Kaduna babu wanda yake tarbarsa kamar shi, balle kuma wannan da suke ganin ya alakantu da shi.
Ya tarbosu tare da yi ma maigidansa tayin sauka a a gidansa ko masaukin baki, amman ba su amsa gayyatar ba domin uzurin da ya kawo su dabam.
Hankali be tashi ba sai da ya ji ana zancen makiyinsa kuma surukinsa, suka dunguma gaba daya suka dauki hanyar gidan. Ba zai iya zare kansa yace ba zai je ba, saboda yana tare da mai gidansa, kuma siyasa ta gaji haka idan aka hadu a rumgume juna ana wasa da dariya kamar babu komai. Ba su fada dalilin tafiya gidan ba sai da suka kusa isa, be yi mamaki ba domin ya hararo haka ganin Turhan a karon farko da Alhaji Bulama ya gabatar masa da shi har yana fadar ga surukinka.
EMILY POV.
Tun a daren Assabar Daddy ya sanar da matarsa cewa yana da baki gobe ta shirya abinci mai kyau da wuri, duk yadda Ummi ta so ta ji ko su waye be bata dama ba sai kawai ya fake da cewar abokan siyasa ne. Sannan ya bukaci ta fadawa Aliyu kar ya shigo gidan gobe sai idan ya kira shi.
"Bakin da za su zo suna da alaka da shi ne?"
"Aa kin san ita harkar siyasa akan boye wasu abubuwan saboda gaba, shi Aliyu ba mutum ne mai son siyasa ba, to be kamata ace kowa ya san da shi ba, hakan kan iya haifar da matsala wani lokacin a cutar maka da naka"
"Haka ne kuma, zan fada masa Allah ya kaimu lafiya."
"Ameen Uwargida kuma Amarya"
Daddy ya fada yana murmushin manyan mutane.
"Ka ji da shi, idan ka tashi auro min yar yarinya dadin bakinka ba zai hana ba ai"
"Ni yanzu ke ma ba hakuri kike da ni ba? Ina na ga lokacin kara miki wani aure? Wahalar ma ai sai ta yi min yawa"
"Uhmm"
Haka dai suka cigaba da hirarsu sama sama har kusan tara na dare, shigowar sirri Daddy yayi amman haka be hana makusantansa da masu saka idon unguwa su fahimci ya sauka garin ba domin dan siyasa ba a boye yake ba, A ranar be kwana ba da ya sallami kowa da abun da ya kamata. Da Aliyu ya zo yi ma Daddy sallama Ummi take fada masa gobe ya zauna ya huta kar ya shigo gidan sai an kira shi domin ba su san saukar yaushe baki za su yi da safe ko rana ko yamma. To him it's awkward and something new, why dan za ayi baki za ace kar ya shigo gidan? Be musa wa Ummi ba domin ta ba shi hujjojinta kamar yadda Daddy ya bata.
Shi dai ya amsa musu ne kawai amman ba dan ya gamsu ba, da ya zafafa tunani sai ya fahimci Turhan ne zai ko ko mahaifinsa, a take jikinsa yayi sanyi wani bangare na zuciyarsa ya raya masa titsiye Emily za su yi, su cilasta mata abun da ba shi take da niya ba, wannan bangaren da ya raya masa haka shi ya sake raya masa kowa baya wuce kaddararsa kuma be zama lallai idan ta koma gidan Turhan ya sake cutar da ita ba a yanzu domin ga dukan alama yayi nadama kuma ya fahimci tana da tsada. Haka ya fito bangaren na mahaifinsa yana ta sake sake har ya nufi motarsa sai kuma ya juyo ya sake turo kofar falon ta Ummi ya shiga.
Nafeesa da Emily ne zaune a falon sai masu aikin Ummi dake zaune kasa. Tun da ya shigo Emily take kallonsa har ya nufi dinning ya dauki cup ya fara auna madara yana zubawa, ba dan ya sha ba sai dan ya saci kallon Emily din, jin yake yana kewarta fiye da ko yaushe, ya san ba zata iya kaunarta a zuciyarta amman idan aka mata dole ba lallai ta tsallake wannan ba, ya gama satar kallon nata sai ya maida madarar a mazubinta ya fice yana bata wani silent look tana karba cike da kauna.
Washe gari da wuri Ummi ta hau aiki tare da masu tayata, innocent her bata fahimci komai ba, har suka kammala hada komai ta shiga ta shirya kowa ya shirya. Emily na ta bude ido ta ga Aliyu ya shigo gidan da safe bata ga ya zo ba, bayan su gama aikin ta ji ba zata iya hakura ba sai ta aika masa da sakon kar ta kwana.
"Yau lafiya baka shigo ba?"
In few seconds ya maida mata amsa.
"Wani uzurin ne ya rike ni?"
"Akwai uzurin da ya fi ganina muhimmanci ne? Wuni yau zai min babu dadi"
"Ke kenan, balle kuma ni da nake jin awanin da nake a gidan a kullum suna min kadan, Ayusher i miss you more life itself, zan zo soon"
Ta aika amsa da sakon Heart emoji ya maido mata smiley face emoji.
After like one hours suka ji shigowar motoci a gidan. Emily tana dakinta tana lasa waya, Ummi kuma ta fita tare da Daddy cikin lullubinta domin tarbon bakin da yace mata za su zo. Ganin Turhan da mahaifinsa ya matukar ba ma Ummi mamaki ga kuma Mahaifin kameela a tare da su, sai dai bata yarda ta nuna ba, aka shigo da su babban Falon Daddy ana musu sannu da zuwa. Masu aiki suka shiga jera musu abun da aka shirya musu.
Tambayayi suka cika cikin Ummi sai a yanzu ta fahimci dalilin Daddy na hana Aliyu zuwa gidan a yau. Alhaji Bulama da Dr A-B ne kadai sukq sha ruwan da aka jera, Turhan da mahaifinsa ba su taba komai ba daman sarakuna ba ko'ina suke ci ko sha abu ba, balle kuma Mahaifin Kameela, da yaken dole na kawai yake.
Turhan na zaune shiru zuciyarsa na raya masa nasara da rashinta.
"ina ganin kamata yayi mu yi abun da ya kawo mu? Domin ni yau zan bar garin nan, kasan yadda abubuwan suke ba koda yaushe muke samu lokaci ba, amman abun da yake da muhimmanci kamar na abokina kuma abokin kasuwancina dole na bashi time dina"
"Haka ne ranka ya dade, da na so ku fara cin abinci, amman bari a kira yarinyar"
Ummi ta yunkura zata tashi Daddy ya hana ta, dugun kar ta tafi ta yi ma ɗanta kamfai, ya daga wayarsa ya kira Nafeesa ya ce ta shigo masa da Emily.
Emily na zaune dakinta Nafeesa ta shigo ta ce ta saka Hijab dinta ta fito Daddy yana nemanta.
"Lafiya?"
Emily ta tambaya domin tun da ya zo ta je ta gaishe shi bata sake shiga bangaren ba.
"Wallahi ban sani ba, amman dai na san lafiya kam In Shaa Allahu"
Emily ta dauki bakin mayafin abayar dake jikinta ta rufe kanta ta saka talkaminta sannan suka fita tare da Nafeesa, suna tafe gabanta na faduwa musamman da suka doshi falon, tsayawa ta yi cak cike da faragaba kamar tace ba zata shiga ba, ganin haka ya saka Nafeesa ta kama hannunta suka shiga cikin falo, Emily kanta na kasa har ta zauna inda Daddy ya nuna ma Nafeesa.
Sannan yayi ma Nafeesa alama da ta tashi ta fita, Emily ta dan dago kai kadan ta kalli mutanen da suka falon gabanta ya buga da karfi, ba dan arba da Turhan kadai ba har dan ganin mahaifinsa da kuma Alhaji Bulama ga kuma mahaifin Kameela a falon.
Daddy ya gabatar mata da kowa daya bayan daya, sannan ya fada mata dalilin zuwansu neman gafararta ne na abubuwan da suka faru.
"Dukanmu nan har ni mu zauna ne saboda neman yafiyarki ga dan mu, yayi kuskure mun sani kuma yayi nadama shiyasa takanas ta Kano ya dauko mahaifinsa da abokan mahaifansa da ni kaina da yake jin zan iya shige masa gaba mu roka masa yafiyarki, kuma muna fatan za ki dube mu da hurhurar dake kan mu ki yafe masa"
Emily ta yi shiru na tsawon lokaci.
"Ki bude baki ki yi magana muna saurarenki, kuma ba wai muna cilasta ki ba ne, kuma ba muna son ki ga kamar mun tsareki ba ne, aa yafiyace muke nema ga Turhan kowa yana kuskure abu ne da kika sani, kowa ya sani"
Cewar Alhaji Bulama. Emily ta dago kai a hankali ta fara magana ba tare da ta kalli kowa ba.
"Na yi tunanin mun wuce wannan gabar, tun kamin na yi magana da shi, na yi da Ammy kuma na fada na yafe masa, gaba daya ni na zubar da abun da ya faru, yanzu ai wata rayuwa muke yi bata baya ba, kuma Turhan uba ne ga Fatima ya cancanci girmamawa ta da yafiya, har a gurin Allah ni na yafe masa"
"Maa Shaa Allah"
Haka kowa ke fadi fuska a sake cike da far'a. Mai Martaba da kansa ya soma magana ana fassara mata.
"Na jidadi da jin wannan maganar, kuma na yaba da hankalin ki da tarbiyarki, a rayuwa ana son mutum ya zama mai yafiya, kuma kin nuna mana ke mai hankali ce ba ki watsa mana kasa a ido ba, mun gode sosai, akwai tsaraba da muka so miki da ita fatan ba zaki raina ba"
Mai fassarar na rufe baki aka shigo da manyan akwatuna biyu aka aje a gefen da Emily take zaune.
"Sai dai kuma ba yafiya kawai na zo nemawa ɗana ba, ko da yake tafiyar daya ce ai, amman dai haka ba zai hana mu fada ba, Emily muna rokon alfarma, ki duba yadda muka zo nan dukanmu kuma da irin yadda yayi nadama yake ta kai da kawo akanki, kuma ki duba yarki da zuri'ar da za ku samu nan gaba, indai har da gaske kin yafe masa kuma kin manta komai toh ki amince ki koma karkashin kulawarsa da igiyar aurensa, kusan shi ne makasudi zuwanmu a nan"
Ummi ta ji abun kamar daga sama, amman babu damar magana saboda Daddy yana gurin zaune, dan haka ta mike tsaye kawai ta fice daga falon. Daddy be wani yi mamaki sosai ba saboda ya hango hakan tun farkon zuwansu gidan. Emily ta kalli Alhaji Bulama wanda shi ne yayi maganar sai ta ji nauyi ba shi amsa.
Dr A-B ya ciro daurin dollars a aljihunsa ya aje kasa.
"Zan fi kowa farinciki idan ta amince, kuma ace ni na biya sadakin kanwar nan tawa"
Emily ta sake daga kai cikin tsananin damuwa.
"Dan Allah ku gafarce ni, kuma ku fahimce ni, bana nufin bata ran kowa, bana nufin zubar da kimar kowa, na yafewa Turhan amman hakan baya nufin na yarda na aure shi, Wallahi ba zan iya zaman aure da shi ba, akwai wanda na so"
"Wake kike so?"
Alhaji Bulama ya tambaya, sai ta yi shiru.
"Ki bude baki ki amsa mana, ko a addinin musulunci bazawara amsawarta ake amfani ba shirunta ba, shiru na budurwa ne, haka Annabi S. A. W ya fada"
Daddy ya ji kamar yace kar ta fada.
"Aliyu..."
Ta furta a hankali, falon yayi tsit na tsawon lokaci, kamar babu wani abu mai rai a ciki, tsabar jin nauyi Daddy ya ji kamar kasa ta tsage ya shige ciki. Turhan ya mike tsaye ya fice falon ba tare da ya kalli inda Emily take ba zaune ba. Sarkin Sudan ya tsare ta da ido.
"Kin san mutanen da suke zaune a gabanki kuwa yarinya?"
Emily ta fashe da kuka ita kanta bata nufin watsa musu kasa a ido.
"Ku gafarce ni dan Allah? Ku fahimce ni ku taimaki rayuwata, ku bar ni ni ma na yaki iskar yanci"
Sarkin ya mike tsaye bayan an fassara masa abun da ta fada ya fice tare masu rakiyarsa.
"Amman baki yi kyauta ba, kuma ba mu tsammaci haka ba"
Cewar Alhaji Bulama sannan ya mike tsaye ya fice, tare da rakiyar Mahaifin Kameela. Dr A-B ya kalli Emily dake ta kuka ya sakar mata murmushi.
"Aliyu kike so?"
Ta daga mishi kai.
"Share hawayenki na miki alkawari ba zan bar garin nan ba sai an daura aurenku, ni ma kamar uba ne a gurinki ai zan iya bada aurenki, na nufin biyan sadaki ba zan fasa ba"
Ya juya ya kalli Daddy ya tura masa kudin.
"A rike wannan a matsayin sadakin Emily, a sanarwa duk wanda ya kamata a sanarwa, zan tafi na dawo daga can zan sanar da Madam Baraka, anjima kadan zan dawo za a daura aurenta da wanda take so, ni dai burina ta kasance cikin farin ciki, amman a tabbatar da shi ma yana sonta gudun abun da zai je ya dawo kar ya cutar mana da ita"
Ya tashi shi ma ya fice, Daddy ma mikewa yayi tsaye ba farinciki ba bakinciki domin shi ma be ga dalilin da zai saka ayi ma Emily dole ga abun da bata so ba. Emily kadai aka bari a falon tana rusar kuka, bata sani ba ko shi ma Aliyun ya juya mata bayan ta watsa ma manyan mutane kasa a ido. Ummi ce ta