Showing 129001 words to 132000 words out of 249044 words

Chapter 44 - Abokin Rayuwa By Khadeeja Candy

03 Dec 2025

14938

da na san laifin da na yi aikata a agaresu ba. Ga kuma lailayin da nake ta yi a boye.
Muna cikin wannan halin wata rana sai fadar sarkin ta yi babban bako. Wani babban mai kudi kuma dan kasuwa ya sauka masarautar tare da rakiyar manyan mutane daga Nigeria. Aka saka mu yi wanka muka fito tsaba saboda zamu tarbi bakon tare da tawagarsa. Sai kuma aka yi dace Turhan da matarsa sun tsallaka sun bar kasar zuwa gurin da be fada min ba, na fahimcin hakan ne ta hanyar rufe wani bangare da aka yi a part dinsu aka hanani shiga na gyara kamar yadda nake, kuma aikin da ake yawan sakani ya ragu ba ma ni kadai ba har da sauran bayin.
Wasu kuma na daina ganinsu wata kila har da su aka yi tafiyar.

Matar Sarkin wanda take zaman step mother din Turhan ta tarbi matar dan kasuwar da ba zan iya fadar dalilinsa na zuwa garin a lokacin ba. Ni da mutum uku aka zaba mu yi Serving din matar dake wanye da abaya kanta da wings ta nada gyalen abayar a wuyanta ga bakin gilashi, da alama dai ba musulma bace shiyasa ta kasa rufe kanta. Kusan shi ne karo na farko da na bar garen Turhan zuwa wani bangare na gidan, wata kila babu wata adatattun bayi ne a lokacin wata kila kuma Allah yayi nufin kubutar da ni ne, shiyasa abun da duk ya faru ya faru.
Muna jera abincin a madaidaicin falon da aka ware mata ina satar kallonta zuciya nata yi min sake sake, yadda zan samawa kaina mafita, domin tun da muka shigo naji tana waya da yaren igbo. Sai da muka gama jera abincin tsab sannan na kalli matar cikin karfin hali da nemawa kai masifa na soma mata magana da yaren na Igbo.

"Dan Allah ina neman taimakonki, na ga ke ma igbo ce yar'uwata dan Allah ki taimaka min"

Sauran bayin da muke tare da su suka kalleni kamar a firgice sai dayar ta fice da sauri. Matar ta kalleni tana mamaki ta ba ni amsa da yaren na Igbo.

"Kina jin igbo ne? Daga ina kike?"

"Daga Nigeria, ki taimaka ki maida ni gida dan Allah, ni yar kabilar igbo ce, daga Lagos na zo aiki gurin wata mata a kaduna sai ta hada baki da wani suka siyar da ni a matsayin baiwa a gurin dan sarkin garin nan, ina zaune a nan ne a matsayin kurma wahala nake sha sosai a nan, gashi na baro ɗana kuma ba shi da lafiya, yanzu kuma idan baki taimaka min ba kashe ni za su yi saboda sun ji na yi magana ba su taba jin na yi magana ba"

Ina maganar da yaren na Igbo ina kuka.

"Amman baki yi kama da mutanen Nigeria ba"

"Wallahi daga Nijeriya nake, a gidan marayu na tashi ban san kowa na wa ba, idan mum tafi zan kai ki har gurin domin ki tabbatar dan Allah ki ceto rayuwata"

Na yi mata karyar an siyar da ni ne domin ba lallai ta yarda ba idan na fada mata dan sarkin garin ne ya auro ni ya mayar da ni haka. Daya daga cikin manyan hidiman bangaren Turhan ne ta shigo ta kama hannuna zata fice sai na cigaba da rokon matar.

"Na yi kasada na jefa kaina a matsala na yi magana idan baki taimake ni ba, shi kenan na rasa rayuwata kuma ɗana ya rasa ni, ke fa uwa ce ki taimake ni dan Allah"

Bata ce min komai ba, a lokacin ne na gane na yi kuskure na jefa kaina a babbar matsala domin ban samu biyan bukata ba. Waje aka fitar da ni can bangaren Turhan aka bar ni tsaye a rana a lokacin har na sadakar na san hadimar zata min hukuncinta ne kuma idan Turhan ya dawo shi ma yayi min na shi. Tsawon awa uku na yi tsaye a ranar kamin hadimar da kanta ta sake zuwa ta kama hannuna muka koma bangaren na Sarkin da sai a lokacin na taba ganinsa ido da ido a cikin fadarsa.
Matar ta nuna ni tana murmushi tana fadar nice da yaren turanci, mai fassarawa sarkin yayi Larabci sai sarki ya daga kai da hannunsa kadan wani na kusa da shi yayi magana sai aka fassara ma matar a nan ni ma na ji yana fadar.

"Sarki yace ya baki ita kyauta"

Matar ta yi godiya sosai sai aka fitar da ni waje, a nan sai da suka dade cikin sannan suka fito fadawan sarkin suka yi ma mutumen rakiya tare da matarsa ni kuma na shiga a tawagar masu rakiyar dan kasuwar a wata mota ta dabam. Hankali be kwanta ba sai da muka bar fadar da muka isa filin jirgi na yi zaton za'ayi mana irin na farko ne, ashe shi saboda isa da jirginsa yake yawo, sai dai hakan be hana a tantance mutanen da suke tare da shi ba, ni kuma bi ta wata hanyar dabam da ni bata hanyar da kowa yake bi ba, sai da aka isa gurin jirgin aka fito da ni daga motar na shiga aka zaunar da ni can baya nesa da mutane. A lokacin ne abubuwa suka fara yi min gizo ina ganinsu kamar mafarki.

Tun da muka tashi ba mu sauka ko'ina ba sai Abuja Nigeria. Da muka sauka jirgin ne matar tasa aka matso da ni kusa da ita ta gargade ni da halshen igbo.

"Ina fatan ba karya kike min ba, domin idan ya zama tsabanin abun da kika fada min toh zaki hadu da mummunan hukunci kuma zan saka a nemoki a ko'ina kika a kasar nan"

Na ce mata na amince, suka shiga motar alfarma mu kuma aka saka ni a wata motar, ina ta kallon gari da titunan Abuja da tunanin dan yancin da na samu har muka isa gidan mijin matar mai kama da wata babbar fadar Sarki, mutanen da suka tarbeta ita da mijinta ma abun kallo ne, a nan na kara gane kudi suna da muhimmanci sosai a rayuwar dan'adan. Da muka sauka gidan sai ta hannata ni a hannun wata mata yar Kaduna tace mata wai ina da zan je na dauko ɗana tana son kar a barni na tafi ni kadai na tafi tare da rakiyar wasu saboda tana son ta gano gaskiya ta, ni dai an kira ni kawai aka nuna min matar da za mu tafi tare, ta hanyar wayar da matar take da yaren yarbanci, na fahimci kudin wacan matar da ta ceto ni wanda ko sunanta ban sani ba. Komai aka bani kasa ci na yi ina ta zumudin ganin ɗana ga kuma tsoro ya cika zuciya gani nake kamar Turhan zai aiko a tafi da ni ne. Hankali be kwanta ba sai da muka bar garin Abuja tare da matar da mijinta da nake kyautata zaton dan siyasa ne.

Guri daya na zauna da matar, da alama ticket din da aka saya min na kusa da ita ne. A nan ta gabatar min da kanta ta fada min sunananta Barakat amman yaranta suna kiranta da Mama Barakat ta fada min ita bayarabiya ce, sannan ta tambayi labarina, ita kan ban boye mata komai ba na fada mata labarina tun daga tashina zuwa auren Khaleepa da kuma Turhan, gaba daya sai ta sauya ta rika kallona har sai da na tsorota, har muka isa Kaduna hawaye ke cika mata ido tana sharewa. Mun sauka Airport din idanuwa a zare kamar wata marar hankali ga rama na yi gaba daya ba ni da natsuwa. Mota daya aka zo daukarmu na shiga gaba ita da mijinta suka shiga baya, duk maganar da mijin yake bata amsawa har ya tambaya lafiya? Tace babu komai. Mun sauka gidanta ba laifi gida ne mai kyau amman ko kadan be kamo gidan wacan matar ta Abuja ba, kuma ita wannan da alama tana da abokiyar zama domin gidan bangare biyu ne, sai da muka fara shiga bangaren na farko ta shiga ita da mijin sai ta fito ita kadai ta shiga motar aka karasa da mu bangarenta.

Na sauko motar ina jin kamar na yi tsuntsuwa na gan ni gaban ɗana, haka dai na daure muka shiga ciki, ta nuna min dakin da zan zauna sannan ta haura sama har lokacin hawaye take hawan ma tana yi tana waigena har ta haura stairs din. Ina ganin ta shige na juya ya saci kafa na fice daga bangaren, da kaina na gate din gidan na fice, tafiya kadan na tari abun hawa na hau na fada masa ya kai ni cocin da take kusa a nan garin Kaduna, babu wata daguwar tafiya sai gamu gaban cocin, na gaishe da mai gadin na fada masa ina tafe da matsala ne amman ina son ya bani kudi na sallami mai achaba tukuna babu musu ya biya mai babur din, sannan ya shiga da ni ciki a tunani idan na je ma Ammy kai tsaye ba zata ba ni ɗana ba dan haka na zabi neman taimakon mutanen cocin bayan na fada musu ina ra'ayin komawa alnahin addinina na Christianity.

Sai suka ba ni shawara na fara tafiya dauko yaron har sai idan ta hana tukuna za su shigo ciki, na ba su addireshin gidanta sannan na cire takardar na rubutawa Ammy martanin karyar da ta yi min cewar danta na kirki ne ya banbanta da sauran, domin na san ba lallai na samu tsayawa na fada mata baki da baki ba, amman idan na bata wasikar zata karanta. Su suka ba ni kudin abun hawa na hau achaba na isa unguwar a lokacin ne tsoro ya yaye min saboda ina son ganin ɗana ta kowane irin hadi, da Allah yayi nufin ba ni nasara ina buga gate din mai gadi ya bude sai da ya dade yana kallona sannan ya gane ni, ya bar ni na shiga ciki na samu falon babu kowa sai ɗana shi kadai yana kallon Cartoon, na karasa da zafin nama na dauke ɗana na aje mata takarda a gurin da na dauke shi na fito yana ihu domin shi ma be gane ni ba, mai gadin ya tsaya tambayar ina zan je da yaro na kai masa mugun halbi a gurin da ya fi komai muhimmanci a jikinsa, ba shiri yaja baya na bude gate din na fice da gudu kai kace sato yaron na yi.

Ina tafe ina waije ko za'a biya ni amman ban ga sawun kowa ba sai da na samu Achaba na hau sannan Ammy ta biyo ni da motarta tana cewa na tsaya na cewa mai Achaba kar ya tsaya, be tsaya ba sai da muka isa cocin na sauka da guduna na tsaya layin mutanen da cocin ke rabawa tallafi. Ammy ta dade tana kallona har sai da mai gadin ya bude min na shige.





TIRKASHI....!!!

A tunaninku tsakanin Auren Khaleepa da Turhan a ina Emily ta fi shan wahala? Waya ya fi gallaza mata?

Team Turhan kuna da katon aiki a gabanku😢 indai kuna son Emily da Turhan sai kun tanadi makaman sallama 🤗





_______________________

Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[6/26, 9:29 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL



🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*


*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️


Page 4️⃣1️⃣


Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika ɗana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne.

Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni.

Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana.

Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da ɗana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada.

Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da ɗana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar.

Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa ɗana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni.

Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login